Showing 54001 words to 57000 words out of 116366 words

Chapter 19 - Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

323

ni sun kwace wayata ballatana na samu lambar Anty Surayya na kirata naji wani Hali yake ciki, a koda yaushe ba na iya barci balle ma Tunda cikina ya tsufa ban cika samun  barci ballatana ni da na ke cikin Damuwa da halin kakani k'ani.
Ko alama ban yarda na bari Amma ta Fahimci wani abu ba, ina son uwata shiyasa ba na fatan ni nayi sanadiyar gayamata abunda zai kara Ruguzata shiyasa na yi shuru da bakina sai dai ina ta addu'an a duk inda Assadiq ya ke Allah ya bashi lafiya ya tada kafad'unsa ni ma kuma Allah ya sauke ni lafiya cikin ikonsa da kudurarsa.

********

Assadiq ya dawo hayyacinsa tun kwana hu'du da faruwar Lamarin, kuma Alhamdulillah an yi Daurin kuma ga dukkam alamu akwai alamun nasara a aikin.
Kuma ba shi da kyamar jiki, da sauri Cuwukan jikinsa suka dauko hanyar warkewa har kumburin kansa ya ragu sai abunda ba'a rasa ba.
Abba ya koma gida sai dai yana zuwa ganin Assadiq bayan kwana daya ko Biyu Auwalu ne yaron Baba Saminu ke tare da Assadiq a asibitin sai Tahir da kan zo shima Lokaci bayan Lokaci.
Hidimar su kuma gabadaya ta na kan Alhaji Jibril ne, Salima kuma ke kawo  abincin safe da yamma da rana ne in tana makaranta Hajiya Murjanatu ke bama direba ya kawo musu anan cikin asibitin.
Kaf yan'uwansa mata ba wacce bata zo ta gansa ba, kuma ganin har ya dawo hayyacinsa yasa wad'anda ba yan garin ba suka koma gidajensu da wuri sai dai kullum suna cikin kiran wayar Auwalu domim tambayar lafiya dan'uwansa Tunda shi ba waya a hannunsa.

Innani dai sau d'aya Abba ya sake Dawowa da ita ta gansa  ganinsa ido Biyu har suna mgana yasa hamkalinta ya kwanta ta daina damun mutane da kuka achan gida, Umma ma kamar ba ita ba, duk sai ta rame Abunda ya faru da Sadiq ya dimauta ta matuka, sai dai zukata sun kwanta tunda suna ganin Sauki sosai sai Hamdala.
Baki yan'uwa da mutanen arziki sun ta tururuwan zuwa kaduna Duba jikin Assadiq kaf mutanen shinkafi har da makota sai da suka zo kaduna Duba Assadiq daga gusai ma yan uwan Mama da mazajen yan'uwansa mata tare da Dangin Umma daga Gummi suma mota guda suka zo duba jikin nasa, kowa kuma ya koma da salama ganin har mgana Sadiq din nayi sannan yana gane wanda ke tare dashi.

Har Hajja kakar Tahir sai da tazo ta Dubashi tare suka zo da Tahir sai yayansa Kasim, nan suka barshi ya kwana su kuma suka koma aranar, Sultana ma wajen sau uku ta zo ta dubashi itama sun fara Jarabawar Neco shiyasa Abba yace ta zauna a gida ta natsu kan jarabawarta.
Da Farko nan aka so a barta wajen Salima tunda mijinta ne ranar da Sadiq ya farfado yaji labari yace ta koma gida shi baya bukatar ta.
Shikenan ta shiga damuwa tana ganin kamar ko tun abunda ya faru ne bai manta ba, shi kuma gani ya yi ina ita ina Jinyarsa ta na mace sannan shi bayason rashin kunya tunda kuma ya lura shi ta koya yanzu.
Har abokansu Jb da Mb sun zo sun Dubashi suka yini kafin su tafi shi dai Shuru kawai ya ke yi baya mgana yana kwance kafafunsa sagale a sama hannanunsa ma yana Sagale sai inda aka juyasa ko wanka ba'a yi masa sai dai ana goge masa jiki bayan kowani kwanaki Biyu.
Yaga kowa ammh bai ga Siya ba, tun washegarin ranar da ya Farfad'o sai da ya yi ma Big sis mganar ina Siya? Saboda lokacin da ya ke kwance yana fama da kansa ita kawai ya ke tunawa har Mafarkin ta haihu ya yi, saboda sanin Halin data ke ciki.
Ita kuma Surayya ta yi ta kiran wayar Hasiya a kashe, kuma ta yi hausan karisawa zariya ta duba ta bai zo mata ba sai da Sadiq ya yi tambayar, tunanin haka ya zo mata alokacin sai aka yi baki abokan Alhaji Jibril tare da su Abba suka shigo tunda ita ta na yawan zuwa duba Sadiq din.
Fitan ta yasa tace ma Auwalu bari taje ta dawo  daga nan ta hau motar Zariya sai gidan Hasiya.
Sai dai Labarin da taje ta iske ya tada mata Hankali bata tab'a tunanin Umma zata iya sa su sajida su zo su aikata irin wannan aikin ba.
Maman suhailat ta samu, abunda yasa ma ta gayamata cewar da tayi ita yayar mijin Hasiya ce, shine Dalilin da yasa Maman suhailat ta kai ta dakinta ta zayyana mata komai.
Da Surayya ta tambayeta yanzu Hasiyar ta na ina? Maman suhailat tace washegarin tafiyata taje gidan yayata ta iske mijinta shi ya gayamata yayar mahaifiyarmu ta rasu mun tafi can garin inda mahaifiyar mu ke zaune.
Kuma yace mata sai bayan an yi kwana bakwai zamu dawo, Hankalin Surayya ya gama tashi ta rasa wata amsa kuma zata baiwa Sadiq in ya kara tambayata Hasiya? Ba ta baro gidan ba sai da ta Rubuta ma maman suhailat lambarta tace da zarar taji Labarin dawowarmu ta kirata ta sanar da ita.
Sai da surayya ta fito zata tafi ne Maman suhailat ta Biyo ta tana tambayata  jikin Abubakar din? Ita kuma tace mata yana ta samun sauki sai hamdala.
Surayya ta koma asibiti cikin Tsananin Damuwa, Allah yasa lokacin da zata yi ma Sadiq sallama su Abba na wajen tare da shi ma za su koma Shiyasa ta samu ta sulale a lokacin har suka isa Gusau ta na mamakin abunda ta aikata ashe kenan Fad'an da akace mallam ya zo ya yi mata bata ji ba tunda tasa a yi ma Hasiya wannan Tozarcin.
Kuma ta yi alkwarin ko a Fuska bazata nuna musu tasan abunda suka aikata ba zata bisu a haka ita damuwar d'aya Sadiq.
Shi kawai take Tunanin hanyar da zata sama masa mafitan da bazai san me ya ke faruwa ba.
Ta kara komawa ganinsa a lokacin ne da ya kara tambayarta ta yi masa karyan ai tazo ta gansa lokacin yana barci saboda nauyin jikinta yasa Abba yace tayi zamanta a gida.
Kallonta kawai ya yi tunda bai cika mgana ba Sosai ammh ta san bai yarda da ita ba, saboda tsaro yasa har Auwalu ta shiryama ko Sadiq ya Tambayesa Wata siya tazo? Yace eh tazo yana barci har Tahir ta gayamawa.
Tahir yace"To tazo din ne? Nima fa ya yi ta tambayana nace ban sani ba."
Surayya sai ta kasa mgana, kawai dai tace su gayamasa tazo ma wajen sau biyu yana barci saboda nauyin jikinta yasa Abba yace ta yi zamanta a gida.
Kamar ta sani dukkansu sai da ya tambayesu suka gayamasa yadda Surayya ta gayamusu.

Tun daganan yasan akwai wani abu, ta yaya yaga kowa sai itace bai gani ba sai ace wai tazo yana barci kaji mganar da Hankali bazai Dauka ba.
A jikinsa yasan akwai abunda ya kamata ya sani bai sani ba, shi damuwarsa d'aya tsohon ciki gareta babu wanda ke tare da ita balle ya taimaketa kuma ba ta da kowa sai shi, hankalinsa ya kan kwanta in ya Tuna tana da yan'uwa a Zariya yasan baza su barta ita kadai ba sai dai kulawarsa ne a matsayinsa na Uban cikin bazata samu ba.
Sai ya rage mgana kwata kwata daga sannu ya jiki shikenan ko Tahir sai ya yini mganarsu bata wuce goma ba.
Kuma abunda ya Fahimta shine ba mai yi masa mganar siya, sannan zuwan Innani ta gayamassa wani kalma in da tace wai bala'i da Annoba ya sauka a gidansa jinin wannan yarinya ba alheri ba ne.
A lokacin bai damu da mganarta ba sai yanzu ya ke auna mgamganunta.
A ransa yasan daman haka zai faru suna zargin duk abunda ya faru da shi Siya itace sila, kuma yana da tabbacin wani abu ya faru wanda ba'a so ya sani to bazai matsa ma kansa sai ya sani ba ammh in ya samu kansa shi zai mike yaje ya gannin ma idanuwansa komai sannan yaji duk abunda ya faru.
Shiyasa ya yi bakam bai kara yi ma kowa mganar Siya ba hankalin Surayya sai ya kwanta a tunaninta in ya samu lafiya sai ta gayamasa ita kuma Umma ta samu natsuwa Tunaninta ya ma manta da ita tunda bata ya yi mganarta ba, ta manta fa matarsa ce dauke da ciki ta ya ya zai manta da ita sai kace wanda ya samu makuwa?
Haka Sadiq ya cigaba da jinya a asibiti har daga ma'aikatansu daga Abuja sun zo dubashi, kuma sun ji dadin ganinsa har yana samun sauki.
Yana da wata d'aya a asibitin aka duba Dorin kuma Alhandulillah duka sun yi kyau, sai aka fara bashi Sanduna guda biyu yana tafiya da su a haraban asibitin Saboda warware kasusuwansa da suka gaji da kwanciya sannan Tuni Rauninka sun fara baki sun dauko warkewa.
Kansa ma an cire bandage ya sabe kumburin gabadaya.

Hannunsa kuma sai dai aka sakamai jakar sagala hannu aciki, kullum yana sanye da gajerun wando saboda Kafarsa, kuma Alhamdulillah kowa yazo yaga Sadiq sai yace ba shi da kyamar jiki ganin cikin Lokaci har ya fara tafiya da taimakon sandunan asibiti. Kuma su kansu likitocin sun ce sun yi mamakin saurin mikewarsa suka yi musu albishir di'n Cewa bazai jima za su sallameshi ya koma gida ya cigaba da kula da kansa.

Auwalu ke Daukan Hotonsa yana Turama yan'uwansa mata suna gani suna jin dadi, Sultana kuma koda yaushe cikin kira waya ta ke yi, in aka basa daga gaisuwa da tambayan ya jiki shikenan ya ke yi mata shuru itama sai ta rasa me zata ce ganin yadda ya yi mata gim da shi, har Umma ta gayamawa ita kuma tace ta yi masa uzuri saboda halin ciwo, ita kuma tana son shi, shiyasa har aranta taji ta tsani Hasiya umma kuma ta bata tabbacin da ita kad'ai Sadiq zai cigaba da zama a matsayin matarsa.
Hatsarin nan da Sadiq ya yi sai ya rage magana kamar ba shi ba, ya koma wani shuru shuru mgana sai in ta zama dole.
Fatansa kawai ya samu saukin da zai iya tafiya yaje ya duba Siya yaga Halin da ta ke ciki, in ya lissafa dai dai cikinta ya fita wata na tara ya shiga goma kuma yasan Edd dinta tun 19 ga watan jiya ne.
Ga shi ba waya a hannunsa da ya yi mganar wayarsa sai aka gayamasa ta lalace ta fashe a had'arin da ya yi, tare da motarsa da bazata gyaru ba saboda yadda in jin Motar ya tashi aiki Abba yace a saidata kawai tunda bazata gyaru ba.
Shi dai bashi da tacewa sai shuru, tunda ana ganin yana kwance ba shi da lafiya in ya matsa da mgana sai kuma ace shi da ba shi da lafiya.
Ammh ya shirya yin abunda rai bazai so ba, matukar ya warke yaga abunda bashi ne ba.
Jinya dai ta yi tsawo kad'an ba da yawa ba, tunda har kusan wata Biyu Sadiq yana asibiti sannan aka sallameshi lokacin yana da wajen kwana sittin da wani abu a gadon asibiti yana jinya.
Direct daga nan sai Gusau gida aka wuce da shi, a kuma bangarensa yace a kaisa tunda Abba ya basa zabin cewa ko gidansa za'a wuce da shi yace a'a a wuce dashi gida.
Kafar ne kawai ta rage hannu kuma ya warke shima sai kad'an da ba'a rasa ba kuma an cire masa wannan Jakar kafar ne ya ke tafiya da taimakon sanda har a lokacin.
Dayake tun a asibitin ana yi masa aski, da ya dawo gida wanka kawai ya yi, sai kuma aske gashi nan da suka taru a jikinsa har kuma Lokacin Auwalu na tare da shi duk Sadiq din yace ya koma gida zai iya kula da kansa ammh yaki yace yana tare dashi har sai ya warke gabadaya.

Umma tafi kowa Farinciki da dawowar Sadiq gida ya ji sauki gida haka ya ke cika da yan'uwansa duk kuma a bangarensa ake zama Har Innani ta koma yini a bangarensa.
Shi dai baya mgana Sosai sai dai ya bisu da ido kawai kuma sai ma da ya dawo gida ya kara tabbatar da zarginsa.
Siya suka dorama alhakin duk abunda ya sameshi.
Abba ne ma daya dawo hayyacinsa a kwanakin baya ya yi ma Surayya mganar Hasiya ita kuma ba kwana kwana ta sanar da shi abunda Umma ta aikata da taimakon ya'yanta.
Abba ya shiga tashin hankali yace maza maza ta sake komawa Zariya ta tabbatar ta samu Hasiya domin taga Halin da ta ke ciki.
Ita kuma a ranar data shirya zata koma Zariya uwar mijinta ta rasu ba Halin tafiya kuma sai abun ya shafe a ranta gabadaya.
Shi Uban gayyar bai manta ba sai da ya yi kwana hud'u da dawowa gida sannan Tahir ya zo dubashi, kuma akaci sa'a Tahir yazo da mota kirar Camry, Motar uban gidansa ba ya kasar shine ya ke zirga zirgan shi da ita.
Yana zuwa Sadiq yace zai kai sa wani waje a motar don Allah, shi a tunanin Tahir nan kusa ne shiyasa bai ce a'a ba, Sadiq ya shirya cikin riga da wando na wani farin yadi, sai ya nannad'e kasan wando, saboda Kafarsa ta dama kuma Tahir yaga harda Hula ya saka baki sake yace"Wai ina zaka je ne?
Kai Tsaye Sadiq yace"Kai dai muje zaka ganin ma idanuwan ka"
Ba musu Tahir ya tashi suka tafi, kuma abunda Sadiq ya shirya ba wanda yasan ya fita ya riga ya gayama Auwalu duk wanda yazo dubashi yace yana ciki ya kwanta Malam Taju megadi Sadiq ya fad'a masa ko Abba kada yasan ya fita.
Sai da suka dauki hanya ne Tahir yace ina zamu je?
Sadiq yace"Zariya."
Tahir ya saki baki kafin yace"Ka yi me a Zariyan?
Kai Tsaye Sadiq yace"In yi me kuma? Ai kasan dai ina da wata matar acan."
Tahir sai ya kasa mgana duk da Big sis bata gayamasa komai ba ammh yasan akwai matsala kuma dai maganar gaskiya shi bai ganta ba, a ransa yace to Allah yasa ba rasuwa ta yi wajen haihuwa ba sai yaji a ransa yana fata da addu'an komai lafiya saboda yasan yadda Sadiq ke girmama waannan zabiyar matar tashi.

Sai ga su a Zariya har kofar gidan da Hasiya ke zaune cikin kuma sa'a suka ga Maman suhailat a waje an kawo mata sakon kaya daga kano.
Tana ganin Sadiq ta iso wajensu bakinta har kunne ta na Fad'in"Barka da arziki Abubakar Allah sarki daman nace in dai kana raye zaka tako kafarka wajen Hasiya."
Mirmishi kawai ya yi mata sai barka da arziki ta ke yi masa ganinsa da Sanda har tana kwallah.
Tun kafin ma ya yi mganar Hasiya maman suhailt na sharan kwallah ta kwashe duk abunda ya faru ta gayamasaa.
Cikin tashin hankali yace"Yanzu ina Siya ta ke?
Maman suhailat tace"Ta na gidan yayarta din nan fati, ba ta ma jima da dawowa ba da farko ta na wajen mahaifiyar tasu ne kasan yayar mahaifiyar ta su ce ta rasu kwanakin baya."
Har tana gayamai itama daga baya ta koma sai ta samu Hasiyar ta dawo nan cikin Tausayi tace"Abunda zai baka sha'awa da yarinyar nan duk abunda ya faru bata gayama yan'uwanta komai ba, cewa ta yi kayi tafiya baka gari ita kad'ai ce ta kunshi wannan bakincikin baiwar Allah.
Ai Sadiq bai gama sauraranta ba ya fad'a mota saboda bacin rai baya ma gani sosai.
Huci kawai ya ke yi, Tahir ma ya shiga ya tada motar Sadiq na nuna masa hanyar gidan, Tahir ganin yadda Sadiq ke huci yasa ya kallesa yana fad'in"Ka bi a sannu Sadiq ka san dai baka da lafiya ko?
Sadiq kamar ya yi kuka yace"Tahir wannan wani irin tozarci ne? Ni ne basa son ganin farincikina ai shikenan dama a hatsarin da na yi mutuwa na yi da kowa sai ya duka ya Dauka."
Da Sauri Tahir yace"Subhanallah kada Bacin rai yasa ka yi Sabo mana."
Sadiq bacin ransa da Maman Suhailat tace har Surayya ta zo kuma ta gayamata ammh shine ta yi masa karya.
Ba dad'ewa sai ga su a kofar gidan Adda Fati Tahir ne ya buga sallama shi kuma Sadiq na gefe rike da sanduna zuciyarsa na faman Bugawa.
Mijin Adda Fati ne ya fito ganin Mijin Hasiya yasa ya fito da sauri sun gaisa sama sama shi da tambayan garin yaya ya samu rauni a bakinsa shima Sadiq a bakinsa da tambayar ina Hasiya?
Mijin Adda Fati ya yi ajiyar rai kafin yace"Suna asibiti da Hasiyar tun safe ta fara zubar da jini, ammh yanzu Yayarta ta kirani tace C.s Za su yi mata yanzu nan."
Sadiq ya ji kamar ya zura a guje saboda Tashin hankali cikin Sauri da rawan baki yace"Wani asibiti ne?
Yace"Kamar inda ta ke awo tace na manta  sunan asibitin."
Sadiq ya juya da sauri yana ce ma tahir yasan asibitin su tafi kawai.
Sai mijin Adda Fati yace shima daman can zai je, kawai sai suka rankaya gabadaya.

Suna tafe Habibu mijin Adda na basu Labarin irin wahalar da Hasiya ta sha, tafi sati daya ta na nakudar tsaye sai yau da safe ne ta fara zubar da jini yasa suka tafi asibiti da Sauri ashe ma haihuwar ta ki Sai an yi mata aiki.
Asibitin musulmi ne, suna zuwa Habibu ya kira Adda Fati sai gashi ta fito Yarkace yarkace fuska duk ta kod'e Saboda kuka da Damuwa.

Itama sai da ta bude baki ganin Sadiq cikin damuwa tace"Abubakar ashe ka dawo? Subhanallah ba dai a wajen aikin ne ka samu raunika haka ba?
Sai ya ma kasa yi mata mgana yana jin wani abu na shiga ransa.
Ya kalli Tahir shima ya kallesa karshe dai Tahir aka bari da fadin"Eh a can ne ya samu d'an hatsari kad'an".
Ta bishi da Allah ya kara lafiya suna tafe ta na fad'amai daman saka hannun mijinta ake jira ko na wani makusancinta zasu shiga da ita tiyata sun ce yan Biyu ne acikinta.
Akwai bukatar gaggawa ceto Rayuwarta da na abunda ke Cikinta.
Shiyasa bata lokaci suna zuwa Adda Fati tace ga mijinta nan Sadiq ya Rattafa hannu aka shiga da Hasiya Tiyata, Sannan kudin Tiyatar ma shi ya Biya bai zo da ko Atm dinsa ba tunda shi babu komai ma a hannunsa Tahir ya ara masa kudin hannunsa ya Biya da shi.
Tare suka yi zaman jugum jugum a asibitin nan shi da Tahir da Adda Fati tare da Adda Rukayya, sai Habiba da Ramatu mijin Adda Fati Shi kuma ya tafi daga baya, sannan Safiya tazo daga baya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login