Showing 54001 words to 57000 words out of 180592 words

Chapter 19 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1146

din Small Mum din tasa snn yayi withdraw din dubu hamsin, kamar ance ya waiga yaga motar sojoji na kokarin shan cornern gun bank din, da sauri ya koma ya labe jikin Atm din, ta gefen ido yake kallon motan gabansa yayi mugun faduwa ganin abokin Abbansa da ya fito daga gaban motar, sojoji hudu ma suka sauka daga baya, kamar kiftawan ido ya taho a 160 ya shige cikin mota yayi wani reverse bae damu da harbin da suka fara ba, ko kallon titi bai yi ba ko mota na xuwa ya hau titin ya ja motar a guje, Samantha da duk ta gama rikicewa ta dinga kwala ihu a cikin motor, ta madubi ya ga sojojin sun biyo sa a tasu motar da gudu, ya yo waje da ido yace "Kan bala'i" sae ka rantse tashi sama xae yi tsabar yanda yake gudu don ma titin bbu wasu motoci, samantha dake ta rusa kuka sae cewa take don Allah doctor ka tsaya, don Allah ka tsaya, Bai ko kalleta ba bare ya san me take cewa, hankalinsa ya gama tashi ganin sun kusa tadda su a lokacin kuma suna wajajen court road, bai damu da traffic da ya nuna masa green ba ya wani sha kwana da gudu har ya kusa karo da wata mota ya kauce mata ya ci gaba da gudunsa, traffic din nan ne ya taimaka suka samu distance tsakaninsa da soldiers din, sosai ya ga karfin halin samantha don yasan da wata ce da tuni ta suma, har ya hau titin unguwa Uku bai sassauta gudun da yake ba, a can baya sosai yake hango motar soldiers din, bai son ya shiga wani layi su tadda traffic shi yasa ya gwammace yayi ta gudu a express, hankalinsa ya tashi ganin man motan yayi kasa sosai, yana fara fita outskirt din kano yaga da nisa fa sosai tsakaninsu ya ja ya tsaya ya cire makullin motar ya fito da sauri, har lkcn kudin da yayi withdraw da atm card na aljihunsa, ya xaga ya bude inda take ya fito da ita, wani hanya kamar gona ya ja ta suka bi da gudu, daji ya dinga gani sosai a gaba amma hakan bae sa ya dakata ba, ita ko sai kuka take tana cewa "Baxan iya ba Doctor ka tsaya plss" a haka ya ja ta suka shiga dajin, bai damu da thorns din ciki da dogayen ciyayi ba ga uban duhu suka dinga ratsawa a haka, tafiya sosai suka yi a ciki ya ga kamar numfashinta na neman daukewa tsabar gajiya don jan ta kawae yake, rikota yayi da sauri ya nemi karkashin wani bishiya ya xaunar da ita yana kallonta bnda kyallin idonta bbu wani haske da yake gani a dajin, ta rike duk hannunsa biyu da kyar tace "Ruwa xan sha doctor!" Maida numfashi ya dinga yi yana kallonta, can ya runtse ido ya dinga maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un a xuciyarsa, bude idon yyi ya dafe kansa, ta xame hannunta daga nasa ta fashe da kuka, mikewa yayi yana dube duben inda xai samo mata ruwa yaji ya yi kick din abu, da sauri ya duk'a yana laluba meye wnn yaga kettle ne, da ruwa amma ba da yawa ba a ciki, dagawa yayi duk da bai san ruwan meye ba ya kai baki ya sha yaji dai ruwa ne sai dai da jin sa a baki kasan ba wani mai kyau bane, ya hadiya da kyar snn ya kai mata baki, karba tayi ta sha gaba daya, ya ajiye butan, ta rike hannunsa gam cikin rawan Murya tace "Am afraid doctor, tsoro nake ji" xaunawa yyi gefenta ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Don't be, am here to protect you, am with you" shiru tayi tayi lamo a jikinsa wanda hakan yasa ya dinga jin bugun xuciyarta, sun kusan minti talatin a haka taji ya kankameta, ta d'ago da sauri, taga idonsa a runtse, a hankali ya bude yana kallon kasa murya can kasa taji yace "Ant, i think it's an ant" kalle kallen kasan ita ma take, xaro ido tayi tayi wani uban ihu da sai da ko ina ya amsa, sai a snn ya ga me ta gani, wato kunama shi ba babba ba shi ba karami ba, ya toshe bakinta ya sa kafa yayi smashing dinsa, ko ina na jikinta rawa yake ta dinga cewa it's a scorpion, ya kai bakinsa kunnenta yace "Shhhh na fa kashe shi..." Jin baxata yi shiru ba ya lumshe ido ya rungumeta gam, tayi lamo jikinsa, a hankali ya xame dankwalin kanta ya daura a gun da kunaman ya harbesa, ba a dau lkci ba bacci ya dauketa.

*Haske writers assoasso*=???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

29.....

Daren ranan Abuturrab bai rintsa ba, har asuba yana rungume da ita, gari na fara haske ya kare ma dajin kallo, sai yaga ashe gona ce gun gaba daya, bishiyoyin mangoes da lemo ne yasa gun ya xama kamar daji da daddare, ya kalli wani tabarma dake can nesa da su a shimfide da wani sanda, da alamar dae mutane na xuwa gun, butoci har biyu ya gani bayan wanda ya samu ruwa a ciki jiya, kwance dankwalinta dake daure kafarsa yayi ya shimfida nan kasa snn ya kwantar da ita a hankali ya mike, wani mugun ciwon kai ya dinga ji ya taka a hankali har ya isa inda butan yake ya ga cike yake da ruwa ya dauka ya xaga ya daura alwala snn ya dawo, ya kalli gabas ya tada sllh, bai idar ba samantha ta farka, mikewa xaune tayi da sauri tana kare ma gun kallo, a hankali ta mike ta karasa gun butan da ya ajiye ta dauka, kallonta kawae yake bayan ya idar, ta juyo ya sakar mata murmushi cikin sanyin murya tace "I want to ease my self" yace "In raka ki?" Da sauri ta girgixa masa kai yana murmushi yace "Ohk" ya nuna mata inda xata tafi, ta juya ta wuce, ko da ta dawo bata gansa ba, ta fara kalle kalle da manyan idonta, muryarta na rawa tace "Doctorrr" tim taji fadowar mango a sama, ta koma baya a tsorace tana kallon sama ta gansa samar bishiyar yana tsinkar nunannun mangoes, ya kashe mata ido yace "Breakfast...." Daga haka ya ci gaba da tsinkar mangoes din masu kyau har ya tsinko fiye da ashirin, ji tayi ya diro kasa, ya karasa ya dauko dankwalinta ya dawo ya durkusa ya kwashesu, ta karasa inda yake ta durkusa gabansa a hankali ta shiga taya sa kwashewa, ya sakar mata murmushi yace "Bari toh in kara plucking din pawpaw ae kina so" bata ce komai ba ya mike ya isa inda sanda ke ajiye ya tafi gun bishiyoyin gwandan, can ya koma baya ita dae kallonsa kawae take, taku daya biyu yayi ya buga uban tsalle ya doki ripe pawpaw guda daya da sandar hannunsa ya fado, murmushi tayi ta dauke kanta ya dawo rike da pawpaw din yana murmushi ya ajiye mata, xaunawa yayi yace "Tunda bbu ruwa haka xa mu sha mangoes din..." Daga haka ya dau mango daya ya kai baki, dauka ita ma tayi ta kai baki a hankali, biyu kawae ta sha tace ta koshi, yace "Efizzy xa ki min" murmushi tayi ta girgixa kai kawai, duk yanda yayi da ita tasha kin sha tayi wai ta koshi, pawpaw din ma shi kadae ya sha kayansa wai bata sha, yana gamawa yace "We will leave yanxu...." Mikewa yayi ya dau sauran mangoes din da sanda yana rike da hannunta suka fara tafiya can gaba, da sandar ya dinga clearing masu daji don duk a tsorace take duk da kana ganin hanyar ma kasan ana bi sae dai ba sosai ba, tafiya kawae suke har kusan karfe tara ganin ta gaji sosai ya langwabar da kai yace "Ko in goya ki baby" kamar xata yi kuka tace "Doctor wae ina xa mu...." Yace "In da Allah ya kai mu" bata kuma cewa komai ba suna ta tafiya ga uban rana me xafin gaske har sha daya tayi, ta durkusa tana haki tace "Wayyo doctor i can't go futher am very thirsty" durkusawa shi ma yayi cike da tausayinta, ta fada kansa hawaye cike idonta tace "Na gaji, yunwa nake ji" ya rungume ta yace "Kiyi hakuri plss, so nake mu fita dajin nan ne so i will find you something to eat..." murya suka ji bayansu, ta kankamesa a tsorace ya juya yaga wani tsohon bafullatani sanye da katon hat wanda hakan yasa ba sosai yake yake hango fuskarsa ba, hannunsa rike da sanda cikin hausan sa da bai fitowa irin ta fulani yace ma Abuturrab "yarinya me ya kawo ku nan" Abuturrab da yaji sanyi sosai a ransa yace "Mun yi 6atan hanya ne Baffa!" Bafulatanin yace "Subhanallahi.... Ina ne xa ku?" Abuturrab ya sake samantha ya mike yana kallon dattijon cikin harshen fillanci yace "Daga kano muke xa mu kaduna barayi suka biyo mu tun jiya da daddare shine muka yo dajin nan" tsohon ya washe hakoronsa da goro yayi masa destroying da fillanci yace "Dama ina ganin ka nasan kai namu ne, ashe d'an uwana ne, barka da arxiki da barayin basu cutar da ku ba" Abuturrab murmushi kawae yake yana gyada kai, dattijon ya kalli Samantha da yaren yace "Sannu yarinya ta barka da arxiki" Kanta a kasa tace masa sun gode da harshen fillanci ita ma wanda hakan yayi mugun daure ma Abuturrab kai ya tsaya kallonta kamar idanuwansa xasu fito, dattijon yace "Rigar mu na nan kusa ku taso mu je ku huta, tafiyar minti talatin ne xae kai mu can, na fito kiwo ne dama na hango ku nayi xaton barayin daji ne, ga can inda na boye shanaye na" dariya Abuturrab yayi tsohon ma yayi dariya yace "Toh muje..." Abuturrab ya kalli samantha ya kama hannunta suka bi bayansa, ya matsa hannunta a hankali yace "Dama kina jin fulfulde shine ko sau daya baki taba gaya min ba" ta d'an yi murmushi bata ce komai ba, haka suka dinga bin dattijon da shanayensa kusan ashirin, su sha wancan kwanan su fito ta wani su kuma shan wata kai hanyar dai gashi nan gashi nan, Abuturrab yasan ko kashe sa xa ayi kila baxae iya gane hanyar ba. Suna isa Rigar dattijon ya juya yana kallonsu da fulfulde yace "Ga 'yar rigar mu nan, da fatan xaku ji dadin xama a ciki na yau dai" murmushi kawai Abuturrab yayi, tafiyar minti goma suka yi suka iso wani gida dake xagaye da kara, Dattijon ya shiga hade da sallama suka bi bayansa, bukkoki hudu ne a xagaye a d'an karamin tsakar gidan, wata mata dake daka tsakar gidan tayi masa sannu da xuwa da yare tana kallonsu Abuturrab, ya amsa yace "Kin ganni da baki 'yan uwanmu koh?" Mikewa tayi ta dauko tabarma ta shimfida tana masu lale, Yace "debo masu nono kafin ki xauna Hansai" wani bukka ta shiga sae ga ta ta fito da kwarya cike da nono ta ajiye masu, Dattijon da ake kira da Alto yace "Ina yarinyar nan ta shiga?" Hansai tace "Taje kai fura gidan tuwaru nasan duk inda take ta kusa gida yanxu" Malam Alto yace "Toh akwae ruwa gidan koh? Allah ne yayi masu katanga da barayi suka afko daji shine fa muka hadu da su...." Girgixa kai Hansai ta dinga yi tana cewa "Allah yayi mana tsari" Wata yarinya da baxa wuce Samantha ba ta shigo gidan kanta dauke da icce, ta karaso ta durkusa ta sauke tace "Inna bak'i muka yi" Malam Alto yace "Ehh wllh gasu nan daga birni suke" ta kalli Samantha tace "Sannu da xuwa..." Hansai tace "Tashi ki shiga da ita ciki ki bata zani ta daura tayi wanka" Mikewa tayi samantha ta tashi ita ma suka shiga wani bukka, bbu komai ciki sae yar katifa da xani a kai, sae jakar gari yayi xafi guda biyu, cement din dakin duk ya farfashe, Samantha ta xauna kasa yarinyar da hausarta na fulani tace "Ki xauna kan katifa" samantha tayi yanda tace, yarinyar ta bude jaka ta fito da wani xanin kayan fulani a linke ta ajiye mata tace "Gashi ki daura" Samantha ta kalleta a hankali tace "ina son in huta ne" yarinyar tace "Toh ki huta" daga haka ta fita, Hansai tace "Kin bata xanin Binta?" Binta tace "Eh ta kwanta wai tana son ta huta" Hansai tace "Toh shknn, maxa ki xo ki hura wuta in daura sanwa tunda mun yi bak'i" Wani sabulu babba me kamshi Alto ya dauko a dakinsa ya mika ma Abuturrab yace "Aminina Hammadu ne da yaje birni ya kawo mun sabulun nn har uku... Gashi ka shiga wanka da shi xaka fi jin dadinsa" Abuturrab ya mike yana murmushi ya karba yace "Toh nagode Baffa" daga haka ya nufi 'yar kewayan dake tsakar gidan don Baffa ya kai masa ruwa Binta ta bi sa da kallo, ko da ya fito Baffa ya kai sa Bukkarsa ya dauko masa wani tsaftatattcen rigarsa irin ta fulani ya basa, Abuturrab ya karba hade da godiya Alto ya juya ya fita, yana gama shiryawa ya fada d'an gadon dake bukkar lkci daya bacci ya daukesa. Burabisko da miyar taushe da k'ashi Hansae tayi ta ajiye masu cikin langar tuwo da miya, Baffa dake xaune da yar radio a hannunsa yace "Bayin Allah da alama sun wahala, a dajin ma suka kwana" ana kiran Azahar Baffa ya tada Abuturrab yayi sllh, Hansae tace "Tafi ki tada ta ita ma tayi wanka tayi sllh" binta ta shiga ta tada Samantha tace "Ki tashi kiyi wanka sai kiyi sllh, Azahar yayi" Samantha ta mike xaune tana mitsika ido, can ta mike ta cire kayan jikinta ta daura xanin, ta kalli binta tace "ki ban mayafi don Allah" Binta ta nemo mata wani dankwali ta bata tace "Mu je in raka ki kewayen na kai maki ruwa" Abuturrab na xaune a tabarma tare da Alto yana shan fura da nonon da Hansai ta dama masu Samantha ta fito da Binta, kallonta ya dinga yi ita ko kallo daya tayi masa ta dauke kai Binta ta rakata har bayin snn ta dawo, Samantha na fitowa daga wankan Hansai tace "Ga buta can ki dauka kiyi alwala" shiru Samantha tayi bata ce komai ba, can ta kalli Abuturrab da idonsa ke kanta, ta girgixa kai a hankali tace "Bana yi" daga haka ta shige Bukkar Binta, wata yar top da xani binta ta bata ta sa, tana gama shiryawa binta tace "Ki fito ku ci abinci wae ke yake jira" Samantha ta mike suka fita a tare, Alto ya mike yace ta taho ta xauna, ta karasa ta xauna kan tabarmar, Fura Abuturrab ya mika mata ta karba ta ajiye, bata bari sun hada ido ba duk da irin kallon da yake mata, shi ya fara sa hannu cikin langar dake dauke da Burabisko da miya yayi bismilla ya fara ci, kasa sakewa Samantha tayi taki cin abincin sai fura da take sha a hankali Hansai tace "Ko xa ku shiga daga ciki naga kamar a takure take" Kamar Abuturrab jira yake yace "Toh" Hansai tace "Binta kai masu abincin daki" Binta ta je ta dau abincin ta shiga da shi bukkarta, Abuturrab ya mike yana kallon Samantha ita ma ta mike ta bi bayansa suka shiga Bukkar, suna shiga ya nuna mata kusa da shi ta xauna, ya dau cup din furan ya mika mata ta sa hannu ta karba yace "Finish it immediately ki ban cup din" ta yi d'an murmushi ta kai baki, kadan ta sha tace "Na koshi" ya hade rai yace "Sae fa kin shanye" girgixa kai tayi ya k??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????wace cup din hannunta ya matso kusa da ita ya rike kan ta ya kai cup din bakinta, bbu yanda ta iya haka ta dinga sha kamar xata yi kuka, sae da ya ga ya wuce rabi snn ya ajiye ya ce "oya sa hannu" lekan abinci tayi tace "What's that" Hannu yasa ya deba ya kai bakinta, ta bude bakin a hankali ya xuba mata, da kyar ta dinga taunawa tana kallonsa kmr me taunar magani, ya dake bai bari yayi dariyar dake cin sa ba, tana hadiyewa tace "Baxan iya ci ba Dr " Ya girgixa kai yace "No, but da dadi fah, there's no other food than this!" Ta fashe da kuka tace "Baxan iya ci ba..." Shiru yayi yana kallonta, can ya kamo hannunta cike da tausayi yace "Toh me xa ki ci" cikin rawar murya tace "Rice!"

*Haske writers asso*=???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

30.....

Shiru yayi ya rasa abinda xai ce mata, can ya sa hannu cikin aljihinsa yaga har lkcn kudin da yayi withdraw na nan, ya rufe burabiskon ya mike yace "To taso mu je" a hankali ta mike ta bi bayansa suka fita, yana kallon Hansai da Alto da yare yace "Baffa xa mu d'an xaga rigar nn...." Alto tace "Toh har kun cinye abincin ne?" Yace "A'a idan mun dawo xa mu ci, furan ya ishe mu" Alto tace "Toh bari Binta ta xaga da ku, sai dai fa ba wani girma ne da kauyan namu ba" tana dariya ta kare maganar shi ma yayi dariya yace "Ni kuma hakan ya burgeni sosai babu hayaniya" Alto ya kwalo ma Binta kira ta fito yace tayi masu jagora xa su xagaye Rigar garki, tace "Toh" snn ta koma ciki, dama shigar fulani tayi dogon gashinta da ke kai wa har kusan gadon bayanta an tufke mata shi gida uku, ta dau sandar kiwonsu tana kallonsu Abuturrab da fillanci tace "Mu je" Samantha dai ko kallonta bata yi ba har suka fita, tana tsakiyarsu suke tafiyar ko wani Bukka suka wuce sai ta fadi masu na wanene duk da fillanci, kai kawai Abuturrab ke kada mata, can ta kalli samantha da yaren tace "Ke bakya magana, ya sunan ki" Samantha bata ce komai ba, Abuturrab yace "Sunanta Fatima amma ana kiranta da Samha" kallonsa Samantha tayi ya wara mata ido, Binta tace "Lah ashe sunan mu daya, to me yasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login