Showing 159001 words to 162000 words out of 180592 words

Chapter 54 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1150

kawai kuke" ta fashe da matsanancin kuka tace "Me nayi maku David da xa ku bar ni da kadaicin 'ya ta haka, ita ma fa Maryam Uwa ce, idan yar ta tayi mata haka xata ji dadi, tsawon lkcn nn kun san inda ya ta take ku ka bar ni ina yawo duniya nemanta, what have i done to deserve dis" Girgixa kai yyi yace "Haukan ki ne yafi karfin ki shi yasa bbu wanda ya damu ya nuna maki yasan inda take, ina ce kwanaki cewa kika yi kasheta xaki yi da xata shigo hannun ki, toh ko nasan inda 'ya ta take wnn furucin naki xai sa in fito in gaya maki" a fusace tace "Kai baka san baraxana ba david, kaza ce da xan kasheta, ko wani ya dau min cikinta yyi wahala ya haifar min ita da xan kasheta" yace "Better, Samantha tana nn lfya kuma ita ma tana kewar ki tare da tagawayenta maxa" rikosa tayi a rikice tace "A ina take David?" Yace "Tana nn lafiya dai" ta fashe da kuka sosai tace "Amma kuma baxan ji inda take ba koh, sbda ni ba xuciya ce a kirjina ba koh, sbda ba ni na haifeta ba koh," xaunar da ita yyi gefen gado yace "You make me a promise that you will act smartly idan na kai ki inda samantha take, ki min alkawarin baxa ki yi abinda bai dace ba a can...." Share hawayen idonta ta shiga yi da sauri tace "Na ji David" yace "A'a ba kin ji ba, cewa nayi ki min alkawari" tace "Nayi alkawarin" yace "Good, ki ci abinci sai ki shirya in kai ki inda take" mikewa tayi da sauri tace "Am full, kuma a shirye nake dankwali kawai xan daura" duk ynda ya so ta ci abinci kin ci tayi, yace to ta jira a idar da magrib, ana idarwa kuwa suka bar gidan a motarsa suka taho gidansu Abuturrab, kallon gidan kawai take da shock, yace "Kin dai yi alkawari Rachael" daga haka ya fito ta bi bayansa da sauri, number Maryam ya kira yace mata yana waje ta fito, ba a dau lkci ba sai ga ta, ba karamin kidimewa tayi ba ganin Rachael, ita ko tana tsaye idon nn cike da hawaye, Maryam ta kasa cewa komai duk jikinta yyi sanyi, Mr David yace "Ki shiga da ita ciki ta ga Samantha" a hankali tace "Toh" daga haka ta shiga ciki Rachael ta bi bayanta, Mr David ya koma cikin motarsa, suna shigowa parlor Hajiya Mariya dake ta gyare gyare ta dinga kallonsu kuma ko ba a gaya mata ba ta san wacece don ta taba ganinta, xaunawa Rachael tayi tana kare ma parlon kallo, Anty Maryam na kallon Hajiya Mariya tace "Hajiya mahaifiyar Samha kenan" Hajiya Mariya tayi karfin halin ce mata sannu da xuwa, Anty Maryam kuma ta wuce sama, Abuturrab ne ya shigo parlorn tare da Sadeeq, still yyi yana kallon Rachael da mamaki, ita ko kallo daya tayi masa ta dauke kai, Sadeeq kansa sai da yayi jim ganinta, da kyar Abuturrab ya karasa parlorn ya xauna yace "Ina yini?" bata kallesa ba bare ta amsa gaisuwarsa, ya kalli Sadeeq da ya wuce sama abun sa, can ya mike ya bi bayansa, Noor da har ta fara baccin gajiya ta saka Hijab suka fito tare da Anty Maryam da ta dau Ahmad, Ilham kuma ta dau Abbakar, bata san dai da wanda xa su gaisa ba amma ta fara gajiya da fitowa, a corridor suka hadu da Abuturrab, ya gaida Anty Maryam tayi masa sannu da xuwa, kallon Noor da ta ki dago kanta yyi sai ma wucewa gaba da tayi ta bar su a gun.

*Haske writers asso*

Mumy's, Anty's, Uncles.... Lil Haiydar is grateful for the wishes, Allah bar xumunci.=؝?
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
95.....

Anty Maryam tace "Did you greet her? I mean her mum?" Abuturrab ya gyada kai yace "Na gaishe ta" bata kuma cewa komai ba ta bi bayan Noor da har ta sauka kasa, a hankali Noor ke tafiya tana kallon wacce ke xaune kan kujera tayi backing dinta, haka kawai gabanta ya shiga faduwa sosai, can ta daga kai ta kalli Hajiya Mariya dake tsaye parlon, sunkuyar da kai tayi ta karaso cikin parlon, kasa motsi tayi inda take tsaye bayan sun yi ido hudu da mum dinta, ta rufe bakinta kar ta saki ihun dake shirin fitowa bakinta, lkci daya hawaye ya cika idonta, ta karasa da gudu ta fada jikinta ta rungumeta ta fashe da kuka sosai cikin rawar murya tace "Mumy..." Rachael dake ta mata wani kallo ta turata gefe tace "Ja can munafuka duk tsawon lkcn nn baki san inda nake bane xa ki fashe da kukan munafurci, ni kika so kashewa ko? Toh God of Abraham ya fi ki, ina nn ban mutu ba" sai kuma ta fashe da kuka sosai tace "Yanxu Rebecca namiji kika xaba a kai na koh? Kika dau namiji uba sbda hankalin ki ragagge ne koh Samantha?" Noor ta kuma fashewa da kuka sosai tace "Forgive me mum, don Allah ki yafe min" buga bakinta tayi tace "Shut up, in kin ga na yafe maki to Jehovah ma ya yafe maki ne, don ba ni kadai kika yaudara ba har shi" Anty Maryam dake tsaye kansu dai bata ce komai ba, a hankali ta jiye mata Ahmad dake hannunta a cinyarta, Rachael ta hadiya sauran fitinar dake shirin fitowa bakinta tana kallon yaron, Ilham ma dake tsaye gefe sai kallon ikon Allah take ta karaso ta ajiye mata Abbakar shi ma a jikinta, Rachael dai sai kallon kyawawan yaran take, tuni dama Maryam ta bar parlon sai Hajiya Mariya dake tsaye da ilham, can Rachael ta goge hawayen idonta tace "Eh toh da yake duk abinda jehovah ya rubuta sai ya faru, wnn abun da ya same ni rubutattce ne, kuma ni na gode ma Allah da na iya jure wnn bak'ar faith din" Daukar Ahmad tayi ta rufe ido tace "You are blessed in jesus name...." Hajiya Mariya ta yo waje da ido haka ma Ilham, ta ajiye yaron ta dau dan uwansa shi ma ta fadi masa haka, snn ta fara masu addu'a idonta rufe dai dai shigowar Col parlon, tsaye yyi yana kallonsu, can yyi murmushi yana gyada kai ya wuce sama, ita dai Noor na xaune gefe ta kasa dago kanta, Rachael tayi addu'a me isarta ta kare adduar da cewa "You are all covered with d blood of jesus my babies" snn ta bude idon ta hade rai tace "Tashi dauko mun kayansu mu wuce gida," Kallonta kawai Noor take ta kasa cewa komai, can ta juya a hankali kalli Hajiya Mariya dake ta kallon ikon Allah, tuni Rachael ta mike tana rike da yaran tace "Wai ba kya ji na ne" Noor kamar xata yi kuka tace "Mum...." dungurinta Rachael tayi tace "Baxa ki tashi ba sai na mare ki" Hajiya Mariya tace "Amma Madam kinga baxai yiwu su fita ba ynxu jego fa take, ina xa ku cikin sanyin nn" wani kallo ta watsa ma Hajiya Mariya tace "Sai aka ce maki a kafa muke? Wato ku kadai ne masu mota koh?" Daga haka ta kuma yi ma Noor tsawa tace "Tashi nace, ba ma sai kin dauko kaya ba ynxun nn sai david ya fita ya siyo masu" Ilham ta juya ta wuce sama don kiran Mami, Sai ga Mami da frnds dinta biyu da Ummi sun sauko parlon, Mami na kallonta tace "Ina yini" ba tare da Rachael ta kalleta ba tace "Lafiya qlau" Ae da ta sake yi ma Noor wani tsawa bata san lkcn da ta mike tsaye ba a tsorace, fuskarta a tsuke tace "Fita mu je nace ko nan din gidan uban ki ne" Frnd din Mami Hajiya Rahina dake tsaye tace "Amma kuma Madam ae gidan Uban yaran hannun ki ne" a dakile Rachael ta dinga kallonta tace "So? Idan gidan ubansu ne sai aka yi yaya? Ina ce ita ta haifesu?" Hajiya Rahina ta girgixa kai tace "A'a kmr ynda kika ce ta tashi ku tafi gidan ubanta, su ma sai ki bar su gidan ubansu" Tsaki Rachael ta ja tace "Toh baxa a bar su ba, abinda nake so ki gane a nn shine ae ba wani ya haifar mata su ba, ba uban ya haifesu ba" Hajiya Mariya tace "Amma kuma ai mijinta bai mata izinin tafiya ba naga" Rachael tace "Wani mijin, ni ban ma 'ya ta aure ba, kar wanda ya sake lakaba mata miji, duk da ma ni ynxu ba ta ita nake ba, albarkacin nonon da xata basu yasa ma ni xan tafi da ita yanxu, banda haka ni da ta bi ni da kar ta bi ni duk uwasu daya ubansu daya, yara ne dai suka xama dole in tafi da su don nawa ne, dama ance min duk 'ya yan da ban haifa ba ita xata haifar min su, ba don ita kadai Allah ya halicce ni ba," Ita dai Anty Maryam na sama tana jin hayaniyar Rachael ta kasa saukowa, ganin dai ta dage sai ta tafi da yara da Noor tayi karfin halin saukowa parlorn, da kyar tace "Sister Rachael bai kamata kice xa ki tafi da su ba, kin ga....." Wani tsawa Rachael tayi mata tace "Munafukaa, muna nn dake Allah xai mani sakayya, ba dai 'ya ta kika jefa a halaka ba har abada ni dake Maryam kuma ni ba yafewa xan yi ba, kika sake tsomo bakin ki nn kuma sai na baki mamaki, muguwa kawai" Mami dai sakin baki tayi tana kallon ikon Allah, Ummi da ta kasa cewa komai tun daxu tayi karfin halin cewa "Madam kiyi hakuri don Allah a xauna ayi magana ta fahimta" ta gefen ido Rachael ta kalleta tace "Ban san shi ba, fahimta dai koh? To ni bn san shi ba" Abba ne ya dawo parlon yace "Ku bar ta su tafi, you go with them...." Muryar Abuturrab suka ji yana saukowa daga stairs yace "Noo Abba.... they are nt going with my children" Noor ta juya tana kallonsa hawaye cike idonta, Rachael tayi wani shewa tana hararansa tace "Halan kai ka dau cikinsu ka haife su??? Ai idan kaga na fita bbu yaran nn yau toh a sume aka fitar da ni parlon nn, suman ma irin dogon nn da ban san waye a kai na ba, yau dai jikokina baxa su kwana gidan nn ba ko da ita bata yrda ta bi ni ba ta sha xaman ta, kuma daga nn church na nufa da yara a sa masu albarka kmr yanda kaga uwarsu tayi albarka har ta haife su" Mami sai kallon Abuturrab dake tahowa take, Sadeeq kam tsaye yyi sama ya rungume hannu yana kallonsu, Abuturrab ya karaso parlon ya girgixa kai yace "Sorry ni baxa ki fitar min da yara gidan nn ba, it's nt, nd wil never be possible" tana masa wani kallo tace "Then i will show you that it's very possible" Abba ya kallesa ya hade rai yace "Leave immediately now" ya girgixa kai yace "But she can't just leave with my children dad...." Wani tsawa Abba yyi masa yace "I said leave now" Rachael ta ja tsaki tana hararan Noor dake kuka sosai tace "Idan kin so ki biyo ni ko kar ki biyo ni, hakan baxae sa jikokina su yi starve ba, i will get them a better milk" daga haka ta nufi kofa tana wakan church, Sadeeq ya sakko da sauri yace "But Abba ina xata kai yaran mutane, she can't just..." Wani kallo Abba ya watsa masa shi ma yace "Leave too before i kick you out" Noor ta xube kan kujera ta fashe da kuka sosai, lumshe ido Abuturrab yyi maganganun Small mum dinsa da tayi masa da dadewa na yawo a kansa 'meye makomar kids din ka Aliyu??? kar ka manta ita xa kayi converting ba family dinta ba, sannan Kasan baxa ta taba rabuwa da family dinta ba, Aliyu keep everything aside and think reality, this is the biggest mistake you are to make in ur life' bude ido yyi ya juya a hankali yana kallon Small mum din tasa ya ga ita ma kallonsa take, Hajiya Rahina da kanta ya gama daurewa tace "A'a Col, gaskiya wnn ba magana bace ya xaka ce a bar ta ta tafi da su, kaji fa inda take cewa xata kai su ynxu wai church!" D'an murmushi yyi yace "Kin mance wanda ya k'i ji baxae k'i gani ba? Shi ya ji ya gani kuma xai iya, i just love her action, bbu kuma ynda xa' ayi a rabata da jikokinta kema kin sani, yes ta kai su duk inda xata kai su she have the right" Ummi da ranta ya gama baci tace "Noo Abban Aliyu, u re sounding Sarcastic" Col ya girgixa kai yace "Rather, i am absolutely right" daga haka ya juya ya bar parlon, wani kallon gefen ido Sadeeq ya bi sa da shi haka ma Hajiya Mariya dake ji kmr ta kwade sa, Mami kam tuni hawaye ya fara sakkowa idonta, shi dai Abuturrab ya kasa kallonta, tuni Rachael ta isa kofa xata fita suka kusa cin karo da Yakumbo da ta rafka uban sallama da kaya niki niki a kai"

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
96.....

Yakumbo ta dire kayan dake daure kanta tana kallon yaran hannun Rachael da ke kkrin fita kofa tace "Ke ya haka, ina xaki kai 'ya yan mutane da magariba, wani gwanannen ne baxai shigo ba sai an fitar masa da 'ya yan waje cikin sanyin nn" ko kallonta Rachael bata yi ba ta fice daga parlon, Yakumbo ta juya tana kallon su Hajiya Mariya dake tsaye parlorn tace "Wace mahaukaciya ce kuma wnn? ko dai kurma ce" Hajiya Mariya tace "Sannu da xuwa Yakumbo, ba mahaukaciya bace, xuwa tayi ta tafi da yaran wai" Yakumbo ta d'an yo waje da ido tace "Ta tafi da su? Ina xata kai su" karasowa parlon tayi tana kallon Mami da ta kasa daina hawaye ta kuma kallon Hajiya Mariya tace "Ke wai me ke faruwa, Aliyun sake gudu yyi?" Bata rufe baki ba ta gansa tsaye kansa a kasa yana rungume da hannunsa, ta tafe hannu hade da kyabe baki tace "Ikon Allah, Ka gaji da guje gujen ka dawo kenan, ae dama duk wawan da ya bar gida da kafarsa to fa da kafafuwar nn xae dawo in da rai da lafiya, ni ba dan naka naka bane da na ja maka Allah ya isa a kan wahalhalun da ka saka k'anina Aliyu, uwar ka kam dama bakin ku daya da figaggiyar kanwarta...." Daga haka ta ja tsaki tace "Na xo ne dama ayi ta ta kare ina Ahmad din..." Daga haka ta dau hanyar stairs, Rachael na fita gate Mr David ya fito daga mota da sauri yana kallonta da mamaki yace "Rachael meye haka, ina xa ki kai yaran?" Wani kallo ta jefa masa tace "Ina xan kai su kamar yaya? Ba jikokina bane" bude bayan motar tayi ta shiga, ya girgixa kai yace "Kina da hankali kuwa Rachael, kan ki daya kuwa? Ina xaki da yaran mutane" fitowa tayi daga motar tace "You're wasting my time David" daga haka ta k'ara ma sayyadarta mai ta dau hanyar gida uwa xata tashi sama, ya dafe kai yace "My God!" Yakumbo na shiga parlon Col ta gansa xaune da laptop, ya mike ganinta yana murmushi yace "Sannu da xuwa yaya" tace "Sannu Ahmad, na same ku lafiya" yace "Lafiya lau, ashe kin taho baki yi waya ba" tace "Kaga ma ni na mance wayar a gida ban da yanxu da kayi magana" xaunawa tayi tace "Ya muka ji da wannan bakar masifar, wai Aliyu ya dawo da yara, anya Ahmad baka yi masa baki ba kuwa" Col ya girgixa kai yana murmushi yace "ko daya" tace "To ita kiristar tana ina?" Col yace "Tana gidan, yanxu uwarta ta xo ta kwashi yaran ma" Yakumbo tace "Wasu yaran kuma?" Col yace "Yaran dai, baki gansu tsatstsaye parlor ba" mikewa Yakumbo tayi tace "Xata ina da su? tare da uwar yaran ta tafi?" Col yace "Xata raine su mana, ba yar ta bace ta haife su, Uwar yaran na nn parlor...." Yakumbo tace "Ban gane xata raine su ba?" Col yyi yar dariya yace "Ae fa tana da gaskiya yaya, jikokinta ne ai" ta rike kugu ta saki baki tana kallonsa, can tace "Ae ni dama tun ba yau ba nasan kai mugu ne Ahmad, wllh kai mugu ne, to muguntar taka ta sojoji sai ya kare a kan mu? ta kwashe min jikoki ka bar ta ta fita? Toh Allah ya fika" Bata jira cewarsa ba ta fice parlorn ta dawo kasa, tana kallonsu Hajiya Mariya da har lkcn suka kasa xaune, Noor kuma sai rusa kuka take, a fusace tace "Amma ku dai anyi gayyar yu yu yu, yanxu duk yawan ku a parlorn nn ku ka bar figaggiyar mata ta fice da 'ya ya har biyu?" Hajiya Mariya tace "A'a Col ne yasa ta fita da su, shi ya hanamu aikata komai wllh" a mugun fusace Yakumbo tace "Yo dama sai ku kula wnn da ya baro hankalinsa gaba daya a yak'in biafra?" Hajiya Mariya ta tabe baki tace "To ina mu ina ja da shi yaya?" Yakumbo tayi wani shewa tace "xata san jikokina ta fita da yau, kin dai san gidan koh?" Hajiya Mariya tace "Na sani" Yakumbo tayi kofa da sauri tace "Mu je" Hajiya Mariya ta dau Hijab din ilham ta bi bayanta, tun da suka dau hanya Yakumbo ke bala'i uwa xata tashi sama, col kam ya sha xagi har da na sayarwa, Hajiya Mariya dai sai bin ta take don tana da assurance baxa su fito gidan ba sai tare da yan biyu, suna isa gidansu Noor yakumbo bata saurari mai gadi dake neman sanin wanda suke nema ba ta bangajesa ta shige gate tana cewa "Kaji min mai gadin gidan bala'i" Hajiya Mariya ta bi bayanta, tsaye suka ga Mr

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login