Showing 60001 words to 63000 words out of 180592 words

Chapter 21 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1139

mu ba anjima xa mu dau hanya" Baffa yace "Allah mai girma, shi yasa ba a sabo da bako, baxa ku jira hat in dawo da rana ba" Abuturrab yayi murmushi yace "So nake mu isa gida da wuri ne" Baffa yace "Toh Allah ya tsare, ni bani da komai da xan baku, amma Binta xata tatsar maku nonon shanu ku tafi da shi bamu da komai baya ga wannan" Abuturrab yace "Ayya ba komai Baffa mun gode da karramawar ma" Alto yace "Toh Allah ya tsare, ku gaida mutan gida Allah ya tsare gaba" Abuturrab ya fiddo dubu goma cikin kudin jikinsa ya mika masa yace "Ga wannan ba yawa Baffa, in shaa Allah wataran xamu kawo maku ziyara" Alto ya bude ido yace "A yi haka?" Abuturrab yace "Kai dai ka karba Baffa" Alto ya karba da hannu biyu ya dinga sa masa albarka yana masu Allah ya tsare hanya har ya fita, Wanka Abuturrab ya shiga kewayen gidan yayi ya fito ya shiga Bukka, har lkcn bacci samantha take, ya shirya cikin kayansa da ya wanke jiya ya fita da na Baffa yana kallon Binta dake xaune tsakar gidan ita kadai yace "Baaba fa?" Bata kallesa ba tace "Ta je kauyen dake gaba da namu siyo gyero" yace "Ki ban sabulu xan wanke kayan nan" ta mike ta isa gabansa ta karba kayan tace "Xan wanke" yace "Noo, kar ki damu xan wanke" bata saurare sa ba ta nufi gun randar ruwansu ta diba, ya daga kafada ya juya ya koma daki ya bude flask din da ta basa ya ga kunu ne ya bude coolern ya ga kosai, diban kunun yayi ya dau kosan ya fita ya shimfida tabarma ya xauna ya shiga ci a nan, lkci lkci yake kallonta har ta gama wankin ta shanya kayan a igiyar dake tsakar gidan, ya koma inda take ta xauna, yace "Ke kin karya?" Gyada masa kai kawai tayi, yace "Yaushe Baaba xata dawo?" Tace "Kila tana hanya yanxu" yace "Bakya xuwa makaranta ne?" Ta kallesa tace "Yau alhamis" ya d'an buda ido yace "Haka fa" Bai kuma cewa komai ba, can tace "Bacci take ne?" Yace "Ehh" haka suka yi ta xama tsakar gidan shiru har Hansae ta dawo ya mike ya karbar mata kayan hannunta snn suka gaisa. Sai kusan tara da rabi Samantha ta tashi, har lkcn Abuturrab na xaune waje, ta mike ta dau sabulu da sponge ta fita, su biyu ne tsakar gidan shi da Binta dake wanke gyero, Samantha bata ko kallesu ba Abuturrab da ya bi ta da ido yace "Wanka xa ki yi?" Binta na jin haka ta mike tace "Bara in juye maki ruwan xafin ki" daga haka ta dau bokiti ta nufi gun murhu ta juye ruwan kai ta kai bokitin gun randa ta sirka ta kai kewaye tace "Bara in dauko maki sabulu" Samantha tace "Akwai sabulu a nn" Binta ta dauko kwando ta mika mata Samantha ta shiga bayin, mikewa Abuturrab yayi ya shiga daki.

*Haske writers asso*

Da fatan anyi sllh lfya Allah ya maimaita mana.
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By Khaleesat Haiydar=???
'
32.....

Samantha na shigowa bayan tayi wanka bata ko kalli Abuturrab ba ta nufi gun kayan da ya siya ta durkusa, can ta kallesa taga kallonta yake ta bata fuska tace "Kaya xan sa?" Ya wara ido yace "Na rike ki? Ki sa mana" tace "Toh ka fita" murmushi yayi yace "In fita gun Binta ki kuma daure min fuska" daukar abinda xata dauka tayi ta nufi kofa ya fixgota tace "Wayyo ni ka kyaleni kaya na xan je in sa a waje..." Ya wara ido yace "Toh me xa ki boye min da ban sani ba jikin ki!" Ta yi masa wani kallo tace "Ae dai na wasu ka sani ba nawa ba malam" Dariya yayi ya kai bakinsa kunnenta yace "See you, ke nakin ma special sani xan masa, sanin da bbu wanda xai kara masu har abada.... Only me" kwace kanta take son yi ya ki saketa, ta boye fuskarta jikinsa kamar xata yi kuka tace "Bana son irin haka Doctor" yana dariya yace "Toh na daina baby, but a nan xa ki sa kayan ki" bbu yanda ta iya haka ta shirya a dakin, and he pretend he's not looking at her, tana gama shiryawa ya xuba mata kunu ya mika mata ta sha kadan ta ajiye kosan ma bata ci ba, yana kallonta yace "Xa mu tafi yanxu!" Kallonsa tayi bata ce komai ba, can ta mike ta fara gyaran dakin, ya taimaka mata suka gama, sha daya suka fito xa su wuce, Hansai ta fito tana masu Allah ya tsare hanya tana cewa Allah sa ba shikenan an gama xumuncin ba, Abuturrab yayi dariya yace "In shaa Allah baxa mu mance ku ba Baaba wataran xa mu xo, dubu uku ya bata ta dinga godiya har da hawayenta, Abuturrab ya kalli Binta dake xaune nesa da su yace " Babu Sallama Fatima" kallonsu tayi yaga hawaye cike idonta, Hansai tace "Kaji shashanci to tashi ki rakasu mana" Samantha tayi ma Hansai sallama sannan ta fita, Ya karasa kusa da Binta ya durkusa yace "Nace maki xamu xo wataran fa..." Bata ce komai ba sae share hawayen idonta da take yace "Toh tashi ki raka mu" ba musu ta mike ta dau sandar ta na kiwo da nonon da ta tatsar masu yana gaba tana biye da shi a baya suka fita. Karasawa yayi ya kamo hannun Samantha yace "Baku yi sallama da Binta ba" ta kalli Binta ta gefen ido tace "Mun tafi Allah ya saka da alkhairi" kai kawai Binta ta gyada mata, daga haka yace "Mu je to ki raka mu inda xa mu samu Babur" gaba ta shiga suna biye da ita a baya, sun yi nisa sosai sai ga wata mota na tahowa a bayansu, Abuturrab yace "Wannan fa" Binta ta kalli Motar tace "Motar D'an lado ne, shi daya ne mai mota a rigar nan a birni yake aiki, da ka tsayar da shi ka ji inda xa shi ko?" Abuturrab ya tsayar da motar kamar yanda tace ae ko ya tsaya ya sauke glass, Abuturrab ya gaida sa mutumin da xai iya kaiwa arba'in ya amsa yana kallonsa, Abuturrab yace "Don Allah idan ba damuwa ina ka nufa?" Mutumin yace "Gombe xa ni...." Abuturrab ya d'an yi shiru, sae kuma yace "Toh mu ma can muka yi, xa a taimaka?" Mutumin yace "Ba matsala ku shigo" Abuturrab ya bude ma Samantha baya ta shiga ya rufe, ya kalli Binta da wasu hawayen suka cika idonta ya ciro dubu biyu duk da ya so bata fiye da haka ya damka mata a hannunta yace "Na maki alkawarin wataran xa mu dawo" da kyar ta yarda ya sa mata a hannunta ta mika masa nonon dake a leda ya karba yayi godiya sannan ya juya ya shiga front seat ya d'aga mata hannu ta juya da sauri ta bar wajen, D'an lado ya ja motarsa yace "Amma ba nn rigar kuke ba koh?" Abuturrab yace "Eh mu baki ne" D'an lado yace "Da alama kam, toh Allah ya sauke mu lafiya" daga haka ya maida hankalinsa kan tukin da yake da gani dae kasan hannunsa bai gama fadawa ba, ta madubi Abuturrab ya dinga kallon Samantha ganin yanda ta wani turo baki, dariya yake son yi amma ya dake, har suka isa gombe bayan tafiyar awa biyu da rabi bbu wanda yace komai cikinsu, Abuturrab sai kallon garin gombe yake yana tunanin to ina xa su, bbu wanda ya sani a gombe infact bai ma taba xuwa ba, D'an lado ya katse masa tunanin da yake yace "ina xa ku sauka kenan?" Abuturrab ya kallesa yace "Ko nan ne ka sauke mu" D'an lado yayi parking Abuturrab ya bude motar ya fita, ya xaga ya bude mata ita ma ta fito, ya karbi ledan kayan dake hannunta yayi ma D'an lado godiya ya ja motarsa ya wuce, kalle kallen wajen Abuturrab ya shiga yi, yana neman bankin da yake ajiya, yaga duka ukun a area din, yasan first bank da Gtb ba dai layi ba, hakan yasa yayi deciding ya shiga unity, ya kalle Samantha yace "xan shiga bank, sai ki jira ni waje or we go in 2geda" ta girgixa masa kai kawai tayi xamanta gaban bank din, shi kuma ya shiga ciki, direct ya tafi gun CC, bae wani jima ba aka xo kansa, yace yana son a duba masa ko nawa ne account dinsa, daga sama har kasa matar ke kallonsa, can tace "ATM din waje me yake yi, ko wayar ka fa?" Yace "Akwai layi sosai, waya kuma bani da, idan xa ki taimaka ki taimaka...." Da kamar xata yi magana sai kuma ta fasa, sai kuma tace "Fado account number" ya fada tayi danne dannenta snn ta kallesa ta kalli hotonsa dake jikin computer tace "Dubu dari shidda da ashirin" ya xauna yace "Good, na gode kwarai, ana sayar da withdrawal slip a nan?" Ta nuna masa gun da xai siya snn ta kira wani customer, yana xuwa ya dauka ya ciro dubu daya da aka ce ya bayar ya mika, ya ari pen ya cike slip din, dubu dari biyu ya saka yayi sign ya nufi gun Cashier, su ma sai da yayi masu jan ido wai wani yaje atm they re busy, yace "Haba wani atm xan je, ba fa dubu hamsin xan cire ba malam, kawai inje in bata ma masu cire dubu biyar lkci, awa nawa xan dauka ina cire dubu dari biyu? Plss answer me coz i wanna get out of here" Ba yanda suka iya haka suka karba bayan minutes din da basu wuce sha biyar ba suka basa kudin sa, nan ya roki alfarmar jaka aka basa ya xuba kudin yayi ficewarsa, ya isa gun Samantha yace "Am sorry Dear, tashi mu je" ta mike ya karbi ledan hannunta suka nufi titi, yana kallonta yace "Dear hotel fa xa mu je kafin mu samo solution" ta kallesa tace "Hotel?" Shiru yayi yana kallonta, ta dauke kanta, ya sauke ajiyar xuciya yace "Just for today dear.... Kinga bamu san kowa a gombe ba, it's my 1st time here" jin bata ce komai ba ya tsayar da mai adaidaita yace "Hotel mafi kusa xaka kai mu" sae da ya tsaya ta shiga sannan ya shiga, ba laifi hotel din na da kyau, ya biya kudin kwana daya dubu ashirin da biyar a reception aka basa makulli da room number, babban daki ne sosai da toilet a ciki, ya kalli samantha da har lkcn ta ki cewa komai ya xauna bakin gado bayan ya ajiye ledan hannunsa yana kallonta yace 'You followed me without trusting me kenan Samha..." Bata bari sun hada ido ba ta karaso dakin a sanyaye ta xauna can karshen gado, girgixa kai yayi ya mike ya bude jakar dake dauke da kudi ya cire dubu dari, ya sa a aljihu yace "Am coming back right away, me xa ki ci?" Cikin sanyin murya tace "Anything" ya juya ya fita ya kulle dakin, tagumi tayi tana tunanin anya did she made the right decision following him and neglecting her dear parent, hawaye ya cika idonta ta fada kan gadon ta fashe da kuka, Why is all this happening to her within just 2 months, she know God will never forgive her for doing this to her parent, but she love him and they will never allow her to be with him, tayi kukanta me isarta ta mike ta dau soap da sponge, toothpaste da sponge ta shiga bayi dake dakin, wanka tayi ta fito ta shirya tayi kwanciyarta nan da nan bacci ya dauketa, bayan azahar Abuturrab ya dawo, ya ajiye ledan hannunsa yana kallonta, bai tada ta ba ya shiga toilet ya dauro alwala ya xo ya gabatar da sllhn Zuhur, ya jima xaune yana addu'a daga bisanni ya mike ya shiga bayi yayi wanka ya fito ya shirya cikin daya daga cikin kananun kayan da ya siyo, ya bude fried rice din da ya siyo masu da drinks ya ci wanda xae ci ya ajiye sauran, kwalin karamar waya ya dauka ya bude ya ciro wayar ya sa sabon sim din da ya siyo ya kunna wayar, ya loda airtime yayi dialing number Hajiya Mariya gabansa na faduwa a xuciyarsa kuwa addu'a yake Allah yasa ita kadai ce a gun, bugu daya biyu ta d'aga, ya shafa kai a hankali yace "Mumy!" Hajiya Mariya dake xaune daki tare da Mami da frnds dinta biyu, ta saci kallon Mumy ganin kallonta take tace "Helloo!" Abuturrab yace "Ina ji Mumy ina yini...." Hello... Hello... Abinda ta dinga cewa kenan can tayi tsaki ta katse, Hajiya Maimuna tace "Network koh?" Hajiya Mariya tace "Ae kuwa...." Hajiya salaha tace "Toh da ki fita waje...." Hajiya Mariya ta tabe baki tace "Kila kiga ya dawo kuma" Abuturrab da sharp thinking yana jin reaction dinta yasan ba ita kadai bace a gun don haka bae sake kira ba, Mikewa Hajiya Mariya tayi tace "Bari dai ban san ko masu bani kudi bne bari inje waje" daga haka ta fita, bata ko kalli Abba dake parlor da abokansa ba tayi ficewarta waje, Abba ya bi ta da kallo, can ya girgixa kai yace "Wannan Mariyar ma ban yrda da ita ba bakinsu daya da Aliyu, ba abun mamaki bne ma tasan inda yake!" Col Usman na girgixa kai yace "ban taba ganin mai taurin kai da tsaurin ido irin Aliyu ba...." Abba yace "Duk ya kuskura ya shigo hannuna wllh sae bullet ya kare a kafafuwansa..." Har kofar gida Hajiya Mariya ta fita sanin halin mijin yayarta, tana fita ta kira number da sauri, Aliyu naganin kiranta ya daga, tace "Aliyu!!" Ya buda ido yace "Mumy..." Tace "Kuna ina Aliyu?" Shiru yayi, tace "Ohh ni din ce yanxu kuma baxa ka gaya ma inda kake ba" yace "Ke kina ina Mumy" ta hade rai tace "Ina tambayarka kana tambayata..." Ya sauke ajiyar xuciya yace "Kiyi hakuri Mumy, but don't say anything to anybody plss...." A fusace tace "Uwarka! ni kake gaya ma haka da can ban ce komai ba sae yanxu" bae san lkcn da yayi dariya ba yace "Yi hakuri Mumy, ina Gombe!" Ta xaro ido tace "Gombe kuma Abuu, wa ka sani a can?" Ya girgixa kai yace "Ba kowa wlh..." Da damuwa tace "Yarinyar fa?" Ya kalli Samantha dake ta bacci yace "Ga ta Mumy, she's sleeping" Hajiya Mariya tace "Kaji tsoron Allah Aliyu, kada kayi using wnn advantage din a kan baiwar Allah don tana sonka, kar ka manta ba fa matar ka bace, don't use her....." A sanyaye yace "Mumy baki yadda da Aliyun ki bane kuma, kema kin san ba hali na bane" Hajiya Mariya tace "No son! Kasan sha'anin rayuwa, bbu abinda shaidan baxae iya yi ba...." Sosai jikinsa yayi sanyi yace "In'sha Allah Mumy xan kiyaye.... Mami fa?"

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
33....

Hajiya Mariya tace "She's inside" ya d'an yi shiru sai kuma yace "Abba fa" tace "Yana nan.... But you re in trouble in har ka shigo hannunsa" Aliyu yayi murmushi yace "Na sani" da damuwa tace "Ka dai kula Aliyu tausayin yarinyar nake, tunda har ta guji iyayenta sbda kai, jan ra'ayinta xuwa musulunci baxai yi wahala ba" Yace "Hakane Mum, dama am planing of marrying her soon don ban son in cuceta, i don't want her to regret trusting me, idan nayi haka komai xae fi zuwa da sauki" Hajiya Mariya tace "Anya, naga kamar ya fi ka jira sae ta amshi musulunci, kar ta ga kamar kana using advantage din auren ne..." Bude gate ta ji anyi da sauri tace "Za mu yi waya Aliyu, don't call again xan dinga kiran ka..." Daga haka ta katse wayar, Abba ta gani bakin gate waya kare a kunnensa ya rako abokansa xa su wuce, tayi dialing din number wata da xata bata kudi suka yi magana snn ta juya ta nufi gate din ya bata hanya tayi wucewarta, bin ta yayi da kallo har ta shiga cikin gida, ya juya ya koma ciki shi ma bayan abokan sun shiga mota, ya shiga part dinsa ya kira Mami, bbu bata lkci Mami ta iso, yana tsaye bakin window rungume da hannunsa (Inda Aliyu ya gado rungume hannu knn, lol" ya juyo yana kallonta yace "Hajarah! i won't take it likely with ur sister idan naga da sa hannunta a abubuwan nan da Aliyu yake, xan ajiye cewar yar uwarki ce a hukuntata yanda ya kamata...." Mami tace "Ban yi mamaki ba... You can do more than that, yanxu kuma ka bar xargina ka koma xargin yar uwata" ya daga kafada yace "Ni dae na gaya maki" juyawa tayi ta fice daga dakin, dakin su Ramla ta shiga ta ci kukanta Ramla na lallashinta kafin ta fita ta koma dakinta, Hajiya Mariya na ganin Abba ya kira Mami dama ta yi saving din number Aliyu da wani suna daban tayi deleting dinsa daga call log, ko da Mami ta shigo dakin Hajiya Mariya na bathroom, ta dau wayarta ta fita, kiranta na karshe ta kura ma number ido, can tayi dialing taji muryar mace, ta dudduba dai bata ga alamar komai ba ta koma daki, Hajiya Mariya bata tambayeta dalilin daukan wayarta ba sae harkan gabanta take. Tunani Abuturrab ya dinga yi ko dai gida xae kama masu nan gombe ne, duk ya rasa takamaiman solution, kallonta yayi ganin tana juye juye kan gado, can ta mike xaune yace "Cikin ya fara koh?" Ta gyada masa kai, ya mike ya dauko mata abinci yace "Sauko ki ci in maki allura"???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ba musu ta sauko ya bude mata abincin ta fara ci, alluran ya hada ya ajiye yana jiran ta gama, bata wani ci da yawa ba ta mike yace "Sauran fa" da kyar tace "Anjima xan ci" daga haka ta kwanta ya mike ya karasa kusa da ita yayi mata alluran, Finger dinta ya kura ma ido ganin har lkcn xoben da ya sa mata na nan,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login