Showing 6001 words to 9000 words out of 180592 words

Chapter 3 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1129

gundumemen Bible, dayan kuma na rike da hannun Samantha, da ganinsu kasan daga church suke, Samantha da ta gansa ita ma sai kallonsa take fuskarta dauke da murmushi har suka iso dai dai inda yake, satan kallon uwarta tayi taga hankalinta na gaba sai rera worship songs take, hannu ta daga masa a hankali alamar bye bye, ya sakar mata murmushi shi ma ya daga mata hannun, har suka wucesa bin su yake da kallo, doguwar riga ce jikinta sai rolling da tayi a kai, girgixa kai yayi ya shiga motarsa ya ja xuwa ciki yyi parking snn ya dawo ya rufe gate din, wanka yayi ya jima xaune yana karatun Qur'ani daga karshe ya mike ya shiga bedroom ya d'an yi xuke xukensa snn ya kwanta. Washegari da ya kasance laraba ana idar da Sllhn Asuba a masallaci drawing din Samantha ya fado masa gashi tace ranan xata yi submitting kuma test dinsu ne, satan kallon Abbansa dake Azkar y??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yi, don kusan ko da yaushe tare suke fitowa daga masallaci, kuma yasan ynxu sai ya bata rabin awa yana xaune, fuskewa yyi ya mike ya fice ya nufi gida, tsaye yyi a balcony yana tunanin ko dai ya bari kila idan xai fita aiki su hadu, sai kuma ya tuna jiya ma through out basu hadun ba, ya shiga gida ya dauka makullin motarsa ya fito ya bude motar ya dauki littafin da textbook din sai math set ya bude gate ya fice, tafiyar minti goma yayi ya iso dai dai gate dinsu, rasa yanda xai yi yyi, gashi har lkcn gari bai gama washewa ba, bai ma ga alamar an bude gate din nasu ba, leken cikin gidan ya shiga yi yaji daga bayansa an daka masa tsawa "Heyyy who you be, who you find?" Juyawa yyi da sauri yana kallon mutumin ko ba a gaya masa ba yasan mai gadin gidan ne, yace "Ehm, Samantha!" Mai gadin ya masa wani kallo yace "Wetin do Samantha?" Mika masa abubuwan hannunsa yayi yace "Give her plss" daga sama har kasa mai gadin ke kallonsa, Abuturrab ya kalli kansa, jallabiya ce milk colour jikinsa, karasowa mai gadin yyi yace "Who make I say?" Abuturrab yace "Aliyu!" mai gadin ya sa hannu ya karba Abuturrab ya juya ya bar wajen, karfe bakwai da kusan rabi yana kkrin rufe kofa Ilham ta karaso, ya juya yana kallonta yace "Pretty!" Tace "Ya Abu ko shigowa ka daina yi dama nasan kafi son haka" dariya yayi yace "Eh mana, baxa ku ma dinga gani ba bare ku dinga yangan bani abinci na" tace "Yaya pls ka ba Abba hakuri ka dawo cikin gida we are missing you" kamar xata yi kuka ta kare maganar, yace "Noo, I like it so much here" tace "Why?" Yace "Nothing" tabe baki tayi tace "Ae shikenan, kayi breakfast?" Yace "Yep, Peter ya kawo min" daga haka ya kama hannunta suka bar wajen yace "Za ki sani latti, ki sa kanki latti" tace "Ya turrab 5k plss" yace "I don't have cash, sai ltr" bai jima gun Mami ba ta fito ya hau motarsa xuwa gun aiki. Da ya tashi dawowa da yamma daga gun aiki da gundumemen K'arensa ya dawo da cage tare da mutumin dake rike da Karen, cikin few minutes aka hada cage din karen mutumin ya fito da karen da bakinsa ke a daure ya turasa cage ya rufe snn ya kunce mouth cuff din dake bakinsa, nan karen ya hau haushi, Abuturrab yyi murmushi yace "Yesss!" Tap ya nufa ya bude ruwa yana wanke hannunsa sannan ya dawi yana kallon mutun yace "Yanxu ya xa ayi karen ya saba da ni?" Mutumin yace "In dai kai ne xaka dinga basa abinci ko da yaushe cikin lkci kankani xai saba da kai" Abuturrab yace "Ohk nagode" nn ya sallami mutumin ya basa kudin mota, yana tsaye yana kallon katon karen da ya fito da halshe sai hakki yake ya ji muryar Mami a bayansa, juyawa yayi da sauri da mamaki tace "Meye wnn kuma Abuturrab?" Wara ido yayi yana murmushi yace "Dog Mami!" Hade rai tayi sosai tace "Uwar me yake a gidan nan?" Ya marairaice yace "Mami gadi xai dinga min ni bana son mutum nafi son dabba!" Bude baki tayi tana kallonsa, can ta girgixa kai tace "Toh ba gidan nan ba kare xai maka gadi, sai ka jira idan ka koma gidan ka na kanka!" Yace "Nooo Plss Mami, bangarena ne nn fah!" Tace "Nace ka fitar min da wnn abun Aliyu" karasowa yyi kamar xai yi kuka ya mata side hug yace "No plss Mami, kinga fa ina jin kamar jiya barayi sun xo anguwar nn, pls ki bar min karen it will be a good watch man for me, bbu abinda masu gadin nn suka iya sai bacci...." Girgixa kai tayi ta juya ta fara tafiya tace "Ni dai bbu ruwana...." Murmushi yayi yace "Yes Mami" main gidan ta nufa ba tare da ta tanka sa ba. Yana xaune misalin biyar kan farin kujera yana danne dannen wayarsa yaji kamar motsi jikin gate, ya daga kai da sauri, sai kuma ya mike ya nufi gate din ya bude, tsaye ya ganta kamar munafuka, tana ganinsa ta koma baya a tsorace, murmushi ya sakar mata murya can kasa yace "Samanth....." Sai kuma yyi shiru a hankali yace "Samha!" Wara ido tayi tana murmushi tace "Ashe kana nan, just came to say a big thank you!" Har da d'an risinawarta ta kare maganan, ya jingina jikin gate ya rungume hannayensa yana kallonsa yace "For what" turo baki tayi tace "For the beautiful drawing mana" Murmushi kawai yyi yana kallon hannunta dake dauke da Bible, mota ce ta shawo kwanan anguwar ta juya da sauri tana kallon direction din, ta xaro ido tace "Jesus! Abbana ya dawo" kallon motar yayi da sauri sai kuma ya matsa daga gun gate din bata jira yace mata komai ba ta shige cikin gidan, wara ido yayi yana kallon motar har ya xo ya wuce snn ya shiga gidan ya rufe gate din, tsaye ya ganta tayi lamo jikin flower, tana ganin ya rufe gate din ta karaso da sauri tace "Ae ya tafi ko, let me leave" kallon gate din yayi yace "I don't think ya tafi fa, tare yake da wasu a motar kuma na ga sun tsaya" kamar xata yi kuka tace "Bbu wani hanyar doctor?" Girgixa Kai yayi yace "Only this.... Ga kujera ki xauna ki jira su wuce sai ki tafi," Da damuwa tace "Church fa xan tafi, I don't want to miss" shiru yyi yana kallonta, can ya juya ya dau wani kujerar yayi xamansa, bin bayansa tayi tana bin gidan da kallo ta xauna kujerar da ya nuna mata tace "Are you the only one leaving here?" Girgixa kai yayi ya nuna mata hanyar da main house din yake yace "My family members are there, my Mum, Dad and sweet siblings" mikewa tayi ta nufi inda ya nuna mata bata wani yi nisa ba ta hango kantamemen gidan daga nisa, dawowa tayi da sauri tace "Uhn! Toh me yasa kai kake boys quatrs?" Murmushi yayi yace "Because I am a boy, an I prefer here" 'yar dariya tayi tace "Ohk that's true, xan wuce church yanxu" mikewa yayi yace "Bari in duba maki ko ya tafi" daga haka ya tafi gun gate ya bude ya leka, rufewa yyi da sauri ya dawo yace "Noo they are still there ki xauna kawai su wuce" bata fuska tayi tace "Lokacin Church na wucewa" bai tanka ta ba hakan yasa ta xauna, haushin k'are taji ta mike a firgice tana kallon direction din, ihu tayi suna ido hudu da katon karen ta juya xata gudu a rikice yyi saurin rikota da sauri, ta fashe da kuka tace "Noo bana son kare pls" xaunar da ita yyi kan kujera ya durkusa gabanta yana kallonta yace "But it's caged" Har lkcn jikinta rawa yake ta kasa cewa komai, dagota yyi ya shiga balcony da ita ya sa ta xauna ya duka gabanta yace "Ohk sorry Plss...." Hawaye ya sakko idonta tace "Ni xan tafi" mikewa yayi ita ma ta tashi, yace "Karen baya komai, it's very frndly" bata ko kalli inda karen yake ba ta nufi gate da saurinta, ya bi bayanta amma tuni ta fice, tsaye yyi bakin gate dinya rungume hannunsa ya bi ta da kallo ganin yanda take sauri, sai da ta tabbatar tayi nisa snn ta juya ta kallesa, d'aga masa hannu tayi, ya juya ya shige gate din yayi banging dinsa, kasa ci gaba da tafiya tayi sai kallon gate din take, can ta juya jiki ba kwari ta ci gaba da tafiya.


=???
' [7/19, 5:58 AM] 0mmer Farouk: =ث? *Noorul Huda*=ث?




4......

Washegari da yamma misalin biyar da rabi Abuturrab na xaune karkashin artificial bishiyar dake dauke da fararen kujeru a karkashi hannunsa rike da Cigarette, dawowarsa kenan daga aiki yayi wanka ya d'an tsakuri abincinsa da ke ajiye a parlor snn ya fito ya xauna ya fara aikin xuke xukensa idonsa na kan k'aren dake ta fama da gundumemen naman da ya siyo masa a hanya, murmushi yayi ya mike ya shiga ciki sai ga shi ya fito da babban drawing board da materials din drawing dinsa, bude board din yyi ya tsayar ya dawo da farin kujera kusa da board din ya xauna dai dai yanda xai dinga ganin karen da kyau, ya fi minti biyar yana kallon karen hannunsa rike da well sharpened drawing pencil din hannunsa, daura hannun nasa yyi kan board din, a nutse ya shiga xana k'aren, ya kusa minti goma yana xana kai snn ya dawo jiki, yyi rabi yaji an tura gate a hankali ya juya da sauri, ido hudu suka yi da ita, ta wara ido kamar mara gaskiya ta k'asa tsaye gu daya tana jujjuya Bible din hannunta tace "Am... Ina yini!" Murmushi yayi ya maida dubansa kan board din gabansa yace "Come in....." Kin shigowa tayi tana yi tana lekan karen dake cage tace "No, am going for service!" Ya kalleta yace "Ohk baxa a gaisa ba knn yau?" Murmushi tayi tace "Gashi na gaishe ka, and I can see you are busy drawing what I can't see from here!" Mikewa yayi ya karasa gabanta, tayi tsuru tsuru tana kallonsa, kallonta yayi daga sama har kasa, yau ma doguwar riga ce sea green jikinta, sai jan veil da ta daura a kanta, cikin idonta dake kyalli kmr ta tara hawaye ya kalla, ta juya da sauri xata bar gate din ya riko hannunta, juyowa tayi tana kallonsa, ya sakar mata murmushi yace "Yea, baxa ki ga abinda nake zanawa daga nan ba sai kin shigo" kallon karen tayi a tsorace tace "Noo, ni ina jin tsoron...." Jawota yayi xuwa cikin gidan ya rufe gate din, tace "Noo Plss...." Janta yyi har xuwa gun drawing board din sai buya take bayansa, ya dawo da ita gaba idonta ya sauka kan xanen, shiru tayi tana kallo ko kiftawa bbu, a hankali ta furta "Waoww....." Kallon karen dake cage tayi snn ta kalli na drawing din ta juya da sauri tana kallonsa tace "Doctor wa ya koya ma drawing haka, you are.... " Rungume hannayensa yayi yace "In koya maki ne ke ma?" Da sauri ta gyada kai, ya ja kujeran ya xauna ya dau pencil din ya ci gaba da xanen, durkusawa tayi a hankali kusa da shi ta dafa kafarsa tana kallon yanda yake xanen cike da kwarewa, muryar Khaleesat ya ji, ya juya da sauri sai kuma ya mike ya xaga ae ko ya hango ta ita da Ilham suna tahowa, dawowa yayi da sauri yana kallon Samantha tun kan yace komai ta mike a rikice tace "Your sister I guess?" Bai ce komai ba ya kama hannunta ya nufi kofar parlor ya bude ya sa ta shiga snn ya rufe ya dawo gun drawing din ya xauna ya ci gaba, Khaleesat da Ilham suka karaso, Ilham ta wara ido tace "Waow ya Abuu.... It's sooo beautiful!" Ta gefen ido ya kalleta yace "Thanks" Khaleesat ta durkusa kusa da shi tace "Yaya wai Anty Ramla tace kace xaka kawo wani karen main house, da gaske ne" ya hade rai yace "You two can see am busy...." Khaleesat tace "Don ma mun taho taya ka hira tunda bbu islamiyya yau?" Bai tanka ta ba, Ilham tace "Toh shknn since he's busy let go inside and....." Mikewa yayi da sauri kmr wanda aka mintsila yace "Go where? Kar warce ta shigar min parlor....." Ilham ta bude ido da mamaki tace "Why?" Wani kallo ya watsa mata ya nuna mata hanyar inda suka fito, ganin bbu wasa tattare da shi yasa duk suka juya suka bar gun, ya bi su da kallo har suka bace, ya ajiye pencil din hannunsa, Samantha dake ta kallonsu ta window ta bude kofa ta fito, murmushi ta masa tace "Ur siblings are cute, they re fine...." Rungume hannuwansa yayi ya daga kafada, tace "Bye na tafi church!" Daga haka ta nufi gate ya bi ta da sauri yace "Wait! Baxa ki jira in gama ki gani ba" tace "Lkci na wucewa xan je church ne fa" yace "Ohk I will be very fast sai ki wuce" shiru tayi ya wara mata ido yace "C'mon" karasowa tayi ya xauna ya ci gaba da drawing din ita kuma ta durkusa kusa da shi, sai da aka yi wani minti talatin kafin ya gama xanen, ta xuba ma board din ido tana kallon katon karen dake ta dambe da k'ashi, can ta lumshe ido a hankali tace "Waow, you are so talented" murmushi yayi yana nodding kai yace "Thank you.... Samanth.. Uhm Samha!" Xaro ido tayi tace "Am not Samha but Samantha!" Ya daga kafada yace "Ohk all same...." Hamma yayi yana stretching din hannunsa yace "Am exhausted, No am hungry rather" tace "Baka ci abinci ba?" Langwabar da kai yayi yace "It's finished...." Shiru tayi sai kuma tace "toh me xaka ci?" Ya juya manyan Eye balls dinsa yace "May be black tea, da yaji kayan kamshi" ta tallabi kuncinta tace "Toh wa xai ma, ko xaka shiga gida ka gaya ma Mumy" ya d'an marairaice yace "She won't, yanxu dinner take yi na sani" a hankali tace "Toh ni in maka?" Yayi shiru sai kuma yace "Yess Plss" mikewa tayi tace "Toh xo ka nuna min kitchen din da komai...." Mikewa yayi yace "Yauwa thanks frnd, shiga ki jira inje can cikin gida in dauko lipton din da scent ingredients" dariya tayi tace "Ohk ohk" yayi murmushi ya juya ya nufi can cikin gida ita kuma ta shiga parlonsa, ba a dau lkci ba ya dawo rike da su a wani bowl, ta mike daga xaunen da take ta karba ya rakata kitchen din, yana tsaye daga bakin kofa ta gama dafa ruwan lipton din da ya dume gidan da kamshi, ta juye masa a flask din da ya nuna mata ya karaso kitchen din yana murmushi yace "Waow thanks frnd!" Murmushin ita ma tayi yayi mata stretching din long fair hand dinsa me dauke da kwantancen bakin gashi, a hankali tayi stretching din nata ya karba yayi shaking dinta, yana kallon kwayar idonta. Fitowa yyi da flask din parlor da cup, ta dau Bible dinta tana kallon agogo taga shidda har ya wuce kmr xata yi kuka tace "Ka ga har lkci ya wuce koh?" Da damuwa yace "Ayya, am sorry...." turo baki tayi tace "Yanxu I've missed church sai gobe kuma" yace "Toh ae nace am sorry, ki xauna in sha lipton din kad'an sai in raka ki har kofar gidan ku" xaro ido tayi tace "Dare xai yi" ya hade gira yace "Ba fa pounded yam nace xanci ba" murmushi tayi tace "Ohk ohk, I will wait" daga haka ta xauna ya dau cup ya bude flask ya debi lipton din ya kai lips dinsa, xaro ido tayi tace "Xai kona ka fa" dariya yayi yace "Na fi ki sanin haka" turo baki tayi ta dau Bible dinta ta bude tana kallo, da ta daga kai sai su hada ido, sun yi hakan ya kusa sau uku, yayi murmushi yace "Why you staring at me?" Kafin ta ce komai yayi saurin karawa da cewa "What are you reading" tace "Uhm! Holy Bible" shiru yyi yana kallonta can yace "Toh karanta min nima in ji" ta wara ido tace "Da gaske?" Ya gyada kai ta mike ta dawo kusa da shi da sauri ta xauna a kasa tace "Ohk I will, give me ur attention" kai ya gyada mata yana kallonta, verse din da chapter ta fado masa snn cikin sanyayyan muryarta ta fara karanto masa content din chaptern tana masa explain, kallonta kawai yake cike da tausayi, can ya lumshe ido ya ci gaba da shan lipton dinsa yana saurarenta, haka ta dinga karatun har ya ji kiran sallah, da sauri ya bude ido yana kallonta yace "Alryt, let stop there for today!" Tayi murmushi tace "Ohk!" Mikewa tayi tace "It's almost dark, xan wuce" yace "But nace xan raka ki ai, ki jira in dawo Masallaci" kamar xata yi kuka take kallonsa, can a hankali tace "Ohk!" Ya mike ya mika mata empty cup din hannunsa yace "Ke ma ki xuba ki sha" ba musu ta karba, ya nufi toilet din parlon ya dauro alwala ya fito yace "will be ryt back! You can lock the door kafin in dawo" Bin sa tayi da kallo har ya fita snn ta mike ta kulle kofar ta dawo ta xauna ta debi lipton din kadan ta sha, snn ta kai sauran kitchen, bin kitchen din ta dinga yi da kallo ganinsa fes kamar da mace a part din, fitowa tayi parlor shi ma ta dinga bin da da kallo can ta juya ta koma kitchen ta dauko sweeper da mopper ta dawo, tattare parlon tayi cikin yan mintuna don ba wani dirt bane a ciki snn ta hada ruwa ta sa freshener din da ta gani ta shiga mopping din parlon, tana gamawa ta goge

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login