Showing 24001 words to 27000 words out of 116366 words

Chapter 9 - Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

312

ina ta san nan gidan?
Surayya ta kalli Umma kafin tace"Umma koma ki zauna na yi miki wani karin bayani."

Ba musu ta koma ta zauna, Innani ma ta daina kuka ta na saurara Abba dai ko a fuska bai nuna wani abu ba.
Surayya ta warware ma Umma komai game da zuwanta Zariya..abu daya ta Boye na canfin da ke bibiyar Rayuwar Hasiya.
Sai kuma na auranta Biyu, ta dai ce bazawara ce, Sadiq ya kama mata haya tana zaune a zariya ya na zuwa ya ganta in ya samu Lokaci.
Sannan ta karishe da fadin"Umma ba wai ina so na kare Sadiq ba ne, A'a ina so ku fahimci namu ne mai laifi, itama ya yi mata karya ne ita da yan'uwanta, sannan dalilinsa na auranta wannan sai shi in yazo ya yi bayani, sannan mganar tasan nan gidan tamin Rantsuwa bata sani ba sai daga baya had'uwarta da Saliha a kaduna da kuma Hoton mu da tagani, tace sai da tazo nan ne taga komai, a yadda ta fad'amin ta na ma sadiq mganar ya kamata ya sanar da mu komai ammh sai yace ta bashi Lokaci yana so ya sanar daku ya na da wata matar kafin Sultana."
Mama ta bude baki kafin tace"Bazawara? Shi Sadiq kamar wanda bakin uwa ke binsa?

Innani ta ja hanci kafin tace"Magajin gida yaci Amana, kuma Amana sai taci sa ja'irin mayaudari kawai yazo ya sakarmin jikata domin bazata zauna da tsohuwar kilaki ba."
Surayya da Sauri tace"Innani ba kilali ba ce fa."
Innani na Hararanta tace"To wacece kuma ta yi aure ta fito ai ta zama kilali yar duniya, ina jikata zata iya zaman kishi da ita? Arhin dinsa sai ya saketa kuma naga abunda da zai hanani ci ma Saddiqu mutumci shi da wannan Dogon abokin nasa mai wuya kamar kauren langa Langa."
Da Sauri Umma tace"Ba ruwan Tahir Innani, Abubakar ne bai Daukemu a bakin komai ba, nima ina goyon bayanki, yadda yaci Amanarmu shima sai Allah ya sa anci tasa, yata bazata zauna da shi ba, tunda wanchan ya zaba sai ya cigaba da zama da ita, Sadiq sai ya saki sultana tun kafin Mahaifinta yaji irin cin zarafin da ya yi ma yarinyar nan "

Kawai sai ta fashe da kuka ta mike ta na fadin"Na yarda dashi, ban taba Tunanin zai karya wannan yardan ba,  Wlh tallahi sai dai ya zaba, ammh har acikin raina ban aminta da wannan auren ba."
Ta na gama fad'in haka ta fice Abba na kiranta bata dawo ba, Innani ma ta tashi ta na dingisa sandarta ta shige dakinta itama ta na shan alwashin idonta idon magajin gida sai taci kwalarsa ya sakar mata jika bazata zauna da bazawarar kilakin matarsa ba.
Abba ne kawai da Mama afalon, shi ta kallah kafin tace"Abban Siyama baka ce komai ba?
Sai Abba ya dago kansa yana kallon Surayya kafin yace"Ki aika a dauko yarinyar nan shima Sadiq din ki gaya maasa yazo gida."
Da haka shima ya tashi ya fice, bai bi bayan Innani ba sanim halinta tunda ta Dauki zafi bazata Sauraresa ba.
Mama kuma sai ta gyara zama ta na kallonsu Surayya kafin tace"Ammh tsakami ga Allah Sadiq bai yi wayau ba, bazawara fa? Kodai farin fatarta ne yaja Ra'ayinsa?
Daga Saddiqa har Surayya ba wacce ta kulata ta gama mganganunta itama ta tashi ta fita.
Suma daga nab Shashen Umma suka koma ta shige dakinta ta Rufe, alamun bata son a dameta.
Sai suka zauna anan falon suka yi shuru kowa da abunda ya ke sakawa.
Saddiqa ta kalli surayya kafin tace"Sai ki kirasa ki fad'a masa ko?
Surayya tace"Zan kira sa, ita Hasiya ina tunanin kawai zan ce ta hau motar haya in tazo tasha sai naje na Daukota."
Saddiqa tace"Duk yadda dai ki ka yi, ni nafi son Sadiaq ya ci Ubansa hannun Umma da Abba saboda gaba"
Surayya dai ba ta ce komai ba, ta na wani Tunani Abba bai nuna wani abu ba, Umma ce ta Dauki zafi ita da Innani kuma a irin kalamansu ba su karbi Hasiya ba.
Kwata kwata su Surayya ba su dauka Mama zata gayama ya'yanta abunda ke faruwa ba, ashe ba haka ba ne ta na komawa daki ta fara kiransu a waya  daya bayan daya Sa'ima ta fara kira ta gayamata sannan Saliha da sauran.
Kuma kowa sai ta yi masa kwatancen Hasiya sannan ta kara da fad'in ance ma bazawra ce, kuma Surayya da Sajida sun je har zariyan sun ganta.
Dukkansu mamaki ya kamasu, Mama ko har da kalaman Umma da Innani sai da ta gayamusu sannan tace su zo gida ayi gabansu Tunda Abba yace a zo da yarinya sannan Sadiq ma yazo gida.
Saliha tafi jin mamaki ta jima tana nanata abun, sai alokacin ta Tuna kiran da Surayya ta yi mata, ashe daman dalilin kenan?
Salima ma Sa'ima ta ke gayamata, da kwatancen yar'uwansu mubarak yasa ta gane wacce Anty surayya ta Turo mata Hoton ta ne, ita ta manta da batun ammh jin haka yasa taji ta na son sanin komai.
Ballatana da Mama ta kirata ta na fad'amata tace an ce yar'uwan mijinta ne, sai ta fad'a mata yadda suka yi da Big sis kwanaki.
Nan ta ke Mama tace salima ta yi musu Binciken wacece Hasiya!
Salima kuma na jin haka a daran ta matsa ma Mubarak sai da suka je gidansu, ta samu zahara'u ta tuna mata, itakuma sai da aka had'u wajen cin abinci ta ke yi ma Abba kwatancen Hasiya.
Hajiya Murjanatu na wajen itace ma tace yar wajen marigayi dan'uwansa mamman ne.

Sai ya tuna, kamar ko yasan Salima na son labarin duka nan ta ke ya fara ba su labarin Hasiya da canfinta na mai farar kafa da tunanin da suke yi ita tayi sanadiyar talauta mahaifinta daga karshe ya rasu da aure aurenta da komai sai da ya fad'a ma yaran kuma agaban Salima.
Hajiya murjanatu na ta kifta masa ido ammh ya yi kamar bai gani ba.
Da ya gama yaga ta na yi masa wani kallo sai kawai ya karkace kai kafin yace"To ko karya na fada? Gaskiya dayace fa daga kinta sai bata Murjanatu"

Salima kuwa suma komawa gida ta kira Mama ta kwashe komai ta fad'a mata, ita kuma duk a daram ta kira yaranta ta fesa musu, suna ta faman Tattauna lamarin yan kusa sun ce gobe suna nan zuwa ayi komai a gabansu.
Ita kuma Hasiya Surayya ta kirata tace in da kudi a hannunta ta shirya ta hayo motar haya in zata iya.
Tace mata zata iya.
A ranar na baro zariya na zo gusai, gwara kawai nazo ayi wacce za'ayi, a tasha Surayya ta zo ta Daukeni zuwa gidanta ta bani daki kuma ta karraamani.
Ta kuma zaunar dani tamin bayanin komai da ya faru yau da safe, ammh bata fad'amin furucin Umma da Innani ba.
Tadai ce Abba yace na zo sannan Sadiq ma a kirashi.
Ta bar ni a dakin da ta saukeni ta fita falo da niyar kiran sadiq.
Sai taga ya kirata ma wajen sau Hudu. Ta na kokarin bin bayan kiran ne sai ga shi ya sake kira.
Sai da ta dauka suka gaisa, ta yi shuru shi kuma dagachan bangaran yace"Big sis mganar nan da na yi ta cewa ina so mu yi, shine yanzu na ke so in ba wani abu kike yi ba mu yi mganar"
Kawai sai tace"ka makara Sadiq na riga nasan  mganar"
Cikin firgici yace"Kin sani?
Mirmishi ta yi kafin tace"Ba na kayi aure a zariya ba? Sunan matar taka Hasiya kuma ma yanzu ta na da ciki ko?
Ai sai Sadiq yaji kamar a cikin kankara ya sandare a zaune.
Yana kwaso in'inan mgana Surayya ta katseshi da fad'in"Umma da Abba da Mama hadda Innani suma sun sani, Sadiq gobe kome ka ke yi ka barshi ka taho gida, in kuma ka ki zuwa ina mai tabbatar maka komai zai lalace."
Cikin rawan baki da na zuciya Sadiq yace"In sha Allahu zan taho da Sassafe.'
Daga haka ta katse wayarta, ta na Tunanin abunda zai iya faruwa a goben.

Abunda bata sani ba suna gama waya ya kira Hasiya, ta dauka kuma Daman Surraya tace kada na bari yasan ina Gusai.
Cikin tashin hankali ya ke gayamin yadda suka yi da surayya sai naji ya bani Tausayi, barin ma da ya ke cewa"Gobe zan tafi gusai siya, ki tayani da addu'a Umma da Abba su Fahimceni, ina son ki har abada ba na fatan Rabuwa da ke. Ki zama cikin shiri akwai yuyuwar ki taho gusai in bukatar hakan ya taso."
Ya yi ta kokarin ya nuna min kada na Damu in sha Allahu bakomai.
Shi tunaninsa daya ina suka san da wannan labarin? Duk da na sani ammh na kasa iya gayamasa yadda abun ya fara ba.
Muna waya ina sharan kwalla, na yi ma kaina alkwarin zan yi duk abunda Assadiq ya ke so, tunda wannan Halin Tsaka mai wuyar da ya ke ciki ba saboda kowa ya shiga ba sai saboda ni.






*Janafty*
*TMWBK3006*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IhAz8h8nRy250ZnGGXwM65

Daren ya kasance mai tsawo a gareni, na kasa barci sai faman juye juye na ke yi, ga ciwon kai sannan ga cikina ya karamin nauyi.
Domin na sha wahala a motar da na shigo zuwa gusau.
Duk yadda Surayya ta rika lallashina da nacin na huta kada na damu babu abunda zai faru, sai naji na kasa jikina ya yi sanyi gabadaya gabbaina sun saki, in na kalli cikin jikina sai naji Rauni ya Rufeni, ba na so abunda muka aikata ya shafi d'an da ke Cikin mu, sannan gefe d'aya ina jin Matukar Tausayin Assadiq duk abunda ya faru ko zai faru saboda ni ce.

Da naga na kasa barci sai na rarrafa na tashi ina jan kafa na fad'a Tiolet din dake cikin dakin na Dauro alwala nazo na daidaici in da Anty Surayya tace min gabas ne na tada salla.
Dakyar na iya yin raka'a hud'u ina tsaye, da naji nagaji sai na koma na zauna saboda girman cikina kamar ana hurashi sai kuma ya koma kasan marata ya yi tulu kamar wacce ta shiga watan haihuwarta, alhalin kuma wattanin cikin wata bakwai ne.
Na yi addu'a sosai acikin daran nan da Fatan duk abunda zai Faru gobe kada ya zama mai Tsauri ga Rayuwata sannan kada ya zama mai kuntata ga Assadiq.
Sai wajen uku na dare na yi barci, kuma kiran sallar asuba a kunnina Tunda daren ne gabadaya ya yi min Tsawon da na kasa samun natsuwa ballatana na iya yin cikakken barci.
Ko da Surayya ta shigo ta tasheni sai ta iskeni ina salla a zaune, tunda da asuba da jan kafa na iya shiga bayi, kafafuna daman tun jiya suka kara Kumbura saboda zaman mota, sannan ga sallar da na yi a zaune da safen sai suka kara hayewa dakyar na ke tafiya.
Sai bayan na idar da sallah ta dawo mu ka gaisa cikin sakewa da Fara'arta kamar yadda na Fahimceta macece mai girmama Dan adam kamar irin Assadiq dina.
Ganin yadda na mike kafafun ne yasa ta kalli kafafun sannan ta koma ta na kallon Farar Fuskata lokaci d'aya ta na fadin"Sannu naga kafar ta tasa ne"
Mirmishi nayi ban yi mgana ba saboda jin nauyi sai itace ta cigaba da fadan"Allah yasa kada wannan yar mganan da za'ayi yau ya taso da naguda fa"
Ta karishe fad'a cikin sigar Zolaya, sai na kalleta kafin nace"Ban kai ga watan haihuwata ba, cikina wata bakwai ne fa."
Sai ta zaro ido ta na kara kallona kafin tace"Wata bakwai fa kikace Asiya.?
Sai na gyad'a mata kai alamun hakane cikin mamaki tace"Ikon Allah gaskiya kina da girman ciki ni da Randami, ni wlh na dauka cikin ya shiga wata na Tara ne"
Sai kawai na sunkuyar da kaina cikin Sanyin murya nace"Haka kowa ke tunani, ana ta mamakin girman cikina shiyasa nake jin nauyinsa a jikina da kafafuna."
Cikin Tausayawa Surayya tace"Sannu dole zaki ji kam, bari na samo miki man zafi ki shafa. Ya samu su sauka kafin mu tafi chan gidan."

Da Toh na amsa mata sai ta tashi ta fita ba jimawa sai gashi ta dawo ita da yaranta ta saka su, suka gaisheni na amsa ina tambayan sunayensu.
Namijine ke ma uwar rad'a sai tayi dariya kafin ta kalleni ta na fad'in"Matar Uncle din ku ce Sadiq, sunanta Asiya."
Sai ya waro ido kafin yace"Mommy ita Anty Sultanan fa?
Batare da wata Damuwa ba tace"Dukkansu  matansa ne Khalil"
Zai kara mgana ta dakatar dashi da cewa su je su yi shirin makaranta.
Sai da suka fice ne sannan ta duka ta na fadin"Bari na taimaka miki."
Ita ta shafemin kafafuna da man zafin nan, tace zuwa anjuma zai saki yadda bazai takurani ba.
Ina tayi mata godiya kamar na yi kwallah ganin yadda ta karbeni batare da ta kyamaceni ba.
Kafad'ata ta dafa cikin sigar lallashi ta na fad'in"Kada ki damu Asiya, ni a wajena da ke da Sultana duk d'aya ne Sadiq dai shine kanina duk da itama Sultanan kanwata ce, ammh a Ture wannan bangaran kuna da tudun matsayin matan kannena ne, kuma nice Babba a gidanmu in ban zama mai gyara ba, bazan so na zama mai barna ba kuma Dan adam ai ya na da Daraja bai kamata wani mutum ya kasance mai dariya ko wulakanta kaddaran wani wanda ba shi ya yi kansa ba."
Har ta fice ina jin kalamanta a raina sannan a gefe d'aya ina kara jin na samu natsuwa a cikin raina.
Kuma man zafin da ta shafamin naji dadinsa sosai, Assadiq ke raina shi na kira ammh sai wayarsa bata shiga ina da kyakyawan zato kila ya taso ya na kan hanya ne.
Adda Fati na kira, a raina nace gwara na fara fad'a mata kada Lamarin ya Rikice na koma da wani Labari wanda su ba su san dashi ba.
Da ta dauki wayata sai da tace min"Lafiya Hasiya?
Saboda taga kiran wayata da Sassafe, cikin Boye yanayina nace"Lafiya lau Adda Fati ya yara?
Ta amsa min Lokaci d'aya ta na tambayata ya nauyin jiki nace mata da Sauki sai tabini da addu'an Allah yasa na sauke lafiya acikin raina na amsa mata da Ameen.
Shuru muka yi na wani Lokaci ita kuma sai ta Fahimci akwai mgana a bakina cikin Wani yanayi tace"Hasiya..! Menene ke faruwa ne?
Cikin karfin hali nace"Adda ina gusau fa Tun jiya."
Cikin mamaki Adda Fati Dagachan bangaren tace"Gusai kuma?
Ta fad'a cikin Sigar Tambaya.
Cikin gyad'a mata kai kamar ta na ganina nace"Eh Adda, ina Gusai yanzu haka ina gidan yayar Assadiq a nan na kwama ma"
Cikin wani karin mamakin Adda Fati tace"Yayarsa kuma? Ke Hasiya yi min gwari gwari ni bangane ba."
Sai na gyara zama na muskuta saboda na gaji da yadda na zauna.
Cikin ajiyar zuciya nace"Labarin mai Tsawo ne Adda, ammh mafi muhimmanci ne shine Assadiq ba maraya ba ne, ya na da uwa da uba a raye sannan shi din d'an Dangi ne. A takaice dai iyayensa ba su san ya aureni ba sai yanzu da yayyensa mata suka gano hakan."

Adda Fati baki ta Bud'e cikin mamaki da Al'ajabi kafin ta samu zarafin magana na katseta da fad'in"Na kiraki ne na fad'a miki Saboda ki sani, ba lalle na dawo da aurena a kaina ba, in komai ya rikice ba su aminta dani ba zan sake dawowa a sakakkiyar bazawara a karo na uku."
Ban jira cewarta ba na kashe wayar Saboda kukan da ke neman kwacemim.
Ina jinta ta na ta sake kira ban bi ta kanta ba, sai ma kaina da na kwantar saman gadon dakin na fashe da kuka, sai da na yi ma ishi sannan na share hawayena, na koma gefe ina sauke ajiyar zuciya.

Acikin cikina nake jin motsin da yasa na Dafe cikin ina yar dariya, sai dai wani abu na bani mamaki ni fa ba Motsin abu daya na ke ji acikina ba, sanda naje awo na karshe na yi musu Complain suka kara yi min scanning suka kuma kara samun Tabbacin Rai d'aya ne aciki sai dai likitan yace ya Danganta da koshin lafiyan jaririn Cikina shiyasa na ke jin motsin kamar yafi rai d'aya.
Ni dai na yi shuru ne, ammh har acikin raina nasan abunda ke cikina yafi guda d'aya saboda nauyin da na ke ji, sannan a tare zan ji suna Taushin Cikina ta bangarori da Dama, na yi dai shuru tunda wannan ne na Farko sannan kuma ban isa na san abunda Allah ya Boye a cikina ba, ko su likitocin ai sai abunda Allah ya ba su ikon sani suke iya sanin.
Ina nan zaune sai ga Anty Surayya da Farantin kayan karyawa ta kawomin.
Tace naci na koshi sai na yi wanka na Shirya in mijinta ya fita aiki zamu tafi chan gidan
Cikin Sanyin jiki na amsa mata, alokacin bata ga idanuwana ba sai da ta dawo bayan na gama karyawa sannan ta lura da fuskata, cikin wani yanayi tace"Asiya ba nace ban da koken koken nan ba?
Sai na dukar da kaina kafin nace"Ban yi kuka ba Anty surayya."
Mirmishi ta yi kafin tace"Kin yi min karya , Saboda ai kinsan Fuskarki bata isa ta Boye kukan ki ba."
Nan ta ke na gane kuskurena da sauri na bata hakuri sai ta kalleni kafin tace"Ni baki yi min laifi ba, saboda kinga halin da kike ciki, matsalane wani abu ya sameki a cikin wannan yanayin naki shiyasa kikaji ina ta miki mganar ki saka natsuwa a ranki in sha Allahu alheri ne zai Faru."
Sai na jinjina mata kai, Tiolet ta shiga tace bari ta dauko Botiki Tankinsu ya lalace baya ba da ruwa sai an kira mai gyara.
Da kanta taje ta juyomin ruwan da ta sanya a gas ya tafasa ta kawomin tace na gasa jikina da kyau, ban mata musu ba na tashi na cire kayana na Shiga wanka kuma kamar yadda tace na gasa jikina sosai kuma naji dadi.
Da na fito man zafin nan da ta barmun na kara mulkema jikina Sai naji duk inda jikina ya Rike daga jiya zuwa yau ya sakeni.
Doguwar rigar Abaya na saka mai Ruwan kasa, tunda kayan Atamfofi sun daina shigata saboda kiban da na kara da kuma cikin jikina.
Nagama saka Rigar kenan ina Dauran gyalen kayan a kaina sai ga Anty Surayya ta shigo itama ta yi wankanta tas ta sha kwalliya sai tashin kamshi ta ke yi.
Kafin ma nayi magana ita tafara washe min baki,ta na fadin"Kin gama Shiryawan Asiya?
Da sauri na gyad'a mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login