Showing 39001 words to 42000 words out of 116366 words
kunya ce ta kamani,ina ta noke jikina ganin Assadiq yaki sakina.
Shi ko Surayya ya kallah kafin yace"To tunda zaku Rufe gida ko na kwana anan ne?
Ya fad'a ya na kallonta ita ko sai Faman balla masa harara ta ke yi, yar dariya ya yi kafin ya cigaba da fad'in"Tunda daman gobe zamu yi tafiya daganan sai mu wuce kawai."
Ko mgana batayi masa ba, sai shigowa dakin da ta yi, ni ko ina ta son kwace jikina ammh yaki sakina.
Surayya na zuwa ta duka ta Masa katon Dundu a gadon baya kafin tace"Tashi ka fita kafin na sab'a maka wlh"
Bayansa ya sosa Lokaci d'aya ya na fadin" Big sis."
Kara Dukansa ta yi, ganin haka sai ya bi ni ya kamkameni ya na dariya ni kuma sai na ke fad'in"Anty Surayya ki ce ya sakeni."
Surayya ta Rarumo Filo ta daga sama ta nuna Assadiq ta na fad'in"Sakarta ko yanzu na yi maka Rufdugu a saman kan ka."
Ganin yaki sakina yasa ta fara makamasa Filo ta na fadin ya sakeni sai da yaga dama ya Cikani ta kuma ja hannunsa ta fitar da shi daga dakin ina gani yana Dafa kafadarta ita kuma tana Turesa.
Sai naji sun Burgeni daga gani suna da kyakyawan Fahimta a tsakaninsu.
Ina ta jin hirarasu har na yi barci bansan Lokacin Tafiyar Assadiq ba.
Washegari tun Asuba Anty Surayya ta sakani na yi wanka na Shirya cikin Abaya na Maryam's Eyptian Abaya Tunda yanzu ne kayan sawa na.
Ko kafin takwas na safe na karya na sha Tea sannan na ci soyayyan Buredi.
Tunda tace Sadiq yace ta kaini chan gida da wuri tare muka fita da Mijinta ya kaimu ya sauke sannan ya wuce wajen aiki.
shima yana ta bani baki da nuna min na kwantar da Hankali ba wata matsala.
20k ya bani bayan Anty Surayya ta bani Ruguna bubu da yawa, ga kuma kayan kwalliya har da kayan jarirai Sabbi Overroll, ta kuma Tambayeni ko mun fara siyan kayan Haihuwa? Sai nace mata a'a, nan take tace zata yi ma Sadiq mganar ya kamata mu fara siya tunda Haihuwan ta kusa
Bangarem Umma muka fara sauka, Sabai ne da Saddiqa su Sadiya sun koma gidajensu tun jiya da Daddare.
Na duka har kasa na gaishe su Anty Saddiqa ce kad'ai ta amsa banda Anty Suba'atu.
Umma kuma har ciki Anty Surayya ta shigar dani na gaisheta, kallona ta yi kawai ta kauda kai bata amsa ba sai ma ta tashi ta shige Tiolet ta barmu nan zaune.
Anty Surayya bata damu ba ta Jani har bangaran Mama, in da su Salima duk suna nan suma dai kalilansu ne suka amsamin cikin sakewa kasa kasa suna karemin kallo.
Mama ce ta amsa cikin sakewar har tana ce min ya bakunta? Kaina na kasa nace lafiya.
Muna zaune Shahida ta kalli Surayya kafin tace"Ki ce gidanki ta ke da masauki kenan?
Surayya ta kalleta kafin tace"Ai ba ma ita ba, ni kinsan gidana masaukin baki ne, ballatana ita Asiya ai ba bakuwa bace yar gida ce Tunda matar Sadiq ne."
Sai gabadayansu suka wani tabe baki, mama da Sauri tace"Umma ta hakuran kenan?
Kai Tsaye surayya tace"Umma ai bata isa ta ja da abunda Allah ya tsara ba, ko bata Hakura ba, ba wanda ya isa ya tada wannan kaddaran na auran Sadiq da Asiya"
Duk sai ta kashe bakinsu, daga haka ta yi musu sallama muka fita bayan Salima ta tambayi Surayya tare dani za'a je zariyan? Tace musu Eh.
Daganan sai bangaren Innani chan mukaje muka tarar da Sultana da Siyama.
Har gaban Innani Surayya ta kaini na gaisheta ta amsa ta na kallon Surayya kafin tace"Ita wannan fa?
Ta fad'a a gatsine Surayya tace"Matar magajin gida ce Asiya."
Da Sauri innani ta washe baki kafin tace"Allah Sarki sannu yar nan, ki yi hakuri da abunda ya faru jiya duk sharrin shed'an ne, mu bamu ki karban ki ba ne, Daman saboda marainiyar nan ne Sulsana ba ta da kowa sai mu, kuma ni daman ban ja ba ina Ruwana da shiga Hurumin Allah. Ni dai yar nan rokona gareki ki rike magajin gida Amana kina dai gani bayan shi Sulaimanu ba shi da wani magaji sai shi, in ya rasashi bansan wani hali zai shiga ba, ni dai fatana kada wani abu ya samu magajin gida shine kawai damuwata."
Sai kuma ta saka kuka ta na wani gyara gilashinta kafin tayi kyafci ta na jan hanci tace"Ashe da rabon zan ga kwan magajin gida ina Raye? Allahu akbar yar nan Allah ya rabaku lafiya.'
Ta ke fad'a ta na jan majina, Surayya na gefe ta na mirmishi.
Sultana da tun shigowarmu ta maida kanta ta sunkuyar sai da ta dago ta na kallon Innani lalle ka tsoraci Duniya ka Tsaraci Innani, yanzu nan fa zagin Hasiyar ta gama yi ta na fadin sai magajin gida ya saketa ammh shine har ta sauya mgana.
Ni dai kaina na kasa, Innani ta na ta addu'a ina amsawa da Amin sai da wayar Surayya tayi kara ta fita waje sai gashi ta dawo ta na cemin na tashi mu tafi Sadiq yace sun shirya.
sallama na yi ma Innani ta amsa ta na Fad'in "Yanzu chan Zariya zaku tafi?
Sai na amsa mata da Eh da sauri tace"To Allah ya tsare haka sulaimanu yace min da ya shigo da safe ya gaisheni, Sulaimanu bawan Allah nan ya zauna yana ta min nasiha, tuni ni na Saduda daman Saboda Sulsana ce in naga ta na kukan nan duk sai na Rude na rasa bayan wa zan bi."
Sai kuma ta yi shuru kafin tace"Ni fa an sakani a Tsakiya magajin gida ma fushi ya ke yi dani Tun jiya ko shashen nan bai kara kallo ba, oh ni Dije in nabi bayan Sulsana ace na yi son kai, in nabi bayan wannan yar Farar sai ace na so bare naki nawa."
Ta ke fad'a kamar gaske ni kaina sai da ta bani Dariya.
Surayya tace"Bakomai Innani in kika so nakin kika had'a da baren kika so gabadaya baki yi laifi ba."
Da haka ta kashe bakin Innani muka fita tana mana fatan Allah ya kaimu lafiya.
Har ta na fadin"Yar nan sai yaushe?
Na kasa bata amsa Anty Surayya tace"Sai tazo gabanki, ai ke zaki karbi zuwan d'an magajin gida."
Innani sai kuka,ta na fadin Allah yasa tana raye zata gani har muka fita bata daina kuka ba.
Muna fita Siyama ta kalli Innani kafin ta yi mgana Sultana ta mike fuu ta shige uwar dakin Innani.
Daga innani har Siyama suka bi ta da kallo, Innani ta tce"Ita kuma wannan me aka yi mata?
Siyama tace"Ba ke bace, yanzu kina nuna kina goyon bayan mu, ammh kuma yanzu kina ganinta kika wani ware mana baya."
Innani ta saki baki kafin ta yi mgana Siyamar ta mike tabi bayan sultana su bacin ransu Yaya Sadiq baisan ma yazo ya Lallashi Sultanan ba.
Innani ta bi su da kallo kafin ta tabe baki tace"Kaji min tsiya, yaran da ba su san abun arziki ba, na yi mgana Sulaimani da magajin gida sun ce ina ja da Ubangiji ai dole nayi shuru da bakina."
********
Mun dauki hanya wajen goma saura na safe, Kamar kada mu rabu da Anty Surayya saboda kirkinta Abba ma ba ruwansa kafin ma na gaishesa shi ya fara gaisheni.
Sadiq ke tukin Abba na gidan gaba ni kuma ina baya, suna tafe sai hiran su suke yi gwanin sha'awa.
Abba ne ke juyawa yana sakoni a Hirar shi kuma Assadiq bini bini sai ya Waiwayoni yana tambayata ya ya? Saboda yaga ina ta mutsu mutsun Tunda Cikin nan ya fara nauyi zama ya ke min wahala.
Ina jin su suna waya da Tahir yace shima ya na kan hanya, sai bayan azahar muka isa Zariya tunda su Abba sun tsaya sun yi sallah Sadiq ya siyamin Tsire da Lemu ni ban ma ciba saboda zuciyata naji ta na tashi.
A samaru muka Dauki Tahir, na gaishesa ya amsa a dakile sai dai ya gaida Abba cikin Fara'a.
Ni na rika numa musu hanyar gidan Baba Tanko har muka iso.
Naga motarsa ma a waje yasa nace musu yana gida, sai Abba yace na shiga nace suna jiransa.
Ina shiga gidan da sallama da duka matansa naci karo suma sun yi mamakin ganina.
Muka gaisa kai tsaye nace"Baba na gida?
Sukace min eh yana gida sai nace a waje ana jiransa nazo tare da baki.
Amaryar ce ta shiga dakinsa ta gayamasa ina tsaye ko wurin zama ba su bani ba sai dai naga sai kallona suke yi kamar sun ga bakuwar Fuska.
Baba Tanko ya fito yana saka Hula Cikin mamakin ganina yace"Hasiya? Ko ba Hasiya bace?
Kai Tsaye nace'Ni ce Baba, ina yini?
Bai amsa ba illah ce min da ya yi"Lafiya? Wasu baki ne ke nemana?
Nima kai Tsayen nace"Mijina ne da mahaifinsa."
Ido ya waro kafin yace"Wai daman auran naki bai mutu ba?
Sai da kuma ya fad'a yaga cikin jikina sai ya yi gaba yana fad'in"To to bari naje na gani."
Na bisa da kallo ina jin wani abu na sukan raina, gajiya na yi da Tsayuwa har sai da na jingina.
Ganin haka ne yasa Amaryan baba ta bani kujeren tsugunno na zauna ina jin bayana sun kara kagewa.
Achan waje kuwa Baba Tanko na fita wazai gani? Sai yaga Alhaji Sulaiman Shinkafi Surukin Alhaji Jibril.
Ya bashi hannu suka ka gaisa lokaci d'aya yana fadin"Ah wa na ke gani kamar Alhaji Sulaiman?
Abba ya yi mirmishi kafin yace"Ni ne, kamar yan'uwan Alhaji Jibril na Zariya ko?
Baba Tanko jiki na rawa yace"Ba Shakka baka manta ba?
Ya fad'a ya na kallon su Sadiq wanda ke sanye da Shadda Deep Blue da Hula Tahir ma manyan kayane ajikinsu nan take ya gane su.
Cikin mamaki ya kalli Abba yana fadin"kada dai kace min wannan d'an ka ne?
Abba ya kalli Sadiq kafin ya yi mirmishi yace"Eh yaron wajena ne."
Baba Tanko sai ya kasa mgana, jiki na rawa ya Bude musu falonsa na waje suka shiga.
Bayan sun gaisa sai gashi ya Dawo cikin gida yana rawan baki a kawo Ruwa ya kalleni zaune ya na fadin"Ke ashe mijin naki surukin Baban ki Jibril ne? Gidansa ai Mubarak ya Dauko mata."
Ina jinsa bance masa komai ba matansa ne ke ta mamaki, suna ta neman jin mgana a bakina na yi musu gum.
Abba ne kadai ya sha ruwa ban da su Sadiq bayan an kara gaisawwa Abba ya kalli Baba Tanko Lokaci daya ya na nuna su Sadiq kafin yace"Ina fatan ka gane su ko?
Baba Tanko yace"Tabbas na gane su shekaru uku haka nan suka zo na Daura masa aure da Daya daga cikin ya'yan dan'uwana da ya rasu cikin Shedu masu yawa"
Abba ya jinjina kai kafin yace"Daman tabbacin hakane na ke so na samu, Saboda alokacin da ya yi auran bai sanar dani ba sai daga baya."
Baba Tanko ya rike baki kafin yace"Kaji ko? Daman sai da na tambayesa, domin nasan da sanin ku dai bazaku bari ya auri bakar tsiya ya kawo muku cikin zuru'a ba"
Abba ya yi mirmishi bai yi mgana ba sai kawai Baba Tanko ya gyara zama yana ba ma su Abba labarin irin bakin tsiyar Hasiya da maganar cewa ita ta yi sanadiyar mutuwar dan'uwansu bayan ya rasa komai.
Tahir ya kalli Sadiq alamun kadai ji ko?shi kuma sai ya yi kamar bai gani ba.
Abba ne ya dakatar da Baba Tanko da cewa za su tafi, 10k ya ijiye masa a gabansa sannan ya mike.
Har waje ya rakosu kamar ya yi musu Sujjada, Sadiq ne yace a kira ni mu tafi sai gashi ya shigo zakada zakadan yana fadin na taso suna jirana.
Na yi ma matansu sallama na fito sai gashi yau nice Baba tanko ke sakama albarka Harda Allah ya Saukeni lafiya.
Daganan har gida suka kaini, Sadiq kunyar tasa bai shiga ba sai da Abba yace ya taikamamin da jakata mana.
Sannan ya fito daga Motar
Ni kuma sai na Roke Abba ya shigo yaga dakina ko ruwa ya sha.
Abba bai yi gaddama ba ya Bude mota ya fito kuma yace Tahir yazo shima ya shiga.
Sai ga Abba da Tahir a falona jikina na rawa naje na kawo musu Ruwa, Abba ya sha shi da Sadiq Tahir kuma yace shi baya jin kishi.
Abba ya saka albarka ba jimawa yace bari su kama hanya tare da Tahir suka fita Assadiq kuma sai da ya Tsaya ya Rumgumeni ya sumbaceni.
Sannan yace na kula da kaina zamu yi waya.
Nice har waje na rakasu sai da naga Fitar motarsu layin sannan na dawo cikin gida Maman suhailat nagani Bakina na rawa nace mata Baban Assadiq ne da abokinsa suka kawoni gida.
Sai ta faramin fad'a ashe ba na garin ammh shine ban ce zan yi tafiya ba kamar ana zaman gaba.
Sai na fahimci laifina na kuma bata Hakuri.
Ranar na kwana cikin Farimciki ko bakomai abubuwa suna Faruwa A yadda ban yi Tunani ko tsammani ba.
Sai dare muka yi mgana da Assadiq yace sun sauka lafiya shima gobe zai koma Abuja Saboda aiki.
Anty Surayya ma ta kirani ta na min bangajiya.
Ranar na yi barci harda makara, wayar Safiya ce ta tadani ma, ta na gayamin an kafa mana Time table zamu fara jarabawar Secomd Semister shine ta ke cemin ta Turamin na duba nagani.
Tashi na kenan ruwan zafi kawai na Dafa nasha Tea sai ga Ramatu tazo.
Naji dadin zuwanta ita ta yi min share share ta dafa mana abincin rana.
Sai bayan mun zauna mun natsa ne na bata Labarin duk abunda ya Faru har na zuwana Gusai da dawowar da su Abba suka yi dani jiya.
Ramatu ta jinjina kai kafin tace"Ni fa daman na yi ta tunanin Mijin ki yafi karfin inda ya saka kanshi, kuma har Nura ya tabamin maganar jikinsa bai nuna Daga kauye ya ke ba."
Cikin gyad'a kai nace"Ni ina na Fahimta na Dauka, duk abunda ya Fadamin gaskiya ne. Sannan bai taba nuna min abunda zan gane wani abu ba"
Ramatu tace"Ammh gaskiya na yi mamaki, sai fa kin yi hakuri kin kuma Dage da addu'a domin kinsan in mata suka yi yawa a gida sai a hankali, fatana dai Allah yasa maman nasa ta yarda ta karbeki."
Na amsa mata da Ameen ina bata Labarin yadda Assadiq ya tsayamin a gaban yan'uwantsa
Ramatu tace"Kaji namijin gaskiya da gaske ya ke yi yana sonki Hasiya."
Ta dade sai la'asar ta tafi bayan mun sha Hira ta yi ta bani Shawaran na kwantar da Hankalina kada na saka Damuwa araina.
Tazo a jiya washegari yau Adda Fati tazo itama yadda na gayama Ramatun haka na maida mata.
Ita kam ta na ta jinjina abun har da zuwan mu gidan Baba Tanko ina fad'amata yadda Baba Tanko ya yi min.
Cikin yar dariya tace"Bai taba Tunanin zaki samu miji kamarsa ba ne, lalle wani aikin sai Ubangiji. allah ya huci zuciyar maman tasa ya Daidaita tsakanin ku gabadaya."
Itama Addu'an tace na Cigaba da yi, kuma tace na kira Amma na yi mganar da ita.
Haka ko akayi a daran na kira Amma na gayamata komai.
Mirmishi kawai ta yi kafin tace"Allah ya kauda Fitina Hasiya, ammh in sha Allahu ina ji ajikina Asssadiq ne mijinki har mutuwarki."
Acikin raina sai na samu kaina da amsawa da Ameen Ameen.
Itama dai tace min na yi addu'a sannan kada na shiga damuwa Saboda abunda ke tare dani.
Haka na cigaba da kula da kaina Gefe daya Assadiq na kula dani Tunda koda yauahe muna tare a waya.
Tuni mun fara jarabawa hakanan na dage da karatu ba wasa tunda muna gama Jarabawar Nce3 first Semister zamu tafi Tp ne, ina ta Tunanin yadda zan yi Tunda a lissafina na haihu a lokacin.
Anty Surayya ma ta na kira na muna gaisawa, Har Saliha ta kirani mun jima muna mgana da ita, itama ba ta nuna min kyama na ta kuma saka ma lamarin albarka.
Ban kuma karajin yadda suka kare ba, ko shi bai yi min mganar ba.
Ballatana nasan matsayan Umma da kuma ita kanta Sultana.
Shiyasa nima sai ban yi masa mgana ba abunda ba'a so kaji gwara ka yi shuru da bakin ka kada ka zake kuma da yawa."
********
Baba Tanko da kansa ya kira Alhaji Jibril yana fad'a masa zuwan Alhaji Sulaimam da mganar auren d'ansa da Hasiya.
Ya ji mamaki kai Tsaye ya kira Abba yana tambayansa ko gaskiya ne abunda yaji ?shi kuma yace masa hakane.
Har Abba ya na masa Tsiyan cewa sun had'a zumunci ta bangare biyu.
Alhaji Jibril cikin bakin ciki yace"Alhaji ka kosan labarin yarinyar nan? Ko baka san cewa ta na da bakin jini a tare da ita ba, duk wanda ya aureta ko mutuwa ko rasa lafiya ko Dukiya."
Abba ya yi mirmishi kafin yace"Duk na san da wannan."
Alhaji jibril yacce cikin mamaki"Kuma ka amince da auran Danka da ita?
In wani abu ya same shi fa? Ga shi shi kad'ai gareka namiji."
Abba ya kateshi da Fadin"Babu abunda zai Faru face abunda Allah ya Rubuta mana, kada wannan ya Dameka Alhaji."
Da haka ya kashe bakinsa har suka gama wayarsu Alhaji Jibril ba shi da wata fara'a a yanayinsa.
Har Mubarak sai da ya Turke yana Tambayansa yace shi bai sani ba Salima bata gayamasa ba, yasan dai taje kaduna Saboda ya kara samun Tabbaci yace Mubark yazo da salima gidan.
Bayan sun zo ya zaunar da ita yana mata Bin diggi, ita kuma ta fayyace masa duk abunda ya faru, har ta fadin"Babu wanda ya yarda da auran nan Daddy, Umma ma tace sai ya zaba ko sultana ko ita wannan Asiyar"
Alhaji Jibril yace"Uhm Ina tsoron abun da zai Faru da Abubakar ne."
Shi har acikin ransa bai yarda da babu Canfi ba
Billhaki da gaskiya shi yana Tsoron kada wani abu ya faru da Abubakar Alhaji yazo sanadin abun ya rusa shi.
Shi ai da ya shiga uku domin ya fara hango ma kansa abunda ya Dad'e yana Buri.
*Janafty*
*TMWB3K09*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IhAz8h8nRy250ZnGGXwM65
Muna cikin jarabawa aka shiga watan azumin Ramadana, ni dai ina ta lallaba Rayuwata tunda yanzu na riga na zama kaya, ina matukar shan wahala na jeka ka dawo saboda makaranta Allah yasa ma ba kullum na ke gwada azumin ba, na fi yi in ina gida shima ba kullum ba, kuma a boye in Assadiq yaji sai ya kama min Fad'an nasan halin da ni ke ciki sai kuma na matsama kaina?
Alhalin Addini ya riga ya saukaka mana.
Assadiq har cewa ya yi ko na hakura da Jarabawar bayan na haihu jariri ya yi kwari sai na koma daga baya sai na