Showing 66001 words to 69000 words out of 116366 words
kawo kararta ta yi masa wani abu.
Shi kuma akace ya yi adalci sannan ya san cewa Sultana Amanqce a wajensa in yaci Amanarta Allah na kallonsa.
Cikin Tattausan lafazi ya kalli Umma kafin yace"Umma ni dai kinsan bani da matsala, diyarki ce ta ke da matsala ki gayamata rashin kunyar da ta koya daga baya bazan dauka ba, in tace bazata bari ba zamu yi ta samun matsala ne Umma."
Da Sauri Umma tace"Kin ji ko? Ke sultana bashi hakuri."
Ta fad'a ta na Hararan Sultana wacce ta sunkuyar da kanta Cikin yaukin baki tace"Kayi hakuri."
Jinjina kai ya yi kafin yace"Na yi hakuri, sai mgana ta gaba Bazan lamunci ta rika aibatamin matata ba, in ita bata san darajan ta ba, ni na sani kuma ni zan zauna da su bisa Amana ne, kamar yadda bazan lamunci ita Siya ta aibatata ba, haka itama bazan taba bari ta aibatata ba."
Umma ta jinjina kai kafin tace"Hakane, Sultana ki gyara don Allah? Ku zauna lafiya da junan ku tare da hakuri da juna."
Kafin ta tafi sai da ta tabbatar da ta daidaita abunda ita ta yi silar lalacewarsa da kanta.
Sadiq ya rakata har bakin Titi ta hau mashi zuwa gida Abba yaso ya Dauko mota Shi kuma yace sai yaje yaga likita ko zai fara amfani da Mota da kafarsa.
Silar Umma yasa Sadiq ya Sauko ammh sai da Sultana ta kara sauke kai ta bashi Hakuri sannan ya hakura.
Shi namiji ne da mace ta zame masa ginshiki kuma ya dad'e baya tare da mace shiyasa bai gwasale kokarin Sultana ba, bayan kuma tana da hakki a kansa da shima ya sauke shi a wannan Daran.
Ita kuma abunda ke ranta itama ta yi tayi, ta samu ciki ta Haihu domin ta fi Hasiya samun matsayi a wajen Yaya Sadiq.
Da kuma kissanta yasa har washegari bai fita ko'ina ba yana tare da Sultana sannan har yinin ranar bai kira Siya ba sai da ya fita sallar mangariba ya samu ya kirata suka yi mgana tace suna gida sun dawo tun da Rana ita da Inna talatu.
Washegari kuma Big sis ta kirasa tace Umma ta kirata tun a jiya tace ta shirya zata rakata Zariya wajen Hasiya ta yi mata barka.
Har acikin ransa yaji dadi da yaso yaje ammh ganin zai koma ganin likita yasa yace bari ya had'a gabadaya.
Umma da Surayya suka tafi Zariya direban Abba kuma ya tukasu.
Daman kuma Surayya sun yi mgana da Hasiya tace mata ta koma dakinta nan suka wuce kai Tsaye.
********
Tun kafin Anty Surayya ta kirani ta gayamin Umma na tafe Assadiq ya gayamin shiyasa na gayama Inna Talatu, Habiba tare da ita muka taho ita ta tashi ta dora girki.
Wajajen azahar suka iso na yi wanka na Lokacin su Asim ma sun sha gayunsu suna tashin kamshi.
Sai a ranar na taba gaida Umma ta amsa min cikin sakewa kad'an duk da bata washe min baki ba.
Anty Surayya ta kwashi yaran ta zube mata a jikinta.
Sai ga Umma ta kura musu ido ta na kallonsu, duk yadda ta so kada yaran su yi tasiri a ranta sai da suka yi.
Farat d'aya taji sun bala'in Burgeta sun shiga cikin ranta da wani kauna.
Tana kallonsu idanuwanta suka kawo kwallah ta kalli Surayya lokaci d'aya ta na fadin"Surayya yaran nan kamar magajin gida Lokacin yana karami."
Surayya na dariya tace"Wlh nima haka nace Umma, sak Sadiq yana kamar su."
Umma ta rumgumesu a jikinta tana saka musu albarka.
Surayya ce ta waiga bata ga Innani ba shine ta yi mgana.
Ina mirmishi nace"Tana dakin maman Suhailat makociyata."
Inna talatu tace"Ta samu hira, maman suhailat akwai labarai a bakinta."
Surayya tace"An had'u da an dace kenan"
Muka yi dariya gabadayan mu, Habiba na aika ta kira Innanin sai gata da Sandarta da Uban gilashinta, jin muryansu Umma yasa ta washe baki ta na fadin"Salamatu kin huce kenan kin zo ganin jikokin naki? To wa ke fushi da yara? Balle yan Biyu kyautar Allah? Gwara da kika maida komai ba komai ba kin ji rayuwar nan ma nawa ta ke, yarinyar nan Hasiya da danginta duk mutanen kwarai ne, zaune na ke lafiya kamar ina cikin gidan sulaimanu."
Umma dai sai ta sauya mganar ta hanyar gaida Innani.
Surayya ma ta gaisheta ta amsa tana zama kan Kujera Lokaci daya tace"ina magajin gida?
Umma tayi saurin cewa"Yana can kinsan sultana ta koma gidanta."
Ta fad'a ta na satan kallona ni kuma ko a fuskata bata Fahimci wani abu ba.
Duk da naji wani iri, ganin har yau da Safe mun yi mgana ammh bai Fadamin ba, wata zuciyar tace ina Ruwan ki Hasiya?
Innani ta tabe baki kafin tace"Au ta gama koken koken iskancin nata ta koma kenan? Yarinyar haushi ta bani ni fa na ke mata mgana ta min banza yo, ni fa uwarta na haifa ba ita ba kuma Tunda taga ni nan na Saduda na bi Allah itama sai ta Saduda ta bi Allah da monzonsa, ohon mata dai ita ta sani, ke Surayya kiramin magajin gida na yi masa nasiha yana cewa yasan Allah ammh kuma baya adalci yarinyar nan ita da yaran nan suna Bukatarsa ammh ko keyarsa bamu gani ba, gwara shima dai yau na yi masa nasiha."
Surayya na Danne dariyanta tace"Gaskiyarki Innani."
Umma kuma sai ta kasa mgana Inna talatu ne ke fadin"Innani ko dai aiki ne ya yi masa yawa."
Innani tace"Wani aiki? Ya warke ne da ya koma aikin nasa ban sani ba?
Ta fad'a ta na kallon Surayya a Dage.
Da Sauri Umma tace"Bai koma ba ammh yace min ya kusa komawa, kuma zai zo ganin likita litini mai zuwa inaga zai zo ya gansu Innani."
Innani ta yi shuru kafin ta samu zarafin mgana Umma tace Surayya ta bama Hasiya ledan da suka zo da shi.
Ledan Atamfofi ne guda uku sai kayan yara masu kyau da yarari na karb'a cikin murna ima nuna ma su Inna Talatu.
Innani sai washe baki take yi tana fad'in"Lalle ana yi da wayan nan yaran."
Umma dai bata biye mata ba, sallah suka yi sannan suka ci abinci Direba ma an kai masa nasa daga waje, Umma sai da Surayya tace Umma ta ijiye su Asim taci abinci sannan ta ba ma Inna talatu su, suna ta wasan su ba su da rigima da rana sai kukan Dare in daya ya fara daya zai kama sai asuba taimakona daya su inna Talatu ai da na raina kaina shiyasa ko kibar Jegon nan na kasa yi, sai dai cikar Haihuwa kawai da ya ragemin Rama na, sannan kumburin da na yi da Ciki har a lokacin kafafuwana ba su gama Saccewa.
Karfe uku da wani abu suka tafi bayan sun yi sallar la'asar, Umma Kamar kada ta rabu da yaran haka nan take jin kaunarsu na ratsata kamar yaran su dawo wajenta da zama haka taji, innani kuma da Umma tace ko zata bisu su koma ne? Tace haka kurum ita ba ta tashi ba, a bari in tagaji da zama ita da kanta zata yi mgana, jin haka yasa Umma ta kama bakinta
A mota ma Hiran yaran kawai Umma ke yi ma Surayya, ita kuma ta na Biye mata ganin da gaske yaran sun shiga zuciyar Umma ba da wasa ba.
Haka da suka koma ta yi ta ma Abba mganarsu tana fadin kamar magajin gida yana karami.
Abba yace shima yaga haka Lokacin da yaje asibiti ya gansu.
Shifa sai gajiya ya yi ya koma yana kallon Umma yana Dariya a ransa tana ce masa kawai Sadiq ya bar Zariya nan ya Dauko matarsa tasa su dawo kusa da su da zama.
Abba na dariya yace"Jikokin su dawo kusa da ke da zama dai zaki ce."
Sai alokacin ta farga da abunda tace, Tsabar kaunar yara ne yasa bata son su yi nesa da ita, ba ta ki a kullum ta rika ganin su ba.
Sai ta yi shuru da bakinta Abba kuma yana jinjina ma Ubangiji mai kowa da kimai in ba'a yi wasa ba yaran nan sune Jarabatan Umma, tana kaunarsu kamar har sun fi Sadiq din matsayi yanzu acikin ranta.
Har Sadiq sai da ya Fahimci haka, ta kirashi tana ta gayamssa yara nan kamar Shi yana karami kuma ta rika ce masa ya gayama matarsa ta kula da su ta daina barin su ba kayan Sanyi kada sanyi ya kamasu su Umma masu jikoki, kamar ba'a taba Haifa mata jika ba sai akan su.
Ranar litini da Sadiq zai je ganin Likita dagacan ya Biya Zariya Tahir ya taho jiya da yammah zai Tukashi su tafi tare, Umma bar bakin mota ta bisu tana kara jaddada masa ya gaishe mata da Twins.
Kamar tace zataje sai kuma ta fasa kada a Fahimci yanayinta.
Ammh da yaran nan ta ke kwana acikin Ramta, ta na son su dawo kusa da ita ta riga ganinsu a koda yaushe.
Sai da suka fara Zuwa asibitin sannan daganan suka dawo ta Zariya.
Likita ya tabbatar da warkewa tare da Samun nasaran gyaran karaya, sannan yace masa zai iya cigaba da Tukinsa ba bu wata matsala.
Sai dai Fatan Allah ya tsare kuma Nasara ma sosai aka samu ganin ko Dingishi Sadiq ba ya yi kafarsa da Hannunsa sambal suka warke.
Sai dai tabbai in da ya samu Rauni ne mutum zai kallah ya Fahimci ya taba samun had'ari.
Ko da suka iso wajena kamar ba Jego na ke yi ba mun cakare ni da su Asim, muka tarbi Babansu cikin Fara'a da Farinciki Tahir kuma shi ta su Asim kawai ya ke yi
Har ya kalleni yana fadin"Kai girmansu ya bani mamaki fa."
Ina dariya ban ce komai ba Assadiq ke fada masa suna shan har da madaran yara kuma basa wasa da Nono.
Bayan sun gaisa da Inna talatu ta ba su waje ta koma dakin Maman suhailat ban da Innani da ta zauna ta rika musu Hira..
Karshenta dai nan muka barsu Tahir da yaran da ita muka Shiga ciki.
Muna shiga ya Rumgumeni ya kamkameni yana shakan kamshin Jikina, mun jima a rike da juna Sannan ya sakeni ya koma ya na kallon Fuskata cikin Fara'a yace"Jegon nan ya yi miki kyau My siya."
Mirmishi na yi kafin nace"Kai ne dalilin haka Abban Asim"
Dariya ya saka yana fadin"Ehye wato na tashi daga Assadiq na koma Abban asim?
Sai naji kunya na koma ina sunne kaina saman kirjinsa, shi kuma yana Biye min tare da Tsokana ta.
Saboda za su tafi shiyasa bamu yi mgana sosai ba, na dai yi masa mganar zan je makaranta da ke kusa damu wata private zan kai musu Tp letter dina kafin su yi hutu tunda an kusa Fara jarabawa.
Sannan mun yi mgana ko bayan na yi arba'in Habiba zata zauna dani har su Asim su fara wayau saboda ni kadai bazan iya ba, sai nace ya kira Adda Fati su yi mgana yace min zai kirata.
Mun shagala aciki mun manta da kowa da komai.
Assadiq ya Rud'e ya na ta kamani ni kuma ina kwace jikina Tunda jego na ke yi ga mikin aikin bai gama warkewa ba.
Sai da Tahir ya rika kiransa a waya sannan ya sakeni ya fito ni kuma sai da na sako uban Hijabi Saboda kunya.
Tahir dubu goma ya ba ni yace a siyama su Asim kayan wasa.
Shi kuma Assadiq yace zai Turamin Sako ta waya da haka muka yi sallama.
Cikin ikon Allah Innani tace zata bisu da na ce har kin gaji damu?
Sai tace"Ina fa, kawai dai naga kamar ban kyauta ba ne, sulaimanu ma na da Hakki a kaina. Kada ransa ya baci yaga nazo nan na tare, gwara dai na koma shima ya ganni hankalinsa ya kwanta kada kuma na yi rashin Adalci."
Ni kaina sai da na yi Dariya Assadiq ne kawai ya Murmusa.
Tahir kuma har yana rike ciki, Inna talatu ta yi cewa zata yi kewar Innani, sai ga Innani na kuka ta na fadin"Ni kaina ba'a son raina zan tafi ba, sulaimanu na ke tausayi."
Sai kuma ta koma kallonsu Asim ganinsu ya sa ta kara kecewa da kuka ta na fadin"Yaran nan abun Tausayi uwarsu kadai ke wahala da su, Ubansu bai san wahalan ya'ya ba."
Assadiq ya kalleta kafin yace"Sai ke kika san wahalan na su ko?
Innani ta ballamasa harara kafin tace"Kwarai nan yara nan ke tsala kukan dare haka muke hana idanuwan mu barci muna wahalan reno, ammh daga karshe baka Gode ba."
Karamin Tsaki kawai ya yi ya fice daga dakin ya bar Tahir na Dariya.
Innani ta kwabe baki kafin tace"Masifaffe duk ya zama wani mafad'aci yo ni ko ubansa Sulaimanu lallabani ya ke yi Ehe."
Naji dadin zamana da innani a wajena na bata atamfa da sabulan wanka da omo har da Turare ta yi ta min godiya ta a sakamin albarka.
tace kuma kada na damu zata dawo daman domin tana jin Tausayin sulaimanu in ba haka ba inda zataje nan zata zauna tare da yara nan ta na tayani renon su.
Har Habiba sai da tace gidan ba Dadi da Innani ta tafi, innani ai akwai hiran ban dariya.
Farida sai dai ta koma bangaran Umma, Shiyasa da Innani ta dawo ta yi ta Murna, innani tace shaf ta manta da Amana a hannunta to gaba kafarta kafar Farida bazata barta anan ba, ba mai Tausayin da zai kula da ita.
Ba wanda yace mata a'a sanin halinta kada ayi mgana ta tada kukanta na Fama sai aka bita da yadda take so.
********
Bayan wata d'aya."
Kwana uku da yin Arba'in din su Asim Safiya ta zo ta goyamin Asif ni kuma na goya Asim mukaje private school d'in da ke kusa damu na kai musu T.p letter a lokacin ma suna Wassanin yara ne sun gama Jarabawa hutu za su ba da.
Na gaya musu tsaikon da na samu aiki aka yi na haihu ganin yaran yasa suka karbeni suka bani accpted letter wanda zan kai makaranta suka ce bayan an dawo hutu sai na fara zuwa..
Jin dadina da Safiya tace ba'a fara zuwa Dubawa ba, makaranta ne na sha Fad'a a Tp office sai da suka ga su Asim sannan suka yarda da uzurina.
Tunda na yi arba'in Inna Talatu kwana daya kawai ta kara ta koma gida, na bata atamfofi guda Biyu Assadiq ma ya siya mata har da waya tunda a gidana na hannunta ta lalace sannan ya bata kudi, muka rabu tana min godiya mu ma muna yi mata.
Habiba ce ke wajena Tunda Assadiq ya yi mgana da Add Fati ta amince daganan na ke bata kudin mota ta na tafiya makaranta.
Assadiq ya koma Abuja wajen aikinsa sannan kuma Abba ya gwangwajesa da Sabuwar Mota Camry mai ruwan madara ta yi kyau motar tunda har nan yazo min da ita mun shiga ni da su Asim mun je yawo.
Yawon arba'in na fara nan cikin gari tunda yace min har wajen Amma zai kaini mu kai mata su Asim in ya dawo sannan zamu je gusau mu yi kwanaki Umma ta matsa yaushe zan kai mata su Asim?
Umma ce ta bani mamaki har waya muna yi da ita, in yau bata kirani ba gobe zata kirani ta ji ya ya lafiyar su Asim har wasanninsu ina kara mata tana ji.
Ni yanzu Hankalina duk ya kwanta, in da nake hangen matsala Cikin ikon Allah komai ya zo ya zama kamar bai Faru ba.
Naje gidan Adda Fati na kwana daya, Gidan Ramatu ma na kwana ita kwana muka yi mganar kayan gyaran jiki nace mata Adda Rukayya tace akwai wata marubuciyar littafan Hausa kayanta na da kyau da inganci.
Ramatu tace in na samu na gayamata itama zata siya ammh sai ta Haihu Tunda Tsohon ciki gareta.
Gidan Adda Rukkaya ne da naje ban kwana ba saboda mijinta na dai yini da ita kuma ta kiramin mai saida kayan gyaran Gudiyo kaya masu inganci daga Chadi.
Surayya Dee marubuciyar Littafin Halinyau, sabo da kaza da kuma bakar Ta'ada, ashe Adda Rukayya tana karanta littafanta ta nan suka saba yanzu kuma suna cinikayar kayan gyara da ita.
Ta kirata a gabana ta fad'a mata na haihu kuma duk da aiki aka yi min ina so na yi gyara nan take tace zata had'amin komai da komai cikin Farashi mai Sauki zata sauko a mota zuwa Jibi
Nima ban yi kasa a gwiwaba na tura ma Adda Rukayya kudin na kuma karbi Lambarta Tunda nace mata Ramatu ma tana so zata siya.
+234 803 277 3332
Washegari Samaru Habiba ta rakani har Gidan da muka zauna na kai musu su Asim su maman Boy dai ana nan jiya i yau ba wani Cigaban Rayuwa.
Na jima a gidan suna ina suka sakani sai da muka yi la'asar muka fito.
A hanya na had'u da wata kanwar Salisu ta na ta kallona ganin haka yasa na gaisheta.
Ta amsa ganina da goyo tare da Habiba yasa tace ko na haihu ne? Habiba ce ta ce mata Eh,Har kuma yaran na Bude mata ta gani ta yi musu addu'a har muka kule tana waigen mu.
A ranar naje Dirimi gidan Baba Tanko da Baba Saminu, na gaishe su tare da kai musu su Asim.
Baba Tanko har Daukansu ya yi sannan ya kalleni yana fadin"kwanaki naji an ce dangin mijin naki sun miki koran kare?
Ban yi mamakin jin ya samu Labari ba, na san kuma daga bakin Baba Jibril yaji kila shima Salima ta fitar da mganar waje.
Shiyasa na yi masa Mirmishi nace"Ai komai ya wuce yanzu in sha Allahu."
Kamar dai ba haka ya so ba, Sai dai bai kara mgana ba, ban wani jima ba daganan na biya gidan Goggon kona muka gaisa ita kam sai faman bugun Ruwan cikina ta ke yi taji halin da na ke ciki da yan'uwan mijina ni kuma ina ce mata komai lafiya.
To ai taga haka dagani har ya'yana muna cikin kama mai kyau ba ma cikin wahala.
Sai da na tabbatar da naje gidaajensu na gaishe su kamar yadda Amma ta bani umarni, har gidan su Safiya naje na yinin mata, Domin ai Safiya kawar Amanace sannan ta zauna a gida na fara shan mganin gyarana da akq aikomin daga kano.
Tunda a satin Assadiq yace min wajena zai sauka sai faman rawan jiki ya ke yi min nasan kuma ba sauki Shiyasa na dagee ina ta amfani da mungunanan kuma naji dadin su sosai.
Kafin ramar jumma'a sai da na tabbatar da nayi zam, ni kaina naji ina son kasancewa da mijina da yammah ya iso, Habiba da rana ta koma gidan Adda Fati ammh kafin ta tafi sai da ta tayani aiki na yi masa girke girke