Showing 48001 words to 51000 words out of 116366 words

Chapter 17 - Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

322

kyalla ta Haihu? Ya yi auren sai me? Ke ki kiyayi kanki ai ita ya fara aura in yaso sai yace ya fasa auranki kuma ba mai yi masa Dole, ammh bai yi haka ba sai ke ce don rashin Mutumcin ki ke har kara fad'in aure ya yi, to ya yi auren sai ki hanasa abunda Allah yace ya yi, ni ai da ya Burgeni ma da uku ya aura sai ku zama ku hu'du naga yadda zaki yi, banda shashanci ko ni Ubanki bayan mahaifiyarki matana Biyu saboda Rashin adalci irin naki don mijinki ya yi aure sai kice zaki fara yi masa rashin d'a."
Daga Umma har Sultana suka yi shuru, Umma ranta ya gama baci saboda ta da na tabbacin Sadiq ne ya Kirasa ya fad'amasa kuma taci alwashin zai zo ya sameta sai ya raina kansa.
Ita kuma Sultana kukan yadda Babanta ya kasa Fahimtar irin cin Amanar da Yaya Sadiq ya yi mata ne, ammh kuma sai ya zo ya Bige da yi mata fad'a.
Fata fata ya yi ma sultana itama Umma ya yi mata nasiha yajawo Hankalinta, ammh duk bata ji ba ta dai nuna kamar ta fahimce shi kuma zata gyara ne.
Kafin tafiyarsa sai da ya jaddadama Sultana ta koma dakinta mijinta yau ba sai gobw ba, kuma sannan ta girmama ra'ayin mijinta. in kuma yaji Sabanin haka zai kara dawowa ammh ta sani dawowar bazata yi mata kyau ba.

Ko karyawa bai tsaya ya yi ba wajen Goma na safe ya Juya ransa bace shi kam Abba lamarin ya yi masa daidai.
Innani kuwa kamar an tsaface bakinta bata yi mgana ba sai dai Mallam Shitu ya sha tabe baki da Harara ta zata zai sako sunanta ne ta yi masa wankan Tsarki duk dai tace ta yafe ammh dai duk da haka dai, sai kuma aka yi sa'a bai sako sunanta ba to ina zai sakota Tunda yasan Halinta.
Sultana kuwa bayan tafiyar mahaifinta ta kalli Umma lokaci d'aya ta na fadin cikin kuka"Umma yanzu sai na koma?
Umma ta kalleta ita tsabar takaicin da ta ke ciki ya hanata mgana, ta na ganin Sultana na gunjin kuka ammh ta kasa ce mata ci kanki ballatana ta iya lallashinta
Tafiyarsa ko awa daya ba'a yi ba sai ga Maallam zakari d'aya daga cikin jikokinsa ya rakosa.
Tunda Abba ya kira Umma a waya ya gayamata zuwan mahaifinta nata gabanta ya fad'i saboda tasan halin Mahaifin na su yana da zafi, shifa ba ruwansa komai girman ki kika aikata ba daidai ba gaban ya'yanki zai yi miki Kaca kaca bai damu ba.
Shiyasa tunda Umma taji Labarin zuwansa jikinta ya yi sanyi sannan a gefe daya kuma na zuciyarta ta kara Kullatan Sadiq wato itama bai barta haka ba sai da ya had'ota da mahaifinta lalle zai gane ba shi da wayau in suka had'u.

Shima a bangaren Innani ya sauka daman ta so tazo d'aya da Innani, itama sosai take jin dadin Hira da shi, mutun ne mai fara'a da barkwanci gashi yana Biye ma duk abunda Innani ta zo da shi baya kusheta Shiyasa da ta gansa ta rasa ina zata sakashi Saboda Murna.
Kamar an bude famfo haka ta shiga labarta masa abunda ya kawosa, har da sauran Labaran da bai sani ba na game da Hasiya.
Kai Tsaye mallam Zakari ya kalli Innani kafin yace"Naga matar jiya tare da ita ya biya wajena, yace Zariya zai kwana yau tun safe zai kama hanyar Abuja"
Sai Innani ta rike baki ta kasa mgana, Shigowar Umma da Abba ya hanata wata mgana.
Umma ta duka zata gaishe shi ya daga mata hannu da sauri yana fadin"mike kawai abunki salamatu yau bazan karbi gaisuwarki ba, sai kin gayamin babban Dalilin ki na kin sakama auran da Abubakar ya yi albarka? Ke shad'aniya ce da ki ke ja da Hukuncin Ubangiji salamatu.?
Yadda ya ke fad'an ne yasa Umma durkushewa a gabansa cikin rawan murya tace"Baba ka tsaya ka Saurareni."
Cikin daga murya yace"To ina sauraranki, fad'i abunda ke bakin ki."
Gatse ya yi mata ammh bata gane ba cikin Rawan baki ta fara fad'in"Baba yaron nan fa aure yaje ya yi a Boye bamu sani ba?
Kai Tsaye yace"Shine mene?
Kallonsa ta yi cikin mamaki bakinta na Furta"Baba.!
"Nace shine menene don ya yi aure baki sani ba, sai daga baya kika sani?
Sai Umma ta maida kanta kasa ta riga daman tasan mahaifin nata bayan Sadiq zai bi.

Cikin fad'a Mallam zakari ya cigaba da fadin"Ke Sakarcin ki bai baki yakamata ma ki godema Allah ba, in da ace yau matar bariki ya samu fa ko da kin ji Labari kina da yarda zaki yi ne? Ko kuma ace cikin da ke jikin Matar ba ta hanyar aure ya same shi ba? Sai ki ce kuma mene a wannan Lokacin Salamatu?
Ya fad'a yana kureta da ido Umma sai kuka Innaani na gefe tace"Haka ma Sulaimanu yace min da zai min nasiha shiyasa na yi shu da bakina.".
Mallam zakari ya kalli Innani ya na fad'in"Ke ma ai naga laifin ki Tsohuwa, kema ai uwa ce ga salamatu har da shi Sulaiman din, in suka yi ba daidai ki had'a su ki yi musu Hukunci, ammh sai ki barta ta na azabartar da yaro kan hanyar gaskiyarsa, kuma ma abun haushin duk kuna zaune kuna kallonta yanzu ba domin yaron nan ya yi Hankalin zuwa ya gayamin ba. Da sai abu ya kwabe ya lalace sannan zan sani."
Innani na jin haka kawai sai ta saka kuka har da Cire gilashi ta na fad"in"Ni ina ruwana, mi ye nawa? Na zabi yin shuru ne tunda abu na tsakanin bare da na gida, in na saka baki a kan lamarin sultana sai Magajin gida yace ina ja da Hukuncin Ubangiji in kuma na saka baki na goyo bayansa sai ace naki na gida na Fifita bare, in kuma na yi shuru da bakina shima bazan tsira ba."
Kawai sai ta fara jan Hanci ta na cigaba da fadin"Kuma salamatu naga ranta ya baci, kuma tsakani ga Allah d'anta ne kada na cika saka baki taga kamar zan nuna mata iyakarta ne, sannan shi kanshi Sulaimanu bata ji mganarsa ba ballatani, ni a suwa? danwake ya shiga hotel ai bazata ji mgana na ba, shiyasa na koma gefe na yi Shuu da bakina kaji dai dalilina ni kam a daina ganin laifina."
Ta karishe fad'a ta na share Hawaye da Haban zaninta.
Malam zakari yace"To shikenan ni yanzu zan ci Mutumcinta, in ku ta raina ku ni bata isa tace zata kawo min wargi ba. Bar ganin kin tara ya'ya da jikoki sai na kwade'ki anan wajen Tunda sakara kike kin girma da tunanin da ko yaran ki na tabbata ba zasu aikata abunda kike aikatawa yanzu ba."
Umma dai ba baki sai shesheshekan kuka ta ke yi gwanin ban Tausayi ita tana gani ta na kan gaskiyarta an ki sauraranta
Mallam zakari kuwa Abba ya shiga yima fad'an me yasa ya Biye ma Umma ta na wannan Shirmen.
Abba ya gyara zama yana fadin"Na yi mata uzirin sanin halinta, na barta ta nuna Fushinta tunda ita uwace ammh ban dauka abun nata zai zarce zatona da Tunanina ba."
Mallam zakari yace"Ai kaji inda aka samu matsala, ai su mata ba'a kyalesu ace za'a ga iya gudun ruwansu wlh kana zaune sake da baki sai su wuce Tunaninka  kamata ya yi tun farko ka tka mata Burki ka nuna mata kai ne sama da ita ba ka zauna ka saka mata ido ta na abunda taga dama ba."
Abba dai sai ya fara ban Hakuri, mallam Zakari kuma sai ya koma kan Umma ya na ta yi mata fad'a ta inda ya ke shiga bata nan ya ke fita ba.
Fad'i ya ke yi"Ke bazaki godema Allah ba, Allah ya baki duka yara natsassu, ba wani mara ji a cikin su, menene abun damuwa saboda ya  yi aure baki sani ba? Naji bai kyauta ba Boyemun ku da ya yi, ammh kuma da kika sani me ya kamata ki yi? Ba sai ki godema Allah tunda auran ya yi ba, ki zauna da Danki ku fahimci juna ammh sai ki zauna kina wani shanshanci wai har kece kike fad'in wai sai dai ya zaba Tsakanin ita yar wajen naki da ita matar nasa? An ya salamatu kina da aldaci kuwa a Rayuwaarki? Kuma kina son ki gama da Duniya lafiya kuwa?
Sai Umma ta kara karfin kukanta cikin rawan murya tace"Baba baka san irin yarinyar da ya aura ba ne shiyasa ka ke goyama yaron nan baya."
Mallam Zakari yace"Bansanta ba, kaji min wata mgana jiya nan suna gidana na ganta har mun yi mgana da ita yarinya karama miye laifinta? Sannan ta na Dauke da ciki abun Tausayi ko ta haka bazaki tausayamata ba, tunda ai kema uwace kinsan komai."
Umma tace"Baaba Matar fa an ce fa farar kafa gareta sannan bakar Annoba ce, shi kanshi Sadiq din ya sani duk wanda ta aura ko ya rasa lafiya ko Dukiya ko rai to Baba wannan matar abar so ce? Ai in nace ya saketa ban yi laifi ba."
Mallam Zakari ya yi shuru ya na kallon Umma cikin mamaki kafin ya kad'a kai yana fadin"Eh na shaida ba shhakka, ashe duk ilimin da na baki kin yi watsi da shi, a wani Nafsin akace akwai farar kafa a musulunci? Sannan ita Allah ce da zata Talauta mutum ko ta kashesa! Kaji wani banzan Tunani wajen salamatu Tunani irin na Jahilan farko da ba su san addini ba"
Ya fad'a cikin takaici Abba na gefe yace"Shi na gani, to Ubangiji shine fa komai, ta yaya don wani abu ya Faru da wani sai ace kuma wani ne ya yi masa  kaga ai an kauce ma sanin Allah ta wannan bangaran"
Cikin fad'a ya karb'e da fadin"Tuni ma an kauce ma Fad'in Allah da Monzonsa sannan Tauhidi ya yi Targad'a, babu iklasi kwata kwata a al'amarim salamatu."
Umma na sharan hawaye tace"Baba kuma fa bazawara ce, auranta Biyu kuma an ce duka mazajen sai da ta nakasu sannan ta rabu da su, ina zan saka kaina in na rasa Sadiq shi kad'ai gareni namiji kwara d'aya tak shiyasa nake yin wannan abubuwan saboda kare lafiyarsa."
Mallam Zakari ya katseta da Fad'in"Kafin ki samu Sadiq din a baya kin san zaki same shi?
Nace kin san zaki same shi?
Umma sai ta girgiza kai cikin fad'a ya cigaba da cewa"Baki san zaki same shi ba Allah ya baki shi, to kin isa ki hanashi ya kwace shi Lokacin da ya ga dama ne? Kuma da kike fadin kina yin wannan abun ne saboda kare lafiyarsa wacece ke da zaki iya kare lafiyarsa, ko daman chan ke kike Tsare da lafiyar tasa? Salamatu kina wani abu kamar mara ilimi Allah ne kad'ai ke tsare da bayinsa ba wayon mu ba, kuma ba Dubaran mu ba ke baki isa ki zama kariya ga Rayuwar Abubakar ba Tunda ba tare kike yawo da shi ko da yaushe ba  kuma da kike wani izgilanci fad'in bazawara to sai me? Su zawarawa ba Mutane ne ba ne? Ko su ba su da rai ne? Ki shiga Hankalin ki fa, ke da kike ganin kanki a gidan mijin ai baki wuce a yanzu ki zama bazawarar ba"
Da Sauri Umma ta Dago ta na kallonsa Lokaci daya ta na nuna kanta da fad'in"Ni kuma Baba?
Kai Tsaye yace"Eh ke fa, kin wuce  ki zama bazawar ce? Kuma kada ki manta ke uwace kina da ya'ya mata Rututu suma acikin su baza su wuce kaddaran haka ta faru da su ba sai naga yadda zaki yi, tunda zawara ne su, bazasu kara auruwa ba."
Umma sai ta kara saka kuka Mallam Zakari kuwa bai barta ba sai da ta yi masa alkwarin taji kuma In sha Allahu zata gyara.
Ba zata kara cewa ya zabi daya daga cikin matansa ba, sannan zata cire bakinta a sha'anin matan Abubakar in kuma ya kara ji to ranta sai yafi haka baci.
Umma bata da mafita sai ban hakuri ganin yadda ya Dauki zafi.
Suna zaune yana kara yi ma ta nasiha ganin ya dauki zafi da farko yanzu kuma sai ya koma nasiha da lallashi.
A lokacin a ka kira Abba a waya daga chan Abuja ma'aikatar Da Sadiq ke aiki.

Tunda Lokacin da mutane suka kawo agaji a wajen da akayi hatsarin an samu dai an cirosa daga motar sai dai wayarsa ta fashe, ta cikin motar aka ga I.d card dinsa na wajen aiki sai wani jami'a cikin  jami'ai masu kiyaye had'ura na titina Road Safey da suka zo wajen
ya dauki lambarsu ya Kira su ya gayamasu bayan ya yi musu bayanin sunan ma'aikacin nasu.
Su kuma daman suna da duka bayanan ma'aikatan su kuma bayan Lambarka kana saka wata lambar ko na mahaifi ko mahaifiya anan suka samu lambar Abba suka kirashi suka sanar da shi abunda da ke faruwa, sannan suka ce za su Turamai lambar jami'in da ya kira su.
Kawai gani suka yi Abba ya mike yana ta jera Uban salati.
Da Sauri Umma da mallam Zakari suka mike suna tambayan lafiya?
Innani kuma har ta fara gyangyd'i kamar daga Sama taji Abba na fad'in"Abubakar ne wai ya samu Had'arin  mota yanzu daga ma'aikatarsu ta chan Abuja suka kirani suna fad'amin."
Sai ga innani ta fado daga kan kujera ta na fadin"Na shiga uku ni Dije, wani Abubakar din ba dai magajin gida ba?
Umma kuwa kasa ta koma ta zauna Dabas ta Dora hannu a saman kai ta na fadin"Shikenan abunda na ke gudu ya faru, na shiga uku na lalace wayyo d'ana."
Mallam Zakari kuwa salati ya saka yana tambayar Abba a ina abun ya faru? Abba yace ba su yi masa wani karin bayani ba ammh sun ce za su turo masa lambar jami'in da ya Kirasu sai ya kira yaji a ina ne? Kuma sannan a wani Halin Sadiq din ke ciki.
Abba jikinsa na rawa ana Turo lambar ya latsa kira bayan bayanin shi mahaifin Abubakar ne wanda ya yi hatsari yanzu aka kirasa daga ma'aikatarsu na Abuja kuma su suka Tura masa lambarsa.
Jami'in yace"Hatsarin ya faru a tsakanin barin kaduna ne zuwa Abuja, kuma mara lafiyan yana asibitin Sojoji na 44 da ke kaduna za su iya zuwa domin ganin Halin da ya ke ciki."
Abba da mallam Zakari ko Tsayawa jin ta ihun su Innani ba su yi ba suna fita Direba daman yazo ya na jiran Abba za su fita kawai suka fad'a mota Hankali tashe.
Sai bayan fitarsu ne Umma ta fito ta na kuka ta yi shashen Mama ta na fad'a mata abunda ke Faruwa.
Mama ta Rude' fad'i ta ke yi"Mun shiga uku, a ina abun ya faru?
Umma na kuka tace"Bansani ba, Abban siyama da Baba da yazo da Safe sun fita ba su yi mana wani bayani ba."
Mama itama sai hawaye hankula suka tashi ita Sultana ihun Innani ne ma ya fito da ita a haraban gida ta na kuka da jiniya ta na fad'in"Bala'i da Annoba sun sauka a rayuwar magajin gida."
Siyama ke gayamata ta na kuka cewa Yaya Sadiq ne ya yi hatsari.
Itama nan da nan ta rud'e daman kuma ta gama kukan fad'an babanta kenan sai kuma ga wani bakin Labari.
Kafin wani Lokaci gabadaya wannan Ahali na nesa da na kusa sun san abunda ke faruwa yan kusa kuwa irin su Surayya, Sadiya, Sajida Sa'ima, sakeena, Sa'adatu duk sun hallara na nesa kuwa irin su Saddiqa da su saliha sai faman kira suke suna tambayan yadda ake ciki.

Abba kuma yace suna hanya har Lokacin ba su isa kaduna ba.
Hankali sun tashi, Innani kuka ta dinga yi ta na fadin in Magajin gida babu shi ne gwara su fad'a mata ta san gaskiyan mgana.
Umma kuwa har sai da idanuwanta suka sauya muryanta ya dishe, Surayya ma ta yi kuka kamar mene, sai dai ita ke ta faman waya da su Abba tana ce musu suma ga su nan za su taso ammh kuma Abba ya hana yace su dakata su fara isa su ga Halin da ya ke ciki.
Sultana kamar mai aljanu sai shidewa ta ke yi, kawai ta na Tuna rashin kunyar da ta yi masa ne ranar kafin tafiyarsa.
Su sajida kuwa ko duba Halin da ke ciki ba su yi ba fad'i suke yi shikenan Sadiq ya Dauko abunda zai kashe shi ba karya komai ya Faru da shi silar wannan bakar Annoban da ya kwaso musu ne.
Umma dai sai kuka bata mgana su Baba sammani ma Tuni sun samu Labari dagachan suma suka ce za su wuce kadunan domin su ga Halin da ke aciki.
Abba sun isa kaduna wajen uku na rana ne, shima domin Direba ya yi gudu ne sosai suna zuwa asibitin 44 shashen Emergency suka nufa Tunda suna ta waya da wannan jami'in yace tare da shi aka kawo Sadiq asibitin shi yaje ya Dauko yan Sanda Tunda cases ne na hadari sai da jami'an Tsaro zasu karbesa.
Sun je sun iske har alokacin Sadiq na Emergency, sai dai yana nan a raye ammh kuma ya samu Raunika, akwai karaya a hannunsa na dama sai kuma karaya a kafar dama sai kuma Raunin da ya samu a kansa da gefen fuskarsa sai kananun Rauninka a sassan jikimsa.

An gode Allah ma tunda ya farfado sai dai baya cikin hayyacinsa sannan sunce Hoton kansa za su yi zuwa Gobe su gani ko Buguwar ta tab'a cikin kansa.
Abba da mallam Zakari sun shiga sun gansa sai ga Sadiq halitta duk ta sauya kansa duk ya kumbura.
Abba ma sharan hawaye Mallam Zakari na sharan hawaye.
Jami'in shi ya ba su kayan Sadiq da suka samu a motar wayarsa da I.D card ,key din mota sai Wallet d'insa mai Dauke da kudi da Atm din bankunansa sai wasu Takardu.
Allah yasa an yi saurin adanasu da tuni an nemesu an rasa.
Suka rabu da  su Abba  suna yi masa Godiya bayan Abba ya yi masa ihisani.
Shi ya gayamusu ba Motar ta da gogesa kawai motar ce ta kwace masa, kuma in da Abun ya takaita ba wata mota mai zuwa a gaba da abun yafi haka Muni.
Abba bai san yana iya kuka ba sai da yaga Sadiq cikin wannan Halin, shiyasa ko da Surayya ta kara kira ya kwantar musu da Hankalin cewa Sadiq na raye kuma jikinsa da Sauki shi yace kada su taho su bari sai gobe ko Jibi.
Su Baba Sammani ne Tunda sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login