Showing 45001 words to 48000 words out of 180592 words

Chapter 16 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1134

Samha kina da kyau, wanda ya xo da ke shine angon naki koh?" Samantha ta sunkuyar da kai kawai, matar tace "Allah sarki, Allah ya bada xaman lafiya da xuri'a dayyaba...." silver head tie mara nauyi matar ta daura mata, sannan ta fesheta da turare kala hudu da ya saka cikin kayan, matar takara mata da nata, snn ta kama hannunta suka fito, tun da suka fito Abuturrab ke kallon Samantha ko kiftawa babu, ita kam kasa dago kanta tayi, duk occupant din wajen kallonta suke ko wanne na fadin maa sha Allah, Har gabansa matar ta kai ta, sai a snn ya mike da kyar ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu talatin din dake ciki ba tare da yace komai ba ya mika mata, farin ciki ya lullube matar ganin tulin kudin, karfin halin kama hannunta yayi suka fita tana binsa duk jiki a sanyaye, suna shiga mota ya kamo hannunta cikin raunin murya yace "promise to be with me no matter the situation we re going to find our self samha..." Kasa cewa komai tayi hawaye ya cika idonta, harde hannayensu yyi cikin sanyin murya yace "Talk plss Samha," rungumesa tayi cikin rawan murya tace "I promise!" Kiss ya shiga yi mata a wuyarta, duk ta rikice tana turasa, da kyar ta samu ya saketa, ta hade kanta da gwiwa, jiki a mace ya tada motar ya ja suka bar wajen, sai da ya je gidan wani abokinsa don shiryawa shi ma, sai dai bai bari ta fito ba ya shiga gidan, ba a dau lkci ba ya fito sanye da suit dinsa na royal blue. Bata bari sun hada ido ba har ya ja motar. Wani lafiyayyen hall taga sun yi parking, tun daga waje kana iya ganin uban motocin dake Parke ga abokansa na hannun dama na jiran isowarsa, yana fitowa ya xaga ya bude mata ya kama hannunta ta fito, wani kallo suka dinga mata gaba dayansu shi dai yana rike da hannunta har ya iso gabansu, sai a snn suka ankare, kusan dukkansu suka sa hannu aljihu suka fiddo sabbin dari biyar biyar suka watsa masa shi da ita, lkci daya suka ce "Happy birthday Aliyu" dariyar yake yayi ya na rike da ita ya nufi hall din suka rufa masu baya. Sai ka rantse d'an sarki ko d'an shugaban kasa ke birthday tsabar cika da haduwar wajen don Aliyu akwai son life, manyan 'yan mata da samari masu ji da kai ne kuma a gun, Gaba daya kallo ya koma kan Samantha, wanda hakan yasa Abuturrab ya ji wani kishi ya rufesa, komai da aka yi design a gun red and silver ne, manyan cake har uku ne a gun, nan aka fara shagalulluka, ita dai Samantha taki sakin jiki, shi ma kuma bai takurata ba, Saudat na daya daga matan da suke gun, sai dai tun da ta kyallara ido taga Samantha hankalinta ya tashi barin da taji wai birthday mate dinsa ce kuma da dukkan alama budurwarsa ce, bbu wanda ya dauko Samantha Christian ce, Abutuurab dai na ta kallon agogo don bai son su wuce tara gun, ko da xa su wuce hakan ma yafi son ya maida Samantha gida, tunda Samantha ta xauna bata tashi ba sai da aka fara hotuna shi ma kuma tilasta ta yayi, ae ko kowa so yake suyi hoto tare, har dai aka gama sai yanka cake, Yayi ma abokinsa magana cewar ya ba ma Dj umarnin kashe wakar da ke tashi coz he wants silent, cikin kankanin lokaci gun yayi tsit, wanda hakan yasa kallo ya dawo kan Abuturrab dake facing din Samantha, kasa kallon cikin idonsa tayi, da mamakinta da kowa na gun sai gani suka yi ya durkusa a hankali on his kneel ya sa hannu a aljihu ya ciro wani box me bala'in kyau ya bude, sai ga kyallin diamond, abokansa na ganin haka suka dauko Mp xuwa inda suke ko wannensu na cewa waowww, Abuturrab ya ciro ring din ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Will you marry me plss?" Tafi hade da ihu ya kauraye ko ina, tuni aka fara video da waya, bbu wanda abun bai burge ba a wajen sai saudat da taji kamar xuciyarta xai fashe, samantha kam hawaye ne ya cika idonta, ta kasa ce masa komai ga ido da ya tsare ta da, da kyar ta gyada kai hawayen idonta ya xubo, cikin sanyin murya tace "Yyess i will!" Dai dai lkcn da ya gama xura mata xoben ya mike ya rungume abarsa, aka dinga tafi da shewa ana daukarsu photo, juyawa saudat tayi ta fice daga hall din da gudu, gift ba na wasa ba Samantha ta samu a gun don har ta fi uban gayyar samun kyauta, karfe tara kuwa ya fita da ita daga gun, duk taki yarda su hada ido, sai da ya kai ta part dinsa ta canza kaya snn ya rakata har kofar gidansu, bata yi wata wata ba ta shige ta bar sa a tsaye, yayi murmushi ya juya ya bar wajen. Xaune taga Mumy a parlor fuskar nan nata bbu alamar rahama, jikinta yayi sanyi ta karasa ta gaisheta kanta a kasa, cikin kakkausar murya Mumy tace "Daga ina kike Rebecca?" Gabanta yayi mugun faduwa tana kallon uwartata a hankali tace "Birthday Mum" Mumy ta mike tace "Birthday din wa" sunkuyar da kai tayi xuciyarta na bugawa tace "A frnd" fincikota Mumy tayi tace "ki gaya min meye hadin ki da likitan dake xuwa gidan nan?" Sosai samantha ta tsorota kafin tace komai uwar ta sauke mata mari cikin tsawa tace "Baxa ki bani amsa ba??? Uban meye tsakanin ku, a ina kika san shi? Har ya sauke ki a mota" Samantha ta fashe da kuka jikinta na rawa tace "Mumy kiyi hakuri don Allah, he's a frnd!"

*Haske writers asso*=???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

24.....

Baki uwar ta bude da mamaki tace "Rebecca yaushe kika fara karya?" Durkusawa samantha tayi cikin kuka tace "Plss Mumy kiyi hakuri am not lying frnd dina ne" Mumy tace "A ina kika san shi?" Rasa abinda zata ce tayi hawaye na sakko mata tace "Kiyi hakuri Mumy" hankada ta tayi cikin tsananin fushi tace "Baxa ki bude baki ki min magana ba?" Jikinta na rawa tace "Watarana ne naje birthday din Suzan shine muka hadu, he helped me" tafe hannu uwar ta shiga yi cikin tashin hankali tace "Nashiga uku, Samantha dama abinda kike yi knn yanzu ban sani ba, when did you change, meye hadin ki da musulmi daga fara bin sa har ya koya maki karya," a fusace uwar ta kuma kai mata mari ta fixgota tace "Maza wuce ki hada kayan ki yanxun nan, dole ki bar gidan nan gobe gobe, baxan bari ki ja mana abun kunya ba, tunda har ya koya maki karya ban san nan gaba me xae faru ba kuma" daga haka ta ja ta xuwa daki, tana tsaye tasa ta gama hada kaya ta tabbata bbu wani abu da tasa a jakar banda kayanta don har wayarta da bata fiye amfani da ba ta karbe, wayar Abuturrab ne dae bata san da shi ba, bedroom dinta ta kai ta ta kulle ta sauko kasa tana huci tana tunanin ghana kawai xata turata gobe tunda tana da visa, Samantha ta hade kai da gwiwa ta dinga kuka, duk ta rasa me ke mata dadi, kallon fingers dinta tayi da sauri taga ring din da Abuturrab ya sa mata na nan, cirewa tayi ta wurgar ta kuma fashewa da kuka, tayi mai isarta ta kwanta nan kasa ta lumshe ido, har ta fara bacci kamar warce aka tsikara ta mike da sauri, kalle kallen dakin ta fara yi tana neman xoben, can ta mike ta nufi ta inda ta wurgar bata gani ba, jikinta yayi sanyi wasu sabbin hawayen suka xubo mata, a hankali ta dinga bin ko ina na dakin tana dubawa, har bayan minti talatin bata gani ba, hankalinta ya tashi ta fara dage komai tana dubawa, kan kace me duk ta juya dakin upside down, da kyar ta ga xoben a wani lungu, ta karasa da sauri ta dauka, dai dai nan aka bude kofar dakin, Mumy, da aunties dinta har uku suka shigo dakin, daya kanwar mahaifinta ce, biyu kuma kannin Mumy ne, Mumy da ta hango xoben dake kyalli hannunta ta karaso da sauri tace "Meye wannan hannunki?" Kasa cewa komai samantha tayi tana kallonsu xuciyarta na bugawa, Mumy ta kare ma dakinta kallo tace "Ubanki kike nema kika rikita min daki, xoben meye wnn kamar na diamond a hannunki" sauke idonta kasa tayi hawaye ya silalo idonta, daya daga aunties din nata a fusace tace "Amma Rebecca ba kurma bace ba dai koh!" Ta fashe da kuka cikin rawar murya tace "Mumy shi ya bani" dafe kirji Mumy tayi cikin tashin hankali tace "Amma na shiga uku ni Rachael, na meye?" Ta sulale nan kasa ta kuma fashewa da kuka sosai tace "He said he wants to marry me" wani jiri Mumy ta dinga ji har sai da Anty Vivian ta riketa, Mumy ta fashe da kuka sosai tace "Ae ni nasan na shiga uku, amma Allah ya tsine ma mutumin nn yar tawa xae yi engaging? Wayyo Allahna kila ma asirce min ita yayi, shi yasa jinina bae taba haduwa da musulmai ba, mugaye ne, matsafa ya ma 'ya ta tsafi, ku kira min David yaji abinda yar sa ta koma, tuni Rebecca ta daina xuwa church na lura, ko taje kuwa bata dadewa take dawowa, Rosary da na bata ta saka sai ta cire, ta bar karanta Bible, ta yaye catechism da dadewa, addu'ar safe yanxu bai dameta ba, kai bata ma yi, Samantha da ko kasheta xaka yi baxata maka karya ba ita ce yanxu da masters a karya, snn ace bae asirce min 'ya ba... Babban abinda ya kuma tada min hankali nayi ta leke ina jiran in ga ta inda xata billo shine yau fa birthday dinta amma yar nn daga ni har babanta bbu wanda tace ma komae abinda bai taba faruwa ba tsawon rayuwarmu tare, ashe birthday d'an iskan ya hada mata" Tana kai wa nan ta kuma fashewa da kuka sosai ta daura hannu a ka, Wani wawan mari kanwar Abba ta dauketa da shi cikin tsananin fushi tace "Waye shi? A ina kika sansa, d'an wani anguwa ne? Me garesa da har ya burge ki kike kulasa?" Kasa cewa komai Samantha tayi sbda wani jiri da ta dinga gani tsabar shigarta da marin yayi, Anty vivian ta rike Sarah kanwar Abba ganin wani marin xata kuma kai mata tace "Haba sis sarah mu bi ta a hankali mana..." Sarah tace "Xaman ta ya kare a Nigeria, gobe gobe xata wuce Ghana, har mu xata dauko ma abun kunya, me xa ayi da musulmi? Yesu yayi mana tsari...." Samantha bata san lkcn da cikin kuka tace "Toh su musulman ba mutane bane? Ina ce Grandfather na har ya mutu musulmi ne shi, kuma dama ba Jehovah ne ya halicce mu gaba daya tare da su ba, kowa da nasabarsa gun Allah.... Kuma a Bible ae dama ance addini xai kasu....." Mumy bata jira jin karashen ba tayi kukan kura sai a kanta, tana duka Sarah na duka, ita kanta Vivian wnn karan wani wawan hauri ta kai mata tana cewa "Rebecca mu kike gaya ma haka???" Da kyar Anty Mary Ann ta ja samantha suka bar dakin, ta shiga da ita wani dakin ta rufe da makulli, Samantha ta sulale kasa ta hade kanta da tiles din dakin, Anty Mary da damuwa tace "Rebecca waye wnn mutumin, meye hadin ki da shi?" Kasa cewa komai Samantha tayi idonta a rufe, xama Anty Mary tayi gefen gado tayi tagumi, tana jin su Mumy na bubbuga kofa kamar xasu cire suna kunduma xagi, daga karshe suka gaji suka bar wajen, Samantha ta mike da kyar ta hau gado ta rufe ido, Mary da ta bi ta da ido ta girgixa kai cike da damuwa, har karfe sha daya samantha bata bude ido ba sai dai ba bacci take ba, mikewa Mary tayi ta shiga bayi, samantha ta juya a hankali taga ta rufe kofar, mikewa tayi ta sauka daga kan gadon da sauri ta bude kofa a hankali kamar kiftawan ido sai ga ta downstairs, Blessing na xaune parlon tana ganinta ta mike da damuwa tace "Sister Rebecca ina xa ki kuma, you re in trouble plss kar ki fita" Hawaye cike idonta tace "Plss don't say anything, kawai kice baki gan ni ba" daga haka ta fice da gudu jin budewar kofa a sama, Blessing ma ta shige kitchen da gudu, ko takalmi bbu kafarta ta fice gidan gaba daya, ae ko Mary na jin budewar kofa ta fito da sauri, ganin dakin wayam ta fice waje dai dai lkcn da Mumy ma ta fito da su Sarah, Mary ta fara kalle kalle hankali tashe, Mumy na ganin haka ta daura hannu a ka ta fara sauka stairs tana cewa "Ae ni shknn na shiga uku na lalace, gudu tayi...." Duk suka bi ta hankali tashe, Mumy ta dinga kwala ma Blessing kira ta fito da sauri, A tsawace tace "Ina Rebecca?" Girgixa kai tayi a tsorace tace "Madam ni a kitchen nake ai...." Kamar Mahaukaciya Mumy ta fita parlon ta dinga kwala ma inusa mai gadi kira ya fito cikin tashin hankali tace "Inusa Samantha ta fita ne?" Inusa yace "Ehh yanxun nan ta fita..." Da gudu su Anty sarah suka fice don bin bayanta, a tsawace Mumy tace "Me yasa ka bar ta ta fita?" Mai gadi yace "Madam ae ba yau ta saba fita ba, in dai xaki kwana church yawanci bata kwana a gidan nan sae asuba take dawowa, nayi xaton yau ma kinje kwana a church ne...." Wani kara Mumy tayi ta daura hannu a ka tace "Yesu!! Ae ni nace dama na shiga uku, Rebecca bata kwanan gida, ina take kwana" kuka sosai ta fashe da, daga haka ta bi bayansu Sarah ita ma da gudu, yau kam samantha bata ji tsoron karnukan dake haushi ba, neman tsoron ma tayi ta rasa, gudu kawai take don tasan da wuya idan ba a san ta fita ba yanxu, tunanin hakan yasa jikinta ya dau rawa a xuciyarta kuwa addu'a take Allah sa Abuturrab bai rufe gate ba, don tasan idan ta tsaya bubbugawa xa a iya risketa kuma tata ta sameta knn gun su Mumy.....

*Haske writers asso*=???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

24/25

Tana isa gate din ta turasa taji a rufe, kasa bubbugawa tayi sai haki take, hasken torchlight ta dinga hangowa daga nesa, ae bata san lkcn da ta fara buga gate din ba, Abuturrab dake xaune ya rike kai a parlor don ya rasa me ke damunsa tun bayan dawowarsa gida ya mike da sauri kamar dama jiran buga gate din yake ya fito ya karasa ya bude, yana ganinta kuwa ya jawota ya rufe gate din gam, sulalewa kasa tayi, ya bita da sauri hankali tashe yace "What Happened Samha?" Mikewa tayi da sauri ta shige parlor ya juya ya bi bayanta, xaune tayi parlon ta hade kai da gwiwa ta dinga rusa kuka, wani mugun tashi hankalinsa yayi, ya dagota yace "Don Allah ki min magana...." Bai rufe baki ba yaji ana bubbuga kofa kamar xa a cire, mikewa yayi da sauri ta rikosa cikin rawan murya tace "Plss kar kaje, Mumy ce..." Kallon mamaki ya dinga mata, lkci daya jikinsa yayi sanyi, su kuwa basu fasa buga gate din ba, ga haushin da karensa ke yi duk ya cika gidan, to bai son a ji a cikin gida, ya durkusa cikin kwantar da hankali yace "Look Samha, bari in je, nasan me xan yi, tashi ki shiga daki" cikin kuka tace "Don Allah kar kaje plsss" rike hannunta yayi yace "Noo, yanxu xa ki ga soldiers din cikin gidan nn sun yo nan, i don't want that, nace maki nasan abinda xan yi" kasa cewa komai tayi sae dai duk jikinta rawa yake, ya mike da sauri ya fita, ae ko sae ga soldiers har uku suna tahowa, ya d'an kallesu yace "No, it's nothing, kila emergency ne, kuyi wucewar ku kawai..." Juyawa suka yi gaba daya sae da suka sha corner, snn ya isa cage din karensa ya bude, karen ya fito kamar jira yake ya nufi gate din, Abuturrab ya bi bayansa, lkci daya ya bude gate din amma ya tare yanda karen baxae iya fita ba, yamutse fuska ya dinga yi kamar mai bacci yace "Any problem??" Bai gama rufe baki ba Mumy ta cakumosa tana haki tace "Ka fito kin da 'ya ta kar in cinna ma gidan nn wuta yanxun nn, fito min da 'ya ta nace!!" Wani kallo ya dinga yi mata yace "Ban gane ba" wani ihu tayi tace "Baka gane ba koh, to wllh yau sae na tara maka jama'a bring out my daughter oo" A fusace Sarah ta bankesa xata shiga gidan, ya hankada ta waje, daga haka ya matsa karensa ya fito ya dinga wani irin haushi yana tsalle duk suka koma baya da gudu sai dai fa hakan bae sa Mumy ta rufe baki ba, duk ta xama kamar wata xautatcciya, can ta fashe da matsanancin kuka tace "Yesu what have i done to deserve this, why my daughter, why rebecca..." Vivian ta dinga jan ta tana cewa "Sister Rachael mu je kawai gobe sae mu je station kinga karen nn sae ya iya cizan mu" da kyar suka ja ta tana kuka sosai ganin kare fa ya dage xae yi cixo don ma Abuturrab na kiransa, suna barin wajen karen ya dawo Abuturrab ya jawosa ciki snn ya rufe gate, ya shiga parlor ya sa key, duk jikinsa yayi sanyi ya karasa bedroom, xaune ya ganta a kasa ta hade kai da gwiwa tana rusa kuka, durkusawa yayi gabanta cikin sanyin murya yace "Am sorry samha, forgive me plss, i know i caused everything" k'in dago kanta tayi, yayi shiru ya ma rasa abinda xai ce, can ya mike duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login