Showing 60001 words to 63000 words out of 116366 words

Chapter 21 - Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

316

nace ya bace bansan inda ya ke ba, kuma na tabbatar musu ko Assadiq ba shi da wani key a hannunsa. Duk da akwai kayana da yawa acan sai Adda Fati ba ta maida kai ba, ganin har alokacin ina asibiti sannan ga Assadiq ya bar mata kudi kuma na kara mata kudin da Anty Surayya ta bani a Hannuna.
Kuma koda yaushe tana kirana tana jin Lafiyata ni da Twins ita da Assadiq.
Safiya ma kusan kullum sai tazo ganina sai a lokacin naga Khairiyya yayarta tare da Mamansu zuka zo dubani tare da ganin yan Biyu.
Ana gobe za'a sallameni Assadiq ya zo shi da Abba da kuma Baba Sammani sai Mallam Shitu da Auwalu da Ranar da Assadiq ya koma Gusau shima ya koma gida.
Ba ni kad'ai naji dadin Zuwan su ba harda su Adda Fati, duk da ba su dad'e  ba domin iyakarsu awa daya suka juya Assadiq ya sake siyamin kayan Tea da madaran yara da likita yace Saboda ruwan Nonon ya yi musu kad'an dole za'a rika had'a musu da Madara.
Bamu yi wata mgana ba illah Tambayarsa da Adda Fati ta yi in da zasu kaini bayan an sallameni yace a kaini gidanta bayan suna in an samu wacce zata zauna dani sai na koma Dakina na cigaba da Jego na.
Kudi haka su Abba suka bani masu yawa ni da yan Biyu ballatana da Assadiq yace tun ranar da aka haifesu ya saka musu suna Sulaiman da Muhammad.
Wato sunan Babana da sunan Abba, sai ga bakin mu ya ki Rufuwa ni da Adda, Abba ma ya yi ta saka albarka har a fuskarsa ya nuna jin dadinsa su mallam shitu ma suna ta saka albarka tare da fatan lafiya mai Dorewa dani da yaran gabadaya.

Washegari likita ya sallameni bayan ya bani dokoki saboda mikin dake jikina, kenan kwana shida na yi a asibitin gidan Adda Fati kuma aka wuce dani Direct dakin da Habiba ke kwana aka saukeni ni da yarana a ramar kuma Inna talatu ta saka Ruwan masu zafi ta yi ma yaran nan wanka suka yi ta tsala ihu nima kuma ta iza keyata zuwa bayi ta gasamin jiki na sosai ina wash wash ta na fadin kwana nawa na yi a asibiti da d'anyen jiki ba gashi ballatana wanka sai dai gogemin jiki kawai suke yi acan.
Bani da zannuwa Atamfa Adda Fati ta siyamin guda d'aya ta farkamin zannuwa uku ina sakawa, su kuma jarirai Adda Fati ta shiga kasuwa ta kara siyo musu wasu, kuma daman dayan akwatina duka kayan haihuwan da Anty Surayya ta siya ne aciki, Anty surayya washegarin ranar da aka sallamomi ta dawo ita da Anty Sa'ima ta zo min da Ferfesun kayan ciki mai yawa tare da Kayan jarirai sannan kuma ta ce ta zab'o ma ya'yanta sunayen yan gayu, Asif da Asim tace zamu rika kiransu Saboda Sakayawa.
Da ita ma mun yi mganar taron suna tace Sadiq yace sai sati ya zagayo za'a yi taron suna, bayan kuma ita cikin yan'uwan Assadiq ba wacce ta kirani sai Anty Saddiqa daga kebbi sai kuma Saliha da ita ba sau daya ta kirani ba sai Anty Sa'ima ta kirani Lokacin muna asibiti ina jin Anty Surayya ke ba su Lambar Adda ta nan suke mgana da ni.

Sun tafi da cewar sai ranar taron suna za su dawo in sha Allahu.
Sun tafi kenan ba jimawa sai ga Salima ta zo ita da Zahra'u da Fathihatu sai ya'yan gidan Baba Tanko su suka rakaso gidan Adda Fatin tunda ba su san gidan ba..ni na ke gayama salima zuwan su Anty Surayya nace mata yanzu suka tafi sai ta kirasu a waya sukace ai sun kama hanya sai ranar suna za su dawo.
Salima sai ta koma gefe da Zahra'u ne da Fathihatu muka yi ta hira suna ta santin yara sai dai abunda na Lura itama Salimar kamar cikin gareta.
Kuma da alamu tana son yara domin haka ta Daukesu ta na ta kallonsu ta na mirmishi.
Kuma ta yi ta daukansu Hoto, Da ta tambaayi sunayensu Habiba ta gayamata, sai tace ga sunan da Anty Surayya tace a rika kiransu ta yi mirmishi tace sunan ya yi.
Sun jima tunda Sai bayan la'asar suka tafi sukace mim sai ranar suna bayan sun gayamin sakon Hajiya Murjanatu tace tana yi min barka kafin tazo.
Zuwa Lokacin nasan haihuwata ta zaga gabadaya dangi, kuma da karin yan Biyun da na haifa yasa gidan Adda Baya Rabo da Jama'a.
Maman suhailat ma bata sani ba bata nan ashe tun washegarin Ranar da su Assadiq suka je ta yi tafiya, sai da ta dawo sannan tazo Dubani ni da twins ta na bani Labarin zuwan su Assadiq.
Ni kuma nace mata ai a ranar aka yi min aiki tunda a asibiti ma suka same mu ka yi ta yi jimami.
Mutanen gidanmu na samaru su mamanboy, sun ta zuwa asibiti Dubani kuma da muka dawo gida ma sun zo sau Biyu, Ramatu kuwa kusan nan ta ke yini sai da yamma ta ke komawa gida Nura baya nan na Haihu ammh ya yi min barka ta waya.

*******
Ana gobe sunan Twins  muka yi waya da Assadiq yace yaso ya shigo ammh bazai samu zuwa ba sai bayan suna.
Muna cikin magana sai yace zai kirani in ya gama mgana da Abba.
Ni kuma daman yace kada mu yi shirin komai kudi zai Turomin na shagalin suna da komai da komai.
Abunda ban sani ba Surayya ta same shi sun yi mgana da tagaji da sha mata kamshin da ya ke yi.
Ammh sai da ya nuna mata bacin ran meyasa bata gayamai ga abunda ke Faruwa tun farko ba?
Anty Suraya ta bada uzurin Saboda Halin da ya ke ciki yasa ta boye mganar ammh ba da wata manufa ba ne.
Da haka ya sauko suka yi mgana ya ce ta kara siyamin wasu kayan fitar suna ni da Twins a dinka sannan mganar abunda za'a yi na shagalin suna ita ta bada shawaran a tura mana kudi sai mu yi komai da kanmu Tunda Hakkin mu ne, raguna ne tace ba laifin in ya siya sai su tafi dashi a ranar suna da Safe in kuma yana ganin akwai walaha ko mijin Adda Fati zai iya wakiltawa ya Tura masa kudin a siya Ragunan ya yanka da Safiyar ranar suna.
Sadiq yace zai yi mgana da Abba, Har mganar Umma sai da suka yi yace Umma ko barka bata yi masa ba, shi kuma bai yi mata mgana ko a fuska bai nuna mata wani abu ba ya samu dai ta sauko ta na amsa gaisuwarsa.
Har mallam zakari sai da ya kirasa ya yi masa barka.
Surayya tace ya kyale Umma zata sauko a hankali ammh mganar su Sadiya fa? Ya kamata ya karbo wayar Hasiya da key din dakinta dake wajensu."
Shuru ya yi kafin yace"Kyale su dani, so na ke yi naga iya gudun ruwan su."
Da haka suka rabu a ranar kuma da ya yi mganar da Abba shima ya Goyi bayan haka Shiyasa da rana ya kirani yace na Tura masa lambar mijin Adda Fati da shi suka yi mgana.
Raguna uku yace a siya sannan ya Turo mana isheshen kudin Hidiman suna yace muyi amfani da shi.
Adda Fati da ta gayamin uban kudin da ya Turo sai da na yi hawaye na kirashi ina yi masa godiya.
Sai kawai yace komai zai yi min bai biyamin kwatakwancin karamcin da na yi masa a rayuwa ba.
A ranar da yammah sai ga Goggo Husai tare da babbar yar Goggo Hassu ita baza ta samu zuwa ba sai Matar Baba Sammani uwargida sun taho daga Shinkafi Domin hallatar taron suna.
Assadiq yaji dad'i sosai shi daman bai ce kowa yaje suna ba wanda yaga dama ne yaje, Innani daman tace in taje suna ba mai kara yi mata wayau ya dawo da ita magajin gida shi da kanshi yace a barta acan sannan itama Siyan zai gayamata Innani zata Tsaya ta kwana Biyu in ba haka ba sai ta kara tada wani Fitinan kuma.

Bayan bayan sun dawo daga sallar Mangariba Shi da Abba, sai Abba ya wuce bangarensa shi kuma sai ya Shiga bangaren Innani ya kara gaisawa da baki suka taba Hira sama sama daganan ya baro su zuwa Shashen Abba ya ci karo da Sultana Tunda aka yi haihuwar wannan ne gani na Biyu da ya yi mata.
Ganin Farko zasu tafi makaramta ta gaisheshi ya amsa fuskarsa a had'e.
Sai kuma yau abunda ya bashi mamaki bata yi masa barka ba daman kuma baya Tsammanin haka Daga gareta Shifa tunda ta nuna masa bata da kunya ya fita sha'aninta..bazai zauna yarinya karama na wasa da Tunaninsa ba.
Kallo daya ya yi mata ya dauke kansa ya so ya wuceta ne sai yaji ta na gaishe shi sai ya Tsaya kad'an yana amsawa.
Kuma ya tsaya ne yaga ko zatayi mgana yaga kuma ta wuce bangaren Umma ya bita da kallo.
shifa yanzu an gama kuresa bazai kara matsa mata ta koma ba, ta yi ta zama tana Biye ma Umma har sai Lokacin da tagaji da ganinta a gabanta tace ta koma shidai kam ya Riga ya gama Tsara matakin da zai Dauka.
Bangaren Abba ya shiga cikin sa'a kuma sai ga Umma da Abba sai Sadiya da Sajida daman dazu yaji muryoyinsu a shashen Umma da Rana shiyasa yaki shiga.
Shifa Tun da yaji Labarin abunda suka aikatama Siya yaji baya son ko ganinsu bai kara yarda sun had'u ba kuma ya gama sanin duk masu kaunarsa acikin yan'uwansa da wad'anda suka kirasa suka yi masa barka da wad'anda suka ja da Hukuncin Ubangiji duk ya san su, kuma ya yi ma kowaccen su wajen zama.
Umma ce kadai bai riketa a rai ba Tunda ita c din sha Kudun ce uwa ce bashi da yadda zai yi da ita ammh su yana da yadda zai yi da su, tunda ba wacce ta haifesa acikin su. Sannan ba wacce ta taba daukan Laluransa ballatana iyalansa.
Ko a hidimar suna nan da kudinsa ne na banki tunda duk wattanin da ya yi yana jinya ma'aikatarsu duk wata suna saka masa albashinsa.
Sannan Abba shi ya ba shi kudin Raguna duk da yace ya barshi ammh yace kada ma yace komai.
Da su ya samu ya yi hidimarsa sannan ya Tura ma Tahir kudinsa da ya ara lokacin haihuwar siya.
Sanda ya shigo ba su san da shigowarsa falon ba tunda yanzu in dai acikin gida ne baya tafiya da sanda ya fara lallaba tafiya hakanan.
Sai in har zai yi tafiya mai nisa ne ya ke dogara sanda.
Ba su san ya shigo ba ya yi tsaye a kofar bangaren Abba da farko ma kamar ya koma sai dai mganar da yaji Sajida na gayama Abba ne yasa ya Dakata.
Karan Surayya suka kawo domin ba su da kunya.
Domin sunga Abba ya yi musu Shuru haka ma shi ma, da ita kanta Surayya shiyasa suke Tunanin ba wanda yasan abunda suka aikata.
Mgana suke akan taki saka su cikin Lissafin wad'anda za su tafi suna Zariya gobe Sajida ta kirata a waya taki Dauka kuma taje gidanta ta yi mata wulakanci shine suka zo suna gayamai ta ya ya zata ware su, ai suma yan'uwan Sadiq ne.
Tsabar yadda mamakinsu ya kamashi sai da ya murmusa yana tsaye.
Abba ne ya hangosa sai ya kira sunansa.
Dalilin da yasa suka san yana falon kenan duka suka waiga suna kallonsa.
Umma kuma na gefen Abba,  ita su Sadiya suka fara samu da mganar tace su gayama Abbansu itama Surayya ta rainata yanzu sai tazo gidan nan bata nemeta ba.
Itama tana so Abban ya tambayeta hala ita ce uwar sadiq din? Domin taga ta zake da yawa akan Lamarin shi da bakar Annobar yarinyar nan. ita fa ba yan Biyu ba ko yan goma ta haifa ma Sadiq bazata kaunaci bala'i da Annoba a kusa da magajin gida ba.
Kuma ganin daga Sadiq din har Abba sun yi banza da ita basa ma mata maganar sai ta fara rena kanta itama ta kwaso kananun maganganunta bata ta san zata bare da su ba.

Karisowa falon ya yi yana gaida Umma, rabon shi da ita tun safe ta amsa lokaci d'aya takallesa kafin tace"Ya karfin jikin naka?
Ya amsa mata da Alhamdulillah.
Umma ta mele baki kafin tace"Ka dai rika Hutawa ina lura da kai cikin kwanaki nan baka san zama waje d'aya kada dai ka manta har yanzu jinya ka ke yi baka gama warkewa ba."
Abba na gefe ya yi yar dariya kafin yace"ina shi ina Hutawa baban yan Biyu ne fa, abun alheri ne ya same shi fa sai ki ce ya koma ya zauna kuma salamatu"
Jin Abunda Abba yace ne yasa Umma ta kasa mgana.
Sajida ce ta kalli Sadiq kafin tace"Sadiq ba mgana"
Kallonsu ya yi dukkansu a dage kafin yace"Sannun ku."
Sadiya ce tace"Wai ya sunan yaran ne?
Domin sun ji kishi kishin sunan yaran, har Umma suka fesama ammh bata ce musu komai ba.
Shi kuma da gayya yace"Sulaiman da Muhammad"
A tare suka had'a baki wajen fad'in"Allah ya raya."
Dagaji ba har zuciyarsu ba ne.
Shuru suka yi gabadayansu ransa sai ya fara baci ganin suna ta kuskus har ya mike kome ya Tuna sai ya koma ya zauna ya na kallon Abba kafin yace"Abba daman ina so mu yi mgana."
Abba ya gyara zama yana kallonsa kafin"Ina sauraranka Abubakar"
Sadiq ya gyara zama yana fadin"Lokacin da Hatsarin nan ya Faru dani ka samu Labarin Sadiya da Sajida sun bi matata har zariya sun ci mata Mutumci da Tsohon ciki suka koreta suka kuma kwace makulin dakin da wayarta har da Atm din bankinta? Ko ka samu Labari?
Abba ya jinjina kai kafin yace"Tabbas na samu labari. Surayya ta sanar dani komai tun a lokacin."
Ya fad'a ya na kallon Umma da ta Tsargu ta sunkuyar da kanta
Su Sajida kuma sai suka fara Zare ido.
Cikin gyada kai Sadiq yace"Yauwa daman dalilina na yin shuru ban Dauki wani mataki ba shine ina fama da jinya sannan aka zo aka yi ma Siya aiki na samu karuwa, kuma ni daman na Riga na gama Tarasu ne Abba zan yi musu iyaka da iyalina kada kace ban kyauta ba."
Kai Tsaye Abba yace"Ka yi musu duk abunda ka yi ra'ayi, domin wannan karin nima sai naci mutumcinsu Tunda sun Tsallake Hurumin da ba na su ba."
Jin haka yasa Sadiq ya mike Zumbur ya nuna su Sajida da yatsa kafin ya fara fad'in"Wallahi Tallahi kun ji rantsuwar d'an musulmi in dan ku ka kara shiga Hurumin matata sai na saka Shari'a ta yi min iyaka da ku gabadayan ku."

A razane suka kallesa Sadiya tace"Eh Saboda mace za ka saka shari'a ta yi mana iyaka fa kace Sadiq?
Kai Tsaye yace"Kwarai ma da gaake, ai ko a yanzu sa'a kuka ci wani abu mara dad'i bai samu matata ba da na rantse da wanda raina ke hannunsa sai na yi kararku, kuma kunsan Tsab za'a hukuntaku saboda kun Shiga Hurumin da na  ku ba, uwa uba kuma kun ci zarafinta a matsayinta ta yar Adam kuma yar kasa."
Mamaki ya hanasu kara mgana sai kallonsa suke yi baki bud'e.
Umma kuma sai Harara ta ke jifanshi dashi baisan tana yi ba.
Cikin Fushi ya Cigaba da fadin"Ina ruwan ku da ita? Ko ku kuka auramin ita ? Ba wanda ya taba taimkamin da sisin kwabo wajen Rike ta, shine kuma zaku rika shiga cikin Rayuwata kuna min katsaladan? A kan wani Dallili na saka ku ne? In ku baku yarda da Allah ba ni na yarda da shi na kuma san duk abunda ya Faru dani mai kyau ko akasinsa daga Ubangijina ne Siya bata isa ta zama Silar faruwar wani abu gareni ba face abunda Ubangiji ya kaddaramin, Kashedi na gare ku shine ni ne dolen ku, dani ku ke da alaqa ba da ita ba, so ban  yi ma kowa Dole ya karfafa alaqa da Siya ko ya'yana ba, ku kyale ni da su ni ne Dolensu ita din matatace ni ya kamata na kula da Hakkokinta tare da Amanarta, ban kuma ce kowacce taje ta yi mata barka ba, ban kuma ce nima ku yi min ba, duk ku je na yafe wanda yaga dama ya yi abu mai kyau kansa ya yi mawa ba ni ba, ni dai karfafan Kashedi na shine ba Ruwan ku da matata in kuma baku ji ba ku sake Shiga harkaarta ku ga yadda Shari'a zata Shiga tsskanina da ku."
Sajida sai ta saka kukan munafunci ta na fadin"Abba Umma kuma gani dai ko? Kuna ji yana fadin zai yi shari'a damu Saboda matarsa ko? Ai dai mu ci Darajan mu yayyensa ne muna gaba da shi."
A fusace Sadiq yace"In kun girmeni ai baku halliceni ba? Ko kuma domin kun girmeni sai na zauna kuna min cin kashin da kuka dama?
Ai girma ba Haihuwa ba ne, bazai hana naci zarafin duk wanda yace ni zai ci nawa zarafin ba, ko da akace bin na gaba na tare da Bin Allah, in babba bai kama girmansa ba karami na daidai da ya taka girman babban ya wuce abinsa."

Umma ta gaji da jin mganganunsa ta mike ta daka masa tsawa kafin tace"Kaji kunya, kai yanzu Saboda Mace ka ke zagin yan'uwan ka?. Mace ma wata bakar Annoba wacce ta so kashe ka."
Kafin Sadiq ya yi magana ya Rigasa da cewa"Salamatu ki koma ki zauna."
Cikin mamaki Umma tace"Abban siyama."
Kallonta ya yi yasa bata karisa mgana ba ta koma ta zauna.
Shi kuma Abba sai ya kalli Sadiq kafin yace"Kyalesu hakanan ai ka yi musu iyaka, nima kuma na shata musu layi matukar ba alheri ne zai kai ku kusa da iyalamsa ba kada ku kara zuwa, sannan mgana ta karshe duk abunda kuka san kun amsa daga Hannunta ku taka da kafarku kuje ku maida mata sannnan ku tabbatar da kun bata Hakuri, in kuma ba haka ba wlh dukkan ku sai na yi mummunan saba muku"
Suna jin abunda Abba yace suka fashe da kuka gabadaya wannan karon na gaske ne.
Tunda ba su dauka har Abba zai Bud'e musu wuta haka ba, Umma kuma da suka Dogara da ita Abba ya hanata mgana.
Sajida cikin kuka tace"Don Allah ka yi hakuri, mu fa Umma ce ta ce mu je mu koreta ba laifin mu ba ne."
Umma ta kallesu ta na Hararansu Abba ya ya hade rai kafin yace"Ya rage naku, ni dai kun ji matsayata itama wacce ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login