Showing 138001 words to 141000 words out of 180592 words

Chapter 47 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1138

fito snn Samha ma ta fito, wasu yan mata ne har su uku suka fito a daya daga part uku dake cikin babban compound din, can sai ga wata ma ta fito daga wani part din da yara uku, duk suka taho da murna gun matar, sai bayan da suka gaisheta snn matar da ta fito da yara uku ta kalli Samha tace "Sannun ku da xuwa, ya hanya" Samha ta kirkiri murmushi tace "Alhmdllh" sauran yan matan ma duk suka gaisheta da fara'a daga haka Umma tace su shiga ciki kafin a kira Magrib, babban parlor ne sosai duk suka xaxxauna Umma na kallon yar ta Farida tace "Farida ku shiga da ita ciki ta huta" Farida ta mike tana kallon Samha tace "Mu je Anty" mikewa Samha tayi ta bi bayanta suna shiga wani daki farida ta nuna mata gado tace "Xauna sai in hada maki ruwan wanka" daga haka ta shiga bathroom, ba a dau lkci ba ta fito ta ciro xani a Press dinsu ta mika ma Samha tace "Ki shiga" Samha ta karba a hankali tace "Na gode" daga haka ta shiga bayin, ko da ta fito har an kawo mata abinci, Sumayya ta dauko mata doguwar rigarta ta ajiye mata da man shafawa tace "Ga kaya nn" Samha tace "Toh nagode, xan yi sllh" Darduma yarinyar ta shimfida mata ta fita, la'asar tayi snn magrib don har an kira, tana xaune kan darduma mata me yara uku wanda da alama wanda ya dauko su a park ne mijinta ta shigo dakin da warmer tace "Sannu bakuwa" murmushi Samha ta kirkira ta kasa cewa komai, matar me suna Maryam ta ajiye warmern tace "Ki ci ynxu kar ya huce" Cikin sanyin murya Samha tayi mata godiya, Maryam ta fita, Sadiya ce ta shigo dakin, ita ma dai 'ya ce ga Umma ta gaida Samha tayi mata ya hanya snn ta fita, da kyar Samha ta mike ta shiga shiryawa, haka kawai hawaye ke xubar mata ta rasa dalili, ta gama sa kayan ta xauna kasa ta jinginar da kanta da gado, Sumayya ta shigo dakin tace "Baki xuba abincin ba Anty" durkusasawa tayi ta bude abincin ta shiga dibar mata, tana diba ta kai mata gabanta, ta dauko pepper soup din da Maryam matar yayanta ta kawo mata shi ma ta ajiye gabanta, Samha ta d'an yi murmushi tace "Baki gaya min sunanki ba" tace "Sunana Sumayya" Samha tace "Nagode Sumayya, ni sunana Samha" murmushi Sumayya tayi tace "Haba dai, welcm to our home samha" daga haka ta mike ta fita daga dakin, ba laifi Samha ta ci abincin sbda yunwar da take ji, da taji ta koshi ta kwantar da kanta jikin gado ta rufe ido, Sadiya ta shigo tace mata ta hau gado mana, mikewa tayi ta hau kan gadon. Tun da Samha ta bar gida Abuturrab ke kwance idonsa a lumshe, shi dai ba bacci yake ba ba komai ba, sai kusan karfe biyar a lkcn ya mike xaune, rike kansa da yyi masa nauyi yyi, ga wani ciwo da kan ke masa, ragowar tabarsa ya dauko ya xari daya ya kunna ya kai baki, me yasa yarinyar nn ke neman sa masa hawan jini da ciwon xuciya ne, can dai yyi karfin halin mikewa tsaye ya kashe sauran taban ya jefar ya fita daga dakin, duk da yasan bata dakin nata hakan bai hanasa tura kofa a hankali ba, he just don't want to believe da gaske barin gidan tayi, bbu kowa dakin as he already know, ya juya da kyar ya wuce parlor, nn ma tsaye yyi na kusan minti goma kmr yana jiran ganin billowanta, can ya nufi kitchen nn ma ya gama tsayuwarsa ya dawo parlorn ya xauna ya rike kai, kmr wanda aka tsikara ya mike da sauri yace "Noo" dakinsa ya koma xai dauka makullin mota sai ya tuna ae ya kai ma Ummi, fitowa yyi ya bar parlon ya fita compound, tafiya kawai yake amma wani juya masa kansa ke yi, ya nemi dakali ya xauna ya rike kan, ta ina xae xai fara nemanta, ita dai ba da kudi ta bar gidan ba, ba kuma kawaye gareta a garin ba, infact bata ma san kowa ba, tunanin hakan yasa shi mikewa da sauri, lkci daya hankalinsa ya tashi, to ina xata je haka, tafiya ya dinga yi har ya isa bakin titi, ganin he is just lost ya ciro wayarsa a aljihu ya shigw kiran Dr Shariff. Karfe goma da wani abu Sumayya ta shigo daki, ganin idon Samha biyu tace "Anty wai ki je in ji Umma" mikewa Samha tayi tace "Toh" Sumayya ta dauko mata hijab ta bata ta sa daga ????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? haka suka fita, Umma na bedroom dinta da yaranta maxa biyu Samha ta shigo da Sumayya, duk da manya ne su ma hakan bai hanasu gaida ta ba suka fita, Sumayya ma ta fita, Umma ta nuna mata gefen gado ta xauna, ta xauna kanta a kasa, Umma tace "Samha xan maki tambaya, but what i hate in my life is lying, kar ki min karya, kar kuma ki ji komai ki bn amsan tambayar da xan maki" Samha ta kasa dago kanta cikin sanyin murya tace "Toh" Umma tace "Kina da miji?" Kasa cewa komai Samha tayi sai hawaye, Umma tace "Nace kar ki ji komai ki min magana" fashewa da kuka tayi, Umma bata hanata ba tayi mai isarta tayi shiru, Umma tace "Answer me now" cikin sarkewar murya tace "Ina da shi Mumy" Umma tace "Na fa ce maki ban da karya" ta dago hawaye na sakko mata cikin sanyin murya tace "Ba karya nake ba Mumy" Umma tace "Toh yana ina?" A hankali tace "Gombe" Umma tace "Toh me ya faru kika bar gida?" Tana share hawayenta tace "Bana son sa kuma, ina son komawa gun iyayena" umma tace "Baki son sa? Yayi maki wani abun ne, kuma ko kin koma gun iyayen naki su ma ba barin ki xa su yi ba, ki kalli condition din ki fa, ki gaya min gskyan me ya sa kika baro gidan" tace "Mum idan na koma gun parent dina they will be happy that i am back duk da nasan i failed them...." Ta fashe da kuka sosai tace "Mum i wish i can start my life all over again, though m nt regretting coz everything happen for my good, but i wish ba ta wnn hanyar Allah ya nuna min *Noorul Huda* ba" Umma ta dafa shoulder dinta da tausayi tace "Kar ki yi Sa6o Samha, kuma nace kar ki min karya kuma kin min, baki da aure knn koh?" Ta rufe kanta jikinta tana kuka sosai tace "Allah ina da aure Mum, but i got married with out d knowledge of my parent, i chose a man over dem, a muslim for that matter" dagota Umma tayi da mamaki tana kallonta, Tana girgixa kai tace "I was born nd brought up in a Christian home, my name is Samantha...." Kallon Mamaki Umma ke mata ta rasa abun cewa, a hankali Samha ta ci gaba tace "I chose Aliyu a muslim over my parent...." Nan da nn jikin Umma yyi sanyi sosai, ynxu fa sai tace Aliyun yaudaranta yyi, kila ma tace sakinta yyi, nan da nan ranta ya baci ba kadan ba, me yasa xai 6ata ma islam suna haka, me yasa xai ci amana yyi betraying trust dinta yana matsayin musulmi, Samha ta sunkuyar da kai hawaye kam yaki tsaya mata, Umma ta riko hannayenta a hankali tace "Tell me about everything daughter.... Islam is nt d way you r thinking right now, share ur story with me" Samha ta gyada mata kai har lkcn hawaye na xuba idonta, a hankli ta soma bata labarin farkon haduwarsu da Aliyu.Umma sai kallonta take tana saurarenta with much interest, Samha bata dakata ba sai da ta kai har karshe, ta fashe da kuka sosai tace "Mum kinga ya min gorin ni na biyosa ae, ya kuma min gorin bn je gidansa da komai ba, ae wnn ba halin musulmai bane...." Rufe bakinta Umma tayi cike da tausayinta tana girgixa kai tace "You don't say anything about Aliyu now, but all this while me yasa ki ka ki karban islam gashi kina sllh, let this nt make you have doubt for islam Samha, rayuwar Antyn ki Maryam bai baki sha'awa, is der anything in islam that's nt good bayan ki cire abinda Aliyu yyi maki, kinsan a ko wani addini akwai dakikai...." A hankali Samha tace "Mum xan karba islam amma ba don na taba auren musulmi ba, xan karbi islam ba don Antyna ba ko kakana, sai don Allah, da abubuwa da dama da musulmai suka min, na shiga hannun musulmai da dama Mum, ban san ynda xan fadi maki kirkinsu da karramci ba which ba kowa ke haka ba a addinin iyayena don basu yrda da kansu ba balle wani, Mum tun daga kan Aunt din Aliyu... duk da addininmu ya sha bambam iyakar son da xata ma d'an da ta haifa ta nuna min, tana daya daga jerin mutanen da baxan mance ba a rayuwata, ban taba ganin mahaifiyarsa ba amma indai suka yi waya ita ma takan ce ya bani mu gaisa duk da rabata da d'an ta da nayi hakan bai sa ta ji haushi na ba, mum mun xauna a rigar fulani da muka bar kano, the muslims we met der where more than kind, sun yi accommodating dinmu ba tare da sanin daga inda muka fito ba ko inda xa mu, basu san xuciyar mu ba amma a haka suka xauna da mu which ba lallai d'an uwana Christian yyi min haka ba, muka je gombe.... Ummi ta min abinda ko wacce ta haifeni sai haka, ta rike ni kmr yar ta, bata taba kyamatata ba a matsayin wacce ba musulma ba, i knw i can never forget her too, haka ma yarinyar ta khadija, fatima kuma nasan mijina take so shi yasa take min abinda take yi, gun ta da sisters din Aliyu kadai na samu matsala su ma kuma ban ga laifinsu ba don if i where to be in der shoes iyakar abinda xan yi knn don na raba jini ba abun wasa bane, a zaria ma na xauna da musulmai da basu san ni ba ban san su ba su ma kuma sun min karamci ba kadan ba, Sai gashi na hadu da ke yau mum, baki san ni ba baki taba ganina ba kika taimakeni tun a tasha, bai tsaya iya nn ba har sai da kika kawo ni gidanki baki damu da ki fara bincike kafin ki yrda in shiga gidan ki ba, sai gashi gaba daya yaranki basu san ni ba, amma suka dauke ni kamar yar uwa duk a rana daya cikin kankanin lkci, dubi ynda kika xauna kina saurarata da xuciya daya baki yi tunanin ko karya nake maki ba kin kuma yarda dari bisa dari, Mum with this i knw islam rahama ne, musulmai daban suke a duk inda suke.... Kuma duk inda na xauna bbu wanda ya taba tilasta ni inyi addininsa ko da wasa, har shi kansa Aliyun, wanda da Christian home ne da tuni an fara fita da ni church, i wil be very proud to be among you, amma ni baxan komawa gun Aliyu ba, i prefer going back to my parent in ma kasheni ne su yi, but na bar Christianity da dadewa a xuciyata, na kuma dade da fadin La'ila ha illallah....." hawaye take sosai ta kai karshe, Umma ta jawota jikinta tana murmushi ita ma idonta ya kada sosai tace "Am happy for you Samha, amma ki yafe ma Aliyu, kinsan duk d'an adam ajizi ne...." Girgixa kai tayi tace "Na yafe masa Mum, ae ya min abinda baxan manta ba amma ni na hakura bana auren kuma, kilan rabon inyi converting ne Allah ya hada mu, don naji har cikin raina bna sonsa kuma, ba kuma yau na fara jin haka ba, for the past 3month nake jin hakan...." Umma tayi shiru kafin tace "Toh dama kana kishin abinda baka so" murmushi Samha tayi tace "Mum da gaske bna son sa yanxu, bna ma son in gansa"

*Haske writers asso*

can ta matse maki=??=?? Samantha
[11/30, 7:59 PM] * +234 806 632 7659, : =ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
84.....

Rudewa Mami tayi ganin aman jini yake tayi k'asa da shi ta dinga kiransa tana jijjigasa cikin tashin hankali, Abba tsaye yyi yana kallonsa da mamaki ya kasa cewa komai, Ramla da Ilham suka sakko jin muryar Mami, wani ihu suka saki a tare, Ramla ta taho da gudu ta durkusa ta rikesa ita ma cikin kuka tace "Ya Turab, Mami me ya same sa, dubi aman jini yake fah" juyawa Abba yyi ya koma parlor ya dau waya ya shiga kiran doctor dinsa. A yau litinin Samha ta xamo daya daga cikinmu bayan an yi duk abinda musulunci ya tanadar kafin yin hakan, wato dai ta amshi kalmar shahada, yanda Umma tayi farin ciki a wannan rana sai ka rantse ta hada abu da ita ne, shi kansa mai gidan ta Alhaji Ibrahim da abokansa biyu sai yaransa maxa gaba daya sun yi farin ciki da lamarin suka kuma yi mata fatan alkhairi suka kuma yi mata addu'ar Allah yasa ta dauwama a islam, shawarwarin da ya kamata suka bata suka kuma yi mata nuni da sai ta kauda kai a duk abinda xata gani gun yan uwanta nan gaba, sauran kuma suka bar ma Hajiya Halima, nan ita ma ta bata nata shawarar, sun jima sosai a parlon da umma bayan barin su maigidanta, ita dai Samha na xaune kanta a kasa, har lkcn ta rasa dalilin kukan da take, Umma tace "Bana son kukan nan daughter, ain't you happy?" Tana share hawayenta a hankali tace "I am" Umma tace "Good, kar ki sake xubda hawayenki, Allahu na tare da ke, kuma shine gatan ki xai kuma ji6anci duk al'amuran ki" kai Samha ta gyada mata, Umma tace "Kina da sunan da kike son a dinga kiran ki da shi ne?" Kallonta Samha tayi sai kuma ta girgixa kai, Umma tayi murmushi tace "Alryt we will call you *Noor* meaning *Light* kina so?" Murmushi Samha tayi a hankali tace "Toh Umma" tace "Kina xuwa Antenatal ne a can gombe?" Kai ta gyada mata ba tare da ta dago ba, Umma tace "Alryt, tafi ki je ki huta, koh gobe sai Maryam ta raka ki asibiti" Mikewa tayi tace "Nagode Mum" daga haka ta wuce daki, a bedroom Umma ta xaunar da yaranta gaba daya da surkanta biyu ta fadi masu matsayin Samha ta kuma basu takaitattacen labarin da Samha ta bata jiya, duk sun ji tausayinta sosai, nan Umma tace "Ke Sumayya tunda kina gida always sai ki dinga lura da ita kina putting din ta through, tun daga kan alwalarta da sallah, kiyi kkrin dinga nuna mata do's nd don't's din islam, snn kiyi kkrin dinga koya mata addu'o'i, har ma da karatun qur'an, i notice she's not totally an illiterate in islam, kema sai ki samu lada gun Allah in kika yi xuciyar ki daya" Sumayya tace "Toh Umma" Umma ta kalli Maryam da Rukayya tace "Ku kuma ta fannin auratayya nake son kuyi putting dinta through" su ma suka amsa, nan tace ma 'ya yan nata duk Noor xa su dinga kiranta da. A hankali Abuturrab ya bude idonsa ya saukar saman dakin, sosai yake jin nauyin idanuwan nasa, kare ma inda yake kwance kallo ya shiga yi a hankali yaga bedroom din kamar na Abbansa, idonsa ya sauka kan alluran dake vein dinsa, kallon ledan ruwan yyi lkci daya ya mike xaune xai tuge yaji muryar Abbansa, "Don't you try that!" Juyawa yyi da sauri suka hada ido, lkci daya abubuwa suka dinga dawo masa, rike kansa yyi jin wani tukukin da xuciyarsa ke yi yace "Nooo" Abba ya karaso da sauri yyi gripping shoulders dinsa yace "Are you okay" ya daura kansa jikin Abbansa cikin rawan murya yace "She's gone Abba...." Mami ce ta shigo dakin tare da Hajiya Mariya jin muryarsa, Hajiya Mariya ta karasa da sauri ta dago sa tace "Aliyu...." Bude ido yyi yana ganinta ya rungumeta cikin raunin murya yace "Mum don Allah don annabi kice mata ta dawo" da damuwa Hajiya Mariya tace "Then ka nutsu tukun son, ba fa inda ta je tana gida dama...." Saketa yyi da sauri yace "Da gaske Mum" bai jira cewarta ba ya yunkura xai mike tsaye tana kkrin mayar da shi amma tuni ya tashi, wani mugun bugu xuciyarsa yyi, ya dafa gun da hannu biyu, Mami ta rude tace "Innalillahi, Col ka kira likitan don Allah" tare suka yi kasa da Hajiya Mariya don kasa tsaye yyi, Strictly Abba yace "If anything shud happen to my son..... Wllh duk sai kunyi mamaki na, i will make sure you two pay for this, yanda ku ka munafurce ni ku ka boyesa da yarinyar for all this while haka xaku nemota ku kawo masa ita ynzu idan ba haka ba......" A tsawace yace "kowa ma sai ciwon xuciya ya kamasa" Wani harara Mariya ta watsa masa ta gefen ido a fusace tace "Don Allah mu wuce asibiti yaya, ki kira masu gadi su taimaka mana a sa shi a mota" fita Mami tayi tana hawaye taje kiran soldiers din waje. Suna xaune a ward din da aka basu su kadai, Ramlah na xaune kusa da shi sai hawaye take haka ma Khaleesat, Ilham kam na gefen Mami ita ma kukan take, Mami dai ta xuba uban tagumi idonta a kansa ganin mugun ramar da yyi, bacci yake amma da gani kasan na dole ne, hawaye ne ya xubo idonta jin abinda likitocin suka gaya mata, Aliyunta da ciwon xuciya kuma, wnn wace irin kaddara ce, sallamar Hajiya Mariya da Ummi ne ya katse mata tunaninta, suka shigo ward din Shariff na biye da su a baya, Mami ta d'an yi murmushi tace "Sannu da isowa Hajiya" Ummi dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login