Showing 90001 words to 93000 words out of 116366 words

Chapter 31 - Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

338

zama wahala in aka tashi nemansa anan.
Kuma ko da ya ke kokarin zuwa Duk karshen wata ya yi mata kwana uku bata gani, ita tunaninta na ba ta na fita Samun jin dadin Rayuwa.
Sannan Assadiq ya fi sona a kanta kuma ta na Tutuyar Ita a Budurwa ya aureta ni kuma ina bazawara ban Canchanci samun wannan soyayyar Daga wajensa ba.
Ko da yaushe ya tafi ya dawo cikin Damuwa ya ke da bacin rai duk da bashi ya ke fad'amin ba ni nake Fahimtar sanin ba wanda zai  bat'a masa rai bayan ita.
Ya aureta domin Cika Umarnin da Biyayyan iyayensa ammh daidai da Rana d'aya bata bari ya Huta ba.
Muna da wata uku a Abuja ta samu Hutun makaranta Lokacin cikinta ya girma watansa na bakwai.
Karshen watan da yazo tace sai ta Biyosa tazo taga waje, Alhalin ko cikin yan'uwansa Anty Surayya ce kawai da Anty Sa'ima suka zo suma wani Biki ya kawosu a kuma ranar suka koma.
Sai Anty Subai ita kuma bikin Dangin mijinta suka zo, itama waje kawai tazo ta gani sai su Asim bata kwana ba.
Ai ko sun sha Rigima domin kai Tsaye yace mata bazata bishi ba, da ta kara sakaa masa kuka ya kira Umma ya gayamata yana ikirarin gaskiya ya gaji da Halin sultana.
Umma kuma ta zo har gidan taci Mutumcinta ta kuma ce ba inda zataje ita bata duba yadda cikinta ya yi nauyi ba, sai Zalama da kishi ne a gabanta ba Fatan Allah ya Sauketa lafiya ba.
Umma ta Rusa mata Tunaninta na zuwa Abuja taga a inda na ke zaune, ammh taji alwalashin in ta haihu sai taje sai dai ayi wacce za'a yi.
Ni bansan cewa ma ta kusa haihuwa ba sai watan gaba da zai je na biyosa saboda Umma su ga yara, ni kuma na Duba Innani da jiki ya kara rikicewa ga ido ya tashi yanzu ko gani ma batayi ga gilashin ammh ya daina mata amfani.

Assadiq da Abba sun yi sun yi ta bari a koma Asibiti Innani tace ba inda zataje a jagwalgwalata gwara su kyaleta har ta Allah ta zo ta Dauketa.
Yanzu Innani tafi karfin Farida ta kula da ita Umma da Mama ke kokari suma kowacce Lokaci bayan Lokaci ta kan leka taga abunda zata taimakama Innanin da shi Tunda ko da Sandar tafiyar ma sai an kamata.
Ga kuma laluran ido mai sa mai rai ya Mutu yana Tsaye.
Ni na matsama Assadiq ya Taho damu tunda kadaici duk ya isheni in ya tafi aiki dagani sai su Asim,su kuma tunda suka fara tafiya suka zama mab'arnata nata, yini na ke yi fama da su.
Ko Umma bata san tare zamu zo ba sai dai suka ganmu kwatsam aiko gida ya Dau murna ga su Asim ga su Asim.
Shashen Umma na sauka kamar yadda na Saba, ammh sai ta saka Farida ta kwashi kayanmu ta maida bangaren Assadiq.
Umma tace Abba ya ba da Umarnin indai nazo nayi masauki a bangaren mijina.
Sultana na gidan sanda muka Iso Tunda ta ganni shikenan Annurinta ya Dauke kallo nan dagani har ya'yana da kowa ke santin su ganin sun Fara tafiya bamu isheta ba.

Nima ko wannan karon naji mganar Assadiq da yace in bata girmamani ta gaisheni ba nima bai kamata na zubar da nawa girman na bita ina gaisheta tana min wulakanci ba.
Na ganta ta kara ramewa ko ni da Cikina na fita kyen gani ta yi baki sai kuraje sai dai haka ta rika Turamin ciki gaba tana wani tale kafa ko an gayamata ban ga cikin ba ne Oho?
Siyama na gidan muka iso ita naji tana yi mata kirari da Maman Biyu.
Sai bayan mangariba Assadiq ya kwasheta zuwa gidansu.
Shashen Innani naje gaisheta na iske ta sha magani har ta kwanta daganan sai na koma Shashen Mama itama na iske bata nan suna bangaren Abba ita da Umma tare da Asim.
Sai Siyama kad'ai na gani da tace min itama yanzu megidanta zai zo ya Dauketa.
To da yake ta na kirana a waya kuma sannan mu kan yi yar Hira a chart,sai na zauna muna hiran inda muka koma ina gayamata zaman bariki ba dad'i yanzu haka wajen mu Biyar ne a Estate din mu, mu biyu ne musulmai Kafayat bayarbiya ce itama.
Saurn  duk ba addinimmu d'aya ba, ni da ya ke ba na fita ba ganinsu na ke yi ba kafayat ne ta shigo waje na sau daya muka gaisa nima na shiga wajenta sau daya.
Ita tana sona saboda su Asim sauran kuma sai dai daga nesa a daga ma juna Hannu ina gayamata na zama kamar mayya ni kadai a gida sai yara in Assadiq ya fita Office.
A bakinta nake jin Diraman Sultana kwanaki na sai ta bi Assadiq a Abuja sannan take gayamin ta gama yad'a cewa itama yan Biyu zata haifa.
Ina dariya nace"Allah ya ba ta."
Siyama tace"Tab Anty Siya wannan cikin na sultana bani da sanin gaibu ammh ina da tabbacin Daya ne aciki."
Ni dai ban ce komai ba sai dai na yi mirmishi.
Ban tambayeta ba ta fara fad'amin daman su Anty Sajida ke zugata kuma shiganta makaranta ta yi Sabbin kawaye suna Hore mata kunni.
Ni dai bakina kanin kafatana Allah ya kyauta kawai nace sai dai abun da ya bani mamaki da tace min har ita Sultana ta janye mata tunda ta samu masu bata Shawaran da ta ke so.
Ko kuma tana ganin tunda ita bata shiga jami'a ba yanzu ta wuce da saninta ni kuma sai na tambayeta me yasa bata Cigaba da karatu ba?.
Kai Tsaye tace mijinta yace ba yanzu ba.
Ni fa duk wani abunda Sultana ke yi ba na sani sai na had'u da yan'uwan Assadiq, tunda shi dai baya gayamin aiko zuwana naji mganganu kala kala na mganar kayan haihuwa tace ma Anty Surayya wanda zata siya mata yafi nawa Tsada sannan kuma ita yan Biyu zata haifa duka maza Saboda haka kayan jarirai na Guda biyu za'a siya.
Da Surayya tace mata a takardan Scan ance yan Biyu ne? Shikenan tace wai ta karyata ta, tunda Sultana ta fara zuwa awo kuma ba wanda ya taba ma ganin Takardan Scan din nata waya sani ko Assadiq din ya gani.
Karshe dai Anty Surayya ta tattara kudin siyayya ta mikama Sultana tace ta siya da kanta shine Ta kira Sajida suka shiga kasuwa tare suka siyo abunda suke so.
Da Assadiq yaji yace a kyaleta tayi duk abunda taga yafi yi mata daidai.
Anty Surayya ta ke gayamin da ta zo gidan muka shige shashen Assadiq in da na sauka muna mgana.
Da yake akwai shakuwa sosai Tsakanina da Surayya muna hiran da ya shafe su sosai tace ai yanzu na Riga na zama SS Shinkafi.

Kwana uku muka yi ranar Litini da Safe muka koma Abuja, sai kuma Bikin Tahir da shima saura wata Biyu har Abuja yazo ya ga inda muke.
Tunda Taron siyasa ya shigo da shi garin Ranar har wajen 12 na dare suna falo da Assadiq suna hiran su.
Yanzu Tsakanina da Tahir sai gaisuwan mutumci da girmamawa.
Mutanen Zariya kuma sai dai mu yi magana ta waya.
Hankalin Amma a kwance tunda ta na da tabbacin ina zaune lafiya da mijina tare da kyakyawan Rayuwa ni da ya'yana.
Bikin Tahir ya matso kuma Assadiq ya gayamin kila Sultana sai ta haihu kafin a yi bikin Tahir, ni kuma a raina sai nake fatan Sultana ta riga haihuwa in muka tafi gusau daga can muka tafi katsina Biki.
Tunda Ankon bikin ma ta hannun Amaryan Assadiq ya siyamin, Tahir ya bata lambata ta kirani na fad'a mata masearuement dina.
Shikenan sai muka fara gaisawa ta Chart, ta na tambayansu Asim tunda tace Tahir na Tura mata Hotonansu.
Hauwa'u Amarya ta gayama Angonta Katsina zan zo wajenta Biki, sai dai na bari in za'a kawota Daura na Biyota tunda anan babban gidansu za'a yi walima sai ta kwana Biyu sannan Mijinta ya dauketa su koma Katsina.

Assadiq yazo yana gayamin nace masa shikenan nima tamin mgamar nace sai abunda Mijin Siya yace.
Shi kuma yace mijin siya ya ba ta dama ta fara sauka katsina a sha Biki lafiya.
Ana saura Sati Biyu Bikin Tahir Sultana ta Sauka an samu mace, na ci Dariya Sanda Siyama ta kirani ta bani Labarin abunda ya faru a asibiti Lokacin da Sultana za ta haihu.
Tun naguda bata kankama ba ta kwanta ta na Raki Umma da Mama suka kwasheta sai asibiti.
Suna zuwa ta rika ce ma likita ita yan Biyu ne acikinta bazata iya haihuwa da kanta ba sai an yi mata C.S.
Likita ya fito yana gayama su Umma su Daya suka gani acikinta.
Sannan Mahaifarta ma bata Bud'e ba kuma zata iya haihuwa da kanta ammh tana fadin ayi mata aiki yan Biyu zata haifa.
Kuma Nurses sun sha Fama da ita a dakin haihuwa ta ki bude kafa ballatana su yi aikinsu ai ta dauka Haihuwan wasa ne sai da ta ganta zahiran ta gane bata da wayau bakinta ya Mutu.
Tana gayamin Umma na ta fad'a tana fad'in bata tab'a sanin sultana mahaukaciya ba ce sai ranar, Ita a tunaninta C.S din wani kayan gabas ne, ko kuma Haihuwan wani cin Tuwo ne ai da ta haihuwa sai bakinta ya yi murus sai ido ga shi ta karu ta sha Dinkin adadin kuka da Ihun da Sultana ta yi bai da iyaka.
Assadiq ko ya sha Allah ya isa yafi cikin kwando.
Tun ballatana da ta farka taga bai zo ba harda kukanta da ya kirata ta fara mai korafin bai zo ya ganta ba Alhalin ya gama kunsa mata wahala ta kusa mutuwa.
Ammh nan da matarsa zata Haihu bashi da ko lafiya a haka yaje ya ganta, ita ko tunda bata da matsayi bai zo ya ganta ba ballatana yaga abunda ta haifa.

Shi dai hakuri ya bata Tunda Talata ne ta Haihu da safe kuma ranar aiki ne shiyasa yace sai Ranar jumma'a zai taho gabadaya tare da Siya.
Sannan can gida ne kowa na tare da ita kuma suna waya da Umma yana jin Halin da ake ciki a ganinsa zuwansa kuma sai ya ke ganin kamar raina kokarin Su Umma ne.
Ita ko daman ga rashin haihuwan yan Biyu sannan ga shi ta Haifi mace gani ta ke yi kamar Darajanta ya sauka.
Hasiya tafi ta har yanzu, kiri kiri taki bama yarinyar Nono wai zafi take ji sai da Umma ta fita yamma da Hankalinta sannan ta fara bata Nono ta na yi ta na kuka.
Kwanan su Biyu a asibiti aka sallamota zuwa gida Bangaren Umma ne tunda itace uwa Dakin ta na baya tun na yanmatanci nan aka gyara mata zata yi zaman jego.
Ko'ina kuma an sanar da Haihuwarta Mutanen shinkafi dai nata mamaki jin ance mace ta haifa kuma ba yan Biyu ba.
Da kuma an ce Sultana ya muka ga D'aya ba Biyu ba? Sai ta fashe da kuka kamar wacce aka yi ma duka.
Tunda kuma ta haihu ta yi ta Turen turen baki ita a dole Assadiq bai Dauketa da Muhimmanci ba.
Ta yi ta kiranshi tana yi masa korafi shi wlh har fama ya ke yi da Fad'uwan gaba in yaga kiran Sultana saboda yasan matsalace da korafi da ba'a yi mata daidai ba.
Tun kafin mu taho na saka Siyama ta turamin Lambarta na kirata domin na yi mata barka.
Inaga ta gane muryata ne cikin Gadara tace"Wa ke mgana?
Ni kuma kai Tsaye nace  mata"Hasiya ce an sauka lafiya?
Kawai sai ta yi tsaki ta kashe wayar na yi ta mamaki daga aabun arziki.
Daganan ban kara kiranta ba sai itace ta kara kirana na dauka ma bata ganeni ba ne daga farko.
Ina dauka ta fara fad'amin mganganun banza wai na hana Assadiq zuwa ya gansu to na sani ban isa na shiga tsskaninta da Mijinta ba.
Har zagina ta yi tana kirana Annoba kuma bazawara.
Ni na gaji da jinta na kashe wayata ta yi ta kira ban dauka ba sai Sako ta Test massages har da wai kada na yi tunanin na haifi maza na cinye gida itama zata haifi nata na zura ido na yi kallo.
Abun nata ma sai ya koma min kamar bata da Tunani yarinyar nan gaskiyar Umma ne mahaukaciya ce.
Ko Assadiq ban gayama ba, na dai ce masa na kira sultana na yi mata barka kuma naga yaji dadin haka.
Su Umma daman tun ranar da aka yi haihuwan na kira su na yi musu barka hadda Abba.
Shirin gabadaya ni na yi tare da yara Tunda daganan katsina zan wuce bikin Tahir shi kuma zai dawo Abuja daga Abuja zai zo katsina Saboda ya Samu Daurin aure.
Ranar jumma'a da yamma muka iso Gusau.

Yara tun a haraban gidan muka Rabu da su to ya'yan dangi ne fa Tare da Assadiq muka fara shiga wajen Abba muka gaisa sai Bangaren Innani.
Allah sarki yau jikin da dana ma, ta na kwance sai dai bakin ne yau ya Bude har suka yi ta hira da magajin gida.
Ni nan na barshi na tafi zuwa bangaren Umma kayanmu kuma an shiga da su shashen Assadiq.
Ko da na shiga shashen Umma cike da baki masu barka.
Anan naga su Anty Sakeena ita kadai ta tarbeni, Sai Umma da tun a haraba muka had'u muka gaisa.
Dakin mejego kuma cike da kawayemta yan makaranta da su Sajida da Sadiya.
Sakeena ta rakani na shiga domin na yi mata barka ammh ina gaishe su ba wacce ta amsa sai kallon banza.
Itama Sultanan kai ta kauda ta na mgana da wata a kusa da ita.
Ni dai naga suna nuna ni suna Dariya suna kuskus kasa kasa.
Sakeena ce ta kalli Sultana kafin tace"Sultana baki ji Hasiya na miki barka da sauka ba ne?
Baki ta tabe kafin tace"Ban ji ba yauwa.!
Daga haka ta cigaba da mganarta ina Tsaye ina yake sakeena ta isa kusa da Sajida ta na fadin"Sajida bani jaririyar Hasiya ta ganta."
Kamar ta watsa mata kankara haka ta mike a firgice ta na fad'in"Wata jaririyar? Wannan?
Ta fad'a ta na nuna jaririyar da ke cikin kayan sanyi a gefen uwarta.
Sultana ta yi caraf ta dauke yarta ta na Fadin"A'a kada a goga ma yata Mugun Jini."
Sadiya ta karbe da fadin"Wlh kuwa gwara ki yi can haka da ita, kada yanzu kajin Tsiya da bala'i su fara Bibiyanta"
Gabadaya sai naji na muzanta idanuwana suka tara kwallah ammh sai na Shanye.
Sakeena ce tace"Haba don Allah, daga abun arziki kuma miye ya kawo wannan mganar?
Sajida tace"Wani abun arziki waya san abunda ta kunso a hannunta tunda ba Allah a ranta? Kawai ta Dauki yarinya ta goga mata wani abun tsiya, tunda ita dai Bakar Annoba ce Tsiya tsiya jinin bala'i da Farar kafa. Tsiya nan ta ganta ta barta ke ai ganin ki bala'i ne da masifa in da kuma kika shiga kika zauna shima bala'in ki zai iya fad'ama waje, gwara ki koma inda kika fito barka ne ko? To mungode Allah ya ba da lada ammh a kara gaba, ban da munafunci miye na Biyo miji barkan kishiya? Zugwai zugwai ko kunya baki ji ba."
Ta ke fad'a ta na nuna min hanyar  fita, kaina na kasa ina kokarin yaki da kaina ba na so na yi kuka su gani sai kawai na yi mirmishi na juya.
Sakeena na bari ta na yi musu mgana sai abun ya koma kanta itama..na fita falon Umma ba na gani Saboda Duhu ya mamaye ganina da kuka da ya taso min hawaye sun fara zubarmin.
Na ci karo da Sa'ima ma ban sani ba tana min mgana ban Tsaya ba, da gudu na tafi bangarena ina kuka.
Bansan cewa fad'a ya hautsine tsakanin Sakeena da Sajida ba Sai da Anty sa'ima ta shiga tsakaninsu.
Kuma a gaban kawayen sultana to ai suma su san komai tunda ta gayamusu komai.
Mgana ta kai kunnen Umma da Abba har da Assadiq da baya nan yaje gida ya yi wanka.
Anty Surayya ta kirasa tace itama Sa'im ta kirata ta na fad'a mata Sajida ta zazzagi Hasiya.

Ya zo gida nan ransa a bace ya so ya ga Sajida ta raina kanta sai kuma ya yi rashin sa'a Abba ya yi ma ta fata fata shima yace in dai ba alheri ke kawo ta ba  kada ta kara zuwa..nima yazo yaga na warware tunda Umma ta bi ni ta yi ta bani hakuri har da Abba ma nace musu komai ya wuce.
Fadan Assadiq a kan Sultana ya sauke ya yi mata Tas yace kuma ba Hasiya ta Tozarta ba shi ta tozarta kuma ya gode ta yi duk abunda zata yi lokacinta ya kusa karewa.
Haka ta dinga kuka tana fadin na yi mata sharri, ita ko baki bata saka ba sannan itace fa ta haihu duk wahalan da ta sha bai Tausayamata ba sai kawai ya kamata da fad'a.
Abunda su ka yi min ko kadan ban sakashi a raina ba tunda ai ba wannan ne na farko abunda na gani ba.
Tozarci ba irin wanda ban gani ba, Shiyasa na maida komai ba komai ba tare dani ake yi ma sultana Hidima.
Yarinya taci sunan Umma Wato Salamatu.
Anyi taron suna Ranar talata ammh bai yi wani armashi ba.
Maijego fuska ta kumbura da kuka Saboda angon karnin yaki siya mata Zinare.
A bakin su Sakeena na rika jin mganar ranar suna, ni kaina da ba Assadiq ba na fara gajiya da Sultana daga wannan sai wannan.
Wai kuma wani iskanci da ta dauko D'an kunnen zinare zai si ya mata taci suna da shi a matsayin Kyautar Haihuwan da ta yi masa.
Shi kuma yace ba shi da kudi akwai bikin Tahir sannan zirga zirgan kai da kawo mai na cinye masa kudi ya kawo mata mganar hidima ta yi masa yawa ga nawa da na yara sannan shi ya ke rike da Hidimar Innani.
Saboda dai shima yau ace yana da amfani a gidan su.
Ammh Sultana taki jin Lallashi tace sai ya siya mata shi kuma yace bazai siya mata ba.
Shikenan ta ke kuka Ranar sunan yarta ta yini ba walwala.

Ni abunda ke bani mamaki gasa take yi dani, taga zoben zinare a hannuna ni kuma Kud'aden da na samu da haihuwan yan Biyu ne da kuma kudin da na ke tarawa a hannuna.
Karami ne ma na dubu 230k na siya Adda Rukayya ta bani shawaran na siya saboda kaddara kuma da na bar kudin duk sai na kashe su, sannan kuma ban siya ba sai da na Nemi izinin Assadiq yace yana da kyau hakan.
Nasan kuma ita tunaninta Wlh Assadiq ya siyamin shine zata saka Rigiman itama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login