Showing 78001 words to 81000 words out of 116366 words
ba. Ba gidajen su har wajen Umma ta Dauke kafa ta Daina zuwa ita kuma Umma ta yi fushi tace a kyaleta Tunda Sultana ta nuna ta na da wacce ta fita, ta koma ta kama yan'uwanta na Shinkafi tare da matannin Ubanta shikenan.
Ita Umma Taurin zuciyar Sultana da Sakarcinta yasa ta fita sha'aninta, da abunda ta ke nunawa na Tsanar ya'yan Sadiq kiri kiri a gaban mutane ita bata damu in ta tsani Hasiya wannan Dabam, ammh yaran fa? Ko ta manta ba jinin Hasiya ne kad'ai ne a jikin yaran ba har da jinin Sadiq, kuma in da alkwari ai Ruwa bazai yi gangancin Dafa kifi Sadiq dan'uwanta da duk inda taga jininsa abun karramawarta ne, ballatana yanzu da ya ke matsayin mijinta.
Tasan da Farko har da ita wajen saka ma Sultana Tunanin Banza ammh Daga baya ta maidata gidan mijinta ta bata Shawaran ta zauna ta yi masa Biyayya da kissan nan na mata ammh Sultana bata ji mganarta ba, ita kuma yanzu Tsakani ga Allah yadda ta ke son yara nan duk wanda yace baya son su itama bata kaunarsa.
Sannan Tunda Mallam yace in da ace Sadiq bai auri Hasiya wannan Rabon ya'yan da ke Tsakaninsu ko da aure ko ba aure sai sun zo duniya.
Acikin zuciyarta taji ta saki komai, ta kuma san inda a lokacin Sadiq yazo da mganaar auran nan tana cikin yan gaba gaban hana lamarin, da Faruwar haka kuma daga baya azo a haifi d'a mara ido ai sai tace gwara da ya yi auran Boye duk daga baya gashi an samu mafita.
Kuma ta fara saki da kiyayyar Hasiya tunda bata taba kamata da wani hali na banza ba, balle ma zuwanta taga kunyarta da Hankalinta da Biyayyarta illarta Daya wannan bakin Canfin da ke tare da ita shi ke kara sanyayamata da Gwiwa, bata kaunar wani abu ya samu magajin gida da gaske ne d'aya Tamkar da Dubu ne.
Ita ce silar had'a auran Sadiq da Sultana tafi kowa son ganinsu tare, kuma ta na son ganin jikokinta ta Tsatson su, Sultana ita ta Rikete tun tana karama Sadiq kuma ita ta Haifeshi tana son su matuka, Soyayyar da ta ke yi musu ne ma yasa ta so kasancewarsu matsayin ma'aurata sannan zata fi kowa Murna in Sultana ta Haifa mata Jikoki.
Sai dai Rashin kunyar da Sultana ta yi mata sannan ta Dauke kafa da wajemta bayan taje ta na yawo da ita wai ta yi mata Gorin Haihuwa yasa Umma ta fita Batunta bata kuma kara bi ta kanta ba.
Kuma hakan da Sultana ta aikata ba wai wani jin dadi ya kara mata ba, kullum tana cikin kunci duk ta rame ta lalace sai kace ta na cikin Wahala.
Abun takaici shine kishin da Zargi sun kasa barinta ta samu sukunun zuciya.
Sadiq har fargaban zuwa Gusau ya ke yi yafi Murna da jin Dadi in yaje Zariyq Saboda yasan har ya gama kwanakinsa ya koma Faranta masa kawai siya zata yi, duk hanyar da zai Shiga Damuwa ta na nisanta kanta da shi.
Ita kuwa Sultana hanyar da zata bata masa ta ke nema, kuma komai zai yi mata sai tace bai yi mata adalci ba ga Zargin bala'i, satin karshe da ya sauka a Gusaubsai da ya yi mata kaca kaca haka suka Rabu zukata ba dad'i.
Bai san waya zaunar da ita ya karanta mata Ranar jumma'a ya ke zuwa zariya ba sannan kuma wai baya tafiya sai Ranar litini.
Kuma ita sai yazo mata Ranar asabar ya yi kwana daya ya koma ranar Lahadi, har ds cewa ita bata yarda ba in ma ana zaluntarta ne bata yafe ba.
Ya dad'e yana kallonta bakinsa a bude yana Tunanin wani irin sake ne ya yi ma sultana haka da ta rainasa?
Tsabar ransa ya baci ko bayani bai tsaya yi mata ba ya balbaleta da Masifa daga karshe yace an zalunceta ta jima bata yi Allah ya isar ba.
Ita bata ga yafi zuwa wajenta sosai saboda su Umma ba, Siya sai ya yi sati biyu har uku bai je ganinta ba.
Da Sun yi waya ya bata hakuri zata ce bakomai ita Kwanciyar hankalinta tajisa Cikin koshin lafiya.
Gusau kuma ya rantse da Allah in ya Dad'e ne ya yi sati Biyu bai zo ba ammh duk da haka bata gani ba har tana kiransa da azzalumi.
Ya fahimci wani abu ta na Dauka wani Rayuwa Siya ta ke yi mai kyau din da ta fi wanda take ciki, ita bata godema Ni'imar Allah da ta ke cikin Gidansa Ba na Haya ba, Allah ya jikan Siya da gidan Haya ta ke zaune kuma bata taba yi masa korafi ba ta zauma da shi Tun bata san cewa shi wani ne ba.
Shiyasa har Gobe Siya ta kwashe matsayi mai girma acikin Zuciyarsa, ita kuma Sultana abunda ta ke yi bata san a sannu sannu take sire masa ba.
Shiyasa wannan karon ya yi tafiyarsa Zariya wajen Siya da su Asim da suka kara wayau suna da wajen wata Hudu da kwanaki, kuma Satin Gusau ya kamata ya je da kuma ya koma Abuja. Ya share kafa ya yi zamansa sai dai ya kira su Umma a waya.
Da an tambayesa shuru bai zo ba sai yace aiki suka yi masa yawa.
Sai da ya yi wajen sati hud'u bai zo gusau ba kanwar naki sultana ta kama kiransa yaki ko amsa kiranta.
Har Tasasai take turamasa na mangaganu ya yi kamar bai gani ba.
Da kuma ya tashi zuwa ranar asabar ya shiga garin kuma da yammah Saboda ya kara nuna ma Sultana kuskurenta Gida ya sauka sai can dare ya isa gidansa.
Taji dawowarsa kila ko Siyama ta fad'amata ta yi masa abinci an ci gayu ammh ko kallo bata ishesa ba ta Riga ta ba'ta garinta a wajensa.
Shi ya kona ma sultana rai ganin ta yi wahala ta masa tarba duk wulakantata da ya dinga yi ammh shine zai dawo tana yi masa sannu da suwa ya kalleta kamar yaga kashi ya shige ciki.
Da wannan Haushin ta bisa ciki Fuu lokacin data shiga ta gansa yana Cire rigane a kansa ta tsaya Hannu rike da kugu ta na fadin"baka lura dani ba ne Yaya Sadiq?
Ko kallonta bai yi ba sai ma kwanciya da ta ga ya yi ya Dauko wayarsa ya na Dannawa.
Kuka ya taso mata ammh sai ta Danne ta taka ta isa gabansa ta saka Hannu ta warce wayar.
Kallonta ma bai yi ba sai kawai ya Juya zai kwanta nan take ta saka hannu ta Juyoshi ta na fadin"Kana ji ina mgana fa?
Cikin kaushin murya yace"Me kika ce?
Ya fad'a ya na kallonta Ido Cikin ido, Sai ta kasa mgana cikin wani irin zafin kishi tace"Na yi maka abinnci ka taso kaci."
Kai Tsaye yace"Na koshi aci lafiya."
Daga haka ya juya mata baya lokaci d'aya yana fadin"Ki tabbatar da kin ijiyemin waya kafin ki fita."
Kawai sai yaji Sultana ta fashe da kuka da karfi harda jiniya.
Ammh bai sa ya waigeta ba Cikin kukan ne yaji ta na fadin"Shikenan tunda ni baka sona ka sakeni na tafi Gidanmu mana."
Yana jinta sai ya yi kamar bai ji ba sai da ta kara maimaitawa sannan ya Juyo yana fad'in"Wani gidan kenan?
Cikin gunjin kuka tace"In da ka auro ni, in kai baka sona Umma na sona."
Wata bazawar dariya ya yi lokaci d'aya yana mikewa zaume kafin yace"Umma? Ke yanzu domin baki da kunya sai ki koma wajen Umma da matsalarki? Kin manta kin gama yawo da ita da cewa ta miki gorin haihuwa?
Sai a lokacin Sultana ta dawo Hayyacinta sai ta dakata da kukanta ta na shan Shessheka.
Cikin takaicimta ya kalleta kafin yace"Yau Umma na gayamin Abunda kika yi mata ta na sharan hawaye, tace bata taba tunanin haka daga gareki ba Sultana, kuma don ma ban zaunar da ita na Fad'a mata irin abubuwan da kike yi min ba, Ai in dai kikace na sake ki ba gidanmu zaki koma ba tunda kince Umma bata son ki yanzu ko ki koma inda ake zugaki ana nuna miki abunda kike yi mai kyau ne, ko kuma ki koma Shinkafi tunda daman kince duk wanda ya bar gida gida ya barsa."
Daga haka ya koma ya yi kwanciyarsa ya kara juya mata baya yana jan karamin tsaki.
Shi kanshi ya sha mamakin Abunda Umma ta fad'a masa, bai dauka Jakancin Sultana ya yi tsanani haka ba.
Sultana kuma sai a yau taji kunyar Nadaman mganganunta ga Umma, su suka taru suka Rufeta ta kara fashewa da kuka tana yi ta na yi har tana dire kafafu yana jinta bai kara bi ta kanta ba.
Sai da yaji tana fad'ar manganuganunta cikin kuka ta ke fad'in"Ka yi wajen wata baka zo wajena ba, ammh nasan kaje wajen matarka kuma ka yi mata abunda ta ke so, ammh shine ni ka zo ka faramin wulakanci da nuna bani da Muhimmamci a wajen ka."
Ta karishe fad'a cikin gunjin kuka yana kwancen yace"Eh baki yi karya ba naje wajenta, kuma ina yi mata abunda ta ke so kuma zan Cigaba da yi mata abunda ta ke so, tunda nima Abunda tasan ina so ko da ban Furta ba shi ta ke kokarin yi min, ki yi koyi da ita domin Siya ta na da Dukkan Sufofin Mace tagari."
Ai Sultana najin haka kamar an Tsunguli bakinta ta bude baki tace"Shiyasa ita ka yi mata ciki ta Haihu, ni kuma da baka kaunata ka kasa yi min cikin da nima zan haihu."
Sai kuka wiwi wiwi kamar wata karamar yarinya.
Kamar wani gaula haka ya mike zaune yana kallon sultana.
Cikin mamaki yace"Shima cikin kina Zargin da gangan na ki yi miki shi?
Kai tsaye tace"Eh mana, ai ita da ka ke so yan Biyu ka bata, ni da baka kauna ko dayan baka bani ba wama ya sani ko yanzu wani cikin gareta."
Cikin Mirmishin takaici yace"Ina fatan Allah ya amsa bakin ki sultana."
Daga haka ya juya zai kwanta kawai yaji ta fado masa a jiki tana fad'in"Nima wlh sai ka yi min ciki, kuma nima yan Biyu na ke so."
Kallonta ya ke yi kamar yaga Mahaukaciya sabon kamu.
Cikin kaushin Murya yace"Ke dagani ba na son sakarci."
Sai kawai ta kara sakamasa kuka tana fadin"Nima ai ina da hakki a kanka in bazaka bani ba shima sai ka fad'amin."
Shifa ya fara Tunanin ko Sultana kwakwalwarta ba lafiya, bai isa ya ce bazai yi mata abunda ta ke so ba Tunda itama ta na da Hakki a kansa.
Duk da ransa baya so hakanan ya Danne zuciyarsa ya biye mata ya bata Hakkinta kamar yadda ta ce.
Yana samun natsuwa ya tashi ya barta nan kwance yaje ya Tsarkake jikinta ita Tsabar ma sakarci da kishinta na Jahilci bai sa ta Fahimci mace na son gyara wajen dawo da Hankali miji a kanta ba.
Tana kwance cikin bargo ta na kallonsa yana Tsane ruwan da ke kansa daga murya ta yi tana fad'in"Allah yasa ka yi min ciki yau."
Tsaki yaja mai girma kafin ya Juyo ya na kallonta sai da ya kariso gabanta.
Sannan ya kausasa murya yana fadin"Ni ban isa na baki ciki ba Sultana, ina so ki sani Ubangiji shine mai komai, shi ke samar da Ciki a jikin mace sannan ya Rayar da shi daga Gudan jini zuwa ya Busa masa rai, ni din banza da na isa na ba da abunda ba ni da Hurumi a kansa? Ki saka aranki Allah ke ba da wa, kema shi zaki Roka ya baki mafi Alheri."
Daga haka ya yi gaggawar Ficewa daga Dakin bayan ya Dauki wayarsa da ta watsar nan saman gado, bai jira jin wata mganarta ba.
Falo ya fita ya zauna ya yi Shuru yana Tunanin Rayuwa, Sultana ta na neman ta hanaahi kwanciyar Hankali.
Ya yi iya Tunaninsa ammh ya kasa gano inda ya tauye mata hakkinta.
Saboda ya mamta da Tunaninta yasa ya Kira Siya har ta fara barci ya tasheta yace su yi hira.
Ya tambayi su Asim tace ta baro su aciki tare da Habiba sun yi barci da Wuri, da alamun akwai su da zarin cikin Dare.
Sadiq har wani gyara kwanciya ya yi a saman kujera na zaman mutum uku, Hira ya ke yi cikin Annushuwa da Farinciki da ya saba kasancewa aciki in dai yana tare da Siya.
Har ga Allah bansan Assadiq na Gusau ba tunda bai gayamin ba.
Hira na saki jiki ina yi masa duk da akwai gajiya tare dani tunda da Safe akwai makaranta Tp din mu sun kara mana wata daya mun samu an zo Dubamu sau biyu saura daya.
Ina basa Labarin yadda su Asim ke da Farinjini a makarantar ne.
Har mai makaranta daukansu ya ke yi su tafi office ko kuma in zai yi zagaye malamai har fad'a suke yi wajen daukansu ni kan nace masa bani da matsalan Renon su Asim yanzu.
Sadiq na dariya yace"Ko? To shikenan nan gaba Allah ya kawo wasu yan ukun lafiya."
Da Sauri nace"Astagafrullah.."
Cikin yar dariya yace"Ki ma shirya, ina harin yan uku ne wannan karon"
Cikin Shagwaba nace"Haba dai ni dai ka bar wannan mganar Assadiq kada ka fad'i gaban yan Amin su amsa hakan ta faru."
Cikin danne Dariyansa yace"To nasan Siyata jarumace zaki iya"
Ya shagala da wayar da ya ke yi baisan Fitowar Sultana ba.
Sai da yaji an fizge wayar hannunsa cikin Tsananin kishi idanuwan Sultana Jajir ta saukemai daya dago ya na kallonta.
Cikin mamaki yace"Miye haka? Ko baki ga ina waya ba ne?
Sultana ta Duba wayar ta kunnata Haske ya bayyana.
"Siya ta.."
Shine sunan data gani ya kira kuma har Lokacin Tana kan layi, kishi ya gama Rufe mata ido yasa ta kara wayar a kunne ni kuma daman n sandare da mamaki tunda kunnuwana sun jiyomin muryan Assadiq yana mgana kafin na gama Tunanin tare da waye ya ke mgana naji muryan Sultana cikin Masifa ta na fadi'n"To tsohuwar kilaki, mai kwacen mijin wata macijiyar da bata ramin kanta, kin kwace min miji na kyaleki duk da haka bai isheki ba sai kuma yana tare dani ki rika kiransa kina masa barikin da kika saba ko?
A fusace Sadiq ya mike yana fadin"Ke sultana bani wayata, kada ki zageta fa"
Ammh sai ta koma da baya ta cigaba da chabamin manganun Tozarci da cin Mutumci ni kuma ban maida mata martani ba.
Illah hakurin da na bata na kashe wayar, ina Tunanin me yasa Assadiq ya kirani yasan cewa yana tare da matarsa?
Acan kuwa Sultana ta Rotsa wayarsa da kasa ransa shi kuma ya baci Haushi ya kwashe shi ya tsinketa da mari nan ta durkushe ta na kuka shi kuma ya duka yana Tattara wayarsa cikin Huci.
Sultana na Dafe da kunci tace"Ni ka mara Yaya Sadiq?
A fusace yace"Kirani da Abubakar dina, zai fi min da kirana da kike da yaya bana so."
Cikin kuka da hawaye tace"Akan wata banzar bazawarar matarka ka mareni? Akan matar da ka sameta a sauran wasu ka tozartani?
Cikin Idanuwanta ya kallah kafin yace"Eh a kan wannan bazawarar da kika raina a kanta na mareki, kuma daga yau ina so ki sani in kika Kuskura kika kara kiranta da banza sai na ci miki mutumci sunanta Hasiya ba bazawara ba, in bazaki Darajata ba a kallah ni ki bani Darajar da Allah yace ki bani, kuma gargad'ina da ke shine na rantse da wanda raina ke hannunsa in baki shiga Taitayinki dani ba sai na jefar da Rayuwarki a cikin Rayuwata sai lokacin ne zaki gane ke din banza ce a wajena."
A fusace ya kwashi farfasshiyar wayarsa zai wuce cikin daki sai kuma ya dakata ya Juyo yana kallonta ya nuna ta da yatsa Lokaci daya yana Fadin"au na manta ban fad'a miki ba, ita wannan bazawarar da kike ganin kin rainata ta fi min ke sau Dubu wlh"
Daga haka ya Buga iska fuu ya Shige dayan dakin ya Bango kofa ya bar Sultana Zaune a saman cafet ta na gunjin kuka.
Tun tana kuka da karfi har ta gaji ta koma yi a sannu kanta ya fara sara mata, nan ta yi barci bata sani ba Sanyin Asuba ya tada ita taja kafafunta ta Shiga dakinta.
Fuskarta ta kalla a madubi har in da ya mareta ya tasa, ita ba marin ne ya dameta ba sai da yace wai Hasiya ta fita a wajensa sau dubu, ita yanzu ashe a banza ya ke kallonta?
Dakyar ta yi sallah sai kukanta ya Dawo Sabo.
Ta rasa wazata tunkara gashi ta bata rawanta da Tsalle a wajen Umma.
Kuma bata isa ta tunkari gidansu da wannan mganar ba kilama Babanta sai ya kara mata.
Daga karshe ta kira Surayya ta na kuka ta gayamata abunda ke faruwa
Saboda tasan su Sajida ba abunda suka isa su yi, tunda Sadiq ba jin mganarsu ya ke yi ba gwara Big sis din.
Surayya kuma Hankalinta ya tashi jin harda duka da safiyar nan duku duku ta yi Driving zuwa gidan a Haraban gidan ma suka hadu da Sadiq ya Dawo masallaci Tunda ya ganta yasan Sultana ce ta kirata ko d'ar bai ji ba shi daman fa ya gaji gwara a san abun yi yarinya karama bazata zo ta hanashi Zaman lafiya ba, ina bata isa ba wlh.
Tare suka shiga gidan tana Tambayasan ina matar gidan? Yace shi bai sani ba ta Dubata.
Ita ta shiga dakinta ta sameta ta na kuka.
Sultana ganin Surayya yasa ta kara jiniyan kukanta.
Dakyar ta lallasheta ta yi shuru kuma ta nuna mata wajen marin taga ya Kumbura.
Duk da Sultana ta fadin duk abunda ya Faru Surayya bata tsaya anan ba ta tarasu tare tace kuma Sadiq ya yi mgana.
Yace shi bazai ce komai ba in har ta bari ya yi mgana sai ta raina kanta.
Abu daya ya sani ya gaji da zama da ita Tunda tana zargin baya yi mata adalci gwara ta fad'i abunda ta ke so ya yi mata kowa ya Huta.
Sai Tsoro ya kama Sultana jin abunda yace ta fara kuka Dakyar Big sis ta lallashesa ya fadi laifin da take yi masa.
Ya ce na farko bata darajashi, na Biyu ta raina shi na uku ta dauki wasu ta fifita sama da shi, na hudu kishinta na Hauka na Biyar ta na zarginsa da bata zama lafiya da shi.
Nan fa Surayya ta yi ma Sultana fad'a Sosai ta kuma sakata ta duka ta bashi Hakuri tare da alkwarin zata bar komai da ta ke yi zata kuma gyara dakyar yace ya Hakura ammh in ta kara ya rantse da kansa