Showing 96001 words to 99000 words out of 116366 words
mgana ina da inda zan je da ya wuce gidan Yaya Sadiq na Abuja."
Umma ta gyad'a kai kafin tace"Na sha'afa ne, Allah ya kai ku lafiya."
Ta amsa da Ameen sai ta fara yi ma Umma korafin Sadiq wajen wata daya da sati bai zo ya gansu ita da Ummi ba tun bayan suna da ya tafi.
Cikin Kishi tace"Umma don ina adalci anan, sai kuma yazo ya yi kwana Biyu yace zai koma sai mutum ya yi mgana aga laifinsa."
Umma na zaune kala bata ce mata ba har tagama mganganumta.
Ummi ce ta tashi ta kuma fara kananun Rigima yasa Umma ta sauko mata yarta ta bata.
Ita kuma tace bari ta shiga bangaren Innani ta dubata.
Kai Tsaye Sultana tace"Allah Sarki Innani, ki gaisheta jiya ma ban shiga na gaisheta ba."
Umma ta harareta kafin tace"ni ce yar aiken ki? In ko da Amana bai kamata Ruwa ya Dafa kifi ba, ace kina gida nan ki yini baki iya leka innani acikin gidan nan ba."
Sultana ta tura bakinta gaba kafin tace"Umma ban samu lokaci ga makaranta ga kula da Ummi."
Umma ta kalleta ta watsar ta yi ficewarta ta bar sultana ta kunkuni ita ya zata yi? Ko dame ake so taji.
Ba sosai yanzu ta ke zuwa bangaren Innani ba tunda ta fara rashin lafiya sai taga dama.
Kuma in ta shiga a tsaye ko zama bata yi, Ita kanta Innanin ta san cewa Sultana ta sauya ita saboda ta kanta ta ke yi bata cika ma damuwa da ita ba.
Washegari da Safe Umma tace Sajida ta dauki Farida su je gidan sultana su gyara mata gobe jumma'a zata koma gidanta.
Sajida ta kalli Umma cikin mamaki kafin tace"Umma ni kuma?
Umma tace"To da wa zan saka? Ku tafi da wuri saboda ku samu ku gama gyaran akan lokaci."
Sajida tace"Umma idda fa na ke yi? Kuma a musulunci ni matar Yusuf ne har yanzu"
Umma tace"Kaniyarki da Iddan, ina saka ki aiki kina cemin kina Idda ne, in matarsa kike me ya zaunar da ke a gabana! Da sai ki zauna gidan Yusuf din ki gama Iddar taki."
Ranar Sajida da kuka ta fita, Sultana na daki ta na jinsu ta na dariya.
Lokacin ma tana waya da kanwarta ne mai bi mata.
Tana fad'a musu zata zo in Yaya Sadiq ya zo ya koma zata zo ta yi sati a shinkafi.
Sajida ba ta da mafita dole ta yi abunda Umma ta sakata.
A gidan Sultana ita da Farida sun ci aiki Tunda gidan ya ji ma kulle duk ya yi kura.
Suna cikin aikin Sadiya ta kirata tace gata nan tazo gida Umma tace ta na gidan Sultana suna gyara.
Sajida tace"Sadiya kinga yadda Rayuwa ta yi dani ko? Na zama yar aikin Sultana ina yayar mijinta na koma kamar kanwar mijinta."
Sadiya tace"Tabdijam, Allah ya kyauta."
Da Sajidan tace Sadiyan ta zo nan gidan su had'u sai ma ta tayasu sai tace megidanta ya yi tafiya daga kasuwa ta biyo gidan Umma gida zata koma zata yi masa girkin Tarba.
Kiri kiri Sadiya ta wucewarta gida kuma Umma ma da ta yi mata mgana haka tace mata.
Sultana kuma Saloon taje bayan ta dawo ta biya gidan kawarta ita ta rakata gidan kumshi aka yi mata.
Sai Yamma Sajida ta dawo sun gaji ita da Farida.
Suna dawowa ba dad'ewa Sultana ta Dawo Umma na ta fad'an ta yi dare ga jaririya a bayanta.
Kai Tsaye tace"Umma kunshi fa naje, haka zan koma jiki fari."
Umma ba ta yi mgana ba Sajida ma da idar da sallah bata tanka mata ba.
Umma taso ta tusa ma Ummi sai taga ta tashi tace zata shiga wajen Innani daganan ta wuce shashen Abba.
Mama bata nan suna kano bikin diyar kanwarta bangarenta kulle ya ke ba kowa.
Kawai sai ta isa gaban Sajida ta mika mata ta na fad'in"Anty Sajida ga yarki, ban yi sallar azahar ba ballatana mangariba."
Ko kallonta Sajida bata yi ta mike lokaci daya ta na fad'in"Salla zan yi, kin ji an fara kiran sallar isha'i."
Daga haka ta kabbarta salla tabar Sultana tsaye rike da yarta.
Ai ko ta gane bata da wayau domin Sajida na gama sallah ta mike ta shige ciki gashi taki yin shuru sai kuka ta ke yi damam kuma sultana bata saba ba, ta saba Umma ke mata reno ko Sajida yau kuma ba ko d'aya.
Duk ta yi wani yarkace yarkace da ita, A fusace ta shiga dakin ta iske Sajida kwance ta na Buga game a wayarta.
Kusa da ita ta tsaya ta na fadin"Gaskiya Anty Sajida baki da imani, kina jin yarinyar nan na kuka ammh kin kasa zuwa amsheta ki lallasheta sallah fa nace miki zan yi gashi har an yi isha'i."
Sajida ta dago cikin mamaki ta na kallon Sultana kafin tace"Ke ni sa'ar ki ce? Ko don kinga ina rage miki wahala shine zaki maidani kamar wata baiwarki? Yau din ma aikin Uban wa naje na yi ba naki ba?
Gabadaya jikina ciwo ya ke yi gidan nan naki bayan kura harda tsohon dattin kazantar da kika saba, nagaji ba daukarta da zan yi gwara tun wuri ki goya yarki ki kama Hidimarki kin ji ma na gayamiki."
Ta fad'a na juya mata baya Sultana ta kalleta rai bace kafin taja tsaki ta wuce.
Sajida ta mike ta na fad"in"Kan bu, Sultana ni ki ke ma tsaki?.
Sultana ta fice daga dakin tana fad'in"To haka kurun me kike yi? Daga nace ki taimake ni ki rikemin yarinya sai ki fara zagina, ni nace a sake ki da zaki wani Huce a kaina."
Sajida mamaki ya sandar da ita a zaune ta ciji yatsa sannan ta girgiza kaj lalle yarinyar nan bata santa ba ne sai ko ta gyara mata zama.
Kanwar dai naki dole Sultana ta goya yarta ta yi sallolin da ke kanta.
Sajida barcinta tayi bata san shigowar Sultana ba cikin dare Ummi na ta tsala kuka tana jin Sultanan na kiran sunanta ta yi mata banza
Acikin ranta tace shegiyar yarinya mara Mutumci.
Washegari tun safe Umma tace Sultana ta shirya ta maida ta gidanta Anty Surayya ta zo, Sajida kamar an matsi bakinta ta kwashe rashin kunyar da Sultana ta yi mata ta gayamata.
Surayya ta kama baki kafin tace"Ita sultanan?
Sajida tace"Wlh ita fa Big sis ai bata da kunya shegiya da kauye ta girma da naga karyan tsiya ni ce zata rika sakawa aiki kamar ta samu wata jaka?
Surayya ta yi dariya bata ce komai ba sai dai ta bama Sajida Hakuri tace ta kama girmanta zata yi ma Sultanan fad'a.
Koda suka tashi tafiya Sajida kin zuwa ta yi, zamanta ta yi a gida daman kuma Yusuf ta ke yi ma nacin don Allah yazo su hadu ita ta bashi Hakuri ya maidata dakinta kafin ta gama Idda tagaji da wannan bala'in yarinya karama ta fara raina mata wayau.
Ta tuna kwanaki har sata ta kulla mata wai an sace mata 1k acikin jaka to waya sace ita ko? Tunda su biyu ne acikin dakin.
Abba shi ya ba da kudi aka yi ma Sultana duk cefanem da ta ke Bukata, Umma da Anty Surayya ba su dade ba suka barota Bayan Surayya ta ce ta tashi ta yi girki domin tarban mijinta Tunda ya taso yace yana Hanya.
Suna fita ta koma ta kwanta ta na bama yarta Nono ta na kuma Chart.
Ita fa bazata iya ba ta na zuwa shinkafi zata Dauki Naja kanwarta ta so ta rika taimakamata.
Sadiq kuma da yamma ya iso gida ya fara Sauka sai a lokacin suka had'u da Sajida.
Kallon kallon suka yi ma juna afalon Umma kowa ya dauke kai.
Sai shine ya kalleta kai tsaye kafin yace"Sannu Sajida ashe kuma abunda ya faru kenan? Allah sarki zawarci ba dad'i ga shi daman kin tsani bazawara."
Sajida ta kallesa ta san mgana ya gayamata, kuma ba laifinsa ba ne da kunya ma ta maida masa martani.
Kasa mgana ta yi kanta na kasa tana Tunanin zama bai ganta ba.
Umma ke tambayan su Hasiya da yara sai ya ke fad'a mata suna Zariya taje karbo Result dinta daganan zata je can garin da Mahaifiyarsu ta ke ta Dubata.
Umma na zaune tace"Allah sarki, kwana Biyu bamu yi waya ba, ba na samun zama sosai Ga Innani ga Kuma Mama bata nan sun je biki."
Sadiq yace"Umma jikin Innani na kara Rikicewa? Yanzu fa na shiga ta na dai kwance ammh ba wannan kuzarin da karfin jikin nata irin na baya?
Umma tace"Ai innani jikin girma ya kwanta Sadiq, yanzu fa komai fa sai an yi mata jikin ya riga ya gama saki gabadaya."
Sadiq yace"Umma zan yi mgana da Abba za'a siya mata keken da zata rika zama a kanta ammh kwanciyar nan ai bata da dad'i."
Umma ta yi na'am da shawaransa sosai shiyasa yace zai tafi gidansa da Daddare zai dawo su yi mgana da Abba.
Yana fita gidan ni ya kirani yana fad'amin ya sauka lafiya.
Ni kuma lokacin ina gidan Adda Fati kwanan mu Biyu da zuwa ni da su Asim.
Sai na gama cuku cikun karb'an Result sannan zan karisa wajen Amma.
Shi ya ke fad'amin Umma na Cigiyata sai naji kunya nima kwana Biyu ban nemeta ba.
Muna gama waya dashi na kirata muka gaisa har na bata su Asim da suka fara mgana Umma rad'am a bakinsu.
Bayan nan mun yi mganar jikin Innani da ita, Innani na ran Assadiq koda yaushe sai ya yi mganarta har ce min ya yi ba domin kada Abba yace ya Dauke masa uwa ba da ya kawomin Innani wajena saboda gani ya ke a gabansa za'a fi kula da ita sosai.
Sai na koma ina gayama Adda Fati yanayin jikin innani, tunda gidanta na sauka ban je gidana ba.
Cikin Tausayawa tace"Allah sarki Allah ya tashi kafadanta, ni ko ina ita abokiyar zaman taki ta yi arba'in ko?
Kai Tsaye nace"Eh sun gama wanka naji Assadiq na mganar."
Adda Fati tace"Har yanzu baku da daidaita a tsakanin ku?
Nace"Babu kam,"
Adda Fati tace"Ki kyaleta ki dai ki yi mata zaman da musulunci yace."
Cikin mirmishi nace"To ni miye nawa? Da ba waje daya muke zaune ba."
Adda tace"Shikenan ma kowa ya Huta."
Mun cigaba da Hirarmu ina ba ta Labarin yadda sultana ta min wulakanci sanda na kira na yi mata barka.
Ammh ban bata labarin abunda ya Faru sanda muka je gusau ba, ko bakomai akwai sirrin da zan Boye musu saboda bansan me gaba zata Haifar ba.
***
Wannan karon dai Sultana ta yi abun arziki ba korafi da Rashin kunya sai ga Assadiq da yin kwanaki Biyar sannan ya biya ta Zariya ya Dauki siya da yara suka koma Abuja.
Kuma Sultana ta nemi izinin zuwa shinkafi yace taje ta ga yan'uwanta da iyayenta jin dadinta ma ya bata kudi masu tsoka a hannunta.
Yana tafiya ta fara shirin zuwa Shinkafi Umma ma ta yi mata Shiri sosai Abba ya ba da Motarsa Direba ya kaita tare da kayan abincin da zata kaima iyayenta.
Sati cur Sultana ta yi a shinkafi an samu ta leka gidajen su Baba Sammani ta kai musu Ummi ta kuma gaishe su.
Taji dadin zama acan tunda ba ta wani Wahala ga kannenta na tayata Renon Ummi daga barci sai chart kadai ta ke yi,
Da ta tashi dawowa motar Haya ta shigo ta dawo kuma tare da kanwarta Naja da ta gama Jssce zata shiga SS.
Mallam bai amince ba sai da ya kira Sadiq suka yi mgana. shi daman tace saboda zata rika taimakonta da Ummi ne ga makaranta da aikin gida.
Kuma ganin kanwarta ne yasa ya amince.
Sai dai Umma ta ganta da yarinya, Ba ta ce don me ba? Sanin halin Sultana yasa Umma bata ce komai ba.
Gidanta ta koma tunda da Farko Sultana taso ta kara shantakewa a gidan Umma ita kuma nace bata isa ba, in tsoro take ji ga Naja nan sannan zata rika taimaka mata.
Dole ta koma gidanta ammh kuma duk Ranar da tazo sai sun yi tanka tanka da Sajida.
Da yanzu duniya ta gama yi mata zafi kiris ya rage ta gama idarta shuru ba Yusuf.
Kwanaki ma taji an ce aure Mahafiyarsa zata yi masa gashi ya hana ta ganin ya'yanta kamar ma daga baya blooking dinta yusuf din ya yi.
Ta fara nadaman Hallayanta Tunda su su suka kaita suka barota.
Biyar yanzu ya fara gagaranta Sadiyan da suka fi shakuwa bata bata ko sisi, Big sis ne kuma ta ke da tabbacin zata bata kudi ammh kunya bazai barta ta yi mata mgana ba.
Ko Anty subai ta kasa kira tasan da ba domin ta sire a idanuwan Sadiq ba tana da tabbacin wlh shi zai kira Yusuf ya yi kokarin daidata su kuma bazata shiga talauci haka ba.
To ko'ina ta bat'a garinta da Kunya a ga ta koma ta na yar murya
Siyama kuma sun tafi lagos yawon Bude ido ita da mijinta.
Abubuwa goma da ashirin sun yi mata yawa da ta rasa yadda zata yi.
*******
Bayan wata daya, tuni Sajida ta fita Idarta yanzu ba matar Yusuf bace ita.
Abunda ta ke tunanin bazai Faru ba sai gashi ya faru ta na cikin Layin zawarawa.
Ta yi kuka kamar ranta zai fita ba mafita karshenta ma ranar da ta fita Idda aka Daura ma Yusuf aure da Budurwa yarinya karama
Sakeena ta kirata ta na fad'a mata kamar Zuciyarta zata Buga haka take ji.
Abba kuma yace abunda ta zab'ar ma kanta kenan Allah ya ba da sa'a.
Umma ma tace shiyasa akace zaman lafiya ai yafi zama dan sarki.
Saboda Halin da ta ke ciki yasa ta koma ta na zuwa gidan Sultana ta yini, ko da ba ta nan ta na makaranta ita da Naja ita ke zama a gidan ta na yi mata girki..saboda acan Umma bata sakar mata Fuska kwata kwata bata jin d adin zaman gidan.
Ga shi Sultana ta yi ta mata wukalanci da gadara ita mai gida duk ta shanye.
A watan da Sadiq yazo ya iske Sajida a gidansa sai da ya yi mamaki.
Sai yaji kuma ta bashi Tausayi Kuma wannan ai ba girma ba be ki koma kina bin matar kaninki.
Shiyasa da kansa ya samu Umma ya yi mata mgana.
Ya lallasheta da Kaddara ne bawa bai isa ya sauya ta ba.
Yace Sajida ta koma gida ta zauna gaban Umma ya kuma Dauki kudi 10k ya bata tare da ce mata in tana Bukatar wani abu ta kirashi.
Naka naka ne, duk abunda Sajida ta yi masa yayarsa ce kuma shi ba Murna ya yi da Farko ba.
Yaji dad'in yadda Allah ya nuna mata Ishara ammh bai taba Tunanin Yusuf zai rabu da Sajida haka ba ya Dauka na gargad'i ne daga baya zai maidata.
Shi kanshi yaji mata rashin dadi sosai.
Sai ga Sajida na kuka a gaban Sadiq kunyar duniya duk ya kamata.
Ko sadiyan da suke had'a waje tare da ita ba ta tsinana mata komai ba.
Kowacce na gidanta ta rike aurenta ita kuma ta na zawarcin da ta ke ganin kamar da gangan ne in mace ta zama bazawara ko auranta ya Mutu.
A baya tana ganin abun Fahari ne A gareta tana ganin Hasiya kamar wata ba mace ba tunda Sadiq ya aureta a matsayin bazawara.
Tafiyar Sadiq a satin Sajida ta kusa yi ma Sultana dukan tsiya.
Wata ranar laraba ne sultana ta dawo makaranta sai ta Biyo nan gida.
Daman nan take sauke gajiyanta.
Umma bata nan ta na shashen Innani ita da Mama.
Sajida ne kadai a falon Umma ta na zaune tana gyaran kumbunanta na kafa.
Da farko da ta shigo sun gaisa har ta Dauki Ummi hannun Naja.
Ita kuma taje ta zubo musu abinci ruwa ne tace Naja ta shiga kitchen ta Dauko musu.
Bayan la'asar haka sai aka yi baki Siyama tazo da yan'uwan mijinta su gaida su Umma da Innani.
Daga bangaren Mama suka zo bangaren Umma.
Ga mama ga Umma a wajen, wata cikin yayar Baban Mijin Siyama suke gaisawa da Sajida.
Kamar an Tambayi Sultana ta yi karaf tace musu"Anty Sajida ce bazawarar gidan mu ba."
Gabadaya sau aka bita da kallo bata damu ba ta cigaba da fad'in"Yanzu shikenan kiri kiri Abban su Amal ya ki maida ke dakin ki? Gaskiya bai kyauta miki ba yasa kin zama bazaawara Anty Sajida ni kuma kunsan na tsani zawarawa yawancin su Yan bariki ne masu kwacen mazajen wasu."
Umma kunya duk ya kamata Sajida kuma sai da taji ba ta taba muzanta irin na ranar ba.
Matar ko cikin Tausayawa tace"Allah sarki, ai ba yin kanta ba ne shi kuma sha'anin aure ai na Allah ne, sai kiga kuma an daidaita a gaba.
Kuma da kike mganar zawarawa yan bariki ne ni na kulubance ki ta wannan bangaran ba haka ba ne, duk wacce kika ga ta zama bazawara ba yin kanta ba ne kaddarace ta fad'a mana, kamar ni anan mutuwa ce sila wata kuma zaki ga sakin na kaddara ne ba macen da zata so ta zama bazaawara da son ranta karya ne wannan burin kowace mace ta zauna a gidan mijinta lafiya lau, saboda haka zawarci ba aibu ba ne sannan ki sani kaddara ce ke maida mace hakan."
Umma da Mama har suna had'a bakin fad'in"Hakane wlh."
Matar ta cigaba da fad'in"Kuma mganar zawarawa duk yan bariki ne wannan karya ne, ke yarinya ce karama daga ganin ki baki san rayuwa ba har yanzu, ni nan shekaran mijina Goma sha hudu da Rasuwa ban yi aure ba, to ina zani gani da ya'ya mata a gaba na? Sannan ba wai bam samu maneman ba ne na samu kawai ban yi ra'ayin auren ba ne kuma Alhamdulillah na tsare kaina sannan na tsare mutumcin ya'yana ba Kasawa bace domin an saki mace ba, Kaddara ne ta Ubangiji da in yace kun yafakum ba wanda ya isa ya dakatar da hakan, sannan domin bazawara ta sake wani auren ba kwacen miji ba ne cika sunar ma'aiki da kuma kare kanta daga zargin mutane ko fad'awa halaka, sannan ki sani itama bazawara mutum ce kamar kowa kuma Cikakkiyar mace maj yanci kamar yadda Budurwa ke da yanci.
Ba Inda Allah ya ware budurwa da bazawara duka sunansu mata, kuma suma sun canchanta su samu farinciki wasu zaki ga sanadin hatsarin mota suka rasa mazajensu! Wasu kuma sanadin mutuwar Fuju'a wasu kuma sanadin Boko haram, wasu kuma sanadin Sakin aure da In Allah ya kaddaro ma mace ba ta da yarda zata yi, ya kamata ki daina Dariyan kaddaran zawarcin wata macen saboda ke ma macece kuma hakan ba abun mamaki ba ne in ke ma ya faru da ke watarana."
Sultana duk sai ta raina kanta Sajida ko hawaye wani na bin wani a kan Fuskata cikin kuka tace"Wlh