Showing 147001 words to 150000 words out of 180592 words

Chapter 50 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1165

hannu hawaye na sakko mata, Umma tace "Sadiya maxa kira min yayanku mu tafi asibiti" da sauri Sadiya ta fita daga dakin don xuwa part din yayan nasu, Umma ta dauko hijab dinta ta sa mata, ixuwa yanxu sunan Umma kawai Noor ke kira don ita kadai tasan abinda take ji, Umma na rike da ita suka sakko parlor, tafiyar ma dauriya kawai take, Sadiya ta dawo tare da Maryam, haka suka fita waje, Maryam ta taimaka mata ta shiga mota Umma da sadiya ma suka shiga motar, Maryam ta shiga gaba, Mijinta dake ta yi ma Noor sannu ya tada motar suka yi asibiti. Kafin su isa asibitin har ta fita hayyacinta, tafiyar ma kasawa tayi bayan sun fito daga cikin motar ta kalli Umma cikin kuka tace "Wayyo Umma Aliyu, kuce ya xo" Umma ta kalli Maryam, Maryam dai ta kasa cewa komai sai kallon Noor take, da taimakon nurses din da Mijin Maryam ya kira suka shiga da ita asibitin sai labour room. Meanwhile Abuturrab kam tunda ya tafi masallaci sllhn Asuba har gari ya waye bai dawo ba, dole Abba ya koma masallacin ya taso sa a gaba suka dawo gida, Mami ta shiga bedroom dinsa tana kallonsa ganin damuwar dake fuskarsa ta xauna kusa da shi cikin raunin murya tace "Don't start that again Son, wai ya kake son inyi da raina ne, baka tausayina Aliyu, tun da Sadeeq ya tafi abun ka ya kara jagulewa kuma, haba son, ya kake son inyi da raina?" hawaye ne ya cika idonsa ya daura kansa a shoulder dinta cikin rawar murya yace "Mami Samha...." Rungumesa tayi ita ma hawayen ya cika idonta tace "I know son, musulmin kwarai fa an san sa ne da tawakali, sau nawa kuma xa ace maka tana hannun mutanen kwarai idan Allah ya yrda....." Da kyar yace "Mami her delivery may be today or tomorrow..." jikin Mami yayi sanyi, ta shafa kansa a hankali cikin sanyin murya tace "In sha Allah xata sauka lafiya albarkacin wannan rana ta juma'ah, kayi ta mata addu'a kaji son" kai ya gyada mata bai iya yace komai ba.

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
88.....89

Har kusan sha biyun rana Noor ban da wahalan labour bbu abinda take, bbu abinda ke kara daga ma Umma hankali irin ynda take kiran Aliyu gashi ta tambayeta ko tana da number sa taki cewa komai, in ta gaji da kiran Aliyu sai ta koma Mumynta da Abbanta, suna nan asibiti har kusan karfe biyar amma shiru, nan likitan ya kira Abbansu Sumayya don yana asibitin shi ma a lkcn yake gaya masa in har wasu awanni biyun suka wuce bata haihu ba to xa ayi mata Cs kar babies su samu matsala, shi dai rasa abun cewa yayi, can dai ya amsa ma likitan ya fita, Umma ya kira ya sanar mata yanda suka yi da likitan, ita ma tayi shiru duk jikinta yyi sanyi, girgixa kai yayi yace "Ina jin Hajiya gwara ki lallabeta ta bada number mijin nata a kirasa ko ya kika ga" tace "Haka ne" daga haka ta koma ciki, ta xauna kusa da ita ta kamo hannunta ta dago kanta, ji tayi kamar ta xubar mata da hawaye ganin yanda ta jigata, ta daure tace "Look at me Noor, ki gaya min gaskiya, kina da number Aliyun?" Noor ta daura kanta jikinta tana girgixa kai ta fashe da kuka sosai tace "Bani da shi Umma, don Allah ku kira min shi mutuwa xan yi wllh" Jikin Umma yayi sanyi ba kadan ba, to ita yanxu ina xa su fara nemo Aliyu? Usman d'an Umma na uku ne yasa aka debo masa ruwa a cup ya yi addu'a ciki ya ba Maryam ta bata, Umma na rike da ita ta kai mata ruwan baki ta kauda kai da sauri tace "Bana jin kishi Umma" Umma tace "Addu'a ne Noor, ki daure ki sha" da kyar ta bude baki ta sha ruwan, bayan kusan minti biyar ta d'an nutsu har ta samu bacci, ashe duk axaban da take ji na wasa ne don cikin baccin taji ciwon da ya linke wanda take yi tun safe, duk ta haukace masu, nurses suka dawo gunta da likita daya, hankalin Umma yyi mugun tashi haka Maryam da tausayinta yasa ta fita kawai, Umma ma dai ta kasa daurewa ta fita, ko minti biyar bata kara ba ta haifo yaranta maza biyu, kukansu ya cika dakin, Hawaye ne ya sakko idon Umma ta shiga gode Allah a xuciyarta, yaran ma basu wani jigata kmr yanda likitocin ke tunani ba. Bayan minti goma aka fito ma da su, Umma ta karbi daya, Maryam dake ta murmushi ta karbe dayan dake ta ihu, Kallon yaran Umma ke tayi ganin girmansu, ita kuwa Maryam tana ganin yaran tasan lallai mahaifinsu ma ba baya ba wajen kyau, tun da aka fito da Noor take baccin wahala, Su Abba da yaransa maza dama tuni suka koma gida ganin ta sauka lafiya har sun ga yaran, Sumayya da Sadiya suka taho asibitin da kayan shayi sai kallon fararen yaran Sumayya take, ta kalli Sadiya tace "They r so cute kamar larabawa sis" Sadiya tayi murmushi tace "Wllh kuwa" sai bayan isha Noor ta farka nan da nan Umma ta hada mata shayi ta bata, da kyar ta dinga shan shayin har ta shanye, Umma tace "Sannu Noor, baki tambayi yaran ki" sunkuyar da kai tayi bata ce komai ba, Anty Maryam tayi murmushi ta dauki yaron dake kwance a gadon yara, farida ma ta dauko dayan suka nufota, gaba daya yaran suka ajiye mata a jiki, kallonsu kawai Noor take ganin su wasu kanana don bata saba ganin jarirai ba, banda dogon hancinta da ya fi na babansu bbu abinda suka dauko nata, sak Aliyu kamanninsu har hasken, irinsu kuma ake kira da identical Twins tsabar basu da bambanci, Farida ta nuna mata dayan da aka sa ma xare a hannu tace "Kinga Hassan ga Hussaini" bata san lkcn da murmushi yyi escaping lips dinta ba sae dai kuma ta kasa daukan yaran sbda kunyar Umma duk da ba ma iya daukansu xata yi ba, Umma tayi dariya tace "Amma gaskiya basu yi kama da ke ba sai dai Aliyu" rufe fuskarta tayi, Maryam tayi dariya haka ma farida, Sadiya tace "Xan so in ga Aliyun nn ni kam" Noor bata iya ta bude fuskarta ba sbda kunya, Umma tace "Toh kin dai san gidansu Aliyu a nan kanon koh?" Shiru Noor tayi bata ce komai ba, Umma tayi murmushi tace "Kya ma bude baki yarinya" A nan asibitin Umma tayi ma yaran wanka tunda kwana xa su yi, da kanta ta kai Noor bayi ta taimaka mata ta dauraye jikinta da ruwan xafi kafin su je gida. Washegari misalin tara aka sallamesu, suna isa gida wanka mai lafiya tayi ma Noor snn tayi ma jariran da suka cika gidan da ihu don tun jiya bbu abinda aka bari aka basu a asibitin sai ynxu da suka dawo gida, Noor na xaune tana kallon ynda Umma ke shiryasu, gani take kmr da an taba su xa su iya karyewa, nan ko su Umma ganin girman yaran suke sosai, da yake ita bata saba ganin jarirai ba bata san girmansu da rashinsa ba. Umma na gama shiryasu sai ga Abba ya shigo nan ya kuma yi ma Noor da ta kasa dago kanta barka, ya dau yaran gaba daya yayi masu addu'a snn ya fita, Ahmad da su Usman ma suka shigo suka mata barka suka ma yaran addu'a su ma suka fita, Anty Maryam ce ta shigo da warmer din pepper soup na kayan ciki ta ajiye dakin tana cewa "Sannu mai jego" murmushi kawai Noor tayi, Umma ta dau hassan ta daura ma Noor a kan kafa ganin da gaske bata iya daukan jariri ba dan tun a asibiti bbu wanda ta dauka sai dai tayi ta kallonsu, Umma tace "Toh fito da maman in ga ko xai karba" Noor ta kasa yin abinda Umma tace sbda kunya, Maryam ta bude mata zip din rigar jikinta, da kyar ta yrda tayi hakan don kunya take ji, ita tunda take ko Mumynta bata yrda ta ga tsaraicinta da girmanta ba banda Abban twins dinta sai Umma ynxu, Umma na xaune kusa da ita har ta ga babyn ya fara shan abincin snn tayi murmushi tace "You now feel the joy of Motherhood dear, Allah ya raya maki su a bisa tafarkin Islam" Noor bata iya ta dago kanta ba, bayan minti uku Umma tasa ta mayar da shi daya side din, sai da ta tabbatar abincin ya isa babyn snn ta dau d'an uwansa shi ma tasa ta bashi, bayan ta gama da babies din ta kwantar da su gefe, da kanta ta xuba mata naman kayan ciki da Maryam ta kawo mata ta dauka ta bata, tana gama ci ta sha magungunanta da aka bata a asibiti snn ta kwanta. Da yamma misalin biyar Ahmad ya shigo dakin tare da Maryam, bayan sun gaisa ya dau Hassan yana kallon Hussain yace "They re really identical, in ji an banbance maku su a asibiti" Umma tace "Hassan din ne a hannunka" yace "Maa sha Allah" kallon Noor yyi yace "Maman biyu bani number mai gidan ki" shiru tayi tana kallonsa, can a hankali tace "Bani da Number sa" Umma tace "Baki da numbersa kuma Noor, you've punished him a lot dear nasan duk inda yake yanxu baya da kwanciyar hankali" kamar xata yi kuka tace "Umma wllh bani da numbersa da gaske" Ahmad yace "Toh kin san gidansu ai koh?" A hankali ta gyada kai, yace "Toh bani address" bata ce komai ba har sae da Maryam tace "Ki bada Noor" kallon Umma tayi tace "Xan rubuta a takarda" aka dauko mata takarda da pen ta rubuta ta mika ma Maryam ta karba ta ba mai gidanta, babyn hannunsa ya kwantar yace "Ya sunan mai gidan naki?" Noor ta sunkuyar da kai tace "Doctor Aliyu" Umma tace "Oh likita ne" Noor tace "Uhm" Ahmad yace "Alryt to, bari in je" sallama yyi masu ya fita. Karfe biyar da yan mintuna Ahmad ya isa dai dai gate din su Abuturrab, ya juya ya kalli Usman yace "I think it's here" bude motar suka yi a tare suka fito suka nufi gate din gidan, Usman ya d'an tura gate din yaji a rufe, bude gate din aka yi, suka ga wani da khakin soldier tsaye, Ahmad yace "Barka da Yamma" Sojan ya amsa masa, Ahmad yace "Tambaya muke don Allah, sorry for the inconvenient, pls akwai Dr Aliyu a gidan nan?" Sojan yace "Eh, yaron mai gidan kenan" Ahmad ya shafa kai yace "Toh madallah ko xa a yi mana sallama da shi pls" Sojan yace "Daga ina ku ke?" Yace "Shagari qtrs" Rufe gate din sojan yyi, Usman ya kalli Ahmad yace "Lallai!! ko waye mai gidan" Usman ya koma gun motarsu yace "Babba ne tun da kaga haka" bin bayansa Ahmad yyi suka tsaya jikin motar, tsayuwar kusan minti goma sha biyar suka yi basu ga an bude gate ba, Usman yace "Anya nn ne gidan kuwa bro, dubi fa ynda aka shanya mu nan" Ahmad yace "Cool down, let wait a little more" bude gate din aka yi sojan ya fito yace "Xa ku iya shigowa" Ahmad yace "Toh godiya muke" daga haka suka bi bayansa suka shiga compound din, sae a snn suka ga sojoji hudu a compound din, gaishe su suka yi, Sojan ya nuna masu karkashin wani Artificial tree mai dauke da kujeru uku yace "Ku jira sa a can" godiya Ahmad ya kuma yi masa snn suka karasa suka xauna suna kare ma makeken compound din kallo, kamar bai son taka kasa haka ya dinga tahowa har ya iso inda suke xaune, gaba dayansu biyun kallonsa suke, ya d'an yi murmushi yyi masu sallama ya ja kujera ya xauna, suka amsa sallamarsa snn aka gaisa, Ahmad ya kalli hannunsa dake dauke da alluran drip yace "Baka da lfya?" Abuturrab yace "Yea, amma naji sauki Alhmdllh" gaba dayansu suka yi masa Allah ya sauwake, Ahmad ya d'an sauke ajiyar xuciya don ba ma sai ya tsaya dogon tambaya ba ya ga kamannin twins din Noor sak tare da Abuturrab, Shi kansa Usman kallonsa kawai yake, nan da nan kuma yaji tausayinsa don kana ganinsa kasan bai da isasshen lfya, Ahmad yyi breaking silent din yace "Dr Aliyu right?" Abuturrab ya kallesa yace "Yea, sai dai bn gane ku ba" Ahmad ya d'an yi murmushi yace "Ehh baka san mu ba dama Dr, mu ma kuma bamu sanka ba, sai dai mun gane ka ta dalilin carbon copies dinka" kallonsu kawai Abuturrab ke yi don bai gane inda suka dosa ba, Ahmad da ya kula da haka yyi murmushi yace "Alryt Dr, mun jima muna jin lbrin ka, mun kuma xo neman taimako ne a gun ka sbda Allah" Abuturrab ya jinginar da kansa da kujera yace "Na me fa?" Usman dai sai kallon yayansa yake don bai gane what he is up to ba, Ahmad yace "Mara lafiya xaka duba mana mu biya ka ko nawa ka bukata doctor" Hade rai Usman yyi yana kallon Ahmad, to what's d meaning of this kuma, Abuturrab yace "Ayya Allah ya bada lfya, sai dai nima bani da lafiyan, am under medication ma na fito yanxu" Ahmad yace "It won't take long Dr, na ga alamar baka da lfya, but ka taimaka sai ka ga kai ma ka samu waraka gun Allah, mun baro asibiti da dama mun baro likitoci da dama muka taso takanas gun ka..." Mikewa Usman yyi don ransa ya gama bacewa yana kallon yayansa yace "Excuse me" daga haka ya bar gun don bai ga amfanin hakan ba, shi dai Abuturrab bai ce komai ba, har ya mance rabon ya duba patient, can ya kalli Ahmad yace "What's wrong with the patient?" Ahmad yace "Ka taba dubata da dadewa kuma an samu waraka a lkcn, i cnt say what's wrong with her" Abuturrab yace "Alryt, a ina ku ke?" Ahmad yace "Shagari qtrs" Abuturrab yyi shiru, can yace "It's kinda far, anyway bari in shiga in fito" Ahmad yace "Toh mun gode Dr, Allah ya yaye maka damuwarka soon" kallonsa Abuturrab yyi kafin yace "Amin" ya shiga ciki, murmushi Ahmad yyi a xuciyarsa yace "Buh he is kind of nyc, he have got a free heart, bai ji tsoron ko cutarsa xa mu yi ba ya yrda xai bi mu duba mara lfya" text ne ya shigo wayar Ahmad ya duba yaga Usman ne, bude content din yyi yaga text din kmr haka, "Haba bro, hakan bai da amfani just tell him what we re here for mu bar nan, stop playing with his sense ko kai ake ma haka baxa ka ji ddi ba" Ahmad bai tanka text din ba sai ma murmushi da yyi, Abuturrab na shiga ya sanar da mami xai je duba patient a shagari qtrs an kira sa, taji ddin jin hakan sai dai kuma yanda taga yanayin jikinsa tace "Buh you re weak son, haka xaka fita gashi ko karewa ruwan bai yi ba" Yace "Worry not Mami, xan iya da baxan iya ba baxan je ba ai" tace "Toh shknn Allah ya tsare" yace "Ameen" drip din hannunsa ya cire, ya sauya jallabiyar jikinsa xuwa kananun kaya snn ya fita, har lkcn Ahmad na nan yanda ya bar sa, ya karasa yace "Am ready" mikewa Ahmad yyi yace "Alryt Dr" daga haka suka fita gun mota, Ahmad ya xauna maxaunin driver, Usman dama na xaune gaban motar, Abuturrab ya bude baya ya shiga. Har suka isa Shagari qtrs bbu wanda yace komai cikinsu, Ahmad yyi parking a compound din snn ya fito yana kallon Abuturrab da ya fito daga motar yaji gabansa na faduwa haka kawai, Ahmad yace "Mu shiga Dr" bin bayansa yyi, Usman ma na biye da su a baya har xuciyarsa ya dinga jin tausayin Abuturrab ganin bai ma yi tunanin ko cutarsa suka kawo sa nn su yi ba ya biyo su da xuciya daya, Xama Abuturrab yyi a babban parlon gidan, Ahmad na murmushi yace "Welcm to our home Dr" Abuturrab ya mayar masa da murmushin, Usman ya wuce ciki sai ga sa sun fito da Umma, tun da ta shigo parlon take kallon Abuturrab, a xuciyarta tace Eh lallai twins sun yi ma Noor wayo, Abuturrab ya kalleta yyi kasa da kai yace "Ina yini mama" xaunawa tayi tace "lafiya lau" mamaki take a xuciyarta anya me innocent face din gabanta xae iya aikata abinda Noor tace, ta kawar da tunanin da wuri tunawa da tayi abun ba a fuska take ba, Umma tace "Sannu da xuwa Aliyu" ya kalleta da mamaki jin ta kira sunansa, can ya sunkuyar da kai yace "Nagode mama" Mikewa tayi ta wuce ciki, ba a dau lkci ba sai ga Maryam ta fito rike da Hassan, Ahmad ya mike ya karbi yaron ya isa kusa da Abuturrab ya mika masa yana kallonsa, kallon jaririn Abuturrab yake kafin ya karba yace "Oh dama baby xa a duba, buh am nt an expert a wnn bangaren, they shud have take....." Shiru yyi yana kallon jaririn lkci daya gabansa ya tsananta faduwa, Usman ya karbi hussain da Sadiya ta fito da ya nufi gun Abuturrab shi ma ya mika masa a hannunsa, Abuturrab ya kallesa shi ma, can ya dago a hankali yana kallon occupant din parlorn, ganin irin kallon da suke masa gaba daya yace "Noo" lkci daya ya mike ya ajiye yaran gaba daya kan kujera ya nufi Ahmad ya rikosa cikin rudewa yace "Noo plss, I want to see their mother, where is...." Makalewa sauran maganan yayi ganin Samharsa da yyi tsaye bakin stairs ta ki karasowa parlon tana wasa da fingers dinta kanta a kasa, wani mugun bugu xuciyarsa yyi, ya dafe kirjinsa da sauri, lkci daya ya fara ganin jiri, idonsa ya fara juya masa, Ahmad ya nufo sa da sauri ganin yanayinsa, kafin ya iso tuni yyi kasa har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login