Showing 108001 words to 111000 words out of 116366 words
sun kara bayyana daman can a baya gyaran jikin na kama sannan kuma cikin ma ba d'aya ba ne da na su Asim
Wanna daga gani in ban yi wasa ba kafin ya girma sai na zama abun Tsoro.
Ita da ta zo min bakunta itace ta Tube ta zage ta gyaramin gidana tas ciki da waje, Assadiq baya samun Lokaci sai Weekend wannan karshen watan ma saboda ni bai tafi Gusau ba.
Ina ji suna waya da Sultana ta na kananun mganganunta da ta saba.
Ya fad'a mata ina da Ciki kuma ya na wahalar dani zai tsaya ya kula da ni.
Nasan dai Sultana na can bakin ciki kamar ya kasheta.
Ta so ta tafi a ranar tunda tace gobe da Safe zasu koma Zariya ni na Hanata tafiya tunda ta kai Dare, har girki sai da ta yi min ta kuma matsamin na yi wanka.
Ni daman ban iya cin komai sai Farar shinkafa ba mai ba manja ba maggi
Hakanan na ke iya turawa in naji kamshin mai ko magi wlh ranar bazan kwana Lafiya ba.
Shiyasa da ta yi mai miya ni sai naci fara hakanan da Assadiq ya dawo shi kanshi yaji dadin ganin gidan da ni kaina.
Allah Sarki har ya Biya ya siyo abinci ni kuma ban yi hausan na kirasa nace kada ya siyo wani abu ba.
Sai fad'i ya ke yi"Safiya kin zo mana Bakunta muna ta saka ki wahala."
Kai Tsaye tace"Ni ai ba bakuwa bace ni yar gida ce, kuma lalura ce fa."
Ina gefen mijina nace"Tun da ta zo bata zauna ba, sai aikace aikace ta ke yi da na yi mgana sai tace ita ba bakuwa ba ce."
Assadiq yace"Gaskiya ne mun gode sosai Allah ya bar zumumci."
Ranar dai bata tafi ba sai da safe suka fita tare da Assadiq zai kaita kafin ya shiga Office.
Sai naji kamar kada ta tafi ammh ba Dama tunda mamansu na ta kiranta za su tafi da wuri, jin ma ba ni da lafiya ne yasa ta barta ta kwana kuma Safiyan ta bani ita mun gaisa ta yi min sannu.
Na gayama Amma bani da lafiya ammh ban gayamata ciki gareni ba, ita da kanta ta gane sannan sun yi mgana da Adda Fati ita ta gayamata zencen zuwan Amna wajena.
Amma ta kirani ta na cewa"Ko dai Habiba tazo wajen ki ne, ni nan ba wani abunda ta ke yi min naga zata fi Amna amfani tunda ta fita shekaru."
Ni kuma ganin Habiba bata taba zuwa ta jima wajen Amma ba yasa nace ta kyaleta kawai ai ba wani abun wahala ba ne Tunda Adda Rukayya ta bani Tabbacin Amna zata yi min komai in dai ba mai wahala ba ne.
Sai Amma tace shikenan Allah ya kara lafiya.
Kafin mu yi sallama sai da tace"Ina Mazajen nawa? Ba sa cefane kuma ba sa zuwa zence?
Ina dariya nace"Amma suna gusau ba su dawo ba."
Amma tace"Kin huta da yanzu ai aikin ya yi miki yawa"
Kai tsaye nace"Ai nace su yi zamansu can sai na warke Amma bazan iya ba ji na ke yi kamar zan mutu."
Amma tace"Ki bar cewa Haka Haseta. Haka kowani ciki ya ke da na shi Tarnakin Allah dai ya sauwake ya kuma Raba lafiya."
Sai naji kunya amsar ma a sannu na amsa ta.
Mun gama waya da Amma kenan sai ga kiran Umma itama muka gaisa ta gaisheni tunda ko jiya ta kirani ta gaisheni da jiki.
Ni da kaina na ke gayamata diyar yayata zata zo ta taimakamin
Umma tace"Eh gwara haka ko ya ya mutum ya ke ai Rahama ne. tunda ga su Asim a wajena."
Cikin karfin hali nace"Umma su sha zamansu wlh, in suka dawo bazan iya da su ba."
Umma na dariya tace"Jiya ai sun yini Hiran Mami, Jiya Asif da rigima ya tshi ashe zazzabi ke jikinsa sai da na bashi mgani"
Sai na ke gayama Umma su Asim ba su cika yawan ciwo ba sai dai ko zawon Hakora da suka yi ta fama da shi Shima din bai ba su wahala sosai ba.
Kaf yayayen Assadiq ba wacce bata kirani ta yi min sannu ba, Hatta Sadiya itama ta kirani ta min sannu Sajida kuma daman tunda muka daidaita lokaci bayan Lokaci muna mgana.
Allah sarki har ce min ta yi in ina so sai ta yi ma Umma mgana ta zo ta taikamin, ni kuma kunya da nauyi suka saka nace ta yi zamanta bakomai.
Bazan iya kwanciya yayar mijina na Hidima dani ba abun akwai wani iri aciki.
Da na gayama Assadiq ma a lokacin Dariya kawai ya yi kafin yace"Ikon Allah Su Sajida an zama gama garin zawarawa."
A lokacin da ya fad'i haka sai da nace"To wai bazaku iya gyara Lamarin ba Assadiq?
Assadiq yace"Abba ya zauna da shi, laifin fa duk na Sajida ne ko za'a gyara sai in shi mijin ne ya dawo yace zai maidata kuma abu ne da ya had'a da Uwa dole kuma ya yi ma mahaifiyarsa Biyayya, ni tausayinta na ke ji ya'yanta Uban duk ya rabata da su Yar kibar nan ta Sajida duk ta ta fi, bakin nan nata da baya shuru da Had'e had'e rayuwa ta gama nuna mata gaskiyan da ake gayamata bata Dauka ba, duk ta zama wata a firgice."
Ya na wannan mganar ina Hasaso abunda ya faru dani Lokacin da Abubakar ya sakeni.
Kusan zauncewa na kusa yi, na fita Hayyacina kai Allah ka raba kowata mace da kaddaran sakin aure da zawarci.
Kamar yadda muka Tsara Tahir ya Biya ta Zariya ranar Wata alhamis ya Taho min da Amna.
Da ya ke wani Taron siyasa ya karfafa ma Tahir shigowa Abuja kuma daman Hauwa'u ta matsa zata Biyosa ta zo wurina yasa ya zo da ita.
Sanda suka iso Assadiq na wajen aiki shima yana sauke su ya wuce inda zaa shi.
Dakin da Sultana ta sauka na sauke Amna da Hauwa'u.
Hakuri na ba ma Hauwa'u na Roketa ta shiga kitchen ta da fa musu wani abu su ci ni dai ba na iya moran kaina Ballatana na Morama wani.
Hauwa'u tace"Haba bakomai bari na shiga na girka"
Da ta tambayeni me zata girka nace abunda zai fi sauki tunda tafiya suka sha. Ni kuma na shige daki na kulle kaina saboda kamshin girki in na shaka ba zaman lafiya.
Ina da sauran miya tun wanda Safiya ta yi ne kafin ta tafi, Sai ta dafa musu Taliya fara suka ci da miya.
Ni kuma na Tura gaya hakanan na sha Ruwa.
Amna kuma ta shiga kitchen ta na wanke wanke, Adda Rukayya ba ta wasa sosai ta ke koyama ya'yanta ayuukan gida saboda Rayuwa.
Muna falo ni da Hauwa'u muna ta Hira, ta na gayamin taji dadin kayan gyaran da ta siya hannun Surayya Dee.
Ni na had'a su tunda na gayamata ingancin kayan tace taji dad'in mganin sanyin nan tare da tsumin nan, ita yanzu kazar Amare ta ke so ta kara siya taci.
Ina daga zaune nace"Ki siya wlh kazarta na da kyau, kuma ta na jimawa a jikin mace ta na aiki, nima fa na so na kara siya sai kuma ga Laulayi da gudu na watsar da su na yi ta kaina."
Hauwa'u na min dariya tace"Result din gyara ne kika gani fa Madam"
Ina jin miyau ya Taru a bakina nace"Uhm ai naga gyara sosai."
Ni na gayamata Surayya ta fara Dahuwar Tatattabaru sosai kuma suke da inganci nan take Hauwa'u tace zata yi mata mgana ta na so.
+234 803 277 3332.
Ina raina Amna sai ga ta, ta zage ta share min gida tas ta goge ta saka Turare.
Ko da ya ke yanzu shekaranta sha uku, ta riga Adda Fati haihuwa ita Adda Fati ta jima ba ta Haihu ba ne sai Adda Rukayya ta dauke girman.
Hauwa'u kuma ta yi musu abincin Dare har da mazajen namu.
Ni nace ta yi girki saboda su kada su dawo ba abinci.
To ba su shigo da wuri ba ma, cikin su ban san wanda ya tsaya wajen d'aya ba.
A tare dai suka shigo gidan suna Hiransu suna Dariya, Hauwa'u ce ta shirya musu abincin ta kawo musu Amna ana sallar isha'i ta yi barci.
Ni kuma saboda kamshin abinci ina daki amma ina jiyo maganganun su tunda ba sa mgana a hankali kamar mu.
Ina ji Tahir na yi ma Assadiq tsiya da cewa yace kawai kuku ya kawo musu daga zuwan matarsa ta zama mai yi masa girki shi da matarsa.
Shi kuma yace masa ai shima an taimakesa yadda ya ke jin yunwar nan in bai samu abincin nan ba ai akwai matsala sannan ga Musulunci akwai taimakon dan'uwa musulmi wannan shima ya yi jihadi ne.
Ina jinsu suna ta cacar juna kamar yadda suka saba
Tahir na ce ma Assadiq ya shiga uku da Jaraba, yana da kananun shekaru kafin ya yi Hamsin ya kai ga ya'ya ashirin
Kilama yanzu haka Sultana ciki gareta.
Amsar da Assadiq ya ba ma Tahir ce ta bani dariya.
Wai ai ni ka shaida lafiyata kai ne dai na ke tunanin ko dai ko dai da matsala ne!?
Sai ga Hauwa'u da gudu ta shigo daki tana fad'in"Abokan nan ba sa jin kunyar fad'in mgana mai nauyi."
Ina kwance nace"In dai Assadiq ne ba'a kada shi a mgana, shi kuma mijin ki tsokana da neman zence."
Dole ai ta bar musu falon ta dawo wajena muna ta Hira.
Tana fad'in tsoro ta ke ji ta samu ciki Tunda ta na karatu.
Ni kuma nace mata abun na Allah ne ta yi fatan Allah ya zaba mata mafi alheri.
Sai wajen sha d'aya na dare Assadiq ya leko yace Hauwa'u ta shirya Tahir yace ba zai iya kwana shi kad'ai ba.
Ina daga kwance sai da na mike cikin mamaki kafin nace"To ba ga dakuna ba, sai ku kwana tare."
Assadiq yace"Haka nace masa, ammh sai naga yana nokewa."
Ni ko kamar da sauri nace"To don Allah Assadiq ka roke sa mana."
Asaadiq yace"Ke kam da son jan zence ki ke yi, kika sani ko yana Ihun dare ba ya so mu ji? Hauwa'u dauko mayafiki dare ya yi."
Hauwa'u kunya ya hanata Dago kai sai ta mike tana fad'in" Kayana na can dakin."
Assadiq ya bata hanya ta fita sai ya kariso gareni ya zauna kusa da ni.
Lokaci d'aya yaga na hade rai sai ya yi dariya kafin yace"Da safe za su dawo kada ki damu kin ji ko my siya?
Ina zumbura baki nace"To me yasa bazasu kwana anan ba?
Hancina ya ja kafin yace"To na gayamiki kada ki matsa, kinsan akwai mazan da ba sa iya sarrafa jin dad'insu kila yana cikin su ne, kinga kuwa da kunya aji ihunsa a gidan abokinsa kuma yadda Tahir ya ke sabon shiga a lamarin kinsan ba'a daga kafa kullun ne Til Down."
Hannu na saka na dokesa a cinyarsa sai ya sosa wajen yana dariya kafin yace"Me kuma na yi?
Ina hararansa nace"Bansani ba, Assadiq ihu fa? Wani irin Ihu kuma?
Assadiq na dariya ya sunkuyo ya na min Rad'a da yasa na fara Turesa ina fad'in"Assadiq..Assadiq.."
Hannayena ya rike duka Biyu ya sama min karfi yana fad'in"Irin wannan irin wannan da ki ke sakani?
Ko na gwada miki irin shi ne?
Ai sai na yi lakwas ina kallonsa cikin ido kafin nace"Ka yi wa girman Allah ka yi shuru."
A kunne ya k'aramin Rad'a abunda ya aikata yasa sai da na koma na cukwikwayosa ina jin kunya Lokaci d'aya da Dariya.
Shi ma yana tayani har yana matsenin hanci yana fad'in"Ke siya kunyar taki ba ta fulani ba ne ko?
Ina Make kafarsa da kafata nace"Ta zamfarawa ne ko?
Baki ya Bude kafin yace"Bangane ba! Allah yasa ba mgana kika maida min ba."
Yadda ya Tsaya ya na kallona ne yasa na Fashe da dariya, shima kuma sai ya Tsaya ya na kallona lokaci d'aya yana girgiza kai kafin yace"Lalle Siya. to nagode."
Gabadaya mun Shagala mun manta da su Hauwa'u sai can ya tuna ya tashi da sauri ya fita Falo wayam.
Sai ga shi ya dawo ya na ce min"Tahir fa tuni ya tasa matarsa sun tafi, falo sai wayam ba kowa."
Kai Tsaye nace"bazai tafi ba, ka zaunar da shi ka na yi masa sharri."
Yana Tube rigarsa yace"Gaskiya na fad'a, bari na yi wanka."
Sai da ya fito ya tuna da bai ga Amna ba da sauri yace"Ina d'iyarki ne, ban ganta ba?
Ina kara shigewa cikin Bargo nace"Ta na dakin can, ta yi barci tun dazu."
Cikin jinjina kai yace"Amma dai taci abinci ko?
Sai na gyada masa kai lokacin Miyau ya cika bakina sai da na tashi dakyar na shiga Tiolet na zubar.
Na fito ina numfarfashi Assadiq ya kalleni yana fad'in"To ke ki samu wani Roba ki rika tara miyan aciki mana, zaki gaji da zirgan zirgan ta shi kuma"
Ina zama gefen gado nace"Ba ka jin kyamata ne?
Hararana ya yi kafin yace"Kyamar me? Ni da na yi sanadin miyan."
Ya fad'a ya na karisowa kusa dani, Dagashi sai karamin wando duk sanda zanga Assadiq a haka ba na iya had'a ido da shi.
Sai na juyar da kai zan kwanta ina Fad'in"Baka jin sanyi ne wai?
Saurin Taro kaina ya yi yana so sai na kallesa naki, runtse idanuwana na yi ina kiran sunansa cikin Shagwaba.
"ASSADIQ.."
Da tafukan hannunsa duka ya saka ya Taro fuskata cikin wani yanayi yace"Meyssa bakya iya kallona a suffata ta Namiji?
Shuru na yi masa, kuma na kasa kallon nasa sai ya ce"To Allah yau sai kin kalleni, ji min yarinyar nan."
Sai ya fara min sosa a wuya kamar tafiyar tsutsa na fara zillewa ina Dariya.
Duk bai ishesa ba sai da ya fara min cakulkuli a ciki dariya na ke yi kamar zan shid'e ina kiran sunansa ammh bayaji sai cewa ya ke sai na kallesa."
Da sauri nace"To to ka tsaya naji zan kalleka."
Cikin Sauri yace"Kin tabbata?
Ina haki da Numfarfashi na Daga masa kaina sai ya kyaleni.
Numfashi na sauke kamar zan dago na kallesa sai kawai na yi saurin Kwanciya na ja bargo na Rufe kaina ina Dariya.
Shi kuma dariya ya yi kafin yace"Siya yanzu ke sai ki yarda zaki iya yi min wayau?
Bi na ya yi ya danne ya tura kansa Cikin Bargo duk da ina faman Turesa ammh ko gizau.
Cikin rad'a yace"Tunda kika sab'a mgana ga Hukuncin ki."
Na Bude baki zan yi mgana naci ya kame bakina ya had'a da nashi.
Da zafi zafi ya ke yi ma bakina Hukunci sannan kuma ya kama Hannayena ya rike su gam da ba na iya wani motsi.
Dole dai na saki jikina, na mika masa Ragamar Rayuwata gabadaya a hannunsa.
Da asuba na kasa tashi duk jikina Tsami ya ke yi min, nasan ko irin Hukuncin Assadiq.
Yana gani ina tafiya dakyar yana min Dariya bayan ya dawo sallar asuba.
Ni kuma na yi masa Fuska na kumbura Fuska har na Dauro alwala nazo na yi sallah.
Bayan na idar kuma na zo na kwanta a can gefe na juya masa baya shi kuma yana duba wani abu a wayarsa.
Sai ga shi har ta bayana yazo ya na Leka Fuskata.
Harara na maka masa ina kara Hura Hanci.
Sai kawai ya duka ya sumbaci Goshina kafin yace"I love u My siya. Allah ya yi miki albarka."
Sai naji zuciyata ta yi haske cikin mirmishin jin dad'i nace"Ameen Assadiq mijin Hasiya."
Ina kwance ina jinsa sanda ya yi wanka, sai da ya fito ne yana Shiryawa na lallaba na fita abun mamaki a kitchen naga Amna har ta saka Ruwan zafi a Butar da na ke Dafawa.
Ta na ta goge goge a kitchen din, tana ganina ta yi saurin gaisheni na amsa ina fadin"Eyee Amna an girma, to me zaki dafa muku?
Kin iya soya kwai?
Ta gyad'amin kai, ammh kada na barta ita kad'ai yasa na tsaya ina gayamata abunda zata yi.
Nace ta saka kayan kamshi da albasa saboda karni.
Falo na koma na Tusho hancina da Hijabi ammh kamshin kwan har ya Fara sakamin tashin zuciya.
Assadiq ya fito cikin Shirin fita yana ganina na toshe hanci yace"Siya to haka zaki cigaba da zama baki son kamshin komai?
Shima yana mgana ina jin kamshin Sabulan wankansa tunda na hanashi saka Turare na kwashe gabadaya na boye.
Kamshi daya na ke shaka na zauna lafiya shine na Turaren wuta.
Ganin ina yunkurin Amai yasa na tashi da gudu na koma daki na kwanta ina toshe kaina acikin Filo.
Ko da Assadiq ya gama karyawa ya zo min sallama na yi barci.
Nima zuwan Hauwa'u ya tadani na tashi na iske Amna ta gyara gidan tas yana tashin kamshi.
Kafin Hauwa'u su koma ita ke yi abincin dare saboda su Assadiq, ammh duka duka kwana Hudu suka yi suka tafi.
Ban so tafiyar ta ba ina ta ce ma Assadiq ya roki Tahir ya bar ta su yi ko da sati.
Yana kallona yace"Siya ke fa wani lokacin kina da rigima, mutum da matarsa kuma sai kice ya tafi ya bar miki ita anan?
Da sauri nace"A'a ya zauna shima ya yi sati mana"
Dariya ya fashemin da shi da ya harzukani na juya masa baya.
Ya yi saurin Rumgumeni ta baya yana Fad'in"Tahir fa yana da abubuwan yi Siya, sai ya zo kawai ya tare a wajen mu? Sorry kin ji to ki bari in kin Hauhi sai mu je wajensu mu yi musu wata d'aya tunda baki son Rabuwa da Hauwa'un"
Yadda ya fad'i mganar me yasa nasan zolayata ya ke yi, Bayan hannuna na saka na Tokare masa kirji.
Shi kuma da yaji zafi sai ya matsemin Nono na guda d'aya.
Da naji zafi na make hannunsa ina Fad'in"Assadiq makasata ne fa?.
Yana dariya yace"To ke ma ki rama a nawa makasan mana?
Ya fad'a yana kashemin ido d'aya.
Kallonsa na yi bakina alaikun naja jikina na sauka daga gadon ina fad'in"A'a ba sai na rama ba, na yafe maka Assadiq."
Kokarin tashi ya ke yi ya Biyo ni na zura da gudu ya kira sunana yana fad'in"Siya ki yi a hankali."
Haka muka cigaba gudanar da Rayuwarmu ni da Assadiq cikin rayuwar da muka zab'a ma kanmu.
Ba zan ce ban taba ganin ma'aurata kamar mu ba, ammh dai za'a dade ba'a samu kamar mu ba.
Ba wai bama samun sabani ne bane muna samu, ammh kuma muna kokarin daidaita kanmu.
Tunda musan hallayan junan mu sai muka ci mganin zama tare.
Tausayin junan mu shi ya fara gina zaman aurren mu, sannan daga baya soyayya da kauna suka Biyo baya.
Sannan ni kuma na zauna da shi Cikin Biyayya, Duk abunda na san zai sab'a ma Assadiq ina kauce masa shima duk abunda yasan zai sosa min rai yana kauce ma aikata shi Saboda kada raina ya so su.
Zuwan Amna ya taimakamin sosai ta iya saukakkun girkr girke, Har Assadiq shima mamakin kokarin yarinyar yake yi har ni sai da ya yi min