Showing 153001 words to 156000 words out of 180592 words

Chapter 52 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1147

da ita ya kwantar, a hankali ya dinga yi mata har ruwan ya salance snn ya kai bathroom ya fito tana kallonsa ya fita dakin, kitchen ya sauka ya bude fridge ya dau lime biyu ya xuba ruwan xafi a cup ya matse lime din ciki snn ya koma daki, da kansa ya dinga bata ruwan lime din har ta shanye ya ajiye cup din, hada ido suka yi tayi saurin sunkuyar da kanta, ya jawota jikinsa a hankali yace "How are you feeling now?" Lumshe ido tayi tace "Fine" bai kuma ce mata komai ba, suna nn a haka har agogo yyi stuck din karfe biyu, murya can kasa taji yace "Thanks for the babies Samha" bata ce komai ba, ya dago kanta yana kallon kwayar idonta ta kauda kanta, ya kamo hannunta yace "Why did you choose to leave Samha, you've caused me so much pains" Shiru yyi, ta koma baya a hankali tace "The babies...." Sai a snn ya kula har lkcn fa babies din sun ki hakura, ya mike ya fita, yana shiga dakin Mami tace "Ya jikin nata?" Yace "Da sauki Mami, bari a kai mata su xata iya basu abincin" Daga haka ya karbi na hannun Hajiya Mariya tace "Kai, wnn yara ba dai fitina ba kamar ubansu...." yar dariya yyi yace "Ke dai kawai don sun hanaki bacci ne mum, sae ma sun koma gun ki gaba daya" Dariyar tayi ita ma tace "Sae in xane su abu d'an sauki" yace "Toh baxa su ba, sai in kai su gun Yakumbo" yana magana ne yana kallon Mami da taki kallonsa ta mika masa Hussain ya fita da su yana murmushi, Hassan ya daura mata a kafa ya xauna yana lallashin dayan yana kallon ynda take basa abincin, bata ji ciwon kamar daxu ba, sai da yaran suka yi bacci duka snn ta kwanta, nn da nn bacci ya dauketa ita ma kmr xata shige jikinsu, ya jima xaune yana kallonsu, can ya d'a yi murmushi ya lumshe ido ya bude, ya hau gadon ya kwanta shi ma. Da Asuba yana dawowa daga masallaci ya tsaya bakin gado yana kallon irin kwanciyar da tayi da yaran kamar xa a kwace mata su, ya girgixa kai ya fita ya shiga dakin Mami, Hajiya Mariya na xaune kan darduma ya dau wayarta ys fita, hotuna ya dinga daukarsu ganin ta bude ido a hankali ya juya da sauri kmr yaran kadai yake dauka, sauka tayi daga kan gadon ta nufi bayi, yace "Kar kiyi amfani da ruwan sanyi" kallonsa tayi ta dauke kai ta shiga bayin, ya bi bayanta, brush dinsa ta dauka ya karasa ciki ya tara mata ruwan xafi ya tsirka snn ya fita, tana fitowa taga dakin wayam bbu yaran, kalle kalle ta fara yi, can ta nufi kofa da sauri suka kusa cin karo ta koma baya tace "Ban ga yaran ba kuma...." Kallon gadon yyi da mamaki fuskarsa yace "Toh ina suke?" Bata kuma saurarensa ba ta nufi kofa da sauri, ya rikota yace "Ina xa ki?" Kamar me shirin kuka tana kalle kalle tace "Xan je in duba su" yace "A ina" bata kuma saurarensa ba ta kwace kanta xata fita ya jawota jikinsa yana d'an murmushi yace "A gidan nan yaran ki xa su bata Wife? Na lura baki da kara, Mami ta daukesu xa a masu wanka toh..." Shiru tayi bata ce komai ba. Ya xaunar da ita gefen gado ya xauna yace "How did you feel rashin ganinsu just for some few minutes, dubi ynda kika hargitse, me yasa baki yi tunanin halin da ni na shiga ba all this while Samha, why did you choose to cause me so much pains??" Cikin raunin muryabm yake magana, ita dai bata bari sun hada ido ba, ya kamo hannunta ya kai kirjinsa a hankali yace "Feel it Samha..." Tana jin irin yanda xuciyarsa ke bugawa da sauri, a hankali yace "It's still not healed Samha, what have i done to deserve this from you?" Jin tayi shiru ya dago kanta a hankali yace "Talk to me Samha" still ta ki cewa komai, can ta sauke idonta a hankali tace "Nima ban sani ba" shiru yyi yana kallon fuskarta, matsawa tayi daga kusa da shi da damuwa tace "They are crying ko ruwan da xafi" wani kallo yyi mata yace "Ko xaki je ki duba?" Ta kallesa tace "A'a kai kaje, ni baxan iya ba" yace "Ashe ba son su kike ba" kamar xata yi kuka tace "Toh ka raka ni don Allah" ya mike yace "Toh mu je" tashi tayi da sauri ta bi bayansa, Mami ce ke ma Hussain wanka, Hajiya Mariya na rike da dayan dake tsala ihu shima jin d'an uwansa na kuka, Durkusawa Noor tayi kusa da Mami kanta a kasa tace "Ina kwana..." Mami tace "Lafiya lau, tashi a sanyi kin ji" murmushi kawai tayi ta kalli Hajiya Mariya ta gaisheta, ita ma ta amsa tana murmushi tace "Toh tashi mana" shi dai Abuturrab kallonta kawai yake, a hankali ta kai hannunta cikin ruwan kan idon Mami da Hajiya Mariya, Abuturrab ya juya da sauri kar yyi dariyar dake cin sa, Hajiya Mariya ta bude baki tace "Lallai Samha ruwan kike dubawa ko da xafi" kunya taji sosai ta kasa xaune waje daya tace "A'a mum, shine yace min in duba..." Mami da Hajiya Mariya suka kallesa a tare, ya juyo da sauri yana kallonta ya xaro ido yace "Ni?" Ta turo baki tace "Eh"

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
92___93

Dariya Hajiya Mariya tayi tace "To basa shi yyi masa wankan yaya" Mami kam murmushi kawai tayi tace "Da shi ma na k'ona sa yana jariri ae" fita Abuturrab yyi yana dariya, Noor ta mike ta bi bayansa, Hajiya Mariya ta rike haba tace "Ikon Allah, kin ga yaran yanxu koh?" Mami tayi murmushi tace "Su xo su tattara ma su bar min gida na sai ki je ki xauna da su, bn yrda da shirun nn na Col ba" Hajiya Mariya ta xauna tace "Wllh nima haka yaya, ba a banxa ba bin mu da ido da yake ya ki cewa komai Allah kadai yasan abinda yake kintsawa a xuciyarsa" Mami ta tabe baki tace "Kar ma yayarsa ta fado gidan, bn fiye son magana ba you know, snn ita ma yarinyar she is nt safe here....." Tabe baki Hajiya Mariya tayi tace "Bbu inda xa su yaya gwara ayi ta ta kare, ina ce ae yafi kowa shiga rudanin halin da Aliyu ya shiga don ma yana boyewa, i knw baxae so abinda xae kara taba ma d'an sa xuciya ba, bar sa ya gama shirunsa da kansa xae dawo yyi mana magana har ma ya bada ragon suna biyu" murmushi Mami tayi bata ce komai ba, Hajiya Mariya tace "Bari ma gari ya waye mu kira Hajiyar gombe, sae a kira kanwar babanta dake maraba ita ma a sanar da ita" Mami tace "Toh ni dai ki dau makulli ki tafi ki dauko ma yaran kayan da kika ce ke gidan ki, bbu kayan da xa su sa fa" Hajiya Mariya tace "Toh bari in kira yaran su rike maki wnn dake taya d'an uwansa kuka" daga haka ta ajiyesa ta fita suka dawo tare da fatima ta dau hassan, Hajiya Mariya ta dau makullin mota ta fita, Abuturrab na shiga bedroom dinsa Noor ta shigo ita ma, ya kulle kofar ya jawota jikinsa yace "Me nayi maki xa ki min irin wnn sharrin haka?" Ta hararesa tace "Toh ae baka ce min xa su gane ba idan na taba ruwan" kallonta ya tsaya yi, can ya lumshe ido ya rungumeta a hankali yace "I missed you Samha, kar ki sake bari na don Allah" lumshe ido ita ma tayi don tasan tayi kewarsa fiye da ynda take tunani, murya can kasa yace "Tell me how you felt when giving birth to our babies" sae da gabanta ya fadi tunowa da irin wahalar da tayi two days back, ta fashe da kuka ba hawaye tace "Ni baxan sake haihuwa ba, bana so" ya wara ido yace "Har ina cewa xa mu bar ma mum dinki wa enan tunda she is lonely without you sai ki sake haifa mana wasu yan biyun?" Da sauri ta dago tace "Da gaske?" Yace "Eh mana" a hankali tace "Toh a bata, xan haifa wasu" kamar warce ta tuno abu kuma tace "Nooo, my babies are muslims" ita kanta bata san lkcn da ta fadi hakan ba, ya dago kanta da sauri, ya xaunar da ita gefen gado yace "Really wife?" Sauke idonta kasa tayi, ya ji dadin furucinta har cikin ransa yace "So will der mother be one day" ta d'an kallesa, sae dai bata ce komai ba, yace "Toh wani sunan xa mu sa ma babies din?" Ta buda hannu alamar bata sani ba, ya kafa mata manyan idanuwansa. A bathroom din Abuturrab Hajiya Mariya ta taimaka ma Noor tayi wanka, suna fitowa ta sa ta shirya cikin sabbin riga da skirt na Ramla ko taba sa su bata yi ba, nn ta nuna mata lallausan rug dake shimfide a dakin da aka tula mata kayan breakfast, tun daga kan shayi da bread, kunu, wainar shinkafa, pepper soup din naman rago da ya ji yaji, sai tuwon masara da aka yi mata duk ita kadai, kuma ba wai da yawa ba, ko wanne dai-dai dai-dai aka yi sa, Abuturrab ne ya shigo dakin bayan fitar small mum dinsa, ya xauna kan rug din yana kallonta don ba karamin kyau tayi ba duk da bbu make up fuskarta, tayi haske haske sosai, yace "Kinyi kyau mumyn twins" bata ce komai ba, ya kai hannunsa kirjinta ganin ynda suka cicciko yace "For only our babies yanxu koh?" Buge hannunsa tayi, yyi dariya, ita kam murmushi tayi ta shiga hada tea, ya gyara xama yace "Shud i join dear?" Kallonsa tayi ta gyada masa kai, nn ya hada masu shayin su biyu, har ya mance yaushe rabon ya bude ciki haka ya ci abinci, ita kanta tasan ta jima bata ci abinci kmr yau ba, ya dawo kusa da ita ya rungumeta ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Ina son ki Samha...." Bakinta ta kai kunnensa a hankali tace "No more Samha, it's Noor... Noor Al-Hudah" kallon fuskarta yyi dai dai lkcn da aka bude kofar dakin ya janye jikinsa da sauri, fatima ta shigo rike da Hassan ta karasa kusa da shi ta mika masa, karban yaron yyi, Noor dama kallo daya tayi mata ta dauke kai, fatima ta juya ta fita, kasa kallon Noor yyi ya buge da kallon yaron dake ta mutsu mutsu da baki yana neman abinci, sai ga ta ta kuma dawowa da dayan shi ma ta mika masa ta fita, mikewa Noor tayi ta haye kan gado, ya bi ta da kallon gefen ido, jin yaran xa su fara kuka ya mike ya isa kan gadon ya xauna kusa da ita a hankali yace "Wife they are hungry" jin bata ce komai ba ya bude xip din rigarta, ta mike a d'an fusace, suna hada ido ta kasa cewa komai, ya sauke rigar kasa yana kallon kwayar idonta, a hankali ta shiga breastfeeding yaron da ya daura mata a kafa yana rike da dan uwansa, bayan minti sha biyar Hajiya Mariya ta shigo dakin tana tsaye daga bakin kofa tace "Aliyu idan kun gama ku je can gun Abban ku da yaran ku gaida sa" daga haka ta fita, haka kawai yaji gabansa na faduwa, Hijab din Ramla Noor ta sa, shi ya rike duk yaran biyu, yana gaba tana biye da shi har suka isa part din Abba, yana xaune hannunsa rike da newspaper idonsa sanye da Glass, kallo daya yyi masu ya ci gaba da karatun da yake, Abuturrab ya karasa kansa a kasa ya mika masa yaran, d'an jim yyi kafin ya ajiye takardan hannunsa ya karbesu gaba daya, ita kam Noor k'asan parlorn ta nemi waje ta xauna, ya kalleta ya nuna mata kujera, sunkuyar da kai tayi bata tashi ba yace "Xauna a sama" bata tashi ba still har sai da ya maimaita snn ta mike ta xauna, Abuturrab ya xauna nn kasa kusa da shi cikin sanyin murya yace "Good morning Abba" ba tare da Abba ya kallesa ba bbu yabo bbu fallasa yace "Morning!" Noor ma ta gaishesa kanta a kasa, ya kalleta yace "Morning, ya jiki" tace "Da sauki" kallon babies din hannunsa yyi, lkci daya yyi masu addu'a gaba daya ya mika ma ubansu, Abuturrab ya karbesu gaba daya, Abba ya jawo takardarsa ya ci gaba da karatun da yake, Hajiya Mariya ce ta shigo parlon da sallama, ganin ynda suke xaune shiru, shi kuma yana ta karatunsa ta kalli Noor tace "Tashi ki je Mami na kiran ki kin ji" kallon Abba tayi ta mike a hankali tace "Sai anjima" yace "Alryt" daga haka ta fita, Hajiya Mariya ta d'an tabe baki tace "Col tun asuba baka gama da jaridar nn ba" bai ko kalleta ba, Abuturrab ya mike yace "Sai anjima Abba" Ba tare da ya dago ba still yace "Ohk" Hajiya Mariya ta karbi yaran hannunsa tace "Ka karbi car key gun Mami ka jira ni xa mu fita" yace "to" daga haka ya fita duk jikinsa a sanyaye, Hajiya Mariya ta kuma kyabe baki ta karasa gun Col tace "Toh Abban Abuturrab Atm card xaka bamu mu je siyo ma jikokin ka kaya, bbu komai nasu a gidan nn" tana magana ne tana kallonsa, can ya dago ya kalleta yace "Ni xan bada Atm card?" Tace "Kwarai kuwa Sir, idan baka bayar ba waye xai bada Col" ya girgixa kai yace "Ki je dai ki karbi na uwarsa, bn yi budgeting siyan kayan yara ba wnn watan" dariya ma ya bata, ta ajiye yaran gefensa tace "Suna dai jin ka kar wataran su ce basa yi da kai kaji haushi, kuma kaya ne dai sae granny ya siya masu" daga haka ta nufi gun da ya ajiye makullin mota don ta hango Atm card din ta dauka tayi hanyar kofa ya bi ta da kallo har ta fita, can ya kalli yaran dake ajiye gefensa, ni dai har na bar dakin da takardata da biro bai daina kallon cute angels din gefensa ba. Bayan kusan awa daya Noor na kwance dakin Mami, sai dai gaba daya hankalinta bai jikinta don bata san inda yaran suke ba, gashi ta kasa tambaya, Ramla dai na ta gyaran press don a xuba kayan babies idan su Hajiya Mariya suka dawo, Mami na taimaka mata, Abba ne yyi sallama bakin kofa, Mami ta amsa sallamar ta karasa kofar da mamaki don ba haka nn yake tahowa bangarenta ba, bude kofar tayi ta gansa tsaye da yan biyu hannunsa yace "A basu abinci" karban yaran tayi tana kallon yanda suka yi da baki wai yunwa, tayi murmushi ya juya ya bar gun, ta shigo ciki ta ajiye su gefen Uwarsu tace "Tashi ki ba basu abinci Daughter" mikewa xaune Noor tayi tana kallonsu har bata san lkcn da tayi murmushi ba. Karfe sha daya na safiyar ranan Ummi ta iso gidan, ba karamin farin ciki tayi ba ganin twins din, ta rungume Noor da ta kasa kallonta tace "Samha kin bamu wahala da yawa" ita dai Noor bata ce komai ba, kaya ba kadan ba ita ma ta taho ma da twins, ganin bata ga Abuturrab ba tace "Ina Aliyun kuwa?" Mami tace "Sun fita da Mariya" Ummi tace "No more sickness knn koh" Mami tayi murmushi bata ce komai ba, Fatima ta shigo tare da su Ilham ta gaida Umminta suka fita, Ummi bata yi minti sha biyar gidan ba Umma da su Maryam da farida suka shigo, Mami taji dadin ganinsu ta tarbesu da fara'a suka shigo har bedroom ganin Noor, ba kaya na wasa ba suma suka taho ma da yan biyu, Mami tace "Amma ya ku ka gane gidan?" Umma tace "Ahmad ne ya kawo mu yana waje" Mami tace "Gashi Abuturrab din sun fita daxu wllh" bata rufe baki ba sai ga shi sun shigo da Hajiya Mariya, kansa a kasa duk ya gaida su, Ummi dai sai kallonsa take kamar tayi dariya ganin ynda yake sinne kai, a xuciyarta kuwa mamaki take duk irin gata irin tasa ya gwammace yyi ta wahala a kan so, Mami tace "Wai kun hadu da Ahmad?" Yace "Eh tare muka shigo yana parlor, na xo gaishesu ne" Mami tace "Ohk, kace ma su Ilham su kai masa ruwa" juyawa yyi ya fita, Noor dai duk a takure take a dakin, Mami na lura da ita tace "Ki je can dakin ki kwanta kin ji" a hankali tace "Toh" kallon yaran tayi ta mike ta fita, tunani ta dinga yi ynxu fa da xata fita gate bai fi tayi taku kadan ba xata isa gidansu, taga mumynta ta ga Abbanta, hawaye ne ya cika idonta tunanin hakan da tayi, ta shiga dakin Abuturrab a sanyaye ta kwanta. Karfe daya da kusan rabi Anty Maryam ta iso gidan, uhm duk ta fi kowa murnar ganin 'yar ta, duk ta rasa inda xata sa ta, ko ta kan yan biyu bata bi ba, Hajiya Mariya dai sai kallonsu take da tausayi haka ma Ummi, Noor na jikinta tace "Anty me yasa baki xo da Ihsan ba" Anty Maryam tace "Xa a kawo su daughter" can a hankali Noor tace "Anty baki tambayi babies dina ba" xaro ido Anty Maryam tayi haka ma Ummi, Hajiya Mariya tayi murmushi tana gyada kai, Anty Maryam ta ja hancinta tace "Amma baki da kunya daughter" shiru Noor tayi tana kallonta, can tayi murmushi ta boye fuskarta jikinta. Sai kusan la'asar Ummi ta bar gidan, ta so su koma da Fatima don next week xa su yi resume Mami tace ta bari sai anyi suna, su Umma dama tun biyu Abuturrab ya maida su gida don Ahmad ya wuce. Noor da dakin Abuturrab da Anty Maryam bayan tafiyar Ummi, Mami kuma na yi ma yara wanka,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login