Showing 51001 words to 54000 words out of 180592 words

Chapter 18 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1133

Mami ta durkusa gabansa ta dago kansa tace "A ina?" Kallonta yayi murya can kasa yace "Mami.... Mami ita nake so and i want to convert her...." Komawa baya Mami tayi da mugun mamaki tana kallonsa kamar idanuwanta xa su fito, cikin rawar murya tace "Aliyuu!" Marairaice mata yayi yace "Mami ni idan ban aureta ba Allah xan iya mutuwa wllh, i will be nothing without her" hawaye ne ya cika idonsa, wanda rabon ta da ganin hakan tun yana d'an shekara goma, ko me xaka yi masa baxa ka taba ganin hawayensa ba sai dai idonsa yayi jajir kirjinsa yayi ta sama da kasa tsabar dacin rai da rashin ji irin nasa, ya daura kansa a jikinta muryarsa na rawa yace "First love support me plss, i love her, ni baxan iya rabuwa da ita ba, kuma Mami idan na musuluntar da ita lada xan samu fah..." Hawaye kawae Mami take duk jikinta yayi sanyi, ita kam tana ganin jarabawa tun da ta haifi Aliyu, ta saita kanta cikin sanyin murya tace "Toh tana ina?" Da kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "Tana gidan Mumy!" Da mugun mamaki tace "Mariya?" Yayi shiru bai ce komai ba, ta sauke ajiyar xuciya a hankali, jin tayi shiru ya dago da sauri yace "Mami plss kar fa ki ce ma kowa haka, don Allah kar ki fadi Mami...." A rude ya kare maganar, cikin kwantar da murya tace "Ka gwammace kayi ta shan wahala knn, to ai shknn, shiru xan yi da baki na idan ma ya kashe ka kai ka ja ma kanka, tashi ka shiga ciki kafin a ganmu dama cewa yake ni ke supporting din ka" kallon d'an kurkukun yayi kafin ya marairaice yace "Mami k'ishi nake ji sosai wllh" mikewa tayi tace tana xuwa snn ta fita, ya fi kowa sanin halin Mami yasan wannan duk pretending take masa, ya kalli bunch of keys din da ta ajiye nan kasa bayan ta bude sa, ya dauka da sauri ya cire biyu ya tona kasa ya boye a cikin d'an room din, yana nan durkushe yana yi yana lekan sojoji biyun dake tsaye waje har ta dawo ya sunkuyar da kansa da sauri, Ruwan babban gora me sanyi ta kawo masa da Hollandia yoghurt, sae dambun nama cike a plate tace toh tashi ka shiga kafin ya yo nan, karban ruwan yayi ya sha kusan rabi, Key din dake ajiye kawae take kallo can ta dauka tana weighing dinsa ta kallesa strictly tace "Ka cire key a nan bani!" Da sauri yace "Key kuma Mami" wani kallo tayi masa tace "mike tsaye" yana tashi ta sa hannu aljihunsa ta dudduba taga babu, ta leka guard room din ma bata ga alamar key ba tace "Toh shiga ciki" ya ajiye ruwan hannunsa fuskar nan tasa kamar xae yi kuka ya durkusa ya shiga ta tura masa abubuwan da ta kawo snn ta rufe gun da kwado ta juya ta nufi kofa, ya bi ta da kallo yana murmushi har ta fita. Ko minti goma ba ayi da fitarta ba yasa key ya bude gun a hankali ya fito, ya dau shirt dinsa dake rataye gun ya kakkabe ya saka snn ya saka takalmansa ya nufi kofa da sauri, lkci daya ya banke kofar ya fice a dari da sittin kafin sojojin su ankara, ae ko suka bi sa da gudu, gudu yake kamar jirgi xae tashi sama, wani soldier ya ciro whistle a aljihunsa ya dinga hurawa, ae ko sae ga sojoji har uku sun fito, Abba ma ya fito balconynsa a sama ya rungume hannu da mugun mamaki yana kallon Abuturrab, komawa yayi don dauko bindigarsa amma kafin ya dawo tuni ya isa gate da karfi ya finciko mai gadin sojan dake bakin gate yana kkrin datse gate din ya wani wurgar da shi ya fixgo gate din ya fice, gudu kawai yake kamar xae tashi sama, wanda hakan ya tsorata mutane duk suka fara gudu su ma, ko kallonsu bai yi ba har ya iso titi ya tsayar da mai adai daita bai jira ya tsaya ba ya afka ciki yace "Mu je muje da sauri....." Mai adai daita ya ja machine dinsa da sauri don shi ma ya tsorata, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya ya share xufar fuskarsa ya bude button din riga.

*Haske writers asso*=???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

27.....
Gani yake kamar ba tafiya mai adai daitan yake ba duk da yasan yayi escaping don baxa ma su san inda ya bi ba, yayi tsaki yace "Malam ajiye ni nan dan Allah" Mai adai daitan yayi parking Abuturrab ya fito yace "Sae dai kayi hakuri bani da kudi" daga haka ya yi gaba da sauri, mai adai daitan ya bi sa da kallo, yanxu kawae so yake ya gansa gidan Hajiya Mariya yasan tun da ya fadi ma Mami kamar an je an dauko Samantha an ba iyayenta ne, makullin motarsa dama tun da aka sa shi guardroom Abba ya karbe da wayoyinsa, wani bike ya tsayar yana kallon mutumin dake kai yace "Ehrm Don Allah malam ka goya ni xuwa Kofar Nasarawa idan ba damuwa..." Mutumin yace "Ba can nayi ba, nama kawo gida ka ga inda xan shiga..." Abuturrab yace "Toh don Allah ara min bike din... Xan dawo maka da shi" wani kallo mutumin ke ma Abuturrab daga sama har kasa baki bude, Abuturrab ya dafa sa yace "Na maka kama da barawo???" Shi dai mutumin kallonsa kawai yake, Abuturrab ya fixge key din yace "Nafi karfin satan machine, kuma i think da wuya a ga barawo Aliyu Haiydar! Sauka ka ban machine malam" kamar soko haka mutumin ya sauka, Abuturrab ya hau ya tada machine din ya figa da gudu ya hau kan titin, alarm mutumin ya saki bayan Abuturrab ya bace masa yana cewa ya hadu da d'an rufa ido. Cikin kankanin lkci Abuturrab ya iso gidan Hajiya Mariya, a sanyaye ya sameta a parlor ya karasa ya xauna yace "Mumy!" Ta kallesa tace "Me kace ma Mami" shiru yayi sae kuma ya mike da sauri yace "Tana ina Mumy?" Hajiya Mariya tace "Kaga ka hada ni da Mami sae da nace kar kace tana nan, to in'sha Allahu nasan duk inda suke sun ma kusa gidan nan yanxu" Abuturrab ya xaro ido ya nufi bedroom dinta da sauri ya samu Samantha kwance amma idonta biyu, ya karasa ya durkusa kusa da ita yace "Xa mu tafi yanxu samha!" Mikewa xaune tayi ya mike ya fita ta bi bayansa, durkusawa yayi kusa da Hajiya Mariya yace "Mumy babu kudi hannu na...." Mikewa tayi cikin harshen fullanci tace ya sameta a daki, bin bayanta yayi ta xauna tace "to yanxu ina xa ku Aliyu?" Ya shafa kai yace "Anywhere mum, kawai ki ban kudi kafin su karaso" Mikewa tayi ta dau purse dinta ta bude tace "Dubu uku kadai ke garen yanxu amma ga atm card!" Duk biyun ta hada masa ya karba, tace "Toh ta ya xan same ka, na kira wayarka duk switch off" yace "Abba ya karbe wayar, ina da number ki a kai i will call you idan na samu waya Mum," Daga haka ya juya ya fice ta bi sa da kallo, can ta fita ita ma, tana kallon Samantha tace "Toh xan kira ku kin ji daughter" Samantha ta gyada mata kai cikin sanyin murya tace "Nagode Mum" daga haka ta bi bayansa, Hajiya Mariya ta bi su da kallo cike da tausayi, suna fita Abuturrab ya kalleta ya langwabar da kai yace "Samha Bike xa mu hau fa!" Ta kalli machine din snn ta girgixa masa kai tace "Ban iya hawa ba...." Dariya ta basa yace "Toh ba sai in daura ki ba" ta koma baya da sauri tace "No ni ban taba hawa ba, bana so" gani yayi lkci xa su bata yace "Toh follow me fast..." Ta bi sa da sauri suka fita, wata hanyar daban ya dauka har suka iso main road ya tsayar da adai daita suka hau, mai adai daitan ya tambayesa inda xa su yace "Mu je gaba kawai" samantha ta kallesa tace "Ina xa mu je" kasa ce mata komai yayi ganin yanda idonta ya fada, ya kamo hannunta a hankali yace "Am sorry for everything samha" bata ce komai ba, ya kalli mai adai daitan yace "Jan bulo xaka kai mu." Suna isa mai adai daitan yayi parking dai dai inda Abuturrab yace yayi, yana sauka ita ma ta fito, ya mika masa dubu dayan hannunsa ya basa canji ya kalleta yace "Mu je" bin bayansa tayi ya kwankwasa gate mai gadi ya bude, suna gaisawa ya shiga gidan ita ma haka, sai a snn a hankali tace "Doctor ina ne nan?" Ya kalleta yace "Gidansu frnd dina ne nan, bbu wayar da xan kirasa shi yasa mu ka xo" Farida kanwar Mujaheed na xaune karkashin umbrella tree da alamar assignment take, tana ganinsu ta mike tace "Lahh ya Aliyu daga ina?" Yace "Mujaheed na nan?" Tace "Ehh yana nan" yace "Kice ina jiransa" tace "Toh" snn ta kalli Samantha tace "Sannu da xuwa" Samantha ta sakar mata murmushi tace "Nagode" daga haka yarinyar ta wuce ciki, ya kalli samantha yace "Mu je ki xauna" bin bayansa tayi suka xauna karkashin bishiyar, ba a dau lkci ba Mujaheed ya fito, ya xaro ido yana kallon Abuturrab yace "Daga ina haka?" Abuturrab bai tanka sa ba har ya karaso ya ja kujera ya xauna yana kallon Samantha murmushi dauke fuskarsa yace "Sannu yan mata!" Samantha ta sunkuyar da kai tace "Ina yini" ya amsa da fara'arsa, Abuturrab yace "Kira farida su shiga ciki, xa mu d'an fita da kai ne yanxu" Mujaheed yace "Ohk" ya ciro waya ya kira kanwarsa ta fito, Abuturrab ya kalli Samantha yace "Samha ku shiga ciki am coming back soon" kallonsa kawae take lkci daya idonta ya kada, mikewa yayi da sauri yace "yanxu fa xan dawo Samha" dago ta yayi suka bar gun daga Mujaheed har kanwarsa suka bi su da kallo, jikin flowers ya tsaya ya daga kanta yana kallon kwayar idonta yace "Ko baki son nan din ne?" Ta girgixa kai bata ce komai ba, a hankali ya kai lips dinsa forehead dinta murya can kasa yace "am coming back soon dear" Daga haka ya kama hannunta suka dawo inda suke ya hada ta da farida suka shiga cikin gidan, A motar Mujaheed suka bar gidan, sun dan yi nisa Mujaheed yace "Kai malam wai ina xa mu" Abuturrab yace "Yi parking muyi magana" Mujaheed yayi yanda yace snn yace "Wnn ba yarinyar nan da ka taba kawowa clinic bace? Dama budurwarka ce?" Abuturrab yace "Ni dai ka saurareni ina son pls ka min wani favour" Mujaheed yace "Na me?" Abuturrab yace "Laifi na yi ma Abba, pls so nake kayi pretending baka san komai ba kaje can gidanmu da sunan kaje daukan ajiyar ka, sai ka duba briefcase a bedroom dina ka dauko min gaba daya Credentials dina, snn akwai atm cards dina har biyu a gaban mirror ka dauko min plss frnd" tun da ya fara magana Mujaheed ya bude baki yana kallonsa, can ya fashe da dariya yace "Me kayi kuma again?" Abuturrab ya tabe baki yace "Oho dai, kawai ni dai nasan tun safe ake cin xalina.... Kaje yanxu plss" mujaheed yace "Abban na gida ne?" Abuturrab yace "May be" Mujaheed ya girgixa kai yace "In dai yana nan baxan iya ba wllh" Abuturrab yace "Oh haka xaka min?" Mujaheed yace "No gaskiya kenan fa, to ita kuma yarinyar nan da kake yawo da fa?" Abuturrab ya shafa kansa yace "Kaga it's a long story yanxu kayi abinda nace idan ka dawo sai in baka labarin," Mujaheed yyi shiru snn yace "Ka fa san halin Dad dinka, xae iya gano hada baki muka yi, why not ka bari da daddare...." Abuturrab yayi tsaki yace "Kai dai kaje ynxu kawai, you have to pretend, sai kace kana ta kiran lines dina basa xuwa, but bani wayar ka daya in case of anything sai ka kira ni" Mujaheed yace "No gaskiya ka bari da daddare?" Abuturrab yyi shiru sai kuma yace "Toh shknn" Mujaheed yace "Da motata xan je?" Abuturrab yace "A'a kawai ka dau tricycle kaga bbu wanda xae xargi komai, kana xuwa kuma ni xaka fara tambaya" Mujaheed yace "Ohk" gidan wani abokinsu suka tafi, suka tsaya har bayan magrib, Abuturrab dai gaba daya hankalinsa na kan Samantha duk da sun yi waya ya fi sau goma ta wayar farida, Bakwai da kusan rabi Abuturrab yace "Toh kaga kar dare yayi kuma Mujaheed ka tashi ka je" Mujaheed yace "Ni dai anya xan je kuwa..." Abuturrab ya marairaice masa, da kyar ya kuma lallaba sa har ya amince daga karshe yace "Toh ina xan sameka?" Abuturrab yace "Ina nan xan jira ka har ka dawo" daga haka Mujaheed ya fita ya dau adai daita ya wuce, Mujaheed na isa yaji gate a kulle wato sai ya xaga ta daya gate din bbu yanda ya iya haka ya xaga, yana shiga ya gaida sojojin dake wajen, sae da gabansa ya fadi ganin Abba a compound suna magana da wani sanye da khaki da alamar abokinsa ne, don compound din akwae haske sosai, yana ganinsu yayi kasa da kai har ya isa gabansu ya risina ya gaidasu, duk suka amsa, Abba yace "Daga ina haka?" Mujaheed yace "Daga gida nake Abba, gun Abuturrab na xo..." Abba yace "Ohk!" Abokin Abba yace "Abuturrab din bai nan ai" Mujaheed yace "Ohk kuma ina ta kiran wayarsa tun rana baya shiga, dama akwai ajiyar da na basa xan karba ne bari in duba ko kofar a bude yake" Abba yace "Ohk" Mujaheed ya sauke ajiyar xuciya ya nufi part din Abuturrab, a bude ya tadda gun ya shiga ya dauko duk abinda Abuturrab yace masa snn ya fito, yayi mamakin ganin sojoji biyu tsaye kusa da balcony sai dai bai ce masu komai ba ya wuce su, yana isa tsakiyar compound ya samu su Abba yanda ya bar su a tsaye ya karasa yace "Abba na dauka xan wuce" Abba na gyada kai yace "Ohk...." Ko rufe baki Abba bai yi ba, Mujaheed ya ji an cafkesa ta baya ya juya da sauri ya ga wani soja ne, sojan ya karbe envelope din hannunsa ya ajiye sa kasa sannan ya fara cajin aljuhun wandonsa ya ciro atm cards din ciki da wayarsa ya jefar kan envelope din, Abokin Abba ya durkusa ya dau Envelope din ya bude ya fiddo abubuwan ciki, banda xare ido babu abinda Mujaheed yake, Abba ya karbi takardun ya kalla snn ya maida dubansa kan Mujaheed, Gyada kai yayi yana wani murmushi ya jefar da takardun kan Envelope din yace "That's a brave play, yeah kun yi kokari daga kai har shi" dukawa yayi ya dau wayar Mujaheed yace "Akwai waya hannunsa ko babu? Kuma kana min karya in sa a kai min kai barrack yanxun nan" Mujaheed da banda xufa bbu abinda ke karyo masa cikin dakiya yace "Ehh Abba akwae daya wayata a gun sa" Abokin Abba na gyada kai yace "Good, kirasa kasa a hands free kace ku hadu a filin polo yanxun nn ya karbi sakon" Da kyar Mujaheed yace "Toh" nn ya shiga kiran daya wayarsa dake gun Abuturrab, Abuturrab da ya fita yana jiransa a mota ya daga kiran da sauri yace "Yane Mujaheed ka dauko?" Mujaheed ya kalli Abba, Abba ya watsa masa wani firgitattcen kallo, da sauri yace "Ehh ehh wllh na dauko! Emm kana ji na mu hadu a filin polo yanxun nn ka karba" Abuturrab yyi shiru, murya can kasa yace "F**k you, ka bari an gano mu knn!" daga haka ya katse wayar ya jefar.

*Haske writers asso*=???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

28.....

Tada motar yyi da sauri tunawa da Samantha da yayi, yasan in dai mujaheed yaga haza to fa xae iya cewa tana gidansu ma, cikin kankanin lokaci ya isa gidansu Mujaheed gabansa na faduwa, kusan a tare suka shiga compound din da kanwar Mujaheed Aysha ta dawo daga makaranta, ya amsa gaisuwarta yace "Kice ma bakuwar da ke ciki ina jiran ta pls hurry" tare samantha suka fito da Farida ta raka su har gun mota ya sosa kai yace "Kice Umma tayi hakuri ina nan xuwa gaida ta, kunya nake ji shi sa ban shigo ba" dariya kawae Farida tayi tace "Ya Jaheed fa?" Abuturrab yace "Ehh yana nan dawowa..." Daga haka ya sa samantha ta shiga mota shi ma ya shiga da sauri, farida ta d'aga masu hannu ya ja motar ya bar layin, yana fita layin motar sojoji na shiga, xaro ido yyi don bai san ko sun gansa ba ya kara gudun tukinsa, sae da suka dan yi nisa ya kalli samantha yaga idonta na waje, wani tausayinta yaji sosai ya kamo hannunta a hankali yace "Samha!" Kallonsa tayi bata ce komai ba, yace "Kin ci abinci?" Kai kawae ta gyada masa, cikin sanyayyen murya yace "Ki kwantar da hankalin ki kar ki sa ma kanki damuwa plss am with you now and forever..." Hawaye ya ga idonta, yayi parking da damuwa yace "Baki yarda da ni ba kenan Samha..." Ta fashe da kuka tace "My parent...." Ya rike hannayenta duk biyun yace "Ni ma na bijire masu duk sbda ke, kinsan irin neman da ake min yanxu? A guardroom Abba na yasa aka kulle ni da safen nan amma sae da nasan yanda na fito, na tura Mujaheed can gidan ya dauko mun Atm cards dina shima yana can nasan an kullesa yanxu kuma nasan xae iya cewa kina gidansu shi yasa na dauke ki, am at risk Samha but i don't care in har ina tare da ke, i love you... I can do anything for your love" hannu yasa ya share hawayen da ke idonta yace "Kar ki damu Allah yana tare da mu!" Sunkuyar da kai tayi bata ce komai ba, ya ci gaba da tukin, a wani atm ya tsaya yace yana xuwa snn ya fita, sae da ya fara duba nawa ne a account

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login