Showing 69001 words to 72000 words out of 180592 words

Chapter 24 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1181

"Za mu kai mata ziyara knn" da sauri tace "Da gaske?" Yace "Yeah sweety, amma ba yanxu ba" daga haka ya mike yace "let me Ablute..." Washegari kamar yanda Hajiya tace da wuri Abuturrab ya shirya yana 'yan dube dube a laptop, aka danna bell, Samha dake goge gogen parlon ta mike ta isa gun kofar ta bude, khadija ce tsaye tayi murmushi ganinta khadija tace "Ina kwana Anty Samha" Samha tayi murmushi tace "Lafiya lau khadija" khadija tace "Ki ce ma Uncle Ummi tace tana jiransa fa" Samha tace "To" snn ta juya ta koma parlon tana kallonsa tace "Wae Ummi na jiran ka" mikewa yayi ya rufe laptop din ya langwabar da kai yace "Ko mu je tare ne baby, ke fa kadai zaki xauna gida" murmushi tayi tace "It's nothing ai na saba..." Yace "Alryt da wuri xan dawo kin ji?" Kai ta gyada masa ta rakasa har bakin kofa yayi peck din goshinta, ta juya da sauri ta koma parlon ya wuce yana murmushi, A parking space ya tad??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????da ta tana jiransa, ya gaisheta ta mika masa car key din ya karba a xuciyarsa yace to da bai iya tukin ba fa, yana gama warming motar ta zaga ta shiga, duk wnn abun fatima na kallonsu ta window a daki, Ummi tace "Samhar fa?" Yace "Tana ciki Mami..." Tace "Duk xata ji bbu dadi ita kadae ga su fatima duk makaranta za su..." Murmushi yyi yace "Ae ta saba Mami" Sae da suka fita compound din tace "Ina matakin karatun ta ya tsaya?" Yace "Waec ta gama recently, but na kai ta tayi jamb registration nn garin" Mami tace "Good..." Daga haka ta dinga nuna masa inda xai bi har suka iso Clinic din, babba ne sosai asibitin, yana gama parking a space din da aka tanada don haka ta fito snn shi ma ya fita, ya bi bayanta xuwa reception, gaisheta nurses din dake gun suka dinga yi ta amsa ta nufi stairs xuwa office dinta, shi dai yana biye da ita har suka iso, Hadadden office ta shiga da shi, ta kunna Ac, ta yaye curtain snn ta xauna ta nuna masa kujera shi ma ya xauna, wayarta ta dauka ta kira wani likita, ba a dau lkci ba wani da baxae wuce Abuturrab ya shigo, ya gaisheta da ladabi ta amsa tace "A new doctor here, xa ayi employing dinsa a nn" Likitan me suna Shareef yace "Alryt, his qualificatios...." Ta girgixa kai tace "Forget that" ya gyada kai, snn ya juya ga Abuturrab ya basa hannu yace "Am Dr Shareef" Abuturrab ya karba hade da murmushi yace "Dr Aliyu" Dr shareef yace "Welcome to our clinic" Ummi tace "Office din kusa da naka xa ka bashi, idan Bashir ya dawo sai ya koma second flour" Dr Shareef yace "Alryt" daga haka ya kalli Abuturrab yace "Mu je Doctor" mikewa Abuturrab yayi yana kallon Ummi, ta dau makullin mota ta basa tace "Ba da dadewa ba xan fita meeting, when it's four sai kayi wucewar ka gida" yace "Toh ke fa Mami" tace "Akwai wani mota a nan xan fita da shi" yace "To nagode Mami" daga haka ya bi bayan Dr shareef suka fita, office din nasa madaidaici ne me dauke da table da office chair, snn da kujeru, sai show glass mai dauke da magunguna da injections a ciki sae gadon Anti Natal, da dai abubuwan da office din likita ke bukata, Dr Shareef yace "Hope you will like it here" Abuturrab yyi murmushi yace "In shaa Allah" Dr Shareef yace "Toh na bar ka lafiya" daga haka ya fita Abuturrab ya xauna kan kujera hade da lumshe ido. Kafin karfe daya patient din da yyi attending ma sun kusa goma, ana bude kofa ya hade rai, nurse din dai ce ta shigo da wani file kafin ta karaso yace "Ke doctors nawa ne a asibitin nn" kallonsa take bata ce komai ba, ya lura she derives pleasure looking at him, ya wani mugun hade rai yace "r you Daft?" Da sauri tace "Sir?" Kin cewa komai yyi yana kallonta fuskar nn tasa kamar hadari, tace "Amm, amm Doctors shidda ne sir...." Yace "Toh kar ki sake shigo min da file.... Fita" juyawa tayi ta fita, ya ja tsaki shi haushin irin kallon da take masa ma yake kawai. Kamar yanda Mami tace ana Asr yyi ma Dr shareef sallama, har ya kai bakin kofa ganin kallon da nurses din ke masa gaba daya ya juyo ya dawo, yace "I am Dr Aliyu, am gonna work here with you all for the mean time, yeah am very free nd friendly amma bana son kallo don Allah..." Daga haka ya juya yayi ficewarsa, wasu suka bi sa da harara, wasu kuma kamar idanuwansu xa su rakasu har gun motar. kusan a tare suka shiga compound da fatima a tata motar, yana gama parking a space dinsu ya kashe motar ya fito, ita ma ta fito da kawayenta biyu, ko kallon inda suke bai yi ba ya juya ya nufi part dinsa, duk suka bi sa da ido, Salima tace "Kaddai ku ce min shi ne" Fatima bata ce komai ba ta dau hanyar balcony dinsu, Billy ta sauke ajiyar xuciya tace "Shine mana" daga haka suka bi bayan fatima Salima na ta waigan Abuturrab da har ya isa part dinsa. Khadija dake parlor da Samha ta mike da sauri ganinsa tace "Sannu da dawowa Uncle" yayi murmushi yace "Yauwa khadija, how you?" Tace "Fine," Daga haka ta nufi kofa yace "Ina xa ki kuma" tace "Dama xan wuce ne" yace "A'a xo kiyi xaman ki" Shiru tayi bata ce komai ba ya kalli Samha yace "Ina yini Ma" murmushi tayi tace "Sannu da dawowa" yace "Thanks dear" daga haka ya shiga Bedroom, khadija ta dawo tayi xamanta parlon tana ci gaba da ba Samha lbrin da take bata. Kwance Abuturrab yyi Maminsa a ransa, haka kawai ya tashi da ita yau yaji ganinta kawai yake son yi, can ya mike xaune ya dau wayarsa, yyi jim kmr me nazari kafin yayi dialing numberta, yana fara ring gabansa ya shiga faduwa, Mami dake parlor ta rungume hannaye tana sauraren tijaran yakumbo, ba ayi ranan da xae wuce bata xo ta xaxxaga mata tsiyar ta fito da Aliyu ba, a da tana addu'ar Allah ya karkato hankalinsa ya dawo gida ko don xarginta da ake a kan tasan inda yake, amma yanxu kam addu'a ma take kar ya dawo don tasan duk inda yake he is fine don ya saba irin haka, matsalar daya ynxu da yar mutane da ya tafi banda haka ya shekara ma bai dawo ba in dai yana lfya ko a jikinta, dai dai nn wayarta ya shiga ring ta jawo da yake neman hanyar da xata bar parlon take duk da bakuwar number ne hakan bai hanata dauka ba upon maganar da yakumbo take cikin dag'a murya, Abba dai sai operating laptop yake, sallama Mami tayi Aliyu yyi shiru jin muryarta, har sai da ta sake maimaita sallaman, da kyar yyi gathering courage yace "Mami..." Sosai gabanta ya fadi jin muryarsa, ta mike ta kuma yin sallama kamar bata ji sa ba ta nufi stairs, a fusace yakumbo tace "Ahmad dubi ni ta tsallake ta wuce ina mata magana...." Abba ya kalli Mami da har ta kai stairs yace "Hajarah!" Ba tare da ta kallesu ba tace "Ina xuwa, Gwaggo na ce ke kira" daga haka ta wuce sama, Abba ya d'an kalli Yakumbo yace "Tana xuwa yaya..." Tabe baki tayi tace "Ta matse mata can, wato Ahmad ynxu shknn haka xa mu xuba ido an kasa sanin inda Aliyu yake, ni tsorona daya fa kar yaje masallaci a aura masa kafura mu shiga uku..." Sai ta fashe da kuka tace "Wllh Ahmad kaf xuri'ar mu kai ma kasan bbu tubabbe, wnn wace irin kaddara ce haka, mu Aliyu xae xuba ma duwatsu a ido, mu xae kunyata, mu xai toxarta?? toh wllh yyi kadan ko da ya auri yarinyar nn ko bayan raina sai an raba auren, mu xai haifa ma jikokin jaraba? Matsawar ina numfashi wllh wllh bbu aure tsakaninsa da tsinanniyar, ko ya aureta kuwa sae ya saketa, bare kullum axumi nake ina roko kada Allah ya basa ikon aurenta...."

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By Khaleesat Haiydar=???
'
Tohm where r u my Fertymerh Zahrah and Ummi Aysha.... ku ma ga naku shuwagabannin Haske, Allah ya kara mana basira baki daya=?
?

38.....
Tun da ta fara Abba ya tsaida abinda yake yana saurarenta, tana kai wa aya kuwa tace "Ko ya ka ga?" Ya gyada kai yace "Haka ne!" Mami na shiga dakinta ta rufe kofar tace "Aliyu!!" Ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Forgive me plss Mami, i know i disappointed you, ki yafe min don Allah..." Tace "Kana ina yanxu?" Shiru yyi, a fusace tace "Baka ji na ne?" Yace "Mami don Allah kiyi hakuri, ina... Ina kaduna..." Tace "Karya kake Abuu, ina yar mutane?" A hankali yace "Tana nan Mami..." Mami ta girgixa kai tace "Yanxu rayuwar da ka xabar ma kanka kaga shi xae fishsheka Abuturrab, warce ba muharramar ka ba kake rayuwa da ka ajiye koyarwar addinin ka aside?" Shiru yyi bai ce komai ba, tace "Aliyu..." Nan ma dai bai ce komai ba, ta kuma san yana jin ta baxae dai yi maganan bane, tace "Toh yanxu meye amfanin haka Abuu, me yasa har gobe baxa ka dawo gentleman ba?" Xaunawa tayi gefen gado ta dafe kanta, can tace "Look kayi min magana ynxu bana son wlknci, tell me what's the meaning of what you did?" Ya bude idonsa dake rufe da kyar yace "I want to convert her...." Mami tayi tagumi tace "Ta haka ake converting din mutum Aliyu, ka dauketa ku gudu kamar wani Indian film kace min you want to convert her?" Murmushi yyi cikin sanyin murya yace "Kiyi hakuri Mami, ke ma kinsan ynxu idan na dawo da matsala, mami you've got to trust me, kinsan abinda xanyi da wanda baxan yi ba, ni bana fasikanci kin sani, just that this the only way out, xan dawo gida in shaa Allah amma har sai naga hankalinta gaba daya ya karkata ga islam, nasan duk abinda nayi ma 'yar wani surely xa ayi ma nawa kidz din kuma har kannina xai iya shafa sbda haka am very cautious of what i do...." Mami tace "A ina ku ke ynxu?" Yace "Muna Gombe Mami" ta xaro ido tace "Wa ka sani a can Abuu?" Yace "Bbu kowa gashi kuma har nasan mutane ynxu har na fara aiki" tace "Da wani CV din??" Yayi murmushi yace "Da na brain dina Mami" Mami tace "Aliyu ka rufa min asiri ka mayar da yar mutane, Aliyu ni wnn abinda kke son yi ko kadan bai gamshe ni ba, yanxu rayuwar nn wa kaga xae yrda xuri'arsa a samu irin haka, ba fa ce maka tayi tana sha'awar addinin ka ba, kai ke cusa mata kawai, gaba nake jiye maka wllh, shawarata kawai ka dawo in taga tana son musulunci xata yi ne ba sbda kai ba... Ka dawo kayi auren da iyayen ka ke son kayi Abuu, ka ajiye shashancin nn da kake yi son" da damuwa yace "Mami ni wllh ita kadai naji xan iya aure... Pls ki bani go a head ko yanxu xan iya aurenta nasan zata amince kuma dawowa addinina baxae mata wahala ba in har na aureta" Mami tace "Toh ba da yawuna ba wllh, in kuma shakiyancin naka har ya kai ka fara tsallake magana ta to bismillah, na fada na sake fada ba da yawu na xaka je a daura maka aure da Christian ba...." Daga haka ta katse wayarta, ya rike kansa. Can ya mike da kyar ya cire shirt din jikinsa ya kwanta kan gado hade da lumshe ido, ya fara bacci samha ta shigo dakin, durkusawa tayi kusa da shi tana kallonsa a hankali tace "Doctor..." Bude ido yyi don baccin nasa bai yi nisa ba, tace "Abinci fa?" Ya mike xaune yace "I've eaten sai anjima" tace "Toh..." Mikewa tayi xata fita yace "Samha!" Ta koma ta durkusa tace "Na'am..." Ganin kallonta kawai yake tace "Doctor i prayed today also..." Yace "Really?" Tace "Yea, tare da khadija, she came back from islamiyya around 1, shine ta xo nan... Tace min ita ma recently tayi waec" Yace "Waow, shknn kin samu frnd knn... Which means you weren't lonely today!" Tace "Yeah, tare muka yi girki da ita, i like her she's very nice" yace "Uhnn! Ai naga alama" ta langwabar da kai tace "Toh ko nima in dinga bin ta islamiyyan i don't want to be staying at home all alone kafin ta dawo" ya sauko da kafafuwansa yana kallonta yace "If that's what you want love sai in sa ki..." Tace "Ehh ina so!" Yyi murmushi yana kallonta yace "Alryt gobe sae ki fara koh?" Ta gyada masa kai, mikewa tayi tace "Let me go back tana parlor, nayi xaton xaka ci abinci ne" yace "Am ohkay dear, ltr xan ci" tace "Tohm" snn ta fice daga dakin ya bi ta da ido murmushi dauke fuskarsa, sosai yaji ddin islamiyyar da tace xata, and he was happy she brought the idea her self. Washegari yana dawowa daga masallaci ya shiga dakin da take ya tada ta, ta mike xaune tana mitsike ido yace "Yau baxa kiyi sllhn ba knn?" Ta kallesa tace "Sllh kuma?" Ya wara ido yace "Alryt dear, yi kwanciyar ki nayi xaton xa kiyi sllhn ne" bata ce komai ba hakan yasa ya juya ya nufi kofa, mikewa tayi ta bude kofar bayi ya juya ya kalleta bai dai ce komai ba ya fita ya shiga wani dakin don shiryawa tunda yyi wanka kafin ya je masallaci yana buttoning din shirt dinsa ta shigo da hijab jikinta, ta karasa dakin tana kallonsa tace "Nayi sllhn" yace "That's very nyc of you love... Allah ya karba" murmushi tayi tace "Me xan yi maka for brkfst?" Yace "Just lipton xa ki dafa dear, akwao bread" tace "Kwai fa?" Yace "Noo, ni baxan ci ba sai dai ke" juyawa tayi ta fita, ko kafin ya fito har ta dafa ruwan Lipton din ta ajiye a parlor da kayan beverage, ya karaso parlon ya xauna ta hada masa tea'n yana kallonta, ganin irin kallon ta sunkuyar da kanta, murmushi yyi ya jawo cup din tea din, tace "Baxan je islamiyyan ba yau?" Yace "Xa ki mana baby" mikewa tayi tace "Tohm bari in shirya" daga haka ta shiga daki, yana gamawa ya fita xuwa part din Hajiya, karo ya kusa ci da fatima da ta fito daga parlon hannunta rike da makullin mota tana sakale da jaka alamar boko xata, Bai ko kalleta ba ya bi ta gefenta ya isa kofar ya danna bell, kin tafiya tayi ta xuge jakar hannunta tayi pretending kmr neman abu take, Khadija ce ta bude kofar ta gaishesa da fara'a ganin shi ne, yace "Mami fa?" Tace "Tana ciki bari in mata magana" daga haka ta juya ta koma parlor, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Wai ka shigo" Bin bayanta yyi suka shiga parlon, dai dai lkcn da Mami ma ta shigo parlon, xauna yyi kan sa a kasa ya gaisheta ta amsa tana murmushi tace "Kun tashi lfya Boy?" Yace "Alhmdllh Mami" tace "Har ka shirya knn, in dai ka gama abinda kke tun da akwai makullin mota gun ka sai ka dinga wucewa kawai boy" yace "Toh Mami, dama samha ce ke son shiga islamiyyar su khadija, ina son in fara xuwa can da ita ne...." Mami tace "Maa sha Allah, kace mata in dai ta shirya ta xo sai in kai ta.... Kai kayi wucewar ka kawai" A hankali yace "Toh nagode Mami" daga haka ya mike ya fita duk da hakan bai gamshe sa ba don bai son Mami tasan bata san komai ba. Fatima dai na nn tsaye fa har lkcn, wnn karan tare masa hanya ma tayi duk don yyi mata magana, ga mamakinta sai gani tayi ya tsallake karfen dake xagaye balcony din yyi wucewarsa.

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
Hmm where are you blood!=?
? Ke ma ga naki, Allah ya kara hada kawunanmu sweet sis Iqram Mujaheed (Maryam M Bello) proud to have a sister like u.

39.....

Parlor ya tadda Samha yace "Dear ki shirya Mami xata ajiye ki a islamiyyan...." Shiru tayi tana kallonsa, ya kamo hannunta yace "Yea, i wanted taking u there by my self but she insisted...." Ta langwabar da kai a hankali tace "Toh" mikewa yyi yace "Yauwa baby, sai ja dawo" tace "Allah ya tsare...." Har ya kai bakin kofa ya juyo yace "Bbu rakiya dear" murmushi tayi ta mike ta bi bayansa suka fita a tare, hada ido suka yi da fatima dake tsaye tsakar compound din ta kasa tafiya, Samha ta kirkiri murmushi tana kallonta tace "Good morning sis fatima" Fatima ta mayar mata da yake tace "Same" daga haka ta nufi gun motar ta da take xuwa makaranta da, Shi dai Abuturrab bai ko kalli inda suke ba har ya isa gun motar da Hajiya ta basa ya juyo yana kallon Samha da ta bi bayansa, jawota yyi gabansa yana kallonta yace "Tohm sweet sai na dawo" murmushi tayi ta gyada masa kai, har xai kai bakinsa nata ko me ya tuna kuma ya bude mota kawai ya shiga tana tsaye ya gama bata wuta snn ya kalleta ya kashe mata ido ya ja motar hade da horn mai gadi ya bude masa gate, Kallon motar fatima kawai Samha take har ita ma ta fita da gidan, ta kusa minti uku tsaye tana kallon gate din gidan snn ta juya da kyar ta koma ciki. Cikin d'an lkci Abuturrab ya saba da doctors din clinic din bayan sun fito daga theatre a ranan, barin da suka ga shima kwararre ne, few nurses da yaga alaman suna da hankali kadai ya sake ma, sai dai fa throughout ranan duk da uban aikin da yyi hankalinsa gaba daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login