Showing 3001 words to 6000 words out of 180592 words

Chapter 2 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1131

kamata ba ki koma ki masa godiya you don't have to pretend shi ma nasan ya gane ki" without a second taught ta juya da sauri ta nufe inda suke xaune, da sauri Abuturrab ya dauke kai, Salman yace "She's coming toward us fah" Salim dake ta kallonta da Ayman suka yi shiru har ta karaso, doguwa ce sosai kuma fara amma ba wani can ba, tana tafe ne kamar iska xae kade ta, yeah she's so beautiful kyau me daukar hankali kuwa, daga nisa ma kana iya ganin girman idonta da haskensa, tana isa inda suke ta tsaya tana kallon Abuturrab da alamar ta ma rasa abinda xata ce, sai fidgeting fingers dinta take cikin in ina tace "I I.... Came to thank you!" Kallonta kawai yake, ya kasa dauke kai, a hankali idonsa ya sauka kan abinda ke rataye a wuyarta wanda hakan sai da yasa gabansa ya fadi ba kadan ba, Salim ya take kafarsa yayi saurin dauke kai, sai kuma ya kalleta yace "Ki gode ma Allah!" Juyawa tayi ta bar wajen da sauri, abokansa suka bi ta da kallo har ta isa gun kawayen ta suka ci gaba da tafiya, Salim yace "Where did you know her?" Bai ce komai ba ya xaro kwalin cigarette ya ciro daya da lighter ya kunna ya kai baki. Tana isa gida ta tadda Mum dinta na tare da baki a parlor ta gaida su da ladabi snn ta wuce sama xuwa dakinta ta jefa jakar hannunta ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta fiddo kananun kaya ta saka ta kwanta, lkci daya ya fado mata, sai a snn taji haushin kanta da taki barin wajen bayan ya shareta, tayi tsaki ta rufe fuskarta da pillow, har ta fara bacci taji muryar mum na kiranta, ta mike xaune da sauri tana mitsike idonta, Uwar tace "Samantha ki fito ga abinci can a dinning, baxa ki Catechism bane?" Tace "Mumy da rana fa yau" hade rai Mumy tayi tace "Kina da hankali kuwa, ranan ne xai hanaki xuwa? C'mon my frnd tashi ki shirya and get out of this house, mates dinki a karkashin wata suke tafiya ba ranan ba?" Daga haka ta fice daga dakin, Mikewa Samantha tayi ta sauka parlor a sanyaye, xaune ta ga dad dinta a d'an study area yana sanye da medicated glasses dinsa, Holy Bible ne gabansa yana karanta wa, karasawa tayi inda yake ta masa side hug bai ce komai ba gaba daya attention dinsa na kan Bible din, murya can kasa tace "ina yini Abbana" kai kawai ya gyada mata ta nufi dinning ta debi abincinta ta xauna nan ta ci, sannan ta koma sama ta shirya cikin wani gown din tayi rolling kanta ta fito rike da bible dinta da Hymn book, dakin Mumy ta shiga ta ganta tana ta shirin fita fellowship ita ma, ta karasa tace "Mumy sai na dawo!" Mumy tace "Alryt dear, kila baxan dawo yau ba sbda vigil da xa muyi, you take of yourself, ga transport din ki a gaban mirror na aiki driver" Samantha ta d'an bata fuska tace "Har da Abba?" Mumy tace "Nooo shi yana gida bbu inda xa shi, xae yi bak'i anjima" juyawa Samantha tayi tace "Ohk bye!" Daga haka ta fita bayan ta dau kudin, da kafa take tafiya har tayi nisa sosai tayi deciding ta bi layin gidansu class mate dinta Esther su tafi church din tare, tafiya take tana d'an wake wakenta, tayi nisa sosai don bai wuce gida hudu xata wuce snn ta sha kwanan gidansu Esther ba, gabanta ya fadi ganin wanda ta gani tsaye jikin motarsa a gaban wani gida ga wata yarinya na tsaye daga kusa da shi, kamar ance ya daga ido suka yi ido hudu, da kyar ta bude baki tace "Ina...ina yini!" Yace "Lafiya lau" daga haka ta wucesa, yarinyar ta bi ta da kallo snn ta kallesa tace "Waye ita Aliyu?" Da kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "A frnd!" Ta tabe baki tace "A Christian frnd?" Bude motarsa yayi ya shige ta koma baya da mamaki tana kallonsa tace "Abuturrab?" Ta glass yake kallonta yace "Even if she's a pagan (Mara addini) it's non of ur business!" Tada motar yayi ya ja ya bar ta nan tsaye ta bi sa da kallon mamaki, can ta juya da sauri taga har Samantha ta bace, a fusace ta shige gida. Abuturrab na isa gida misalin sha biyu na dare yayi parking ya fito ko ba a gaya masa ba yasan Abba ya dawo ganin Prado dinsa, bae ko kalli sojojin dake tsaye ta ko ina a compound din ba ya shiga parlor Ramlah ta leko daga kitchen murya can ciki tace "Ya Abu Abba yana neman ka..." Yayi mamakin ganinta a kitchen a wnn lkcn gashi bai ji mai take cewa ba ma, xai karasa inda take suka ji muryar Mami tace "Kina da hankali kuwa Ramlah" juyawa tayi da sauri ta koma kitchen, hade rai yayi ya gaisheta shi kenan kullum cikin laifi kuma sai yayi ta xaman gida kamar mace, infact mayar da duty dinsa na clinic xuwa dare ma xai yi kawae, Mami ta amsa gaisuwarsa ba tare da ta kallesa ba xai haura sama sai ga Abba ya fito daga parlonsa, tsaye yayi gabansa na faduwa ya d'an risina ya gaishesa Abba yace "Daga ina kake Aliyu?" Sunkuyar da kai yyi ya ma rasa abinda xai ce, can dae yace "Abba taimako na tsaya yi a....." Abba ya girgixa kai yace "No! You can't just be coming into my house when ever you wish at any time, don haka ka tattara inaka inaka ka koma boys quatr snn ka bude gate din can kaga idan yaso ko da yaushe ka ga dama xaka iya shiga ka fita bbu wanda ya sani, bbu wanda kuma xai hanaka, do what I say immediately now, stupid you!" kansa a kasa yace "Toh Abba, Allah ya huci xuciyar ka" Ramlah ta karaso parlon kamar xata yi kuka tace "Abba pls forgive him for the last..." Wani kallo ya mata ta juya da sauri ta koma kitchen, Abuturrab ya haura sama ba a dau lkci ba ya fito da jakunkunan kayansa da komai nasa da xai bukata, har lkcn Abba na tsaye parlor haka ma Mami da bata ji dadin hukuncin ba, Fita Abuturrab yyi ya kira mai gadi ya taya sa daukan kayan, tsakanin main gidan da boys quatr ba wani tafiya bane can, sai dai ba lallai ka ma san me ke faruwa can ba barin ma da Abba yace ya bude gate din can, cikin yan minutes ya gama mayar da kayansa can snn ya koma yayi ma parent din nasa sai da safe ya dawo, dariya ya dinga yi shi kadai a parlor yana tafa hannu ya fada kan kujera yace "Waow waoww enough privacy!" ya mike yana murmushi ya shiga inda dakuna suke ya xabi wanda yake so ya shigar da kayansa, ya dau lkci sosai yana gyaran dakin sbda kura don ba a fiye amfani da wajen ba sai dai a sauke baki, Abuturrab ba dai tsafta ba cikin few hours ya tsaftace dakin da bathroom ya kure Ac ko ina ya dawo yana kamshi ya shimfida bedsheet, snn yayi kwanciyarsa don ya ci abinci a waje, nan da nan bacci ya daukesa, washegari Monday yana shirin fita office aka danna bell daga waje ya karasa ya bude, Cook ne rike da tray din breakfast dinsa ya d'an bude ido yace "Ohh I thought girkin ma nan xa a dawo yi min" cook din dai bai ce komai ba ya gaishesa Abuturrab ya karbi tray din yace "Thanks" har ya tafi ya kirasa ya basa spare key din parlon yace "Gashi ko bana nn idan ka kawo min abinci ka shigo kawai ka ajiye" Cook din ya karba da ladabi yace "Ohk sir" daga haka ya juya ya wuce shi kuma ya koma ya ci gaba da shirinsa snn ya yi breakfast ya dau makullin motarsa ya fita, main house ya nufa ya gaida Mami ta amsa tana kallonsa tace "Hope you are now satisfied with the punishment?" Murmushi yayi yana shafa kai Mami tace "Ka canxa halin ka Abuu, you are grown up fa yanxu, soon xa ka ji Abba ya fara maka maganan aure idan kuma kaki fidda mata na tabbata fiddo maka ita ba wahala xai masa ba, you are 30 yanxu amma kaki nutsuwa ka san inda ke maka ciwo koh" murmushi yayi yace "Mami ni fa ba dauko maku magana nake ba, ba sata nake ba, ba kisa nake ba, kuma... Um Mami ni bana neman mata kin sani fa!" Bude baki tayi da mamaki tace "Ehh lallai Aliyu ashe baka da kunya..." Dariya yayi yace "Allah Mami, naga wa ennan sune rashin jin, kuma duk bana yi" harara ta 6alla masa tace "toh shaye shayen fa da bin abokan banxa" xaro ido yayi ya dawo kusa da ita yace "Ohh Mami wllh ni na bar wannan abun da dadewa bana shan komai yanxu" wani kallo tayi masa tace "Cigarette din fah?" Ya sosa kai yace "Uhm Mami shi ma ina kkrin in ga na daina wllh, just continue praying for me" ta shafa kansa tace "Toh Allah yasa haka son. Be a good man plss, sannan ka canxa abokan ka" mikewa yayi yana murmushi yace "Toh Mamina na tafi aiki...." Daga haka ya fita da sauri ya nufi parking lot, yana shiga motarsa ya bar gidan, dai dai traffic kamar ance ta juya ya ga Samantha a bayan mota sanye da uniform alamar sch xata, mamaki ya cikasa, why yake haduwa da ita frequently now, bayan ko taba ganinta bai yi ba kuma daga layinsu xuwa nasu gidan bbu wani nisa can amma bai taba lura da ita ba, ita ko ganin yanda yake kallonta ta daga masa hannu hade da yin murmushi, murmushin ya mayar mata ya gyada mata kai snn ya ja motarsa don an basu hannu ya dau hanyar gun aikinsa.

=???
' [7/19, 5:58 AM] 0mmer Farouk: =ث? *Noorul Huda*=ث?





3......
Karfe biyar saura Samantha ta dawo sch, duk da driver ne yaje daukota amma a titin anguwar tasu ya ajiyeta wai xai je dauko Mumy daga church, yawanci a nan take yawan sauka sai dai ta karasa da kafa, tafe take jakarta a bayanta da ganinta kasan a gajiye take, wani mota that look familiar ne ya xo ya wuce a guje ta bi motar da kallo, bai yi wani nisa ba taga kuma ya tsaya, ita dai tafiyarta kawai take, a hankali ya dinga dawowa baya har ya iso inda take ya sauke glass, d'an bude ido tayi ganin wanda ke cikin motar, kafin yace komai tace "Good evening," yace "Evening, let me drop you" kai ta gyada masa ta karasa ta bude front seat ta shiga ta rufe sannan ya ja motar, bai ce mata ba ita ma haka sai dai ynxu kam ba gudu yake ba, ji tayi yace "Ur name?" Ta kallesa tace "Samantha!" Ya d'an kalleta snn yace "Samantha?" Tayi murmushi tace "Samantha David!" Ya gyada kai yace "Nyc!" Tace "Urs?" Kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Aliyu Ahmad!" Murmushi tayi tace "Nyc name," kallon Stethoscope din dake sakale gaban motar tayi tace "You are a doctor?" A takaice yace "Yes" bata kuma cewa komai ba har ya iso gaban gate din gidansu ta kallesa tace "Thank you" yace "Welcm" har xata fita sai kuma ta tsaya ta kallesa tace "Every doctor can draw perfectly, will you pls help me draw the Diagram of the Mammalian heart and Human Skeleton?" Kallonta ya tsaya yi, can yyi Murmushi da ya bayyana light dimple dinsa yace "Really? To ni ban iya ba" kamar xata yi kuka tace "Allah nasan ka iya Plss ka min mana" shiru yayi yana kallon yanda karamin bakinta ke motsi sai kuma yace "Ohk," cike da murna tace "Ohk to bari in dauko materials din" dakatar da ita yayi yace "Am exhausted I can't wait, idan mun sake haduwa sai ki ban" daga haka ya daga mata hannu ya ja motar ta bi sa da kallo, cikin minti biyar ya isa nasu gidan ana bude masa gate yayi parking har xai nufi kofar main parlor ya tuna ai fa ya koma Boys quatr ynxu, dariya yayi ya nufi can, wanka kawai yayi ya dawo ya debi abincinsa dake ajiye snn ya ci ya kwanta don ya gaji sosai, shidda saura ya mike ya fita ya xaga boyz qtrs din gaba daya, ya bude gate din da Abba yace, ya fita waje da farin kujera ya xauna yana kare ma street din kallo don sai yyi shekara bai bi nn ba duk da bayan gidansu ne, baxa ka taba cewa akwai mutane unguwar ba tsabar shiru, tafe suke su biyu da alamar sun dawo daga church ne, tun daga nisa ya gano ta ta yanda take tafiya, haka ya dinga kallonsu har suka karaso, ta xaro ido ganinsa tace "Doctor!" Wara ido yayi bai ce komai ba ta karasa kusa da shi da sauri ta sauke jakar dake goye bayanta ta fito da materials din drawing din ta mika masa tace "Na kama ka" murmushi yayi ya karba yace "Nawa xa ki biya?" Ta langwabar da kai tace "Ko nawa, amma service before payment" dariya yayi wanda hakan ya fito da ainahin kyansa na d'an pillo, ya kuma bayyane fararen set din hakoransa masu daukar ido, shiru tayi tana kallonsa, yace "Ke me wayo ko?" Murmushi tayi tace "nan ma gidan frnds din ka ne?" Ya girgixa kai yace "Gidanmu ne" bin gidan tayi da kallo tace "Da gaske?" Yace "Yeah!" Tace "Hmm Ohk, to yaushe xan karbi xanen?" Yace "Ran da na gama" tace "Noo we are submitting it as test on Wednesday" yace "Ohk, xan yi anjima" tace "Yauwa na gode bye" daga haka ta nufi mai aikinsu blessing dake jiranta. A ranan da daddare Abuturrab ya xauna misalin karfe goma a gun da ya tanadar as study room, ya bude textbook din da ta basa domin Duba xanen a jiki ya kwafa, tabe baki yyi ya rufe, lumshe ido yyi na kusan minti biyar yana nazarin diagram din heart a xuciyarsa, can ya bude ido ya dau well sharpened pencil din ya shiga xana Big Mammalian heart gwanin ban sha'awa ko wani curve ya basa hakkinsa, sosai Heart din ya xanu yyi kyau kamar drawing din Artist, cikin few minutes yayi labelling ko ina snn ya ajiye pen din ya lumshe ido yana nazarin skeleton, bude idon yyi ya bude wani page ya shiga rangada babban xanen Human Skeleton, ko wani k'ashi sai da ya tabbatar ya xana, ya gama tsaf snn yayi labelling ya gama ya rufe book din yana hamma ya mike ya shige bedroom ya fada kan gado sai bacci. Washegari da xae fita aiki bae bari ya mance materials dinta ba in case ko xa su hadu, ya ajiye back seat snn ya bar gidan bayan ya shiga ya gaida Mumy, amma bai ganta ba ranan, da ya baro gun aiki ma haka ya dinga dube dube a hanya ko xai ganta amma har ya isa gida bai ganta ba. Karfe takwas na dare ya shirya ya fita hankalinsa kwance ta gate dinsa bbu wanda ya sani bare yyi querying dinsa inda xa shi, gidansu Saudat ya nufa don yyi missing dinta tsakanin jiya da yau, yana isa ya kirata, ba a dau time ba ta fito sai dai kumbure kumbure kawae take, yyi murmushi yace "Why the pouting?" Ta hararesa tace "Ka manta bari na tsaye kayi ranan ka wuce?" Kamo hannunta yayi yace "Ohk Am sorry dear, how you doing?"ta turo baki tace "Am good" ya shafa kansa yace "So what's new?" Tace "Baxa ka shiga ciki ba?" Yace "Noo, an san kin fito ne?" Tace "Just my little sis" yace "Mum fah?" Tace "She's in her room" yace "Toh rakani mu je mu dawo yanxu" tace "No the other time I escorted you ka sa ana ta min wani kallo a club ni baxan je ba" ya wara ido yace "Wa yace maki can xan je?" Ta hararesa tace "Ban san ka bane" dariya yayi yace "Plss baby we are not staying long fa kawai rakani xa ki yi Akwae abinda xan karba ne" shiru ta d'an yi, sai kuma a hankali tace "Ohk, just thirty minutes before ayi noticing bana gida" hannun ta ya kamo yace "Ohk dear" daga haka ya tada motar ya dau hanyar club din nasu, duk da bin sa da Saudat take club kaffa kaffa take da kanta kuma bata sake ma kowa fuska, don tana mugun sonsa shi yasa bata iya kin yin abinda yake so, Saudat kyakkyawa ce ta ajin karshe, irin matan da samarin xamani ke so, Abuturrab bai yi amfani da wnn advantage din son da take masa ba ya cutar da ita, iyaka kawai ya rike mata hannu sae d'an peck, coz he always keep it at the back of his mind dat shi ma yana da k'anni mata, bai kuma son komai ya samu lovely sisters dinsa, hakan yasa yake yaki da duk wani yaudara na diya mace, kafin minti talatin din kuwa ya maida ta gida bayan sun shiga eatry ya cika ta da kayan ciye ciye, ba shi ya koma gida ba sai kusan sha daya sai a snn ya kuma farin cikin basa side dinsa da Abba yyi, ynxu bbu wanda xai ma san ya dawo bare yace daga ina yake, yana parking gaban gate din ya fito xai bude don bbu mai gadi a side din kuma bai ma bukata, yana bude gate ya dawo xai shiga motar ya hango Samantha da wata mata da baxata haura 40 ba, wai! Da ganinta kaga rikakkiyar Christian, skirt ne jikinta shi bai kai kasa ba amma dogo ne sosai, sae wani bujejen riga da tasa tayi tuck in dinsa cikin rigar, kanta na sanye da irin hulan nan nasu na pastress, hannunta dauke da wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login