Showing 84001 words to 87000 words out of 116366 words

Chapter 29 - Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

329

Rana tunda yanzu jikin Innani ya fara saki tafiya ma dakyar ta ke yi ko da Sandar bata cika ma yawan fitowa ba. Jikin tsufa sannan ga Shekaru shiyasa yau lafiya gobe Ciwo ga shi bata san asibiti sai dai Likita Abba ya Dauka ya na zuwa gida ya na Dubata.
Yanzu duk hiran Innani ba shi, sai dai ranar da taji jikinta da karfi zata saka akawo mata su Asim ta Biye musu su yi ta wassani, nima muna zence da ita Sosai yanayinta kad'ai in ka kallah zaka san Innani shekaru sun yi nisa duk da bata cikin wahala ammh jikinta ya fara saki na alamun shekaru ya fara tafiya.

Kuma ni in dai yana gari iyakata da shi mu gaisa shine ma ya yi ta kirana a waya yana son ganina kuma nasan Dalili saboda kada ma ya Rutsani a daki yasa ban cika zama a daki ba, in ba Falon Umma ba ina bangaren Innani Tare da Farida ina tayata kula da Innani da ta zama sai dai a lallab'a yanzu.
Sau d'aya ya tab'a min Magiya na bishi muka je Hotel muka kad'aice da sunan mun je gidan matar abokinsa kuma Tunda muka dawo naga kamar Umma ta Fahimci abunda ya Faru ban kara yarda na bisa ba.
Tunda dai ni kaina ban taba jin Labarin a garin gusau yana da wani aboki ba, d'aya na sani shine Tahir kowama shi ya sani.
Ko ya yi min magiya ba na Biye masa zuwansa na karshe har cewa ya yi na koma gidansa na zauna tare da Sultana kafin na koma zariya.
Ba halina ba ne yi masa gaddama ammh na tuna yadda na wulakanta ne a baya da ya kai ni Shiyasa da Sauri nace masa bazani ba, ya bar mata gidanta nima ina jin dad'in zama tare da Umma.
Kuma nace masa Anty Surayya ta na zuwa Lokaci bayan Lokaci ita da su Anty Sakeena.
Tunda bayan bikin Siyama duk naje gidajensu mun kara gaisawa, gidan su Sajida ne ban kara marmarin komawa ba.
Hatta gidansu mama naje, ni fa yanzu a gusau in da ban je ba kad'an ne sosai nasan gari.
A lokacin kallo na ya yi kafin yace"Siya yanzu ke sanin gari yafi miki Bukatun  mijin ki? Ni ne fa Assadiq din ki?
Ina marairaicewa nace"Ka yi hakuri To, ba haka ba ne kaga ina tare da Umma kuma naga kana da wata matar ba gauro ka ke ba."
Kallona ya yi na wani Lokaci kafin yace"Shikenan, tunda an hanani Babba, to ko sumbata ne a rika bari ina Rage zafi da shi."
Ban hanashi ba nima na taimaka masa muka samu natsuwa da gangar jikin juna.

Kuma a bangarensa ne abun ya faru Ranar ma Umma na cikin Dakinta kanta ke ciwo ta samu ta sha mgani ta kwanta shine ya jani bangarensa.
Yaso ma na rika zuwa bangaren nasa in yana gari saboda ya rika Samun Abunda ya ke so.
Ni kuma kunya da kuma ganin girman Lamarin a gidan surukai yasa na ki yarda da mganarsa.
Duk iya wattanin da na yi a Gusau sultana na bar miji ta na cin karanta ba Babbaka.
Ban taba nuna Damuwata ba, kuma ko sau d'aya ban taba yi ma Assadiq korafin nagaji ko zan koma Zariya ba.
Kwatsam dawowar nan da ya yi lokacin ina da wata uku a gusau su Asim har sun fara rarrafe har kuma suna kama abu su Tsaya.
Wattaninsu goma kenan  suna samun shan madara kuma Umma ta kara sawa mun dage ma basu kunin ne yanzu ko Babansu sai da Nishi ya ke d'agasu.
Gashi har sun fara Haddace kowa na gidan in suka ga Abba ko Assadiq sun rika mika hannu kenan suna gwaranci haka suke yi ma Umma da Mama da farida su wai sun san su.
Ita Umma bata damu da zama na ba, bataki ma na zauna tare da ita ba saboda bata san yin nesa da jikokinta.
Bansan cewa Abba ya kirasa a waya ya yi masa mgamar bai kyauta ba, in a nan zan cigaba da zama nima a nema min muhallin zama na kamar Sultana.
Har da Umma ya yi mganar ita kuma ta nuna masa in ma hakame sai dai na zauna a bangaren Sadiq din tunda ba kowa aciki yanzu, Saboda yara sun saba da nan d'in.
Abba kuma yace a bari mijina ya yanke abunda ya ke ganin yafi masa Sauki.
Ni duk bansan anyi haka ba sai da Asaadiq ya zo washegarin da ya dawo da yammah ya sameni a cikin dakin da nake kwana ina gyara kayan su Asim da aka wanke a kuma goge musu.
Bayan mun gaisa shi da kanshi ya Dauko Labarin abunda ya faru tunda Farko har karshe.
Ya cike da bani Umarnin na Shirya zan koma Zariya na yi parking d'in sauran kaya na kuma yi sallama da yan'uwana Abuja zai tafi dani Gabadaya.
Cikin mamaki na Bud'e ido kafin yace"Ni kuma? Abuja?
Kai Tsaye ya gy'adamin kai, alamun Tabbacin haka sannan da bakinsa ya ke fad'amim Umma taso na zauna a bangarensa saboda su Asim.
Ni dai ban ce komai ba Tunda mgana na Hannunsa bayan ya tafi ne Umma ta kirani har Dakinta itama ta gayamin Bukatar mijina.
Kaina na kasa nace"Umma tunda kina so mu zauna anan din, sai mu zauna shi sai ya tafi da Sultana."
Umma tace"Da ke yace zai tafi Hasiya, ita Sultana yace ta na makaranta. Bakomai fatana kawai ki kula da su Asim sosai."
Sai naji kwalla sun cika Idona cikin Sauri nace"Umma to dukkan mu ya barmu anan mana, ni kaina bana son zuwa ko'ina na barki."
Umma ta yi wani mirmishi kafin tace"Kada ki damu dani, ai ya kawo min Hujjojinsa kuma na gamsu da su kije ki fara shiri yace sai kin koma ta Zariya ko?
Sai na gyad'a mata kai cikin wani yanayi, mun dad'e zaune kowa na tunani acikin ransa kafin ta sallameni na koma dakin da na sauka.
Sai kuma naji bana son Tafiya Allah Sarki bako Rab'a.

Kuma daman ni komawata Zariya yazo min adaidai, Saboda Safiya ta kirani tace an fara Sreening din Result dinmu tun tuni ni ba na nan, sai na tabbatar mata ina nan dawowa in sha Allahu cikin satin da zai shiga.
Sai gashi kafin kace me, mganar komawata Abuja ya shiga kunnuwan duka yan'uwan Sadiq.
Ban sani ba ashe tunda Assadiq ya Furtama Sultana zai tafi dani Abuja ta Buga Tsalle tace bai isa ba sai dai ya Fara tafiya da ita in kuma ba haka ba, bata yarda nima ya tafi dani ba.
Ni bansan ma sun yi haka ba, sai a bakin Anty Surayya na ke ji sanda ta ke maimaita Umma.
Itama Umma ai su sajida sun zo suna ta kananun maganganun bai kamata ta yi shuru ba, a dalci Sultana ce ya kamata ta bi shi Abuja bani ba.
Umma dai ta yi banza da su ta yi kamar bata ji ba, Su kuma suka kara Zuga sultana da idanuwanta ya Rufe ta mamta cewa ita yanzu karatu ta ke yi, a yadda ta nuna ma zata ijiye karatun ta bisa saboda ni kada naje.
Ni dai ban bi ta kan kowa ba na gama duka shirina Tunda yace a wannan Satin in yazo zai maidani Zariya da kansa.
Kuma har ga Allah sai da Tafiyar ta taso ya ke bani Labarin a ma'aikatansu  suka ba su Gida da Mota shi dai bai karb'i mota ba, gida kawai ya karb'a duk wata za'a rika Cirewa acikin albashinsa sannan Estate ne kamfanin ya gina musu na ma'aikantan su ne.
Ranar Jumma'a Assadiq ya Dawo bai kuma zo gidan ba sai da Safe gidansa ya sauka.
Sai dai tare da Sultana suka zo, ni ina wanka Umma ta yi ta lekoni su Asim suna wajen Abba daman tun safe Umma ke wankesu tas ta shirya a bunta.
Sannan Tun ina wankan naji ana ta kiran wayata, ina fitowa naga Assadiq ne sai na bi bayan kiranshi tunda mun yi da shi yau Asabar zamu wuce Zariya ya kwana lahadi, litini da Safe ya koma Abuja zai barni sati Biyu na gama da makaramta da sallama da Yan'uwana sannan sai yazo ya Daukeni.
Yana daukan kirana ko gaisuwata bai amsa ba yace na zo bangaren Abba yanzu.
Sai na fara Tunanin Ko lafiya? Ina cikin Tararradin abunda ya Faru na Shirya cikin Wata bakar Abaya na Maryam's Epytian Abaya sai na yi amfani da wani purple din Hijabi.
Ina zuwa sai naga Sultana Fuskar nan nata duk ta jeme saboda kuka sannan ga ciki tunda har ya fito duk Kishi da zargi bai barta ta yi wani kumari ba.
Gefe na zauna a kasa ina gaida Abba su Asim na ganina suka fara zillo ya Sake su yana fadin"Sun ga mamansu zasu gujeni"
Mirmishi kawai nayi ban yi mgana ba, ko da suka zo kusa dani ban dauke su na, Mama ce da ta shigo daga baya ta Dauki Asif, Umma kuma ta Dauki Asim suka rikesu a jikinsu suna musu wasa.

Assadiq na kallah Fuskarsa ba Fara'a mun had'a ido da shi, har sau biyu banga ya sakarmin fuska ba.
Sai dai da na yi masa mirmishi kad'an ya kuma maidamin da na Fatar baki.
Abba ne ya katse shurun da kallon Sadiq yana fadin"Magajin gida ne ya kirani da Asuba yace zai zo tare da Sultana yana son zai yi mgana da mu tare da matansa gabadaya Saboda warware wata matsala."
Ya fad'a kafin ya dagata yana kara kallon Sadiq da ya yi shuru bai yi mgana ba.
Umma tace"To Allah yasa lafiya?
Sadiq ya sauke Numfashin bacin rai kafin ya nuna Sultana yana fad'in"Itace zata jawo in ma matsalar ce zata faru Umma"
Cikin mamaki Umma tace"Topha me ya faru ne?
Ya gyara zama yana fadin"Kan zencen Tafiya da Siya Abuja ne, tunda na gayamata ta hana kanta sukuni wai ko na tafi da ita ko kuma duka bazan tafi da ko d'aya acikin su ba.
Umma ban taba fad'a muku wani abu game da abubuwan da Sultana ke yi min ba, zaki tuna wani zuwa da Hasiya tayi nace ta sauka a gidana?
Umma ta gyad'a kai alamun ta tuna shi kuma ya Cigaba da fadin"To Umma wulalanci ta yi min dagani har Siya, shiyasa washegari bayan na koma nace ta koma wajen ki ta zauna Sultana ta ce gida gidanta ne Tunda da sunanta Abba ya bani gida, tundaga Lokacin na saka ma raina Hasiya ba zata kara zuwa gidanta da sunan ta zauna ba, sannan Lokacin da ma'aikantan mu suka yi mana mganar gida, na so na yi ma Sultana mganar zan tafi da ita Abuja Saboda ina da mata Biyu, bai kamata na rika zama ni kadai acan ba, kuma Dalilina alokacin Saboda Hasiya na karatu itama kuma ba ta yi, har ga Allah da Farko ita na yi niyar kaiwa Abuja ta zauna Saboda nasan halinta na Zargin tsiya da nuna ana mata ba daidai ba.
Itakuma Siya zata dawo gusau ta zauna kusa da ku sai na rika zuwa ina ganinta Abba nasan ko a daji na ce Siya taje ta zauna na rantse Abba bazata taba yi min gaddama ba, ballatana yau ace ta Turkeni ta na son  jin Ba'asi.
Nasan halinta Shiyasa na zabi tafiya da Sultana da Farko, ammh Saboda ta na Daukam zugan su Sajida sun kitsa mata Siya na karatu itama ta matsamin sai ta koma makaranta ni kuma tana gayamin nace shikenan Tunda haka ta ke so a lokacin na so ne sai ta koma can na nema mata Jami'r Abuja, sai kuma ba ta Fahimta ba tafi Daukan mgangansu munafukan su Sajida sama da tawa mganar, Shiyasa bayan an gama gina gidajen an bamu key na yanke shaawaran tafiya da Siya Tunda tagama karatunta, ita kuma ta zauna a gidanta na nan tare daku ta Cigaba da karatunta ina zuwa ina ganinta a wata sau daya in sha Allahu."
Abba da su Umma suka yi shuru suna jinjina mganganun Sadiq.
Sultana kuma sai kuka tana fadin"Ni ai baka gayamin Abuja zan koma tare da kai ba, in da ka gayamin da ban shiga makarantar ba kuma yanzu ma bata baci ba ana Transfer."
Kai Tsaye Sadiq yace"Haka su Munafukan suka kitsa miki?
Cikin kuka tace"ni wlh ba wanda ya ke zugani na ran.."
Umma ta katseta da fadin"Karya kike yi kuma anan Sultana, ai Sajida da Sadiya manyan banza ne marasa Tunani, nasan komai duk zuwa gidanki da suke yi suna Dora ki kan mgamganun banza.
Ta koma ta na kallon Sadiq kafin tace"Hukuncin da ka yanke ya yi daidai magajin gida, Hasiya ta koma wajenka da zama ita kuma ta zauna a gidan da tace da sunanta aka Si ya."
Mama tace"To ban da sakarcin Sultana, Hasiyar mai sanyin hali ma ba ta da girman ki in da kin kwantar da hankali lafiya kalau za su zauna."
Umma ta yi Tsaki kafin tace"Ai ko ta kwantar su Sajida ba za su kyaleta ba, Abban Siyama ka kirasu ka ci mutumcin su in ba haka ba sai sun raba auran Magajin gida da Sultana da Shiga da Fitan su."
Sadiq yace"Umma gwara su kashe mata auran kila ta yi hankali, ni ban mata iyakata da su ba yan'uwanta ne tunda sun fini Daraja a wajenta Fine, ni ne dai na yi musu iyaka da Matata da Rayuwa kuma na basu Lokaci ne suka kara Cikani duk sai sun kara Rena kansu."
Abba ya yi shuru kafin yace"basu bar Abunda suke yi ba kenan? Ku kyaleni da su, ke kuma Sultana ki yi hakuri ki bi umarnin mijin ki kin ji ko?
Sultana ta rushe da kuka tana Fadin"Abba ni tare da shi na ke son na zauna, ina fama da laulayi mai zafi ba na iya barci ni kad'ai"
Umma ta saki baki tana kallon Sultana ita da Mama.
Sadiq kuma ko kallo bata ishesa ba yasan halinta ni kaina na kasa ina mamakin makirci irin na Sultana.
Kai Tsaye Abba yace"Ki dawo wajen Umanki, daman ai wajenta ki ke in baya gari ko?
Umma tace"Sosai kuma muna nan ai zamu kula da ita, renon cikin ma duk a dakina ta yi jinyar kuma ai tare da Hasiyar da ta tsana muka yi mata Wahala"
Sai kuma ta kara saka kuka har da wiwi kamar karamar yarinya Abba ya koma ya lallashinta.
Ta na kuka tana fadin"Abba to kace masa ya tafi tare dani, in na kwana Biyu sai na dawo."
Kafin Abba ya yi mgana Sadiq ya yi saurin taran Numfaahinta da cewa"Kinsan Allah ko da bakunta bazan tafi da ke ba. Abuja gidan Siya ne ke kuma ga gidan nan a gusau kamar yadda kikace da sunan ki Abba ya bani gidan, itama da sunanta na karb'i gidan saboda haka ki zauna a gidanki itama ta zauna ana ta gidan.
Iya adalci da san zan yi miki kenan , kuma kinga ban rabaki da masu baki Shawara ba sai ki ba da Himma."
Abba ya jim kafin yace"Sultana ki yi hakuri ki zauna saboda karatun ki."
Umma tace"Kada ma Allah yasa ta Hakuran, kana wani bata Hakuri "
Abba yace"Salamatu komai a sannu ake bi."
Ina zaune na gyara zama ina Fad'in"Abba ni na hakura sai na zauna anan din ya tafi da ita."
Sultana na jin haka ta daina kuka, Abba kuma sai ya yi shuru bai yi mgana ba.
Kaina na kasa ammh nasan ina shan Harara wajem Assadiq
Umma ce tayi karaf tace"Hasiya tare zaku tafi, kai Tashi kaje ka shirya ku zo ku tafi ba ko ba Zariya kace zaku tafi ba yau?
A sannu yace'Eh zan kaita can saboda akwai Sreening din da zatayi a makaranta sai kuma sallama da yan'uwa sati biyu dai nace zan koma na Dauketa zuwa can."
Umma tace"Hakan ya yi, Allah ya tsare maza ka tashi kaje ka Shirya kada ku yi yamma, ita kuma wannan kabar mana ita anan."
Sultana ta kara saka kuka tana Fadin"Don Allah Umma ki ce ya tafi dani."
Umma tace"Bazan ce ba, da kike zaune anan wani abu ya cinyeki? Ko duk baki san da haka ba ne sai yanzu."
Sultana ta yi shuru ta kasa mgana, Saboda ita kishinta da bakincikinta Zai tafi da ne zai je ya bani duniya ban da ita, ita kuma zai barta anan sai yaga dama yazo ya ganta.
Haka su Sajida suka kitsa mata, tare da bata Shawaran ta yi ta rigima tace bata yarda ba in yace karatu tace ai za'a iya Transfer indai ya nace zai tafi da Hasiya to itama tace sai ta je, Daga karshe sai da ya fasa tafiya da kowacce Shiyasa ta hanashi zaman Lafiya tun jiya da ya sauka a garin ta ke masa rigimar ita ta fasa karatu tare za su koma Abuja, shi kuma yace bata isa ba nan ne gidanta anan zata cigaba da zama.

Sadiq kuma Tuni ya bi umarnin Umma ya fice abunsa bayan ya gama Hararata kamar Idanuwansa za su fad'o, ni kuma na kauda kai ni na yi hakane Saboda a samu masalaha ni bani da damuwa su je can ni sai na zauna anan tare da su Umma.
Allah na Tuba wani Dare ne jemage bai gani ba? Ai sai dai daran mutuwarsa.
Abba kuma ya Cigaba da fad'a akan su Sajida Mama ce ta kara da cewa"ai ni ko su Salima nace su fita sha'anin shiga abunda ba ruwansu, kada su je  su ja da ikon Ubangiji."
Umma tace"Suma ki kyalesu lokaci suke jira, duniya zata koya musu hankali, ko ni da na haifi Sadiq din na saki nace Allah yasa albarka to su kuma Munafunci me suke ta kai kawo a kansa?
Ni dai duk ina zaune ina jinsu, Sultana kuma na ta jan majina ta na Shesshekan kuka, Umma ta kalleni tace na tashi naje na shirya tunda zamu kama hanya ne.
Abba ma yace haka ya kamata Kada magajin gida yazo yana jirana.
Nima Umarninsu na bi na koma Bangaren Umma na cigaba da shiryawa.
Can sai ga Sultanan ta Shigo bangaren Umma, ta kuma bi ni har cikin Dakin da na sauka ta iskeni na gama had'a kaya na da na su Asim gabadaya.
Assadiq kawai na ke jira ko sallama bata yi ba haka ta shigo kanta Tsaye.
Na dago ina kallonta cikin mamaki ammh dai ban yi mgana ba.
Sai na maida kaina kan wayata na Bude data muna Chart da Safiya rokonta na ke yi, ta taimaka in na dawo ta rakani cikin makaranta na yi Screening.

Ganin haka yasa ta tsaya a gaba na rike da kugu tana fad'in"Dole ki kalleni ki watsar mana, kinsan dai nafi karfin ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login