Showing 42001 words to 45000 words out of 180592 words

Chapter 15 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1151

wayarsa ne ya tashesa kusan magrib, dai dai shigowar mami dakin tace "Lafiyan ka Aliyu, baccin yamma ana xaune kalau?" Mikewa xaune yayi ya dau wayarsa yayi picking call din, daga daya bangaren aka ce "Hello!" Abuturrab yace "Good evening" "Evening, kana gida ne doctor" cewar mutumin kenan, sae a snn Abuturrab ya dau murya yace "Yeah ina gida sir, ya aiki?" Mr David yace "We Thank God, daughter na ne bata da lafiya, i want you to check on her if it's ohk by you and you re less busy pls" Abuturrab da hankalinsa ya tashi lkci daya yace "Ohk sir, i will do that right away!" Daga haka ya katse wayar ya kalli Mami dake tsaye har lkcn tana kallonsa yace "Mami na gaji da yawa ne yau" tace "ko abincin fa baka ci ba" mikewa yayi tsaye yace "Bari in dawo daga masallaci Mami" daga haka ya fita, ana idar da magrib ya tafi gidansu Samantha, bayan sun gaisa da mai gadin ya shiga, mai aiki ce ta bude masa kofa bayan ya danna bell, ya amsa gaisuwarta ya tambayeta inda Samantha take tace tana bedroom, ita ta raka sa har sama, ya bude kofar dakin suka yi ido hudu da mahaifiyarta dake xaune dakin alamar dai likita take jira, tana ganinsa ta hade rai sosai, ya sunkuyar da kansa ya karasa dakin ya gaisheta da ladabi, da hanci ta amsa masa ta mike ta fice, Abuturrab ya durkusa kusa da gadon yana kallonta ganin yanda lips dinta yayi ja, hannu ya daura forehead dinta ya ji dumi, a hankali yace "Samha..." Bude ido tayi da sauri ta mike xaune, ya kamo hannunta yace "Ina ke maki ciwo?" Hawaye ya cika idonta ta ki cewa komai, cire bargon jikinta yayi yace "Talk plss" ta sauke idonta kasa, ya tsura ma wuyarta dake dauke da farin cross ido, a hankali ya kai hannu kai xae tsinka ta rike hannun da sauri tace "Mumy ce ta sa min" bai kulata ba ya tsinka shi ya jefar gefe daya, ta sauke hannunta tana kallonsa, kallon kwayar idonta yake shi ma, hawayen da ke makale idonta ya gangaro ta daura kanta a shoulder dinsa cikin sanyin murya tace "Ni fa ban ce komai ba doctor, and you re angry, kayi hakuri pls..." Ya harde hannunsa da nata ya lumshe ido yace "Noo, kin fa ce baxa ki iya aurena ba" ta fashe da kuka tace "Nooo ni bnce haka ba fa..." Shiru yayi yana jin saukar hawayenta a shoulder dinsa, ya shafa kanta a hankali yace "But nace kiyi addinin ki inyi nawa fa, still kika ce it's impossible" girgixa kai tayi tace "Bayan kana rabani da duk wani abu na addini na shine xaka ce min haka, yanxu fa ka tsinka min rosary dina...." Buda ido yayi jin abinda tace, ya dago kanta yace "Ohh you gat me wrong samha..." Da sauri tace "Noo i am right" yace "You re sick kuma rosary din nan is a burden....." Hade rai tayi tace "A tunanin ka ba, kayan jikina bai xame min burden ba sai rosary" yace "Alryt am sorry baxan sake ba..." Bude kofa aka yi ya koma baya da sauri blessing ta shigo da gani kasan mumy ce tace ta taho, Ya kalleta yace "Taimaka mana da cup of tea pls.." Tace "Toh" snn ta fita, ya kamo hannunta yace "Toh yanxu ina ke maki ciwo" kanta ta nuna masa, yayi shiru yana kallonta, can yace ohk yanxun nan xae daina, lumshe ido yayi ya manna bakinsa kan goshinta, turasa ta fara yi tace "Doctorrrr" ya rike kanta gam ya sauko da ba lips din har kan hancinta sannan bakinta, yayi mata light French kiss, turasa tayi ta hade rai, ya wara mata ido ya koma baya yace "Alryt am sorry wife...." Blessing ce ta shigo da cup din tea ya karba ya mika ma Samantha, ta6awa tayi tace "Akwai zafi ai" ya ajiye sa kan bedside drawer yace "Toh bari inje in dawo yanxu" da ido ta bi sa har ya fita, gida ya koma ya dauko mata drugs ba a dau lkci ba ya dawo, har lkcn blessing na dakin, yayi mata kallo daya ya karasa gun Samantha ya dau tea din da ya ajiye ya kai baki yayi sip dinsa snn ya mika mata yace "Toh ya huce" hannu tasa ta karba, aka bude kofa Mumy ta shigo, mikewa yayi ya bude ledan maganin ya gwada mata yanda xata sha ya ajiye ya d'an saci kallon mumy ya ganta tsaye fuskar nan a murtuke, dukawa yayi kamar xae dauki abu murya can ciki yace "I will call you ltr..." Daga haka ya juya, bai bari sun hada ido da Mumy ba yayi mata sallama ya fita. Kamar jiya yau ma sha biyu da wani abu ya kirata, tana kwance ta dau wayar tayi picking ta kai kunne, daga daya bangaren yace "How you feeling now?" Tace "Da sauki..." Yace "Sai kice Alhmdllh..." Ta buda ido tace "Alhmdllh kuma?" Yace "Yess" tace "Tohm Alhmdllh" yayi murmushi yace "Good, a ina muka tsaya jiya a maganar mu?" Bata ce komai ba yace "Samha..." Cikin sanyin murya tace "Na'am" yace "Baki son maganan ne?" Girgixa kai tayi kamar yana ganinta tace "A'a fah" yace "Say something now" da kyar tace "Duk yanda kace doctor" murmushi yayi yace "Ohk we'll talk about that face to face...." Cikin sanyin murya tace "Toh" "Me xa ki bani for my birthday?" Wara ido tayi tace "Woaw, it's also my birthday month, wani date ne naka?" Yace "Da gaske kema month dinki ne?" Tace "Eh mana, my birthday is on 10th june...." Da mamaki yace "Are you for real?" Tace "Yes mana" yace "Woaww what a concurrent! It's same with mine" tace "heey doctor ba wani nan..." Yace "Am serious samha, i was also born on 10th june" tace "Wow so we re birthday mates?" Yace "Yeahh and we gonna celebrate it together.... No wonder shi yasa kike da kyau kema kamar ni... Haka kuma xa mu haifi yara duk june 10" Ta xaro ido tace "Uhm?" Yace "Yess am serious baby, today is 3rd, 7 dayz to our birthday!"
Tun daga lkcn wayarsu ya xama constant don xaman gida kawai take, duk bayan awa biyu sai ya kirata, hakan kuma yasa bai damu da rashin ganinta ba tunda suna waya, a haka har ya rage kwana daya birthday din nasu, da daddare yana daki ya kirata yace "Baby plss ki daure ki fito yau mana, i want to see you" ta kalli agogo taga har tara da rabi tace "But baka kalli agogo ba koh doctor" yace "Na kalla mana ai ba dadewa xa kiyi ba" xata yi magana yace "Plssss" kamar xata yi kuka tace "Doctor....." Yace "Plss" turo baki tayi tace "Na ji" daga haka ta katse wayar, tayi tagumi, can ta mike ta dau hijab ta sa ta kashe wutan dakinta ta fita, ko blessing dake daki bata sani ba, tana isa gidan bata gansa parlor ba, ta bata fuska tana kallon kofar daki, a bayanta taji sa a tsaye ta juyo da sauri ya wara mata ido yace "Welcome..." Tace "Toh kiran meye" kama hannunta yayi ya shiga da ita kitchen yace "Am hungry kuma potato and egg nake son ci, hope Mumy baxa ta neme ki ba" shiru tayi bata ce komai ba, can a hankali tace "Ohk... Mumy ta tafi church" Yace "Good, cire hijab din" tace "No xan yi a haka" gun da potatoes suke ta nufa ta debi wanda tasan xai yi masa ta fara ferewa da peeler, cikin kankanin lkci ta gama, duk yana tsaye yana kallonta, kafin minti goma har ta gama, ta daura ruwan Lipton ta juya tana kallonsa tace "Ko baxa ka sha ba" yana rungume da hannunsa yace "Xan sha mana" kayan kamshi ta xuba ta rufe snn ta dau dankali da kwan ta fita ta kai parlor ya bi ta da kallo, tana dawowa kitchen din tace "Toh kaje ka ci kafin ruwan shayin yayi" ya girgixa kai yace "No xan taya ki jira a nn" murmushi tayi bata ce komai ba, haka suka ta tsayuwa har ruwan ya tafasa ta juye flask snn suka fito, sai da ya tilasta ta suka ci abincin a tare, nan ya sa masu film a system tun tana cewa ita gida xata wuce har ta hakura tana kallon, kamar ance ta kalli agogo taga sha biyu saura 'yan mintuna, xaro ido tayi tace "Na shiga uku, doctor kalli agogo" mikewa take son yi ya riketa yace "But it's late Samha...." Turasa tayi tace "Let me plss, ni bana son kana min irin haka, you are just letting me betray my parent, ni ka sake ni" a fusace tayi maganar ta mike ya bi ta da kallo har ta isa kofa ta dawo don daukar takalmanta dake bakin kitchen, lkci daya aka bude kofar parlon, still tayi a gun tana kallon kofar, Ramla, Khaleesat, da Ilham ne suka shigo a tare, juyawa yayi shi ma yana kallonsu sannan ya kalli agogo da mamaki, ko kadan bai lura da abinda ke hannunsu ba da mamaki yace "Lafiya?" A tare duk suka bude murfin ruwan gora me sanyi dake hannunsu suka tuttula masa gaba daya a jiki lkci daya suka ce "Happy birthday....." Bai gama recover ba duk suka fice da gudu suna dariya, me Samantha xata yi banda dariya, ya kalli system dinsa da aka yi masu wankan tare ya mike da gani kasan ransa ya gama baci ya shige bedroom, Samantha ta langwabar da kai ta karasa parlon ta dau system din ta kashe ta ajiye kan kujera a bude, snn ta dauke lallausan rug din da ya jike ta fita da shi waje ta shanya, ta koma kitchen ta dauko mop da bucket ta share ruwan da ya malala a parlon bbu bata lkci ta gama ta wanke mop din, ta dawo parlor tayi jim, can ta kalli agogo sai kuma ta nufi bedroom din, xaune ta gansa gefen gado ya rike kai, ta xaro ido tace "Baka cire kayan ba?" Bai tanka ta ba haka yasa ta karasa ta durkusa gabansa tace "Doctor...." Ganin bai dago ba tayi shiru tana kallonsa, a hankali ta dago kan nasa suka hada ido, kamar xata yi kuka tace "Toh ka cire kayan kar sanyi ya kama ka mana" unbutton din shirt din ya fara yi, ta mike tsaye ta taimaka masa ta cire, tana kallon singlet din jikinsa tace "Toh ka cire doctor" mikewa yayi ya bude closet ya fiddo wasu inners ya shiga bayi, ba a dau lkci ba ya fito, a hankali ta juya masa baya, ya fiddo pyjamas dinsa ya saka, ita dai tana tsaye tana fidgeting din fingers dinta, kamar ance ta juyo ta ga belt hannunsa ya nufi kofa, da sauri ta bi sa ta rikosa tace "No doctor daga suna maka wasa, they just wished you happy birthday, kalli fa hana idonsu bacci suka yi har sae da sha biyu yayi, kai baka san wasa ba?" Ya wani hade rai yace "Ina wasa da su ne xasu xuba min ruwan sanyi a jiki" bata fuska tayi tace "Toh meye don sun xuba ma ruwan sanyi, after all they wished you a happy birthday" karamin fridge din dake dakin ya nufa ta bisa da kallo ya bude ya ciro ruwa me sanyi ita dai kallonsa take taga ya nufota yana bude ruwan, wani k'ara tayi xata gudu ya cafkota, ta kwala wani k'aran jin ruwan sanyi, ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????k'adan ya xuba mata ya ajiye, ta fashe da kuka ya wara mata ido yace "Happy birthday...." Kwace kanta tayi xata fita ya rungumota yana dariya yace "Ashe ba dadi" dage hijab dinta xai yi ta rike da sauri tace "Bana so...." Da karfi ya cire hijab din ya ga yar fingil rigar bacci ne jikinta, ya ja ta xuwa kan gado ya kwantar da ita ya rufa mata bargo murya can ciki yace "Go to sleep it's late" daga haka ya fita ya rufe kofar parlor ya dawo, a rufe ya ga idonta ya dau blanket ya xaga inda take ya durkusa cikin sanyin murya yace "Happy birthday wife!" K'in bude ido tayi duk da tana jinsa, xae mike yaji murya can kasa tace "Happy birthday also dear...." Murmushi yayi ya mike ya kashe wutan dakin ya fita parlor yayi kwanciyarsa.

*Haske writers asso*=???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

23.....

Da asuba ya rakata har gate dinsu don tace karfe bakwai Mumy xata dawo, ya rungume hannayensa yana kallonta yace "dont forget karfe shidda plss love..." Ta kallesa tace "Nace maka ni ban san yanda xanyi ba fa, Mumy xata tambaye ni inda xan je, idan nace mata church nasan ita ma xata je idan bata ganni ba kuma sai in ce me" yayi shiru yana kallonta, can yace "Toh kice mata gidan kawar ki xa ki je mana" turo baki tayi tace "Allah yasa ta bar ni" daga haka ta d'aga masa hannu ta shiga gida. Har bayan la'asar Samantha tunanin me xata ce ma Mumy da xata bar ta ta fita take, can dai ta dau shawarar sa na cewa tace gidan kawarta xata je, ae ko biyar da kusan rabi ta shiga dakinta ta sameta ta xauna gefenta a hankali tace "Mumy xan je gidansu Victoria kinga ta daina xuwa nan don bana xuwa gidansu...." Tsit tayi tana mamakin kanta don ita dai tasan bata karya gashi yau Abuturrab yasa tayi, duk jikinta yayi sanyi ta fara wasa da fingers dinta, Mumy dake mata wani kallo don taga alamar karya take wanda hakan ya daure mata kai wai yau samantha ce ke kkrin hada karya, bata dai nuna ta gano ta ba tace "Tun safe kina gida baki ce xa ki ba sae da yamma tayi?" Shiru tayi bata ce komai ba, Mumy tace "Toh tafi kar ki dade amma" Samantha ta kasa cewa komai kuma ta kasa kallonta, can dai tace "Toh Mumy driver ya kai ni" Mumy ta xuba mata ido sai kuma tace "Toh kije kiyi masa magana" mikewa tayi ta fita ta koma dakinta, hawaye ya cika idonta ta rasa dalili, wayarsa dake gunta ta dauka ta kirasa, yayi mamakin ganin kiranta ya dauka yace "Wife!" Hade rai tayi tace "You made me lie to my mum, ni bana karya kasa nayi karya" sai kuma ta fashe da kuka, yace "Alryt, shknn yi xaman ki a gida kawai, it's nothing and i don't want you to lie because of me" daga haka ya katse wayar, jikinta yayi sanyi ta sake kiransa ya ki d'agawa, ta fashe da wani kukan ta xauna gefen gado, can kuma ta mike kamar mara laka ta shiga bathroom, wanka tayi ta fito ta shirya cikin abayarta tayi rolling, sosai tayi kyau duk da bata yi wani kwalliya ba, ta boye wayarta a jaka ta fito tana rike da jakar, Mumy dake shirin fita church tayi ma sallama ta fita driver ya ja ta xuwa inda tace wato gidansu Victoria, mintin ta sha biyar a gidansu Victoria ta sake kiran Abuturrab, wnn karan sai da ya kusa katsewa ya dauka, kasa cewa komai tayi amma kiris ya rage ta fashe masa da kuka, shi ma dai kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "ya aka yi samha?" Ta fashe da kukan da ke cin ta tace "Bayan kasa na fito gida shine ka ki daga kirana koh?" Da mamaki yace "kin fito da gaske? Kina ina" cikin rawar murya ta gaya masa, ya lumshe ido yace "Alryt, gani nan xuwa am sorry plss" daga haka ya katse wayar, shidda da 'yan mintuna ya iso anguwar, tun da ta fito gate yake kallonta har ta karaso ta bude gaban motar ta shigo, ya lumshe ido yace "Am sorry samha" bata ko kallesa ba ya tada motar suka bar gun, wani babban gun make up taga yayi parking, ta kallesa tace "Me xa mu yi a nan?" Ya fito daga motar ya zaga ya bude mata ta fito tace "Me xa mu yi a nan mana" Yace "Follow me ko kuma in kama hannun ki" daga haka yayi gaba ta bi bayansa kamar xata yi kuka, babba ne gun kwalliyan sosai, har kunshi ana yi da gyaran gashi, matar dake gun da alamar ita ce me gun tayi masu sannu da xuwa da fara'a ya nemi kujera ya xauna, Samantha ma ta xauna sai dai duk gabanta faduwa yake, Abuturrab yace "Madam light make up nake son ayi mata...." Samantha ta hade rai tace "Make up kuma!" Bai kalleta ba yace "Xan je in dauko kayanta yanxu...." Matar tace "Muna gyaran gashi da kunshi na amare, bari in kawo maka list ka ga bbu abinda bama yi a nan" Abuturrab yace "No ba sai an kawo ba, a gyara mata gashi kawai sai make up" daga haka ya mike yana ma Samantha wani kallo da manyan sexy eyes dinsa har ya fita, ji tayi kamar ta rusa kuka, nan matar da yaran gun suka taho don yi mata abinda yace. Sai bayan magrib ya dawo rike da leda ya mika ma matar yace "A dan yi sauri madam lkci ya wuce" babu yanda samantha ta iya haka ta bi matar. Gown ce me d'an karen kyau ja with long sleeves, mai ratsin silver daga saman wuyar kawai, dama gata fara gown din ya wani haska ta sai ka rantse amarya ce, gashi kamar an auna ta, ya fito mata da shapes dinta tun daga sama, tayi kyau iyakar kyau, ga gashinta da aka gyara mata bakikirin da shi ya xubo har kasan wuyarta, matar sai maa sha Allah take cewa tana kallonta, necklace ta sa mata da earrings suma silver sai bracelet da wristwatch, ta fiddo takalmi me ratsin ja da silver ta bata ta saka, matar da samantha ta gama tafiya da imaninta tace "Ya sunan ki 'yan mata?" Samantha ta sunkuyar da kai a karo na farko da taji wani iri tace mata sunanta Samantha, murya can kasa tace "Samha!" Matar tace "Ki gode ma Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login