Showing 39001 words to 42000 words out of 180592 words

Chapter 14 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1135

ido yayi ya saketa yace "Da gaske baby??" Ja baya ta dinga yi kawai sai gani yyi ta juya a guje ta nufi kofa ta bude ta fice. Washegari asabar da yamma Abuturrab ya iso gidan Mr David da da magungunan da xai ba Samantha jiya ta gudu, Mumy ya tarar xaune parlor tare da Mr David din bayan an masa izinin shigowa ya gaisheta ta dinga masa wani kallon mamaki, Mr David ya mike yace "Likitan da nake fadi maki kenan" daga haka yace ma Abuturrab ya taho sama, Abuturab ya bi bayansa suka wuce saman, yau ma bbu wani 6ata lkci ya gama basa medication din, ya tambayi samantha, Mr David yace ta tafi church, shiru Abuturrab yyi sai kuma yace "But da ta hakura har ta samu sauki" mika masa magungunanta yayi, yayi masa sallama ya fita, Sai da ya isa kofar fita sannan ya juya ya kalli Mahaifiyar Samantha ya ga kallonsa take yi, yace "Sae da safe Ma!" Wani kallo tayi masa ta mike fuu ta wuce sama, yayi murmushi ya fita, a bakin gate ya hadu da samantha, tana ganinsa ta koma baya da sauri, motarsa ya nufa ya tsaya ya rungume hannayensa yana kallonta har xata shiga gate sai kuma ta tsaya ta d'an saci kallonsa taga idonsa na kanta, kamar mai counting step ta nufi inda yake ta tsaya nesa da shi, tace "Good evening!" Yace "Da wucewa xa kiyi?" Kallonsa tayi suka hada ido tayi murmushi ta girgixa kai, ya lumshe ido yace "Come here" tace "Ba gani ba?" Ya harareta ya nuna mata gabansa, kamar xata yi kuka tace "Kaga daga church fa nake, am tired! Am feeling dizzy" Yace "To tafi...." Shiru tayi tana kallonsa, can ta karaso gabansa a hankali tace "Gani" dago kanta yayi yana kallon kwayar idonta yace "Me yasa kika fita baki da lafiya?" Ta sauke idonta tace "I went to church, Mumy tace in je" Wani kallo yayi mata yace "To daga yau kar ki sake xuwa har sai kin samu lafiya...." Ta xaro ido, ya gyada kai yace "yes I mean it...." Tace "to ae addu'a ake min a can ma" ya tabe baki yace "Good sai kiyi ta xuwa...." Kallonsa ta tsaya yi, ya juya ya bude motarsa ya shiga ya tada, ta lumshe ido ta bude tace "Ohk ohk, baxan je ba kuma" hararanta yayi, tayi kamar xata yi kuka tace "I mean it baxan je ba...." Yace "Better! Taho ki ji" karasawa tayi kusa da glass din motar tace "Mene?" Yace "Matso mana" matsowa tayi, dai dai kunnenta yace "Drugs dinki da prescription na gun Abba, you make sure you take all before going to bed, since you ran away yesterday....." Bata jira ya karasa ba ta juya da sauri don gaba daya ta mance da incident din jiya, ya rikota da sauri ya jawota yayi planting mata kiss a cute lips dinta, ta kwace kanta da gudu ta shiga gida. Ranan litinin Samantha ta kare exams dinta na Waec, karfe uku driver ya je dauko ta a sch, kamar ko da yaushe a bakin layi ya ajiyeta ta karasa wai xai je kasuwa Mumy ta aikesa, tana isa dai dai gidansu Abuturrab ta ga motarsa a waje, ta tsaya tana kallon gate din ko me ta tuna kuma ta fasa shiga xata wuce aka bude gate, sai ga shi ya fito, wara ido yayi ganinta yace "Ina kuma xa ki?" Tace "Wucewa nake yi ai" yace "Uhm, i see yaushe xa ku gama waec din?" Tace "Mun gama" yace "Waow da gaske baby, but shine baki fada min ba?" Ta langwabar da kai tace "Gashi na gaya ma!" Yace "Alryt... Plss ki xo anjima da yamma i have a surprise for you, yanxu xan tafi gun aiki ne i forgot my office key...." Tace "Baxa a bar ni in fito ba...." Xai yi magana aka bude gate sai ga Mami ta fito, gaba daya ya mance tace xai ajiyeta a hanya, kallo daya Mami tayi ma Samantha tace "Aliyu da ban fito ba wucewar ka xaka yi knn?" Ya shafa kai yace "Ohh Mami wllh mancewa nayi...." Samantha da ko ba a gaya mata ba ta gane mum dinsa ce ganin kamar da suka yi da Hajiya Mariya ta risina tace "Ina kwana..." Mami ta kalleta murmushi dauke fuskarta tace "Lafiya lau yan mata ya makaranta" murmushi kawai samantha tayi kanta a kasa tace "Sai anjima...." Daga haka ta juya ta wuce, Mami ta bude bayan mota ta shiga Abuturrab ya shiga motar shi ma ya tada, sai da yayi reverse Mami tace "Ina ka samo wnn kuma?" Ta madubi ya kalleta yace "A anguwar take, she's.... A frnd!" Mami tace "Amma ba musulma bace?" Shiru yayi na kusan minti hudu, cikin sanyin murya yace "Me kika ga Mami?" Mami dake danna waya tace "Me na gani a ina?" Yace "Da kika ce ba musulma bace" Mami da har ta mance xancen da suke tace "Ae musulinci ba boyayyen addini bne, duk inda kaga musulmi xaka gane....." Yace "But Mami uniform ne fa jikinta with Beret!" Tace "So? 'Ya mace musulma dai da ta taso gidan tarbiya baxata bar gida xuwa makaranta ba hijab ba, ko da kuwa makarantar ba a saka hijab xata sa d'an karami idan ta isa gate ta cire..." Abuturrab da idonsa ke kan titi murya can kasa yace "But mami ae lullubi ba shine abinda xai sa ka gane mutum me addini ba, a xuci....." Tunda ya fara Mami ke masa wani kallo bata bari ya kai aya ba a tsawace tace "Meye hadin ka da yarinyar nan Aliyu, who is she?" Shiru yayi har sai da tace "Baka ji na ne?" A hankali yace "She's just a frnd Mami...." Tsaki tayi ta ci gaba da danna wayarta, bai sake cewa komai ba har ya isa inda xai ajiyeta, yayi parking ya juya yana kallonta yace "Mun kawo Mami" bude motar tayi ta fita tana kallonsa tace "Yaushe xaka koma gida?" Yace "Zan bar clinic karfe hudu" tace "Ohk...." Yace "Xan biyo in dauke ki ne?" Tace "No, kafin lkcn ni na koma gida..." Daga haka tace "Allah ya tsare" sannan ta shiga gidan, ya kusa minti uku kafin ya ja motar jiki a sanyaye ya bar wajen. Karfe biyar da wani abu yana xaune kofar gida yana danna waya blessing ta xo wucewa, mikewa yayi da sauri ganinta yace "Hello!" Ta juya tana kallonsa sannan tace "Ina yini?" Yace "lafiya lau, plss wait in baki sako ki ba Samantha!" Da sauri ya shiga gida ba a dau lkci ba ya fito rike da takarda a linke ya mika mata tare da dubu daya yace "Ki bata pls" karba tayi tace "xan bata, nagode" daga haka ta wuce, ya sauke ajiyar xuciya ya koma ya xauna. Samantha ta fito daga wanka bayan magrib blessing ta bude kofar dakinta ta karasa da sauri tace "Sister Rebecca wannan Doctor din yace in baki takardan nan..." Da sauri Samantha ta karba Blessing ta juya ta fice kafin Mumy ta fara nemanta, xaunawa tayi gaban mirror tana goge jikinta tana gamawa ta dauko lotion ta fara shafawa sannan ta dau turarruka fiye da kala biyar ta feshe jikinta da su, sai da ta gama ta dau takardan ta bude, rubutu ta gani kamar haka "ki taho don Allah am waiting for you love...." Ajiye takardar tayi hade da tabe baki ta mike ta dauko kayan baccinta ta saka snn ta tusa gashinta a net, ta kusa minti talatin xaune, can ta mike a hankali ta bude closet dinta ta dauko daya daga hijabs din da take sawa lkcn sanyi ta saka shi har kasa, ta kashe wutan dakinta ta fita, tana waige waige kamar munafuka har ta fita daga gidan. Ta jima tsaye bakin gate din gidan kafin ta tura a hankali ta shiga ta rufe, bbu kowa parlon ta tsaya bakin kofa tana kare ma ko ina kallo, fitowa yayi daga bedroom, yayi murmushi yana kallonta ya karaso yace "Woaw she came!" Rufe kofar yayi yasa key yace "Welcm love" ta hade rae tace "me yasa kace in xo?" Yace "I just want to see you" turo baki tayi tace "Bude min kofa in wuce...." Wara ido yayi yace "Noo, not until you repeat what you said yesterday...." Juyawa tayi da sauri tace "Noo, plss ka bar ni in wuce..." Murmushi yayi yace "Then ashe xa ki kwana a nan" kamar xata yi kuka tace "Plsss..." Ya daga kafada yace "Ohk let see" daga haka ya tafi three seater yayi kwanciyarsa, ji tayi kamar ta fashe da kuka, wayarsa ya dauka ya jona earpiece ya makala a kunne hade da lumshe ido, ta kusa minti talatin tsaye parlon ganin ya ki cewa komai ta juyo a hankali ta ga har lkcin idonsa a lumshe suke, can ta karasa kusa da shi ta duka tana kallonsa sae ta ga kamar bacci yake, kasa dauke idonta a fuskarsa tayi, can ta cire earpiece daya a hankali ta kai kunne taji karatun Qur'ani yake ji, mayar masa tayi, ta matsa kusa da shi har lkci tana kallonsa, a hankali tace "I... I said i... Love you!" Kallon fingers dinsa tayi ta kai hannunta tana kallon Ring din azurfan dake hannunsa har biyu, lumshe ido tayi ta daura lips dinta a hankali, rike hannunta yayi ta sake sa da sauri duk ta daburce xata mike ya ki saketa ya mike xaune.

*Haske writers asso*=???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

21.....

Kin bari su hada ido tayi tana girgixa kai tace "Doctor plss ka sake ni..." Yace "Noo..." Kwankwasa kofa aka yi suka kalli kofar a tare, ta xaro ido tace "Wayyo ka sake ni..." Saketa yyi ya mike yana kallon kofar, ta tashi da sauri tayi hanyar bedroom, karasawa gun kofar yayi yace "Waye?" Muryar Ramla ya ji tace "Ni ce!" Yace "What?" Tace "Abba yana kiran ka wai..." Yace "Alryt ga ni nan xuwa" tace "Toh baxa ka bude ba yaya?" Yace "Yess" tabe baki tayi ta juya ta wuce, juyawa yayi ya shiga bedroom din ya ganta tsaye bakin kofa, tana ganinsa ta juya, ya rungume hannayensa yace "Ashe kina sa Hijab?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ina wayar da na baki?" A hankali tace "Yana gida!" Ya juyo da ita yana kallon fuskarta yace "ki ajiye shi kusa da ke yau, i will cal you" ta sunkuyar da kanta tace "Toh" yayi murmushi yace "Mu je in raka ki" hanya ya bata ta fita sannan ya fita shi ma, har kusa da gidansu ya rakata yana kallonta yace "Kar kiyi bacci fa, i will call you..." Daga haka ya juya ya wuce ta bi sa da kallo, snn ta nufi gate kamar mara laka ta shiga. Abuturrab na isa gida ya wuce parlor din Abbansa, Abba dake waya tun shigowarsa ya ajiye bayan ya gama yace "Aliyu!" Abuturrab yace "Na'am..." "Kadai san in ka raina ni to yakumbo ta wuce raini a gun ka koh?" Cewar Abba kenan yana kallonsa, Abuturrab ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai, Abba yace "Tashi ka je...." Ba musu ya mike murya can kasa yace "Kayi hakuri Abba dama..." Kofa Abba ya nuna masa, hakan yasa ya fita kawai, sha biyu saura ya gama abinda xai yi ya rufe laptop snn ya dau wayarsa yayi dialing layinsa dake wayar da ya ba Samantha, tana kwance hannunta rike da hymn book tana dubawa kiran ya shigo wayar dake gefenta, langwabar da kai tayi ta dauka ta yi picking ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Hope baki yi hacci ba?" Tace "Yanxu xan yi..." Yace "Tafi ki wanke idon..." Murmushi tayi ta make kafada kamar yana ganinta, yace "Ina son in maki wani tambaya samha..." Tace "Samantha not samha..." Yace "Noo samha not Samantha.." Tace "Uhm to ina jin ka..." Shirun kusan second ashirin yayi kafin yace "Za ki iya aurena?" Kasa cewa komai tayi sbda mamaki da ya cika ta, yace "I know you re there!" A hankali tace "Aure kuma?" Yace "Yeah.." Ta girgixa kai tace "But ae bbu aure tsakaninmu da kai, our religion differs, am a Christian, you re a muslim..." Yace "Akwai aure tsakaninmu...." Da mamaki tace "How?" Ya shafa kai yace "Sai kiyi addinin ki in yi nawa!" Wani shirun ta kuma yi words dinsa na mata yawo a kai, murya can ciki yace "Samha!" Kasa amsawa tayi, cikin sanyin murya yace "Baki so na kenan..." Jikinta yayi sanyi still ta rasa abun cewa, kiranta ya kuma yi kamar xata yi kuka tace "Ni ban san me xan ce ba..." Yace "Ki ce za ki aure ni" tace "you know that's very impossible, taya hakan xai yiwu bayan addininmu daban daban...." Lumshe ido yayi yace "Nace maki kowa addininsa xai yi, i see nothing wrong with that...." Rasa ma wani tunani xata yi a lkcn tayi, xata iya auren Abuturrab kuwa? Did she even love him? She know she so care about him.. Tunanin hakan sai da yasa gabanta faduwa sosai, to in ta yarda xata aure sa Mumy da Abba fa? Ya relative dinsu xa su dau xancen... Muryarsa taji yace "Samha!" Hawaye ne ya cika idonta ta kasa amsawa, da dadewa tasan she had alwayz like him, amma bata taba tunanin har xae shigo da xancen aure tsakaninsu ba, a hankali taji yace "Shikenan sai da safe" lkci daya hawayen idonta ya xubo cikin rawar murya tace "Doctor kasan baxai yiwu ba, My parent... My relatives, my...." Kuka ta fara masa, duk ya rikice yace "Kuka kuma... Pls stop it now" kasa daina kukan tayi, yace "OMG don nace xan aure ki shi yasa ki kuka, ok am sorry baxan sake ba..." Daga haka ya katse wayar, ya jefar gefensa ya kashe wuta yayi kwanciyarsa, hade kai tayi da gwiwa ta fara kuka, daga karshe ta gaji ta kwanta, kasa bacci tayi daren ranan, maganganun Abuturrab kadai ke mata yawo a ka, sae kusan karfe uku ta samu bacci ya dauketa, Mumy ce ta tasheta karfe takwas da minti sha biyar, ta mike xaune, Mumy tace "Baki tashi kinyi morning devotion din ki ba wnn wani irin bacci kika yi" Kallon idonta Mumy tayi tace "Me ya samu idon ki, kuka kika yi ne?" Samantha ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "kai na ke min ciwo..." Mumy tace "Kai kuma? Toh tashi ki shirya sai kiyi breakfast ki sha magani," daga haka ta fita, da kyar Samantha ta mike tsaye don ji tayi gaba daya kanta ya mata nauyi, bathroom ta shiga ta wanke baki tayi wanka sannan ta fito, tana goge jiki Abuturrab ya fado mata wanda hakan sai da yasa gabanta ya fadi sosai, hawaye ya cika idonta, jiki a mace ta karasa shiryawa, Blessing ta shigo da tray dake dauke da breakfast ta ajiye mata ta gaisheta snn ta fita, da kyar ta iya shan tea xata kwanta sai ga Mumy ta shigo da magunguna ta bata ta sha, mumy tace "Thank God sai da ku ka gama jarabawa ciwon kan ya same ki, ki kwanta xuwa anjima mu ga" daga haka ta fita, Samantha ta kwanta hade da lumshe ido, ta kasa daina tunanin Abuturrab ta kuma rasa dalili, a da tasan yana yawan fado mata barin idan suka dade basu hadu ba, amma tun daga jiya da daddare xuwa yau sae ta ga ya fi na ko da yaushe, to fushi yayi ne yasa ya kashe wayarsa amma ai gaskiya take fada, runtse ido tayi ko bacci xae dauketa amma shiru, sae a lkcn tasan ashe fa ta damu da shi haka. Har washegari Abuturrab bai sake kiranta ba, ita dai tasan bbu wani ciwon kai but da Mumy ta tambayeta me ke damunta sai tace ciwon kai, tun da take abu bai taba tsaya mata a rai kamar yanda wannan ya tsaya mata ba, ta kasa dauke tunanin a ranta, Mumy ta kira Abba dake Lagos ta fadi masa bata da lafiya xa su je asibiti, Abba yace ba sai anje ba xae turo likita, Abuturrab na xaune office yana aikin gabansa, baka taba cewa abu na damunsa sai dai da xaka shiga xuciyarsa ka ga tulin damuwar dake tattare da gun sae ka tausaya masa, babban damuwarsa bai san yanda xae yi da Yakumbo ba don yasan shi ake ta jira, gashi ya kasa daina tunanin Samantha, yasan ba fault dinta bane that's just the fact but kawai ya shareta ya kuma dau ma kansa alkawarin ko ba yanxu ba sai ya aureta ko da kuwa threatening din kisa xa ayi masa, Tun a daren yake raya ma kansa to ko ya koma ga saudat, yana jin kuma xuciyarsa ta aminta da hakan coz he gat no option. Daren ranan ya shirya ya tafi gidansu Saudat, tun da yayi parking a kofar gidansu yake kallon motar dake parke gaba da nasa ganin kamar akwai mutane a ciki, ae ko sai ga shi an bude motar saudat ta fito, tabe baki yayi ya tada motarsa kawai yayi reverse ya bar gun, bai bar layin ba kiranta ya shigo wayarsa, ya ci gaba da tukinsa ba tare da ya sake kallon wayar ba. Washegari Wednesday yana xaune office ya hade kai da table Mujaheed ya shigo, har ya karasa gun table din Abuturrab bai dago ba, mujaheed ya bugi table din yace "Bacci kake a bakin aiki doctor?" Dagowa Abuturrab yayi yana kallonsa yace "Daga ina haka?" Mujaheed yace "Asibiti na xo bani da lafiya mana" murmushi Abuturrab yayi yace "Ohh i see" mujaheed yace "Ya na ganka haka kamar kana tare da damuwa" Abuturrab yayi yake yace "Damuwa kuma, am just tired ne, ya aiki?" Mujaheed yace "Alhmdllh"

*Haske writers asso*=???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

22......

Hira suka ta yi a asibitin har bayan la'asar suna fitowa daga masallaci ko wannensu ya dau hanyar gida, yau kam Abuturrab a main house dinsu ya sauka, Mami dake parlor ta bi sa da kallo bayan ya gaisheta har ya haura sama, wanka yayi ya fiddo jallabiyarsa a daki ya sa yayi kwanciyarsa. Ringing din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login