Showing 96001 words to 99000 words out of 180592 words

Chapter 33 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1152

na yo nan a guje...." Tsit yyi ganin Sojojin sun shigo suna tahowa Balcony, wasu kuma sun xaga baya, wasu na tsaye daga gate, Hajiya Mariya ta wani murtuke fuska ganin Abban Abuturrab don shi ne ma gaba, gabanta ya isa yace "Ki ban number mai gidan ki mun shigo masa gida ba izini..." Tace "Ko me ya janyo hakan?" Yace "Za ki sani nan ba da dadewa ba, basu hanya su shiga...." Ta girgixa kai tace "Babu wannan xancen Abban Ramla, ya xa ku
shigo min gida haka ina matsayin matar aure mai gidana bai nan, wannan ko ni nace Aliyu ya bar gida da yar mutane sai haka ai, ni wllh ina ganin mutuncin ka a matsayin ka na mijin yayata banda haka bbu abinda xai sa na ci gaba da daukan wnn cin fuskar haka...." Wayarta ta latsa a fusace ta kira Mami, Mami na dagawa tace "Yaya kiyi hakuri, amma gaskiya bana son wnn abinda Abbansu Ramla ke min, duk fadin kano ya rasa warce xae dinga xargi kan barin Aliyu gida sae ni, a kan wani dalili xae kwaso min bariki guda na soldiers ya shigo min gida ko mai gidana bai sani ba...." Mami dai na sauraranta bata ce komai ba sai dai ita ma gaba daya ranta yyi mugun baci, katse wayar tayi tace "Toh sai ku shiga ku fiddo Aliyu...." Daga haka ta fice fuu ta bar masu gidan gaba daya. Hakan bai hana Abba yasa an duba masa gidan ciki da bai ba amma bbu Aliyu bbu alamarsa. Sae bayan Magrib ya koma gida, har lkcn kuma xuciyarsa ta kasa yrda cewar Aliyu bai je gidan Hajiya Mariya ba, har karfe tara Mami bata je part dinsa ba, abinci ma su Ramla tasa suka kai masa, tun da suke bata taba yi masa irin haka ba, da yaso sharewa amma kawai ya tashi ya tafi can dakin nata, tsaye yyi bakin kofa yace "Hajarah baki ji dawowata bane?" Tace "Gaskiya, don na bada tare da Aliyu xa ku dawo gidan nan yau..." D'an murmushi yyi ya juya ya fita daga dakin.

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
59.....
Bayan magrib Aliyu na kwance Sadeeq ya kira Zainab, basu ji ma suna waya ba yace ta ba Samha wayar, tana mika mata ya kalli Abuturrab ya mika masa wayar yace "Ur wife" mikewa xaune Abuturrab yyi ya karbi wayar, Sadeeq ya mike yace "Let me get us something to eat" daga haka ya fita, Abuturrab ya kalli screen din wayar jin shiru yaga har lkcn ba a katse ba, A hankali yace "Assalamu alaikum" duk da yasan it's wrong, Samha dake xaune dakin tare da Zainab da kanwarta ta sunkuyar da kai bata ce komai, murmushi Zainab tayi ta mike ta fita Hafsat ta bi bayanta, Abuturrab yasan tana jin sa hakan yasa yayi shiru shi ma, jin shirun yasa cikin sanyin murya tace "Ina yini?" Ya langwabar da kai yace "Baki amsa sallama ba wife?" Murmushi tayi kmr yana ganinta tace "Peace be unto you too" ya wara ido yace "That's sweet baby, how you?" Tace "Lafiya lau" yace "But do you like it there?" Gyada masa kai tayi kamar yana ganinta tace "Yeah" yace "How about the cramps?" Tace "Da sauki" d'an shiru yyi kafin yace "Kin ci abinci kuwa" tace "Mun ci yanxu" ya lumshe ido yace "Baby you re now mine" bata ce komai ba don bata ma gane abinda yake nufi ba, yace "An daura auren mu daxu...." Dago kai tayi da sauri tayi shiru, lkci daya mood dinta ya canxa, a hankali yace "Samha!" Nan ma bata ce komai ba, yace "I know you re there" Da kyar ta bude baki tace "ban gane bane" Yace "You are now my wife in shaa Allah" tace "How?" Yar dariya yyi yace "I will explain better idan na xo yarinya" Bata kuma ce masa komai ba, yaso ce mata yana kano amma ya fasa don bai son daga mata hankali, yace "Gobe xan xo idan Allah ya yrda kin ji Babynah" "Toh" kawai tace masa yace "Kin sha drugs din ki?" Tace "Na sha" yace "Good, sleep tight wife, xan inyi isha yanxu" tace "Toh" ya kuma yi mata sai da safe ya katse wayar. Washegari shi ya kira Hajiya Mariya, nan ta gaya masa inda xa su je wato gidan wata kawarta. Karfe goma sha daya suka isa gidan suka tarar har ta je tana jiransu, bayan sun gaisa yake tambayarta Mami fah, tace "Tana hanya, yanxu na kirata, kun karya kuwa?" Ya gyada mata kai yace "Mun yi break Mum" Sai kusan sha biyu Mami ta iso gidan, da yake tun kwanaki biyu da suka wuce tace ma Col xata fita da wnn excuse din ta fito yana bacci ma ta baro gidan, tun da Abuturrab yaji shigowarta gabansa ya shiga faduwa, Sadeeq kam kallonta yake don ya santa years back, ta karaso parlorn tana kallon Abuturrab fuska daure, ba tare da ya kalleta ba ya mike tsaye duk jikinsa yyi sanyi sosai, karasawa yayi gabanta ya rungumeta, duk yanda ta so hanasa yin hakan kasawa tayi, ji tayi duk wani bakin ciki da ta shiga a baya tun barinsa gida ya gushe lkci daya a xuciyarta jin d'an nata a jikinta, a hankali tayi karfin halin janyesa jikinta, ya durkusa kan kneels dinsa ya hade kansa da kafafuwanta yace "Forgive me Mami, i know i failed you, i disappointed you, i caused you go through a lot...." Tuni hawaye ya kawo idonta ta durkusa gabansa tace "Why did you choose to make me look at fault always, Why Haiydar, me yasa baka san farin ciki na, me yasa baka jin ddi idan baka sa ni cikin matsala one way or the other ba" bai iya ya dago kansa ba, Mikewa Sadeeq yayi ya fice daga parlon don bai ma son ganin scene din sak irin yanda suke da mahaifiyarsa ko da yaushe, Abuturrab kam bai iya ya dago kansa ba jin furucinta, jin hawayensa a kafarta ta dagosa tana kallon fuskarsa, tun bayan tasowarsa yau ce rana ta biyu da ta kuma ganin yana hawaye, ta dake tace "Daga ina kake Aliyu?" Sunkuyar da kansa yayi a hankali yace "Kaduna" Ji tayi kamar ita ma ta fara hawayen ganin irin ramar da yyi, wannan wani irin so ne Aliyu ke ma yarinyar nn har yake neman hallaka kansa, hannunsa ta kamo cikin sanyin murya tace "Ina yarinyar take Ali?" Sai a snn ya kalli kwayar idonta ya ga damuwa karara cikinsu, ya lumshe ido cikin rawar murya yace "Ki yafe min plss Mami, sbda fushin ki gare ni babban masifa ce, na tuba Mami" Mami tace "Ce maka nayi ina yarinyar mutane? Ina ka kai ta?" Ita kam Hajiya Mariya tagumi tayi haka kawarta dake xaune tana kallonsu, Abuturrab ya kalli small mum din tasa snn ya sunkuyar da kai cikin sanyin murya yace "Tana kaduna Mami" Mami ta dago kansa tana kallonsa tace "Toh in har na isa da kai ka koma yanxu ka maidota!" Ya daura fuskarsa a kanta hawaye na sakko masa cikin sanyin yace "Don Allah kar ki ce min haka Mami, wllh baxan iya rabuwa da ita ba, ki min rai, i can't do without her....." Jikin Mami yyi sanyi ta daga kai tana kallon Hajiya Mariya, Tuni hawaye ya kawo idonta tace "Toh me kke nufi da mu Aliyu, ya kake son mu yi maka, wnn wace masifa ce ta same ka" Da kyar yace "Mami ba masifa bace sonta kawai nake tsakanina da Allah" Mami da hawaye ya shiga sakko mata tace "Waye kke tunanin xai bar ka ka aureta Aliy, Abbanka ko Yakumbo ko kuma iyayenta?" Girgixa mata kai ya shiga yi har lkcn kansa na jikinta a hankali yace "Mami addu'ar ki gare ni xai sa komai ya xo min da sauki, Support me my world" Shiru Mami tayi, hakan yasa ya dago kansa da yayi jajir yana kallonta, tausayin dan nata ba kadan ba ta dinga ji har cikin ranta, wanda hakan yasa hawayenta ya ki tsayawa, Hajiya Mariya mikewa tayi ita ma hawayen idonta ta bar wajen, rungumeta yayi cikin rawar murya yace "Mami ni ban san irin son da nake mata ba....." Shafa kansa Mami tayi tace "Ai so ba hauka bane son, yarinyar nn ba muharramar ka bace amma kke xaune da ita gida daya ka mance koyarwar addinin ka" ya girgixa kai yace "Mami i tried my best ban saba ma ubangijina ba throughout our stay together, kuma Mami...." Kasa karasawa yayi don bai san yanda xata dau xancen ba, ta dago kansa tana kallon kwayar idonsa tace "Kuma me?" Sauke idanuwansa kasa yyi a hankali yace "She's now my wife..." Kallonsa Mami take ko kiftawa bbu, can tayi karfin halin cewa "How?" Cikin sanyin murya yace "Daxu mijin kanwar Abbanta yasa aka daura auren, they re muslims" Mami bata iya tace komai ba sai dai wasu sabbin hawayen ne ke sakko mata, hade kansa ya kuma yi da kafarta shi ma hawayen na sakko masa, da kyar tace "Aliyu har xa a daura maka aure without consent dinmu..." Ya girgixa kai yace "Forgive me mother, i knw i failed you, kar ki yi fushi da ni, I've gone through a lot, kullum hankalina ba kwance yake ba, amma idan kin ce in saketa..." Shiru yayi sai kuma cike da karfin hali yace "Sae in saketa, i won't fail you again, amma nasan da sonta xan bar duniyar nan, Allah ne ya jarabbceni mami, nasan tun tasowata nake sa ku magana amma kinsan Mami tunda nake ko frnds Christian ban son yi, ban taba shigowa gida da nonbeliever ba bana son su, i don't like them, sai gashi lkci daya, i knw jarabawata kenan a duniya...." Hawaye yake sosai, Jikin Mami yayi sanyi sosai ita ma hawayen take tace "Allah yasa hakan shine mafi alkhairi Aliyu, na yafe maka, dama ni baka min komai ba, Allah ubangiji ya hada kanku, ita kuma Allah yayi mata rahama.... Allah ya sassauta lamarin ya huci xuciyar Abban ka" Rungume Mami yayi ya ma rasa abinda xai ce mata, Kawar Hajiya Mariya dake xaune ita ma ta ci nata kukan tana murmushi tace "Toh yaushe xa a kawo mana amaryar Ali" Kallonta yyi, yyi murmushin karfin hali yace "Idan Allah ya yrda" Mami na share fuskarta tace "Ku fara shirin barin garin nan yanxu" daga haka ta mike tana kallon Hajiya Farida dake xaune tace "Ki kira min Mariya don Allah" Hajiya Farida tace "Ki shiga tana daki Mami" Dakin Mami ta nufa, Hajiya Farida tace "Allah sanya alkhairi Ali, ka yi kkrin kyautata mata yanda xata yi sha'awar addininmu don kanta, Allah bada xuri'a dayyaba, ya huci xuciyar iyayenku" Bai iya ya dago kansa ba yace "Ameen mum nagode" ba a dau lkci ba Hajiya Mariya suka fito da Mami, Hajiya mariya ta karasa gabansa ta xauna tace "Idan Allah ya yrda xan xo inda ku ke Son, Allah bada xaman lfya, amma kada ka cuceta Ali" sunkuyar da kai yayi bai iya yace komai ba, Balcony Mami ta nufa ta sami Sadeeq xaune, yana ganinta yyi kasa da kai yace "Umma ina yini?" Murmushi tayi tace "kai ma ka ki girma har ynxu ko Abbakar, ka biye wa Aliyu kuna ja ma kanku fitina gun mahaifan ku koh?" Bai dago kai ba illa murmushi da yake yi kawai, tace "Allah ubangiji ya shirya min ku gaba daya..." Sai kusan karfe biyu Abuturrab suka fara shirin barin kano, Mami ta kuma yi masu nasiha sosai ta dau atm card dinta ta basa duk jikinta a sanyaye sai taji kamar kar ya tafi, yaji ddi sosai ya rungumeta, Hajiya Mariya ce ta kai su har Park ta jira sai da motar ya tashi snn ta juya ita ma a sanyaye ta koma gida.

*Haske writers asso*

Afuwann!!
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
60.....

Tunda suka baro kano Abuturrab ke bacci har suka kusa Zaria, Sadeeq kam ya samu wani gaye sai hiran kwallo suke a motar, shi ya tada Abuturrab da suka isa Zaria, bayan sun sauka ya kalli Abuturrab ganin mood dinsa yace "But you ought to be happy frnd kun yi reconciling da Mum fah, why the dullnes" Abuturrab ya d'an yi murmushi yana shafa kansa a hankali yace "Am having headache Sadeeq, it's all stress" Sadeeq yace "Allah ya sauwake, xa mu je can gidansu Zainab ynxu koh?" Kai Abuturrab ya gyada masa, sae da suka yi la'asar snn suka shiga gidan bayan sun isa, har parlor aka yi masu iso, Kanwar Zainab ta kawo masu ruwa da lemo, ba a dau lkci ba mum dinsu ta fito, suka gaisheta da ladabi ta amsa da fara'arta tana masu sannu da xuwa, tana barin parlon Zainab suka fito tare da Samha, tun kan su karaso parlorn Abuturrab ke kallon Samha ko kiftawa bbu, Abaya ce jikinta baki yayi mata kyau ba kadan ba ta daura veil dinsa a kai, d'an wet lip ne kan pinkish lips dinta, ya sauke idonsa kan fingers dinta da aka yi ma jan lalle da ya haska su, duk sai yaga tayi masa kyau ba kadan ba, Gefen Zainab ta xauna ta d'an saci kallonsa ganin kallonta yake tayi kasa da kanta, murmushi dauke fuskarsa ya amsa gaisuwar Zainab, Samha ta kalli Sadeeq cikin sanyin muryarta tace "Ina yini" yyi murmushi yace "lafiya lau, ya ki ke" tace "Lafiya" Abuturrab dake kallon Samha har lkcn yace "Good evening ma'am" murmushi tayi tana wasa da fingers dinta tace "Ina yini" bai amsa ba ya dau glass ya debi ruwa ya fara sha, yana ajiyewa ya kalli Sadeeq yace "Frnd xa mu tafi ynxu ne ko sai ltr" Sadeeq yace "As you wish" Zainab tace "Kar ku ce min yau xa ku wuce min da sabuwar kawata" dariya Sadeeq yyi yace "Sabuwar kawar ki kuma amaryar Abokina ba..." Ta d'an buda ido tace "Toh Allah ya nuna mana lkci" yace "Lkci ya xo har ya wuce ae, matar sa ce fa ko don ban fadi maki ba Soulmate" ta xaro ido tace "Are you kidding?" Ya girgixa kai yana murmushi yace "Am not!" Kallon Samha da taki dago kai tayi, kawai sae tayi murmushi tace "Wlh i taught we re of the same category, Allah sarki, i never knew she's married, Allah bada xaman lafiya" Sadeeq yace "Ameen, kin ga sae ku fara xumunci tun kafin mu yi namu auren koh" dariya tayi haka ma Abuturrab da yace "Toh Allah ya nuna mana" sai kusan karfe biyar suka bar gidan bayan an tilasta su sun ci fried rice da aka xubo masu, dubu goma Abuturrab ya ba sis din Zainab suka rakosu har bakin gate snn suka koma cike da kewar Samha don haka kawai Zainab taji tana burgeta ga ta da kyau sosai da kunya a cewarta. Suna isa titi Sadeeq yace "Frnd xan shiga kd ina da wani appointment... Ku kam dole ku kwana nan tunda Frnd din aunt dinta tace xaka kai masu ita..." Abuturrab yace "Yea, nasan kila they've being tryn calling me gashi na kashe wayar tun daxu" Sadeeq yace "Sae ka kira su ka sanar da su gobe xaka kai masu ita" Abuturrab yace "Alryt frnd" kallon Samha Sadeeq yyi yace "Toh amaryar mu xan koma kaduna, xa mu dinga gaisawa a waya, Allah ya sanya alkhairi...." Murmushi tayi ta sunkuyar da kai tana jujjuya ledan hannunta tace "Allah ya tsare hanya" daga haka Abuturrab ya basa hannu yace "Am soo grateful Abbakar Allah bar mu tare, you re a really a frnd in need, xan shigo kd kafin mu bar garin" Sadeeq yyi murmushi yace "Aiitt, Allah ya kawo ka" daga haka suka rabu Abuturrab ya bi sa da kallo sai yaji kmr kar ya tafi. Napep ya samu yace ya kai su nearest hotel, sai kallon Samha da taki barin su hada ido yake a Adai daitan har suka isa wani hotel me kyau, ya fito snn ita ma ta fito ya ba mai adai daitan kudi, ya kama hannunta da nufin su shiga hotel din ta warce hannunta, bai ce komai ba ya nufi gate din hotel din ta bi bayansa. Yana karbar masu daki aka basa makulli ya bar reception din, ita dai tana biye da shi, babban daki ne mai kyau da makeken gado, ganin tsaye tayi bakin kofa ya juya yana kallonta, taki barin su hada ido, murmushi yayi yace "Yar shariyar ce a kusa baby?" Kin cewa komai tayi ta ki kallonsa kuma har lkcn, bai kuma ce mata komai ba ya kunna Ac yyi kwanciyarsa, ko minti goma bai yi da kwanciya ba bacci ya daukesa, har fa lkcn Samhan ku na tsaye tana kare ma daki kallo, lkci lkci kuma ta kallesa, can dai da taga kmr baccinsa yyi ta karasa dakin ta ajiye ledan kayan hannunta ta xauna can karshen gadon tana satan kallonsa, can ta mike a hankali ta dawo gefensa ta xauna tana kallon fuskarsa, sosai taga ya rame lkci daya jikinta yyi sanyi, ta fi minti ashirin tana xaune wajen kafin ta sauka kasa a hankali ta kwanta kan tiles din dakin, har aka fara kiraye kirayen magrib tana k'asa kwance, jin xa a tada sllh ta mike xaune tana kallonsa, ganin ya juya kansa xuwa daya side din ta mike ta isa kusa da shi a hankali ta durkusa tace "Xa a tada sllh fah doctor" jin baxae taba jin ta ba a haka ta dan tabo hannunsa a hankali, dauke hannunta tayi jin jikinsa da xafi, ta mike ta karasa xuwa daya side din ga mamakinta sai taga idonsa biyu, durkusawa ta kuma yi gabansa da damuwa tace "Are you sick?" Murmushin karfin hali yyi mata a hankali yace "it's just headache dear" xaunawa tayi gefensa kamar xata yi kuka tace "toh baka sha magani ba kuma" mikewa yyi xaune da kyar yace "Xan sha" xata yi magana yayi mata murmushi ya kamo hannunta yace "I will be alryt baby, bari in je sllh xan siyo magani" daga haka ya tashi ya shiga bathroom, tana nn

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login