Showing 78001 words to 81000 words out of 180592 words

Chapter 27 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1177

fita taga har ya kusa balcony, ta bi bayansa da sauri, nan bakin kofa ta gansa durkushe sai kkrin amai yake ya kasa, ji yyi gaba daya cikinsa ya hautsine amma ya kasa amai, ga wani mugun bugu da xuciyarsa ke yi, ta durkusa gabansa ta rikosa hankali tashe tace "Me ya faru doctor, baka son abincin ne, ni da khadija fa muka yi..." Bai iya ya ce komai ba, jin hannunsa a shoulder dinsa yasa shi fara jin saukin abinda yake ji, ganin ya fara nutsuwa yasa tayi shiru tana kallonsa, a hankali ya dago idonsa da yayi jajir yana kallonta, sauke idonta kasa tayi, sai ji tayi ya rungumeta, tayi lamo jikinsa tana jin bugun xuciyarsa, duk yanda ya so bude baki yayi mata magana kasawa yayi, lkci daya hawaye ya kawo idonsa, ta dago a hankali ganin haka sai ta fashe da kuka, cikin sanyin murya yace "I love you Samha, i will be nothing without you... Kar ki bari son ki ya xama ajalina, don't make me a living dead...." Ta rungumesa cikin kuka tace "Why is all this happening to us... Why did you teach me how to love you deep...." Saketa yyi ya goge fuskarsa jin motsi a balcony ya mike tsaye sai ga Ummi ta shigo, wani kallo take masa daga sama har kasa strictly tace "What happened?" Rasa abinda xai ce mata yyi, tace "Baka ji na ne boy?" Da kyar yace "Mami... Ji nayi i want to throw up...." Kallon Samha da ta tashi tsaye ita ma tayi ta hade rai tace "Me kika xo yi nan?" Kamr xata yi kuka tace "Ummi, naga..." Kofa Ummi ta nuna mata tace "This shud be ur last, kada ko da wasa ki sake shigowa nn, leave now" A hankali tace "Toh Ummi..." Daga haka ta fita, Ummi ta kallesa tace "If you like throw up till tomorrow...." Daga haka ta juya tayi ficewarta, ya jingina jikin bango xuciyarsa na bugawa. Samha na komawa bata yarda ta je dinning ba tayi shigewarta dakinsu Khadija ta kwanta duk jikinta yyi sanyi, har ta fara bacci Khadija ta tada ta wai ta tashi tayi Isha, mikewa tayi ta shiga bayi. Karfe goma Yusuf ya shiga bedroom din Umminsa, as usual tana aiki, ya xauna tace "Ya aka yi Barrister..." Ya shafa kai yace "Gobe Abba xai taho week end ko Ummi?" Ta girgixa kai tace "Sai next week" yace "Okay, Ummi wai Aliyu ashe matarsa ce yarinyar nn" Ummi ta kallesa tace "Wa ya gaya maka?" Yace "Khadija..." Ta girgixa kai tace "Ba matarsa bace...." Lumshe ido yyi na kusan second biyar kafin ya bude a hankali, shiru Ummi tayi kamar bata so fadin hakan ba, duk yusuf na lura da ita, can tace "Amma ba wai nace kaje ka fada masu bane, i mean ur siblings, shi kuma you don't say anything to him about it... Yanxu ka tashi kaje can part din nasa sai ku kwana tare" da sauri yace "Why???" Ta kallesa tace "Sbda ina son ku yi xumunci sosai, he is very good nd brave..." Yace "A ina ma kika samo sa Ummi?" Tace "You leave now, sai da safe... You've interrupted me enough...." Murmushi yayi ya mike yace "Aiit Mother, sai da safe... But in ji dai bai da ji da kai, idan naga haka xan dawo inyi kwanciyata a nan" murmushi tayi tace "No, he is nyc son" sai da safe Yusuf yyi mata ya fita, a parlor ya kusa cin karo da Samha da taje dauko ruwa kitchen ta koma baya da sauri, ya koma gefe yace "Yi wucewar ki..." Gefensa ta bi ta wuce kanta a kasa, shi kuma ya nufi kofa da system dinsa xuwa part din Abuturrab, kwance ya samesa parlor Abuturrab ya mike xaune ganinsa, Yusuf yace "Hi Dr, came to spend d nyt here, hope m welcome..." Murmushin karfin hali Abuturrab yayi yace "Of course you are Brrstr..." Yusuf yace "Ohh tnx..." Daga haka ya xauna gefen Abuturrab yana kkrin kunna system dinsa yace "As I've said before, i am yusuf, born nd brought up in Abuja... I school in Uk, i soo love football" daga haka ya kalli Abuturrab dake kallonsa, Abuturrab yace "Uhn! That's nyc... I was born nd breed in kano, studied Medicine nd Surgery in Uk, amm may be i do love table tennis, and.... Snooker" dariya yusuf yyi ya kai masa Knuckle, Abuturrab ya dunkule hannunsa yana murmushi ya kai kan nasa, Yusuf yace "It's nyc meeting you...."

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By Khaleesat Haiydar=???
'
44.....
Abuturrab ne ya fara mikewa bayan awa daya yana kallon Yusuf yace "If you er done sai ka shigo ni xan kwanta yanxu" Yusuf yace "Aiit...." Daga haka Abuturrab ya shiga daki yayi kwanciyarsa sai dai ya kasa bacci, ya rasa me ke masa dadi a duniyar, har Yusuf ya shigo bayan kusan minti talatin bai yi bacci ba, sae dai idonsa a lumshe suke, Yusuf ya shiga toilet ya dauro alwala snn ya fito yayi kwanciyarsa. Da asuba kusan a tare suka tashi duk suka yi alwala suka fita xuwa masallaci, ko da suka dawo yusuf ya koma yayi kwanciyarsa shi kuma Abuturrab ya shiga bathroom. Kafin karfe bakwai har ya gama shirinsa, bai tada yusuf dake bacci ba ya dau makullin motar dake gun sa ya fita, yana warming motar yaji an kwankwasa masa glass ya daga kai ya ga fatima ce tsaye, ya dauke kai snn ya sauke glass din, ba tare da ya kalleta ba ya shiga jiran jin abinda xata ce, a takaice tace "Good morning" har lkcn bai kalleta ba yace "Morning how you?" Tace "Ummi tace in kira ka" yace "Ohk..." Juyawa tayi ta bar wajen, sai a snn ya daga kai ya bi ta da kallo, can ya bude motar ya fita ya nufi part din Hajiya, yana shiga parlon ya xauna, Ummi ta fito daga kitchen ya sauke kai kasa ya gaida ta ta amsa tace "Baxa kayi break ba boy?" Yace "Xan yi a office..." Tace "A'a ka jira dai kayi kafin ka tafi ka ji... Me ya same ka jiya wai?" Daga kai yayi ya kalleta yace "Ba komai Mami, am ohk now..." Kallonsa kawai take bata ce komai ba, can dai tace "Shknn ka je khadija xata kawo maka kayan karin, naga kamar baka son cin abinci a nn koh?" Murmushi yayi ya mike yace "Toh nagode Mami" daga haka ya mike ya fita, karasawa yayi ya kashe motar snn ya shiga parlonsa ya xauna, bayan kusan minti bakwai aka bude kofar, daga kai yayi yaga fatima ce ta shigo rike da tray na breakfast, ya kauda kai har ta karaso ta durkusa gabansa ta ajiye tray din, ta dau cup xata bude flask ya dakatar da ita yace "No.. No kiyi tafiyar ki...." Bata tanka sa ba ta bude flask din xata xuba ruwan shayi a cup din, yace "Wai ba kya ji ne, i said..." Dago kai tayi tayi masa wani kallo ta xuba ruwan a cup snn ta rufe flask din ta shiga hada tea'n, mamaki ne ya cika sa, tana gama hadawa, ta ajiye gabansa ta bude plate din dake dauke da Irish da kwai sai plantain, snn ta mike tayi ficewarta ya bi ta da ido, can yayi tsaki ya dau tea din. Damuwa bai barsa ya ci break din da yawa ba kawai ya mike daga karshe ya fita ya hau mota ya fice xuwa office. Khadija da Samha na shirin tafiya islamiyya Ummi ta shigo dakin, tana kallon Samha tace "Ki bari gobe ki je Samha... Ita khadija ta yi wucewarta" Samha tace "Toh" Khadija ta turo baki tace "Sbda me Ummi.... Yau fa kika ce xata fara" Ummi bata tanka ta ba ta fita, haka khadija ta gama shirinta ta wuce ita kadai ba don ta so ba, Samha kam tayi kwanciyarta don dama duk sai taji ma xuwa islamiyyan ya fita kanta... Tana kwance ita kadai dakin aka bude kofa ta kalli Kofar, Yusuf ne tsaye wajen ganin ita kadai ce dakin bai karaso ba yana kallonta yace "Good morning" ta mike xaune tace "Ina kwana..." Ya d'an yi murmushi yace "Kin tashi lfya?" Sunkuyar da kai tayi ya juya ya fita ta koma ta kwanta, mai aiki ce ta shigo tace mata Ummi na kiranta, ta dau hijab dinta ta sa ta fita xuwa bedroom din Ummi, xaune ta ganta gaban computer, ta xauna kasa tace "Ga ni Ummi..." Ummi ta kalleta tace "Tashi kiyi xaman ki sama..." Ba musu ta mike ta koma gefen gado, Ummi tace "Samha..." A hankali ta dago tana kallonta tace "Na'am" Ummi tace "Duk tambayar da xan maki ki fada min gaskiya, kar ki ji shakkan komai kin ji daughter...." Samha ta gyada mata kai, Ummi tace "Do you have interest for islam?" Kallonta kawai Samha take bata ce komai ba, Ummi tace "Talk to me dear..." Hawaye ne ya cika idonta, a hankali ta girgixa kanta alamar A'a, shiru Ummi tayi tana kallonta, can tace "Baki da interest knn?" Samha ta gyada mata kai, Ummi tace "Toh me yasa kika yarda kika biyo Aliyu" hawaye sosai take yi, ta kasa cewa komai, cikin sanyayyan murya tace "You take me as ur mother Samha, tell me what's in ur mind kar ki ji komai...." Samha ta shiga goge fuskarta bata ce komai ba, Ummi tace "Tell me why did u follow him bayan baki da ra'ayin addinin islam..." Murya can kasa tace "I don't know... Buh i know i love him shi yasa na biyosa, snn ya taba ce min in yi addinina yayi na sa...." Da mamaki Ummi ke kallonta, can tace "Toh me yasa kike sllh, har kike sha'awar shiga islamiyya, kuma wa ya koya maki sllhn?" Wasu sabbin hawayen suka kawo idonta cikin rawan murya tace "Aunt dina dake kaduna musulma ce ita ta koya min sllh, she is my dad's younger sister...." Ummi tace "Toh islamiyyan da kike son shiga fa?" Shiru tayi bata ce komai.... Ummi tace "Talk daughter" ta share idonta a hankali tace "Kawai dai ina son xuwa ne...." Ummi tace "Toh kince you don't have interest for islam me yasa kika yarda da musulmi kika amince masa har kika biyosa kin san baki son musulinci?" Kuka ta shiga yi a hankali, Ummi tace "Kuka kuma? Ni ban ce ki min kuka ba Samha...." Bude kofar dakin aka yi Yusuf ya shigo da sallama... Kallonsa Ummi take, shi ko idonsa na kan Samha barin da yaga hawaye idonta, Ummi tace "Ya aka yi Yusuf?" Kallon mum din tasa yayi snn ya kalli Samha, da harshen fillanci yace "Ummi kukan me take yi? Me ya faru?" Sharesa Ummi tayi ta kunna computern gabanta, Samha kam bata dago kanta ba, can Ummi ta kallesa da yaren ita ma tace "You leave now...." Da damuwa yace "But Mum she is crying...." Hade rai Ummi tayi hakan yasa ya juya ya fita kawai, Ummi ta kalleta ganin kukan gaba yake karawa cikin sanyin murya tace "Tashi ki je Samha we'll talk later" kamar jira take ta mike da sauri don da alama bata son xancen ta fita daga dakin Ummi ta bi ta da kallo cike da tausayinta. Daki ta koma tayi kwanciyarta, tayi kukanta me isarta snn bacci ya dauketa.

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By Khaleesat Haiydar=???
'
45.....

Sai bayan Khadija ta dawo daga islamiyya Ummi ta wuce clinic don bata son barin Samha ita kadai, karfe uku saura Abuturrab na xaune office yana attending ma patient kiran Ummi ya shigo wayarsa, dauka yyi ya kai kunne hade da yi mata sallama, Ummi ta amsa tace "Kana office boy?" Abuturrab yace "Ehh Mami..." Tace "Toh ina jiran ka" daga haka ta katse wayar, yana sallaman patient din ya mike ya fita xuwa office dinta, sai da tayi masa izinin shigowa bayan ya kwankwaso kofar snn ya shiga da sallama, kallonsa take ganin yanda ya rame sai taji tausayinsa ba kadan ba, ya karaso kansa a kasa ya xauna kujera yace "Gani Mami" ajiyar xuciya ta sauke tana kallonsa har lkcn tace "You will think i'm mean ko boy, ko daya wllh am only trying to put u on d right way ne, kaga yarinyar nn ba muharramar ka bace, it's nt decent it's nt proper ku xauna roof daya da ita... Kasan da haka kuma, ni ban ga laifin ku ba Aliyu, nasan soyayya gaskiya ce amma tunda har ka buda min cikin ka i can't continue watching u disobey Allah, ina son ka tamkar d'an da na haifa a cikina right frm d time i saw u... Yanxu kai ka gaya min me xuciyar ka ke raya maka a kan yarinyar nan... What's d next step u wanted taking kafin abinda ya faru ranan da daddare" bai iya ya dago kansa ba cikin sanyin murya yace "Mami ni bani da niyyar cutar ta aurenta nake son yi...." Ummi tace "Aure? Ta ya amma" ya langwabar da kai yace "Kin ga idan na aureta conversion dinta xuwa islam baxai dau lkci ba..." Murmushi Ummi tayi tana girgixa kai tace "Na xaunar da ita mun yi magana daxu kasan abinda tace min?" Girgixa kai yayi, Ummi ta ci gaba "She said she don't have interest for islam boy, haka tace min, na kuma yi mamakin jin hakan" Da sauri Abuturrab yace "Noo Mami, she's just confuse ne wllh, buh wanda bai da interest ae baxai dinga sllh ba, kinsan Mami tun da dadewa fa na rabata da duk wani abu da xai dinga kusantarta da Christianity, kuma duk ta hakura ta bari" Ummi tace "That's because she love's you, soyayya yasa ta biye maka boy" yace "No Mami baya ga soyayya ma idan mutum har xuciya yake abun sa ai bbu abinda ya isa raba sa da shi.. Her dad was a muslim then fa, kakanta ma Musulmi ne har ya rasu, kawai mahaifinta bai da rabo ne, amma in shaa Allah shi ma xai dawo hanya madaidaiciya, uwar ta kam dama ba a magana tayi nisa sosai" Ummi dake ta kallonsa ta gyada kai cike da gamsuwa tace "Haka ne boy, na kuma lura abinda yasa ta fara loosing interest sbda nisanta ku da juna da nayi ne, buh i have no other alternative kada in xamo uwar banxa, abinda baxan bar d'a na yayi ba to d'an wani ma baxan bari yayi ba.... Kuma xancen xaka aureta ynxu bai taso ba boy, ka bari sai ta amshi islam don kanta ba don auren ka ba... Xaka aureta amma not so soon, ynxu dai ka dinga yawan shigowa a kai a kai ta daina jin kadai cin da take ji, komawanta can ne dai baxae taba yiwuwa ba, kai da Yusuf kuyi xaman ku a can tunda xai jima sosai a nan, one more thing boy pls pls ka daure kaje gida ko don mahaifiyar ka..." Kallonta yayi da sauri yace "Sai ince Samha tana ina, baxa ki gane ba Mami ai ina kai kaina gida yanxu ni nasan kano yayi ma Abbana kadan yyi min hukunci sae dai Abuja, xan je gida amma ba yanxu ba" kallonsa kawai Ummi take, can ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shknn boy, kai ma ka rage ma kanka damuwa bana son kana raman nn, Samha dai ba rabaka nayi da ita ba, duk lkcn da kake son ganinta sai ka shiga har hira ma kuyi, i won't stop that" ya d'an yi shiru sai kuma yace "Toh Mami nagode, amma plss let this continue to be a secret btwn us bana son a san she's nt my wife" da damuwa ya kare maganar, Ummi ta gyada kai tace "Alryt boy" a hankali cikin sanyin murya yace "Mami... mami ko yusuf ma fa kar ki ce masa ba matata bace...." Shiru Ummi tayi tana kallonsa, Gabansa ne ya fadi sosai ganin kallon da take masa, sai kuma tayi saurin gyada kai tana murmushi tace "Aiit, u can leave now boy.... I will let no one know" Mikewa yayi ya mata sallama ya fita, for the 1st time tun bayan faruwan incident din ranan yaji hankalinsa ya kwanta sosai. Fatima ce xauna balcony da kawayenta biyu handouts a gabansu Khadija da Samha suka fito, Khadija tace "Sister xa mu je siyo airtime..." Fatima tace "Ohk" Bin su da kallo fatima tayi suna yin nisa billy tace "Kin ki gaya min dalilin dawowar yarinyar nn part din ku..." Fatima tace "How many times do i have to tell you nima ban sani ba kuma ban san ta yanda xan sani ba Billy, I've snooped, I've put an eye all to no avail.. Ummi ba gaya min xata yi ba, that silly khadijah of a being ma ko da tasan abu she won't tell me" farida tace "Buh guy din ya fara sake maki kuwa?" Fatima bata ce komai ba ta dau handout din gabanta, Billy tace "i have a plan for you teemah..." Yusuf na xaune karkashin artificial tree dake compound din gidan yana waya amma idonsa da hankalinsa na kan Samha da khadijah dake tahowa, Samha ta saci kallonsa suka hada ido ta dauke nata da sauri, khadija tace "Yaya xa mu je siyo card..." Yace "Card?" Tace "Eh, airtime" yace "Ohk, taho in maki transfer" Tace "Toh yayana thank you..." Daga haka ta kama hannun samha suka nufi inda yake, kujera ta ja ta xauna tana kallon Samha ta dauko mata wani kujerar tace "Sit" Samha ta kirkiri murmushi ta girgixa kai tace "Thank you" Yusuf dake kallonta yace "Why?" Bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, yace "Ki xauna" bbu yanda ta iya haka ta xauna kan kujerar, yana danna waya yace "1000 ya maki yawa koh?" Ta xaro ido tace "Noo yaya, ya isa fah" yayi murmushi yace "Tohm! Waec bai fito ba har ynxu koh" tace "Ehh muna ta jira..." Samha dai kallonsa kawai take, height dinsu xae xo daya da Abuturrab haka ma haskensu, tana kkrin tantance wanda ya fi kyau cikinsu ya dago kai ya ga tana kallonsa, mikewa tayi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login