Showing 15001 words to 18000 words out of 116366 words

Chapter 6 - Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

311

ce yasa ba ta taba Furtama kowa ba.
Sun Rabu da Sajida akan sai goben, Direban mijin Surayya zai tukasu zuwa zariya, ita kuma Saddiqa daga bangaranta surayya tace ta jira su Dawo daga zariyan
Saddiq ita kanta hankalinta a tashe ya ke, Wayau ta yi ma Khairiya tace ashe Hasiya kawar wata kanwarta ce, sai daga baya ta ganeta, daman kuma ta rasa lambarta ta na son adireshin Hasiya saboda kanwar nata na son in ta shiga zariya taje wajen Hasiya.

Shine khairiyan tace bari ta yi ma kanwar nata mgana, sai gashi har da lambar Hasiyan aka Turo mata.
Daga khairiya har Safiya ba su san abunda hakan zai haifar ba.
Ballatana Hasiya da ke chan bata san abunda ke faruwa ba.
Uwa uba Uban gayya Sadiq da ke chan Abuja kan aikinsa bai taba kawo ma kansa abubuwa zasu lalace masa batare da ya sani ba.







*Janafty*
*TMWBK3004*


*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/IhAz8h8nRy250ZnGGXwM65


*LAME NIG!*

*KASAITATTUN MATA MUN GAISHE KU*.
*AISHA LAME TA KAWO MUKU DUKKAN NAU'IN KAYAN KWALLIYA*.
*KUNSAN GWANAACE WAJEN BAWA FATA HAKKIN TA*
*KUN TUNA KYUAN FATAR GUDUYO KO?*
*KUN TUNA DAI YADDA BULKACHUWA KE SIYAWA YABI KAYAN KWALLIYA NA ORIFLAME KO?*
*TO KEMA GARZAYO KI ZABI NA KI, KO TA ZABA MIKI WANDA ZAI FI DACEWA DA FATARKI*.
*BA IYA KAYAN ORIFLAME BA KAD'AI.*
*TANA DA PRODUCTS DABAN DABAN MASU KYAU, MASU MASTAKAITAN FARASHI*.
*KU TUNTUBE JIKAR DADAR MARINA A WANNAN LAMBAR 07036662633*.
*ADO DA KAMSHI NE SIRRIN GAYU*

Washegari.
Zariya.

Yau Alhamis muna da karatu a makaranta, ammh saboda yadda na tashi cikin nauyin jiki yasa na yanke shawaran bazan fita ko'ina ba.
Kafafuna ne na lura yau sun kara tasawa, sannan kamar cikin jikina ya sauka a saman kafafuna haka na rika ji, Dakyar na iya tashi na yi shara da goge goge saboda wajen kwana hud'u ban iya taba komai acikin dakin ba.
Assadiq ya kirani Tun asuba shi ya ma tasheni sallar asuba, kuma bayan na idar ya sake kirana mun yi mgana, sai da ya tabbatar da lafiyata kalau sannan yace na koma na kwanta na Huta.

Ban yarda na fad'a masa yanayin da na ke ji ba, yanzu sai ya d'aga Hankalinsa ya kasa natsuwa, kuma naga lalurorin ma su cikine, shiyasa ban gaya masa ba dama ya tambayeni zan shiga makaranta ne sai na amsa masa da Eh! Har kuma yace zai Turomin kud'i ya na tunani na hannuna sun yi kasa.
Ko da na gama gyaran dakin nan, sai da koma na zauna ina ta faman Numfarfashi na tsawon wani Lokaci sannan na tashi na shiga kitchen na Dumama ragowan Tuwon da Maman Suhailat ta zubomin jiya.
Tuwon masara miyer karkashi, rabi na ci jiya na rage na safe, ga uban wanke wanke jibge  na fara tunanin ko na kira Adda Fati ne Habiba tazo? Domin har ga Allah zan sha wahala in nace zan tsaya na yi wannan wanke wanke.
Sai da na gama cin Tuwon sannan na fara Tunanin wanke kwanukan, abun dai sai a hankali ina yi ina faman Hutawa, kafin na gama baya na ya kage, kafafuwa sun kara nauyi, ko gyara kitchen din ban yi ba, na koma cikin Daki na kwanta da na huta sosai har sai da naji ina jin barci barci.

Sai dai ban kwanta ba, ta shi na yi na sake ruwan zafin da na saka a kittle, na shiga wanka na gasa jikina, da na Fito sai na Shafa mai, saboda kaya na duk sun matseni na dai na saka su, iyakata Dogayen Riguna da T.Shirt da riga da zani.
Kuma duka sun yi datti, na had'a zan kira Habiba ta zo ta je gidan Adda Fati da shi ta wankemin, Tunda ni dai yanzu ina gabda daina Daukan Laluran kaina.
Sai na Bude bangaren da Kayan Assadiq suke cikin Wadrope d'ina na Dauko wata farar T.Shirt dinsa na saka na dauka ma zata yi min yawa Tunda ta na da fad'i ammh sai naga ta shigeni gabadaya, sai na had'a ta da wani zanin Atamfata na saka Hula.
Wayata na dauka na yi masa Hoton kaina da Rigar ina Dariya a raina nace in yazo zan nuna masa rigarsa har ta faramin kad'an.
Game na fara yi a waya ta, daganan bansan Lokacin da barci ya kwasheni ba, sai da naji kamar daga sama ana ta Bugamin kofa, na mike da sauri wajen saukowa daga kan gado har sai da naji kafafuwana sun sage, kuguna ya amsa sai da na tsaya na yi salati na d'an sarara sannan na fita zuwa falo ina kokarin gyara hulan kaina.
Har na isa kofar dakin knooking a ke yi cikin Sanyin murya nace"A na zuwa."
In da ace nasan abunda zan gani in na Bude kofar nan, na tabbata ko da kud'i aka had'ani bazan taba Budewa ba.
Gwara rashin Budewan akan Bud'ewan, ina jin d'an cikina na Motsi lokaci bayan Lokaci ammh yau da na ga Yan'uwan Assadiq Tsaye a gaban kofar dakina sai da naji kamar abunda ke cikina yafi d'aya, Saboda yadda cikina ya murd'a naji ta ko'ina ana juyi tare da irin naushi kamar dai akwai abunda yafi d'aya acikin cikina.
Tsabar kad'uwa yasa sai naji kamar an kafeni a wajen, bakina na rawa tare da kiftawam idanuwana, zuciyata kuma ta na barazanan fitowa waje saboda Tsabar tsoro da Firgici.

Yadda na ke kallonsu ido waje haka suma suke kallona, na gane su bayan ganinsu a hoto dukkansu na gansu a bikin Sultana da Assadiq har mun gaisa.
Ina rike da Kofar Rud'ewa yasa na ma kasa saki, Sajida ce ta kalleni kamar Idanuwanta zasu fado kasa saboda takaici Cikin gatsali tace"Ke ce Hasiya?
Sai kawai na samu kaina da gyad'a mata kai ina jin marata ta Daurewa kamar ace haihuwa zan yi, Sajida zata kara mgana Surayya ta kalleta kafin ta girgiza mata kai alamun tayi shuru, kaina ta dawo da kallo kafin tace"Zamu iya shiga ciki?
Ta fad'a kai Tsaye ta na kallona, sai a lokacin na lura da yadda na tare kofar, cikin daga kafa na matsa baya ina fad'in"Eh eh! Ku shishigo sannun ku da zuwa"
Bakina tare da bugun zuciyata su ke tafiya, Surayya ce kan gaba Sajida na bayanta Dauke da yarinyarta a saman kafad'anta.
Tsabar Rudewa na kasa bin bayansu, Sai da na tsaya dafe da kuguna acikin raina ina maimaita"Innalillahi wa"inna ilaihirraju'un shikenan abunda na ke ta gudu ya zo ya faru, ai shikenan"
In da ina da yadda zan yi bazan bi su ciki ba, fita zan yi na nemi mafaka ammh kuma bani da wata mafita, sai dai a chan kasan raina ina Tunanin ko dai Saliha ce ta aiko su? Sai naji kamar mganar ba ta zauna a raina da hakan zai faru ba.

Da jan kafa na kariso falon na iske su har sun yi ma kansu matsugguni a daya daga cikin kujerun falon.
Surayya wayarta ta ke dannawa ta yi shigar alfarma sannan Fuskarta bata bayyana abunda zuciyarta ke ciki ba  Sajida ko sai faman kalle kalle ta ke yi cikin Raini da wulakanci.
Kamar wacce wani abu ke cizo a kafa haka na kasa tsayuwa a gabansa sai na juya da sauri na shiga kitchen jikina na rawa, na dauko musu Ruwan Gora guda biyu kofi na saka cikin wani Farantin silba.
Na Kwaso ina rawan kafa da na zuciya na kawo gabansu na sauke sannan na Durkushe ina jin kamar ina cikin wani abu mai zafi saboda yadda Tsoro da firgici suka saka naji kamar ina cikin zazzabi mai zafi.
Surayya ta kalleni yadda na zauna duk a takure sai tace"Ayya kinga ta shi ki koma saman kujera"
Kaina na kasa ammh na kasa mgana a raina ina fadin ko dai ko dai?
Saboda ban ga alamun sun san wani abu ba.
Kamar daga sama naji Tace"Hasiya ko?
Sai na dago da sauri ina kallonta kafin nace"Eh eh ni ce."
Kai Tsaye tace"Nasan kila kin gane mu, in ma baki gane mu ba mu yan'uwan Saliha ce, mun had'u da ke da kika zo mana Biki a gusau."
Cikin yaken karfin Hali nace"Eh an yi haka sannun ku da zuwa."
Surayya ce kad'ai ta amsa kafin ta kalleni na wani lokaci.
Sajida ta kalleta ta na fadin"Big sis mu yi abunda ya kawomu, na kosa mu bar nan.".

Surayya bata ce komai ba, sai dai ta mike ta zo ta zauna kusa dani, jikina na rawa naji na sake zaman Dirshan a kasan Tayels, Kallona ta ke yi ni kuma na kasa kallonta kallo d'aya zaka yi min kasan bani da gaskiya.
Cikin Kakkausan murya Surayya tace"Hasiya tambayarki na zo yi takanas daga Gusau zuwa garin da ban taba zuwa ba, kuma ina so komai na Tambayeki ki fad'amin gaskiya, in kuma kika yi min karya nan gaba zai zame miki matsala, ita kuma gaskiyarki in kika tsaidata Allah shi ne zai nuna miki aikin gaskiya, ina fatan zaki fad'amin gaskiyan Abunda kika sani"
Ina salati a cikin raina, a fili kuma sai na gyad'a mata kai zuciyata na rawa nace"In sha Allahu zan fad'a miki iya gaskiya abunda na sani."
Sai ta gyad'a kai kafin naga ta Dauko wayarta ta Danna ta saukemin wayar a saman Fuskata, lokacin da na yi arba da Hotona ni da Assadiq sai da naji na fara fitsarin da na matse, cikin gwalalo ido na kalli Hoton sannan na koma ina kallonta tare da mamakin ina suka samu wannan Hoton?.
Ko Assadiq ne ya nuna musu?
In kuma ba shi ba ne, na tabbata yau karya ta kare, sannan kuma muna cikin Tsaka mai wuya.

Surayya sai da ta gama ganin yanayin Firgicina sannan tace"Waye wannan a tare da ke? Wace alaqa ne a tsakanin ku? Mun ga Hoton a Duniya, mu kuma bamu san ke wacece ba, gudun yanke Tunanin da ba shi ne ba, sai na yi Tunanin na Bincika komai kafin mgana ta kai wajen manya."
Ta dakata ta na Sauke Numfashi ganin har na fara sharan hawaye.
Cikin kasa da Murya tace"Ni sunana Surayya kuma ni ce babba a gidanmu, ina daukan girman da Allah ya bani da Muhimmanci, Hasiya ki gayamin iya gaskiyan ki meke tsakanin ki da kaninmu Sadiq? Domin hankalina ya tashi da naga wannan Hoton ina Fatan kada tunanin da na ke yi ya zama gaskiya."
Bani da mafita sai na Fad'in gaskiyata, kuma na tabbata in ma na yi karya sai sun gane, tunda ga shi sun samu kyakyawan Hujja a garemu.
Kaina na kasa ina sharan kwallah zuciyata Tuni naji ta tsinke, na amince zan fad'i gaskiyata ammh kuma zan rokesu Kada su rabani da Assadiq a Lokacin da zuciyata bazata iya Daukan Rabuwa da shi ba.
Sajida cikin dakamim Tsawa tace"da ke fa ake mgana, malama kina bata mana Lokaci."
Kawai sai na fashe musu da kuka, Surayya ta daga ma Sajida Hannu cikin bacin rai tace"Sajida kada ki kara mgana na gaya miki."
Sai ta maida kallonta kaina cikin sigar lallashi tace"yi hakuri Hasiya,ki gayamin a ina kika san Sadiq?
Kaina na kasa nace"Na san shi, Mi. MIJINA ne shi."
Sajida ta Dafe kirji kafin tace"Mun shiga Uku miji kuma?.

Ita kuma Surayya ina jin Sauke Ajiyar zuciyarta kamar na samun salama.
Kafin tace"Har na tsawon wani lokaci kuke a matsayin ma'aurata?
Cikin kuka nace"An fi shekaru uku."
Surayya ta kalli Sajida itama ta kalleta cikin mamaki, a cikin Ran surayya sai da ta murmusa Sadiq Sadiq shegen gora ne.
Wato tun zamanin ya na Hidimar kasa kenan, ya yi aure batare da kowa ya sani ba, gaskiya ya na da karfin Hali.
Sajida kuma tsabar mamaki ma ya hanata mgana, ta bude baki yafi sau uku sai kuma ta Rufe domin ta kasa iya yin wata mgana.
Surayya ta mike hannayenta goye a bayanta ta tsaya a gabana ta na fadin"Menene shaidar da zai sa mu tabbatar da gaskiyan mganar ku ma'aurata ne ba zaman banza ku ke yi ba.?
Da Sauri na Dago ina kallonta kafin nace"Wlh ba zaman haramci mu ke yi ba, kowa a dangina yasan mun yi aure, kuma abokinsa ya sani sannan a gidan Baffan mu ma aka Daura mana aure."
Surayya tace"Tahir?
Sai na gyad'a mata kai, mirmishi ta yi daman tasan Tahir zai san komai Tunda ita dai bata san Sadiq da wani Amini  bayan Tahir ba, akwai tabbacin yasan komai daga Farko har karshe.
Sajida ta kad'a harshe kafin tace"Shi yanzu Tahir da had'in bakin shi aka ci Amanar mu ko?
Ba wansa ya tankata, ni ina ta kuka ita kuma Surayya ta na ta nazarin mganganuna.
Kai Tsaye tace"Cikin jikin ki na shi ne?
Sai na samu kaina da gyad'a mata kai, Shuru ta yi ta na kallona kafin ta koma ta zauna ta na fad'in"Me yasa kika amince kika auresa baki san Danginsa ba? Sannan kin zo gusai kenan hakan ya tabbatar min da cewa kin san ko mu su waye ko?
Ina jan majina nace"Sai daga baya na san ku, ammh shi bai taba gayamin ba  asalima yace shi maraya ne ba shi da kowa sai kakarsa."
Cikin mamaki Surayya tace"Bangane ba?
Haka kurum naji ina son na gayamusu komai Tundaga Farko, sai kawai na gyara zama na fara ba su Labarin waceceni tundaga Farko Har karshe ban boye komai ba, Aurarranki da na yi tare da aurena da Assadiq da duk abunda ya faru, har Inplant din da Assadiq ya sakamin sai da na fad'a musu.
Daga karshe na fad'i gaban Surayya na rike kafafunta ina kuka ina fad'in" Don girman Allah ku yi hakuri kada ku ce zaku rabani da Assadiq, in kuka rabamu ina zani? Baza mu iya rayuwa ba bu shi ba, da ni da abunda ke cikina."
Na karishe fad'a cikin gunjin kuka, kamar zan shid'e da alamu  jikin Surayya ya yi sanyi, a ranta ta na Tunanin dama har yanzu akwai masu banzan Tunanin Canfe canfe, daman akwai mutanen da ke fuskanta Tozarci akan abunda ba su da masaniya a kan haka.?

Ta kasa dago Hasiya, kamar wani shashe a ranta ya Tausayama Hasiya, sai kuma yanzu ta kara yarda da Dalilin Da yasa Sadiq ya aureta Tausayi ne da Taimako daga karshe kuma Allah ya rubuta da akwai Rabo da zama mai Tsawo a tsakaninsu.
Sajida kuma ido kawai ta ke zarewa cikin Firgici ta ijiye yarinyarta a gefe ta mike ta na fad'in"Ki ka ce auran ki na Biyu Sadiq ne na uku? Mun shiga uku mun Lalace Taurin kan yaron nan ya sa ya jawo mana Mugun iri acikin zuru'a? ammh uwarki dai itace batulu duk alherin da ya yi mata sai ta saka masa da Sharrin Bin Rayuwarsa? Ai tasan ke Annoba ce meyasa ta nace sai ya aure ki? Wannan wlh zalumci ne, in wani abu ya samu dan'uwan mu na rantse da Allah sai Abba ya karar da duka Ahalin ku, matsiyatan banza kawai da Wofi."

Ta fad'a cikin bacin rai, Surayya da ta daka mata tsawa cikin Fushi ta kira sunanta" Sajida."
Sajida cikin fusata tace"Big sis ke baki hango abunda na hango ba ne? Sadiq kadai garemu yanzu in wani abu ya sameshi ya zamu yi?

Kai Tsaye Surayya tace"Ba bu abunda zai same shi face abunda Allah ya tsara masa, da zai samesa da ya samesa Tuntuni, tunda ba yau suke tare ba, ki koma ki zauna ki kuma Rufemin bakin ki anan wajen"
Sajida ta koma ta zauna ta na fad'in"Bazawara! Bazawara Kai ina wannan Had'in kwata kwata bai yi ba, da sake wlh"
Ta fad'a ta na jin kamar ta Rufe Hasiya da duka, tsanar ta taji ta kara shiga ranta, daman tun jiya ta ke tsine mata tun kafim ma tasan abunda ke Tsakaninsu.
Ina duke gaban Surayya ina kuka bani da tacewa domin nasan irin wannan Ranar ta na zuwa.
Surayya ce ta saka Hannu ta Dagoni ta kuma mikar dani Tsaye ta zaunar dani saman kujera ta na fadin"Ki rage wannan kukan kin ga Halin da ki ke ciki ko?
Fuskata Hawaye shabe shabe da hawaye da majina na kalleta ina fadin"Bazaku rabani da Assadiq ba ko?
Sai kawai ta yi min mirmishi kafin tace"Bamu isa mu rabaki da mijin ki ba, tunda ai bamu muka had'a ku ba Allah ne, ki kwantar da Hankali in sha Allahu Alherinne zai Biyo baya."
Ban san Surayya Sosai ba  ammh kuma sai naji na aminta da mganarta.
Da tace na daina kuka sai na Daina na koma saka bayan Hannuna ina share hawaye.
Sai da na natsu sannan Surayya tace"Duk da ina Babba  bani da ikon yanke komai a rayuwar Sadiq ya na da magabatansa, zamu koma gida zan sanar ma iyayensa, so na ke Sadiq ya Fahimci Babban Kuskuren da ya yi, na yi aure ba da sanin iyayensa ba."
Sai ta d'an dakata ta na Kallona kafin tacigaba da fad'in"Hasiya ki kwantar da Hankalin ki, kema ba laifin ki ba ne ya zauna da ke da karya kamar yadda muma ya lullubemu cikin karya, ki yi min alfarma Rufe zuwan mu a matsayin sirri bazaki taba bari Sadiq ya sani ba kin ji ko?
Sai na gyad'a mata kafin nace"Bazan gaya masa ba, daman kuma ina ta ce masa ya sanar da ku game dani, sai yace yana jiran Lokaci ne, abunda na ke tsoro kenan ko da yaushe ina cikin Fargaba, ina tsoron kada daga baya ku zo ku sani ku ki karb'a na ni da Abunda ke Cikina."

" Ai ba zamu taba karb'an ki ba, Daga ke har shegen cikin jikin ki, da kike kokararin Dangantamu da shi, mu Sultana Kad'ai muka sani matar Dan'uwan mu, in dai ba ita bace ta haihu bazamu iya karb'an Datti acikin Zuru'armu ba."

Sajida ta fad'i haka cikin Tsanar Hasiya har ya na bayyana a saman fuskarta, sai na kasa kallonta Saboda yadda naji kuka ya tasomin sai kawai nace"Ku yi hakuri don Allah, kada abunda ke cikina ya fuskanci hukuncin da ba laifin sa ba ne."
Surayya ta balla ma Sajida Harara kafin tace"Wlh da na san abunda zaki yi kenan da ban zo da ke ba."
Jin haka yasa Sajida ta yi shuru, ammh ta na ta kunkuni ita kad'ai.
Surayya ta yi banza da ita, ta koma ta na kallona cikin sanyin murya tace"Kada ki damu Hasiya kin ji ko! Tunda har kun yi aure komai zai zo da sauki, ki rufe wannan mganar in muka koma gusai zan sanar da su Abba, kila akwai bukatar ki zo Gusai Domin tabbacin, zan baki lambar wayata in bukatar hakan yaa ta so Direban da ya kawomu zai zo ya Dauke ki kin ji ko?
Cikin Tsoro na kalleta kafin nace"Assadiq fa?
Surayya tace"Zai san komai Daga baya, kada ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login