Showing 9001 words to 12000 words out of 180592 words

Chapter 4 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1124

kayan wutan gaba daya cikin mintunan da basu wuce talatin ba ta gama komai ta mayar inda suke snn ta dawo parlor ta xauna tana kallon agogo taga har bakwae da sha biyar, ji tayi kmr ta saka kuka, yanxu ina xata ce ma Mumy ta je, haka tayi ta xama har bakwae da rabi, can ta mike ta dau Bible din ta, taji an kwankwasa kofa, still tayi gabanta na faduwa, kaddai yan gidan ne, karasawa tayi a hankali tana leka window ta ga shi ne tsaye, takalminta ta sa ta bude kofar hade da hade rai ta fito xata wuce ya riko hannunta ya wara ido yace "Wait in raka ki mana, Abbana ne muka hadu a mosque ya aikeni fa" ta kallesa kamar xata yi kuka tace "Toh yanxu ina xan ce ma Mumy naje bayan tun six thirty ya kamata in dawo gida" ya langwabar da kai yace "tell her you went to visit a sick frnd" shiru tayi tana kallonsa can ta girgixa kai a hankali tace "My religion is against lies, we don't tell lies" kasa ce mata komai yayi ya kuma kasa daina kallonta duk sai bai ji ddin amsar ba, can yace "And my religion also! Lying is one of the greatest sin in islam" Wani kallo tayi masa sae kuma tayi dariya tace "amma karya kace inyi a gida yanxu fah!" Kallonta kawai yake duk sai yaji ya tsani kansa hakan da yace mata, "I was only joking, idan nace ki shiga wuta sai ki shiga, religion din ki ya hana karya amma bai hana fita night birthday ba koh?" A bit annoyed yayi maganar hakan yasa tayi shiru tana kallonsa bai kuma kallonta ba ya karasa cikin parlon yayi xamansa ta bi sa da kallo, can ta juya cikin sanyin murya tace "Ohk, good nyt" a takaice yace "Nyt!" Ta fita daga parlon, ta kusa minti biyar da fita sai kuma ya mike shi ma ya fita, ko alamar ta bai gani a layin ba, yayi jam din gate dinsa ya bi ta da sauri, yana shan kwana ya hango ta tsaye ta rakube jikin wani flower ya daga k'afa ya karasa gun da sauri, k'arnuka biyu ya gani a gun suna xaune shine yasa ta kasa wucewa, dafata yayi ta fasa wani ihu a tsorace ya juyo da ita da sauri ta fado kansa ya rungumeta, lamo tayi jikinsa yana jin yanda kirjinta ke bugawa kamar xai fito, a hankali tace "Doctor!" Yace "Yes matsoraciya" janyeta yayi jikinsa ya rike hannunta suka ci gaba da tafiya har suka wuce gun karnukan tana shishshige masa, bbu wanda yace komai cikinsu har suka iso bakin gate din gidan nasu ya sake hannunta ta kallesa cikin sanyin murya tace "Thank you" murmushi yayi ya rungume hannayensa yana gyada mata kai, ta mayar masa da murmushin ta bude gate dinsu ta shiga ta daga masa hannu snn ta rufe gate din, lumshe ido yyi ya bude sannan ya juya ya bar wajen. Samantha na shiga gida suka kusa cin karo da Mum dinta bakin kofa, uwar ta hade rai tace "Where are you coming?" Shiru Samantha tayi tana kallonta a tsorace, "Baxa ki bude baki ki min magana ba kina kallona, karfe shidda aka tashi church, daga ina kike yanxu?" Sauke kanta tayi kasa, ta mata wani tsawa tace "Ba kya ji na ne?" Kamar xata yi kuka tace "Am sorry Mum, baxan kara ba" Mum din ta daure fuska tace "Wato ba daga church din ma kike ba ko....." Dad din Samantha ne ya karaso bakin kofar Samantha ta kamo hannunsa hawaye cike idonta tace "Abba kace ma Mumy tayi hakuri baxan kara ba, am so sorry" patting din shoulders dinta Abban yayi yace "It's ohk love kar ki sake dadewa church da an tashi ki dawo gida" kai ta gyada masa, ya ja hannunta suka bar wajen. Karfe tara Samantha na shirin kwanciya Mumy ta shigo tace "Oya tashi ki shirya mu je vigil tunda gobe friday da wuri xaki dawo sch sai kiyi bacci" Samantha tace "Mumy but karatu nake son xan....." "C'mon my frnd tashi kiyi abinda nace, karatu ya fi addinin ki ne" mikewa Samantha tayi bata kuma cewa komai ba ta fara shiri uwar ta juya ta fita, sai da suka yi ma Dad sallama snn driver ya fita da su xuwa church a mota, suna kusa kai wa dai dai gidansu Abuturrab Samantha ta hango gate din a bude sai gashi ya fito da mota, dai dai tsakar titin ya bude motar ya fita ya shiga gida don kulle gate din, masifa Mumy ta shiga yi Driver na taya ta don ya tare masu hanyar wucewa, Abuturrab ya fito da niyar xai basu hakuri Mumy ta sauke glass cike da masifa tace "Kai halan titin nan na Ubanka ne?" shiru yayi yana kallonta don sarai ya ganeta, Samantha sai kallonsa take, can ta kamo hannun Mumy tace "Mumy kiyi hakuri kila bai san...." Turata uwar tayi tace "Uwarki, shi makaho ne bai hango motar mu ba?" Abuturrab ya dauke kai ya nufi motarsa ya bude ya shiga ya gyara parking ya basu hanya, har suka wuce idonsa na kan motar. Ranan Juma'ah yana isa main road xai je masallaci ya hangota tana saukowa daga motar gidansu, tana sauka kuma motar ya wuce, xata wuce motarsa yace "Hello!" Juyowa tayi da sauri tana ganinsa tayi murmushi ta d'aga masa hannu.


=???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

5.....

Ganin yaki tafiya ta karasa kusa da motar tace "Ina yini?" Yace "Lafiya ya schl?" Kai kawae ta gyada masa yace "baki yi bacci bane see ur eyes!" Langwabar da kai tayi tace "We went for vigil" ya kalli wrist watch din hannunsa yace "Come in let me drop you" ta xaro ido tace "Ba masallaci xaka je ba?" Yace "There is still time" xagawa tayi ta bude front seat ta shiga, yayi reverse ya juya, a hankali tace "Sorry for what happened yesterday night" murmushi yayi yace "Yeah am at fault, gaskiya mama ta fadi" bata kuma cewa komai ba har suka iso bakin gate dinsu yayi parking ta bude motar ta fita ta rufe snn ta jingina jiki tace "Thank you" gyada mata kai yayi tace "Don't forget to pray for me fa" murmushi yayi yace "Alryt," daga haka ta nufi gate shi kuma ya tada motar ya bar layin. Washegari da ya kasance asabar Abuturrab na dawowa daga masallaci ya shiga main house don gaida Abba kasanacewar yana gari, Abba ya amsa gaisuwarsa idonsa dake dauke da glass a kan laptop din dake gabansa, can Abuturrab ya mike da nufin wucewa Abba yace "Ina fa da magana da kai Ali" komawa yayi ya xauna yace "Toh gani Abba" Abba bai ce komai ba har na kusan minti biyar sai kuma yace "How about planing of settling down Aliyu!" Shiru Abuturrab yayi don sai da gabansa ya fadi, Abba yace "Yes it's high time you do that, you will be thirty one soon...." Abuturrab ya sauke kansa kasa kana yace "Abba komai fa lokaci...." Abba ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Don't tell me that, Sai yaushe lokacin xai xo?" Shiru yyi bai ce komai ba, Abba yace "Go and think about it pls" a hankali yace "Toh Abba nagode" daga haka ya mike yyi masa sallama ya fita, bedroom din Maminsa ya nufa ya sameta xaune har lkcn kan darduma, Khaleesat kuma na kwance kan gado tana bacci, ya xauna bakin gadon, can ya gaji da xaman yayi kwanciyarsa kawae, sai kusan bakwae Mami ta gama Azkar dinta ta mike ta dauke darduman tana kallonsa don idonsa a lumshe yake tace "Abuu are you sleeping?" Bude idon yayi ya mike xaune sannan ya sauko kasa ya gaisheta ta amsa tace "Ka tashi lafiya?" Yace "Yea, but Abba spoilt everything" Mami ta d'an bude ido tace "Me kuma ya faru" ya marairaice yace "Mami wai maganan aure fa Abba ke min, yaushe ma na girman" Mami tayi murmushi tace "Mancewa kayi, jiya ka girma" yace "Allah Mami kije kiyi masa magana kice ur son is not grown up yet, yaushe ma kika daina ban madara da daddare?" Dariya Mami tayi ta xauna gefen gado tace "Silly you! c'mon tashi ka ban waje, it's better kaje ka xauna ka yi tunani da kyau kaga what's good for you, kilan idan kayi aure zaka nutsu" mikewa yayi yace "Am not ready for marriage Mami, toh waye xai xama mijin ma idan aka yi auren... Ita ko ni" Bai jira cewarta ba ya fice ta bi sa da kallo tana murmushi, jallabiyar jikinsa ya cire ya dau kayan sport dinsa ya sa ya dau chill Coke a fridge snn ya fito ya nufi gun da yasa aka tula masa kayan gym, ya kusa awa daya gun yaji kamar an bude gate, xagayowa yayi da sauri, tsaye tayi bakin kofar tana kallonsa hannunta rike da littattafai tana sanye da bakar abaya tayi rolling kanta, ganin kallon da yake mata yasa ta kasa tsaye gu daya, can tace "Um Good morning" sai kuma ta juya da sauri xata wuce, yace "Frnd!" Juyowa tayi, ya mata murmushi ya karasa kusa da ita ya rungume hannayensa yana kallonta, sunkuyar da kai tayi, yace "Ina xa ki this early morning?" Dago kai tayi ta kallesa tace "Lesson, waec lesson!" Yace "Ohh that's nyc, how was ur nyt?" Ta wara ido tace "Splendid! Xaka min assignment plss sir" langwabar da kai yayi yace "Assignment kuma, which?" Tana kkrin bude littafin tace "Physics and Biology" mika masa tayi ya karba yana kallo snn yace "Uhm!" Tace "You are busy koh?" Ya kalleta yace "Sai yamma zan fita aiki, am around now" cike da shagwaba tace "Toh ka min plss" kallonta kawai yake, can yayi murmushi yace "Ohk, but I will only show you how to solve it, and you do the rest by ur self" ta xaro ido tace "But am going to lesson...." Yace "Wannan ma ai lesson ne" shiru tayi tana kallonsa, ya mika mata littafin yace "Shiga ki ajiye a ciki, tare xa muyi" a hankali ta sa hannu ta karba littafin ta nufi cikin parlon amma da gani ranta bai so ba, ya sauke hannunsa ya bi ta da kallo sai kuma ya juya ya koma gun gym din ya dau sauran coke dinsa ya shiga parlor, tsaye ya ganta ya karashe shanye coke din ya wurga can din yace "Why standing like a soldier?" Murmushi tayi ta d'an dosana kugunta jikin kujera, ya karasa parlon yace "Let me freshen up sai mu fara" kai ta gyada masa kawai ya dau hanyar bedroom dai dai lkcn da aka danna bell, dawowa yayi da sauri ita kuma ta mike tana kallonsa da damuwa tace "ur sisters koh" bai tanka ta ba ya nufi kofar ya leka ya ga peter ne dauke da breakfast, bude kofar yayi ya karba ba tare da ya amsa gaisuwar da yake masa ba yace "Thank you" sannan ya rufe kofar ya karasa parlon ya ajiye, har lkcn tana tsaye tace "Kar sisters dinka su xo fa" yace "Bbu kowa gidan fa, duk sun tafi islamiyya" a hankali ta koma ta xauna, ya wara mata ido snn ya wuce, ya kusa minti talatin kafin ya fito sanye da farin polo da 3qtr baki ya shigo parlon yace "Sorry for keeping you waiting" murmushi kawai tayi ya xauna kan rug ya matso da tray din breakfast din da aka kawo mai, ya kalleta yace "Je kitchen ki kawo wani cup plss" ba musu ta mike ta wuce kitchen din sai ga ta ta dawo da cup ta samesa yana hada tea me kauri, ta ajiye masa cup din ta koma ta xauna, ya hada wani snn ya kalleta yace "Taho muyi breakfast" ta xaro ido tace "Noo, ni fa na k'arya" gyada kai yayi yace "Ashe ko baxa ayi assignment din ba yarinya" ta marairaice tace "Da gaske fa doctor na ci abinci" ya hade rai sosai yace "Toh ai shknn" shiru tayi tana kallonsa sai kuma ta mike ta karaso kamar xata yi kuka ta xauna, yace "Allah ya taimake ki da bbu abinda xan maki" murmushi tayi ta sunkuyar da kai, ya ajiye mata cup din tea a gabanta, snn ya debi potatoe, yam, egg, plantain a plate daya ya ajiye mata sai pepper soup din naman ram ya ajiye mata, ta marairaice tace "baxan iya cinye su ba Dr" yace "Ohk to mu ci tare" dawowa yayi gefenta ya xauna ta kallesa ta gefen ido, ya dau fork daya ya ajiye mata daya snn ya soma ci, da kyar ta iya daukar fork din don duk a takure take ta dauki potatoe ta kai baki a hankali tana satan kallonsa, sai cin abunsa yake, ganin yanda take tsakuran abincin ya ajiye fork din hannunsa yana facing dinta yace "Kinsan Allah idan baki ci abincin nn ba bbu abinda xan maki" ta xaro ido tace "Kaga ina ci fahhh" hararanta yayi ya ci gaba cin abunsa, haka yasa ta bude ciki ta ci abincin sosai don sai da suka cinye wanda ya diba snn ya shanye tea dinsa ya mike yace "Fast ki shanye tea din mu fara" kai kawai ta gyada masa kamar xata yi kuka don ta koshi. Yana kallo ta dawo kusa da shi daga kasa ta xauna tace "Doctor na gama" kallon wajen yyi ya ga wayam ta kwashe komai yace "Are you sure kin shanye shayin kuwa" ta turo baki tace "In kawo cup din ka ga?" Ya gyada kai yace "Alryt! Kwaso books din" mikewa tayi, tayi yanda yace ta ajiye su a kasa, ya sauko ya rage volume din Tv din, ya bude physics book din yana kallo, shafa beard dinsa yayi ya lumshe ido ya bude yace "Ohk, listen attentively" tace "Toh" a nutse ya shiga mata solving din questions din yana mata bayani, ya maimaita ya kai sau biyar har sai da tace ta gane, yayi forming questions uku ya bata tayi ta karba tana kallo, ya mayar da hankalinsa kan kallon da yake, tana gamawa ta kallesa tace "Am through" karba yyi yana dubawa, can ya gyada kai yace "Then do ur assignment now" tace "Toh" snn ta fara assignment din, ko da ta gama tare suke yi biology din har suka gama, ta kalli agogo taga goma ya kusa ta kallesa kafin tace komai yace "Lokaci ya riga ya wuce, just read ur note...." Xaro ido tayi tana kallonsa tace "Ohk to xan tafi gida" yace "Mum xata tambayeki why you came back early" shiru tayi bata ce komai ba, yace "So it's better ki jira time yyi sai ki wuce" ita dai bata ce komai ba, yyi kwanciyarsa kan 3 sitter ya canxa station, wani American film ake yi tayi tagumi ita ma tana kallon movie din, gajiya tayi ta bude essential bio dinta tana kallo, kmr ance ta dago kai ta kalli Tv abinda ta gani yasa ta kallesa da sauri, lumshe ya ga idonsa, bata kuma kallon Tvn ba ta mike da sauri tayi hanyar kitchen, plates din da suka yi breakfast ta shiga wankewa tana gamawa ta gyara kitchen din snn ta fito da sweeper da mop har lkcn rufe ta ga idonsa sai ta ga kamar bacci ma yake, gyaran parlon ta fara yi da yake bbu wani kura cikin few minutes ta gama gyaran ta mayar da komai inda yake ta dawo ta kalli agogo ta ga sha daya ya kusa, one sitter ta xauna ta canxa station xuwa Bollywood, bata yi minti goma tana kallon ba ta jinginar da kanta jikin kujera sai bacci, bude ido Abuturrab yayi ta dalilin wayarsa da ya ji yana ring a bedroom ya mike xaune yana kallonta ganin yanda ta takure kan kujeran tana bacci, mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya durkusa, long lashes dinta kawai yake kallo ko kiftawa bbu can ya sauka idonsa kan dogon hancinta kafin d'an karamin bakinta, hannunsa ya daura kan fingers dinta ta bude ido da sauri, ya mike yace "You are not comfortable xo ki kwanta a can" xata yi magana ya kama hannunta ta mike ya nufi kan kujeran da ya tashi daga yasa ta kwanta snn ya wuce bedroom, missed call din Abokinsa Mujaheed ya gani ya shiga kiransa back, bugu uku Jaheed ya daga, daga daya bangaren yace "Ina ka shiga man?" Abuturrab yace "Was having a Nap at the parlor, ya aka yi?" Jaheed yace "Alryt gani tahowa....." Da sauri Abuturrab ya katse sa ta hanyar cewa "Yanxu fa xan fito office ku hadu a can" Jaheed yace "It's urgent....." Abuturrab ya kalli agogo yace "Ni na ma shirya fa, fitowa kawai xan yi" Jaheed ya d'an yi tsaki ya katse wayar, Tabe baki Abuturrab yayi xai shiga toilet ya ji ana danna bell, fitowa yayi da sauri, ga mamakinsa ko motsi Samantha bata yi ba, baccinta kawai take, kofa ya nufa a leka waje yaga Mami tsaye, xaro ido yyi ya juya da sauri ya isa gun Samantha tashinta ya shiga yi ta bude ido a hankali tana kallonsa, sai kuma ta mike xaune tana kalle kalle dai dai lkcn da Mami ta kuma danne bell tace "Abuu?" Mikewa Samantha tayi a tsorace tana kallonsa da kyar tace "Ur Mum?" Bai ce komai ba ya kama hannunta ya wuce bedroom dinsa da ita tana shiga ya rufe kofar snn ya fito ya koma gun Kofar ya bude, sai ka rantse daga bacci ya tashi yanda yyi da fuska, Mami tace "Bacci kake?" Gyada Kai kawai yayi, tace "Ohk sorry, ka xo ku gaisa da Yakumbo ta xo" shiru yyi yana kallonta sai kuma ya hade rai yace "Mami maimakon kice na fita aiki?" Mami tace "Go and freshen up ka fito ku gaisa nace, bana son magana" daga haka ta juya ta bar gun tana kallon karen dake cage abinsa, girgixa kai tayi tayi gaba. Abuturrab yayi tsaki ya juya ya koma bedroom dinsa, durkushe ya ganta bakin kofa ya buda ido yace "Me kike a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login