Showing 27001 words to 30000 words out of 116366 words
kai alamun Eh, sai ta juya ta na fad'in"To dauko Hijabinki ki biyoni falo zaku gaisa da Dr ne."
Ba musu na dauki hijabina dogo wanda ya kaimin har gwiwa fari na saka nabi bayanta zuwa falo, na iske ta zaune ita da Mijinta da alamu ma yana Shirin fita ne.
Kaina na kasa na kariso tunda naji sanda tace"ka ganta dai Dr."
Nayi kokarin na Durkusa sai na kasa na rike baya ina Cije baki da Sauri yace"Ke zauna kan kujera a bunki, ina ke ina Durkushe a wannan Halin da kike ciki."
Jin haka yasa na zauna saman kujera kaina a kasa ina gaisheshi ya amsa Lokaci d'aya ya na kallona sannan ya na Bina da Sannu sannu.
Surayya ya kallah kafin yace"Allah Sarki itama ai yarinyace kamar Sultanan nan."
Surayya tace"Eh ko zata girmeta da kad'an ne, kila ta yi sa'ar salima."
Sai ya jinjina kai kafin kuma ya murmusa yace"Abubakar Sulaiman Shinkafi i like u Staryle, ina son kanin nan naki Surry, Yana da wani irin Confident da Natsuwa tare da Hankali."
Ta na kallonsa tace"Sadiq ne, Abba kan ce karamin su babbansu."
Ya na yar dariya yace"Gaskiya ya fad'a ko ni da na ninka shekarunsa bazan iya yin abunda ya yi ba, in kika Lura ko magana ki ke da shi farat daya zaki Fahimci ya na Tauhidi da kiyayewa Sabon Allah, ga shi he is so kind Mutum ne Simple Straighth Forward. Kai Tsaye zaka ga ya na yin abu ba shayi bakomai ga Tausayi da zuciyar Taimako."
Surayya na jin dadin kyakyawan Hallayar Sadiq da mijinta ke zayyanowa game da kaninta tace"Duk gidanmu ba kamarsa Sadiq na da kyakyawan zuciya."
Dr yace"Sosai fa, kema wani Lokacin kuna kamanceceniyar Hali shiyasa taku tazo daya sannan Namiji ne fa tsayayye, zai iya rike mata Hud'u kuma su zauna lafiya."
Ya dago ya na kallona kafin yace"Ya sunan ki ne?
Kaina na kasa nace"Hasiya!"
Cikin mamaki ya kalli matarsa kafin ya yi mgana ta Rigasa da cewa"Asiya sunanta."
Ina jinsu kamar zan ce ni ba Asiya sunana ba, sai kuma na fasa kada kuma na fara wuce iyakata.
Cikin Yanayin maganarsa daga gani yana da barkwanci yace"Gaskiya kin yi sa'a Asiya, kin yi sa'ar samun Nagarttacen miji irin Sadiq."
Sannan ya kalli Surayya kafin yace"Kudos to Sadiq, zan so mu had'u na sara ma Namiji Uban maza.".
Hararansa ta yi kafin tace"Sai wani kod'asa ka ke yi ban gane ba ne?
Yana yar dariya yace"Kina jinta ko Asiya? Kwantar da hankalin ki in zan kara aure ke zaki fara sani."
Cikin gatsene tace"in ban sani ba ina ruwana Dr? Ba kaina zata zauna ba, ai ta mallam ba ta wuce Ameen"
Dariya ya sska mata ya na fad'in"Eh kaji ta. Allah yasa to da gaske ki ke."
Ya fad'a Lokaci daya ya na jan hancinta ba ita kadai ba har ni sai da na yi dariyan barkwancinsa.
Ta make hannunsa ta na masa Hararan wasa mikewa ya yi ya na Fadin"Asiya na tafi, kada ki damu You are Welcome in to Shinkafi Family da yardan Allah."
Kaina na kasa ban yi mgana ba sai dai na yi mirmishi nace"A dawo lafiya."
Nan suka barni a falo Surayya ta tafi raka mijinta.
Sai da sukaje haraban gidan bakin motarsa Sannan ya kalleta ya na fadin"Gaskiya Surry kada ki bari a wulakanta yarinyar nan, abar Tausayi ne da labarinta da kika bani, kuma ina da Tabbacin shima Sadiq Tausayinta yaji Shiyasa ya yi auran nan ba wanda ya sani."
Surayya tace"Hakane ai da kanta ta fad'a tace taimakonta ya yi saboda mahaifiyarta."
Dr yace"Nasan ta bangaren Abba game din mai sauki ne, Umma ce da Kakarku nasan sai kun yi ta ban baki da Nuniya."
Surayya tace"Kamar ka sani domin tun ajiyan Umma tace bata yarda da wannan auren ba, ko ya saki Asiya ya zauna da Sultana ko kuma ya saki Sultana ya zauna da abunda ya zab'a, innani kuma kasanta Allah da su Allah ya isa jiya ta yi ta makama Magajin gidan nata."
Dr ya jinjina kai yace"Daman ai za'a sha fama, ku dai ku tsaya mata don Allah, Umma ta Duba maraicinta tare da Rabon da ke tsakaninsu Thank god ma, sun yi aure da ta hanyar zina aka samu wannan cikin fa?
Surayya tace"Nima tunanin da na fara yi kenan a farko naji Tsoron Allah ya kamani nace to yanzu inda ba su yi aure ba fa? karfin Rabon da ke Tsskaninsu yasa ya lalace."
Cikin yar damuwa yace"To kin gani, ya kamata dai a duba lamarin cikin Fahimta sosai."
Surayya ta tabbatar masa da cewa in sha Allahu zata iya bakin kokarinta.
Sun yi sallama ya shiga mota ta mika masa jakarsa ya karb'a ya na fadin"Yanzu Zaku tafi chan gidan ne?
Sai ta girgiza kai kafin tace"Anya! Inaga sai anjuma kada mu je ta ga mutane ta kasa sakewa, kila sai Sadiq din ya iso."
Daga haka Suka yi sallama ya tada Mota ta na daga masa hannu sai da megadi ya Bude masa get ya fita Ssnnan itama ta koma cikin gida, Direba ya tafi kai yara makaranta daganan zai kai motar gareji, tana Tunanin ita zata Tukasu ita da Asiya zuwa gida anjuma.
Tana komawa falo ta ga Asiya har ta yi barci nan saman kujera.
Sai ta kara jin Tausayinta a Fili ta Furta baiwar Allah yanzu haka jiya bata samu barci ba.
Sai ta kyaleta ta koma dakinta ta Dauki wayarta sai ta ga Saddiqa ta kirata wajen sau uku bata kusa sai ta bi bayan kiran.
Taji tsoro da taji saddiqa na gayamata labarin ya bazu a kunnen har wad'anda ke nesa, yanzu haka ma Shahida daga katsina ta na hanya, Salima ma an ce ta taho, Subai'atu ke fad'amata ta kirata da Safe tace zata zo gusai itama zata zo ne? Sai ta nuna mata a'a bazata samu zuwa ba tunda sai adaran jiya ne Surayya ta kira Subai'atun ta na gayamata komai da kanta.
Surayya ta rike baki kafin tace"To duk waye ya fad'a musu?
Saddiqa dagachan bangaran tace"Kema kina da son jin magana wazai gayamusu wacce ta wuce mama"
Surayya sai ta kasa mgana, Saboda Daman Mama irin matan nan ne da komai ya faru sai ta kira ya'yanta ta fad'a musu macece dai mai son hira da ya'yanta akan komai..abunda ba Halin Umma ba kenan wani abun ma sai an jima da yinsa su ke sani a bakin yan Dakin Maman.
Saddiq ta katse mata Tunani da cewa"Saliha ce kawai kila bazata zo ba, ammh tun safe su Sakeena da Anty Sa'im suke gidan nan kuma nasan kan mganar ne."
Surayya tace"Allah ya kyauta."
Sai kuma ta kashe wayar saboda abun ne yazo mata a yadda batayi Tunani ba.
Bata dauka mama zatayi haka ba, taso ayi komai cikin sirri a gama sai daga baya kowa sai yaji, Tunda dai kowa ya sani bata da zabi illah ta daga waya ta Kira Sadiya da Sajida da sa'adatu tare da Sajida tace su zo gida yau akwai taro.
Dukkansu ba su yi mamakin kiran ba, a cire Sajida da tasan komai sauran sun ce su Sakeena ne suka kirasu suna fad'a musu abunda ke Faruwa suma kansu ya kulle daman suna Shirin zuwan gidan su ji in da kuma aka Haihu a Ragaya
Tana mgana da Sadiya a waya ta na gani Saddiqa na kiranta ba ta yanke ba.
Kuma suna gama mgana da Sadiya Subai na kiranta sai ta daga suna mgana ta na kara yi mata wasu bayanan ita kam sai fad'a ta ke yi ta na zagin Sadiq daman kuma ta na da fad'a Tun asali ita.
Da surayya ta fad'a mata abunda Mama tayi sai kawai ta yi tsaki kafin tace"Allah ya kara masa uban wa yaja? Da bai aikata ba, wazai yi yawo da mganarsa. Kuma hukuncin Umma da Saddiqa ta fad'amin ya yi daidai sai dai ya zaba don Ubansa."
Jin yadda ta Dauki zafi yasa Jikin Suryyya ya yi sanyi, ta so ayi wannan abu cikin Sirri ne bata Dauka abun zai kwabe haka ba.
Bata kara sarewa ba sai da Subai ta tabbatar mata da ta na hanya itama zata zo, sai ta ci uban Sadiq kuma sai ta kara Zuga Umma saboda yasan abunda ya yi bai kyauta ba.
Da farko Surayya bata damu ba ammh yanzu ta da fahimci gayya ne guda za su had'u masu bambamcin Ra'ayi sai taji tsoron abunda zai Biyo baya.
Ita Asiya take Tausayawama ba Sadiq ba tasan shi Namiji ne kuma duk tsiya dai shi nasu ne.
Falo ta lekoni sai ta iske har na gyara kwanciya sai barci na ke yi sai ta kyaleni ta shiga ciki ta na Tufka ta na faman warwara.
Sadiq ta yi ta kira da farko wayarsa bata shiga sai daga baya ammh kuma baya Dauka.
Sai kuma Hankalinta ya tashi ta Dauko ko wani abu ne ya same shi, sai da ya turo mata sakon ya na kan hanya ya kusa isowa gusau sannan ta samu natsuwa.
*******
11:13am
Karfe sha d'aya na safe Sadiq ya iso Gusau motar haya ya shigo daga Abuja bai zo da Motarsa ba, saboda Halin Fargaban da ya ke ciki bazai iya Samun natsuwar tuki ba.
Farko gidansa ya fara sauka Dake millions Quaters, ammh sai me Sultana bata nan, megadin gidan da Abba ya saka kuma ya ke biyansa albashi ya fad'a masa yace Tun safe suka fita da farko ya dauka Sun tafi makaranta ne.
Ya na da key din gidan a hannunsa dashi ya yi amfani ya Bude gidan ya shiga ya ijiye kayansa ya yi wanka sannan Ya taho nan gidan.
Yazo ya iske Abba baya nan ya fita Mallam Tajudeen ne ya ke fad'a masa Tun daga bakin get.
Shashen Umma ya fara isa, nan ya Iske Saddiqa da Sadiya, a yanayin kallon da suke masa yasa ya san suma susan komai sai kawai ya had'e rai, ya na cin mgani hannayensa suna sarke cikin Aljihun saukakken Farin yadin da ke jikinsa dinki riga da wando na zamani.
Umma na cikin daki, taki fitowa sai daya bita da kansa ammh kuma ya na durkusawa da niyar gaisheta yaga ta mike tsam ta bude kofar Tiolet ta shige da farko ya zata, ta shiga ta kama Ruwa ne zata fito sai da yaga yafi minti ashirin Umma bata fito ba ya zargi wani abu tunda shi dai bai ji karan Ruwa ba, kuma yaganta da wankanta tas ba wanka ta ke yi ba, in ya gane daidai shi ne bata son gani.
Cikin wani yanayi ya fito daga Falon sai kuma ya had'e da Sajida da ta iso ba Dadewa sun had'a kai da juna suna ta kuskus.
Suna ganinsa sai suka yi shuru suna kallonsu kallo daya ya yi musu ya Dauke kai zai fita, daman su Sadiya sun gaisa da shi da ya shigo, Sajida ce dai daman ba su gaisa ba.
Har ya kama hanyar Fita Sajida tace"A'a Sadiq ba mgana ne abun?
Kamar zai wuce sai ya fasa ya Juyo ya na kallonta kafin yace"Sorry ban lura da ke ba ne, Sajida ya gida da yaran?
Bai jira amsawarta ba ya fice suka rakasa da kallon mamaki.
Sajida ta rike Hab'a kafin tace"Wai yasan an san abunda ya aikata kuwa?
Saddiqa tace"Oho masa, zuwa yanzu ai ina jin yasan karyansa ta kare, Big sis ta gayamasaa tunda Abba da kansa yace ta kirasa tace yazo."
Sadiya tace"Ammh shi ko a fuskarsa ba alamun Tsoro ko nadama aciki.'
Sajida tace"Nima ai abunda nagani kenan, uhm baku san Sadiq ba ne yanzu sai ya rufe bakin kowa da Ayoyin Allah tare da Hadisan manzon Allah, Salallahu alaihi wasallam.
Sai Saddiqa da Sadiya suka yi dariya.
Shi ko ya na fita sai ya rasa ina zai nufa, kawai sai ya tsaya nan kofar Bangaren Umma yana Tunanin ta ina mganar auransa da Hasiya ta bayyana?
Duk iya hangensa bai hango masa wata kafar da ya bari a bud'e ba.
Tun jiya ya yi Tunanin ko Tahir ne? Ammh da ya kira Tahir ya yi challaging dinsa ba su kara rabuwar dad'i ba ma wannan karon.
Domin Tahir masifa ya faramai yana fadin da ya shiga tsaka mai wuyar da ya Sanya kansa aciki sai ya Kirasa ya na masa mganar Banza to ya saurara masa chan ya karata Tsuntsun da ya ja Ruwa shi ruwa zai yi ma dukan Tsiya kada ma ya kara kiransa daga karshe ya kashe masa waya.
Daganan ya kara tabbacin ba Tahir bane to waye? Ko dai Siya ce ta gayama Saliha? Ammh kuma ya na da kyakyawan yakini da Tabbacin Siya bazata yi abunda bashi cikin Tsarin sa ba.
Yana nan tsaye ya na wannan Tunanin bai ji ko zuwan Siyama ba sai jin muryanta ya yi ta na gaisheshi.
Cikin Firgigit ya dago ya na kallonta cikin mamakin ganinta.
Bata jira amsawarta sa ba, Saboda sai taji tana jin Haushinsa sannan ta na taya kawarta Sultana kishi.
wacce tun safe Umma ta kira su a waya tace sultana ta kwaso kayanta ta dawo gida.
Sanda suka zo Umma sai taki cewa komai, Siyama ce ta je bangaran Mama ta na fad'a mata abunda ya faru sai Maman ce ke zayyane mata abunda ya Faru, nan take taji ta na jin Haushim Yaya Sadiq tunda yaci Amanar Sultana.
Ita kuma Sultana har Anty Saddiqa kasa gayamata komai tayi, sai ta wuce bangaren Innani chan ne Innani ta zauna ta na kuka kamar an yi wani mugun abu ta warware ma Sultana komai har ta na cewa Hasiya tsohuwar kilaci ce Tunda an ce bazawarace ma ya aura ba yarinya ba, Ta yi tayi ma Sadiq Allah ya isa a gaban Sultana ta na kara fadin bata bashi har abada kuma bai isa ya yi ma Jikarta kishiya ba.
Sultana bata san ya ake jin girman Kishi a cikin zuciya ba sai yau, kasa sarrafa kanta ta yi taji gabadaya zuciyarta na wani irin zafi, wani irin bala'in kishin Sadiq ta ke jin acikin Zuciyarta tare da jin Haushin yadda ya Wulakantata ya iya auran wata mace kafin ita, Sai ta fara kuka ita kuma Innani ba lallashi sai faman Zugata ta ke yi, ta na fadin ta yi hakuri Sadiq fa ko ya zaba ko kuma ya saketa kowa ya yi ta kansa.
Ta na chan bangaren Innani ta na kuka, innani na gefe ta na kara iza Wuta, Farida ce kad'ai taje makaranta Allah yasa su sultana suna kokarin Fara jarabawar Fita ne.
Sadiq ya bi siyama da kallo da ke neman Shigewa bangaren Umma.
Cikin shakewar murya ya saka baki ya Kirata sai ta dawo ta Tsaya a gabansa.
Cikin mamaki yace"Baki je makaranta ba ne!? Ina sultana?
Kanta na kasa tace"Umma ta kira tace mu kawo kayanmu mu dawo gida."
Ido ya zaro kafin yace"Ita Umman ta ce haka?
Sai ta dago ta na kallonsa Lokaci daya ta na gyad'a masa kai.
Cikin Fad'uwar gaba yace"To yanzu ina ita Sultanan?
Kai Tsaye Siyama tace"Ta na bangaren Innani."
Aransa ya Furta Tabdijam, yasan ai kuma komai ya lalace tunda ya na da tabbacin Innani ba ta tab'a gyara abu ba sai dai ta bata.
Kai tsaye yace Siyama taje kawai shi kuma sai ya isa bangaren Mama su gaisa itama ya iske su Anty Sa'im, Sakeena da salima wacce ta iso itama da wuri.
Kamar na falon Umma suma daga gaisuwa ya hade ransa ya duka ya gaida Mama ta amsa ta na ta kallonsa cikin mamakin ganin ko razana bata gani a tare dashi ba.
Daman kuma suna mganarshi ne ya Shigo sai suka yi shuru, suna ta maida yarda aka yi, Salima na kora musu wasu bayanan daga bakinta.
Mama saboda maganar na cinta sai da tace"Sadiq sai kuma mukaji wani al'amarin na ban mamaki?
Kai tsaye ya kallets kafin yace"Kamar na me fa?
Sai Mama ta kasa mgana, ta koma ta na kallonsa shi kuma kawai ya mike ya yi mata sallama ya fita.
Ya na fita Sakeena tace"Tabdijam yau akwai kallo a gidan nan"
Salima tace"Ya Sadiq ya iya lauya jibesa kamar baisan abunda ya faru ba."
Mama ta yi shuru saboda ta kasa mgana, Daman ita fa tasan Sadiq ba shi da Tsoro ba lalle su ga wani Razana a fuskarsa ba.
Shi ko ya na fita sai ya rasa ina za shi, saboda a wannan Lokacin ya na jiran Hukuncin Abba ne, Umma kuma daman yaga ta riga ta dauki nata.
Abu daya ya sani shine ya yi kuskuren yin aure ba da sanin iyayenshi ba.
Ammh bai yi kuskure domin ya yi aure ba, sannan zai Tabbatar da cewa an yi masa Adalci kuma an yi ma Siya itama adalci.
Yana Tsaye a haraban gidan, sai ga Subai'atu ta shigo gidan bayan mai adaidaitan da ta hawo daga tasha ya kawota da Sadiq ta fara cin karo ya na jingine jikin motar Abba.
Tun daga nesa ta ke hararansa shi kuma sai ya yi kamar bai gani ba ya tareta ya shiga yi mata sannu da zuwa.
Wani kallo ta yi masa kafin tace"Sai kuma idonka kenan Sadiq? Tare da bazawaarar matarka ta ka kake ko kai kad'ai kazo?
Sai da yaji wani iri, ammh sai bai yi mgana ba, shi fa daman yasan irin wannan Ranar ta na zuwa sai dai Shirya mata ne bai yi ba.
Sai kawai ya Daure Fuska kafin yace"Ni kadai nazo mana."
Saboda bayan Surayya da Saddiqa ba wanda yasan Hasiya ta zo.
Surayya tace kada Saddiqa ta yi zencen da kowa.
Kai Tsaye ta kallesa kafin tace"Kai yanzu kana karamin yaronka da kai har kasan kayi mata Biyu? Kuma ka rasa waza ka aura sai bazawara Sauran wani katon?
Kamar ya bata amsarta sai kuma ya fasa, yana jin zafin bazawarar da ta ke kiran Siya da shi sai dai shi yanzu fad'a ba nasa ba ne.
Shiyasa ya na tsaye Subai ta gama gayamasa dukkan maganganun da ke bakinta ta kuma zageshi son ranta shi da Siya sannan ta wuce cikin gida
Ransa ne yaji kawai ya fara baci, yana mamakin wai suna kyamatar Siya Saboda ita bawarawace kenan susan komai da ya danganceta kenan.
Turkashi lalle akwai kura.
Gajiya ya yi da tsayuwa sai ya yi Tunanin ya tafi bangaren Abba, duk da shima kunya ya hanashi ya Kirasa.
Yana kokarin juyawa yaji Hon a bakin get sai ya dakata.
Mallam Tajudeen na Bude kofa yaga Motar Big sis, na shigowa gidan Saboda Hankalinsa na wajen Surayya bai kalli wacce ke gefenta ba ya Dauka cikin yan'uwansa ne dai.
Ammh kuma ya sha mamaki bayan Surayya ta faka Motarta ta fito, ta dayan bangaren yaga wata ta fito mai kama da Siya dinsa.
Kara waro ido ya yi sanda suka Doso sa, Hasiya na yin baya baya Surayya ta Rike mata