Showing 114001 words to 116366 words out of 116366 words
Gudiyo da Yabi.
Tunda naga na samu natsuwa Su Asim da alamu dai sun zama yan gusau nima sai hakan ya fi min dad'i.
Junior ba shi da rigima in na yi masa wanka yaji Ruwan zafi shikenan sai barci.
Assadiq kuma na wajen aiki sai na Tattara hankalina na maida shi kan Rubutun da na fara ina so naci karfinsa.
Da karfin gwiwan mijina da taimakonsa tare da shawarwarin marubutan da na nema kan Rubutun na kamallah Rubutun bayan daukn Lokaci mai tsawo.
Wanda daga baya har sai da na Sare kamar na hakura sai kuma Assadiq yace tunda na fara na karisa.
Sai da na gama Tas duk na Tura musu suka Dubamu kuma suka yab'amin sosai.
Auntysis ta yi min sharhi mai Tsawo sosai Anty Habiba kuma tace Rubutun da na yi bata tab'a tunanin zan iya yin shi ba sanina da ban tab'a Rubutu ba.
Surayya Dee ita ta taikamamin da Editing ta gyaramin ka'idojin Rubutu a cewarta Rubutun zai amfani al'umma zata taikamamin ya fita yadda zai zama mai kyau da amfani wajen al'umma.
Assadiq ya bani shawaran na nemi cikin manyan marubutan maza ko da wata Shawaran da za su taimakamin da shi.
Sai na bashi damar haka, bayan na Tambayi Lambar ALHAJI AHMAD ADO GIDAN DABINO.
Na bama Assadiq ya kirasa ya yi masa bayani mutum mai barkwanci da ba ma mutane Lokacinsa.
Da yardan mijina muka Tattauna da shi ya yi min jinjina sosai sannan yace zai fanshi Copy 10 in na Buga in sha Allahu.
Sannan watarana in na Shigo kano zamu had'u zai taimakamin da wasu daga Cikin Littafansa da za su kara taimakamin sukara karamin kaifin kwakwalwata
A lokacin dariya na yi kafin nace"Ai bazan kara wani Rubutun ba, wannan ma saboda labarin Rayuwata ne shiyasa na Rubuta."
Shima Mirmishin ya yi min kafin yace"Na duba Rubutun ki, kuma na yaba miki ina da kyakyawan yakinin a nan gaba Mutane za su karu da Basirarki."
Da ya ke na Tura masa shima ya Duba min tare da gyaramin inda ya kamata.
A kano suka shigemin gaba na Buga Labarina mai taken TSAKA MAI WUYA.(LABARIN HASIYA)
Wacce HASIYA MAMMAN KONA TA RUBUTA.
A kasa kuma na saka (MATAR ASSADIQ).
na kuma yi sadaukarwa ga Mahaifaina guda Biyu, Alhaji Mamman mammadi kona da Mahaifiyata Hajiya Aisha Jari Mamman.
Sannan nace littafin Babban Tukwaici ne ga Mijina Babansu Asim ABUBAKAR SULAIMAN ABUBUKAR SHINKAFI(MIJIN SIYA).
Na gaida yan'uwana da kawayena da suke tare dani daga Farko har karshe.
Alhamdulillah ba abunda zan ce ma Allah sai godiya.
Assadiq ya Dauki nauyin Buga littafin Copy 200, Tahir ya ce ya fanshi ma Hauwa'u copy goma.
Adda Fati ta fanshi biyar ita da Adda Rukayya.
Ramatu ma haka ita da Safiya.
Abba ma da Assadiq ya gayamasa yace abu me mai kyau ya famshi Copy 30.
Duka yan'uwan mijina sun fanshi Littafan nan kuma sun tayani yawo dashi domin ya samu karb'uwa cikin Sati Biyu wanda aka Buga duka ya kare, kuma ni da farko a kyauta na so na bayar da shi Assadiq yace a'a na amshi kudi ko ba da yawa ba.
An sake Bugawa sannan kuma ya shiga Hannun mutane ta dalilin yan'uwan mijina da yan'uwana Tunda suna harkan jama'a.
Sannan Marubuta ma sun yi min kokari sosai.
Na kuma gode musu, sai bayan da na Fitar da Hardcopy da wattani uku na Fitar da Sofy copy din shi ta Kafafen Sada zumunta.
Ammh Shi a kyauta na ce a yad'a shi kuma Kyauta ne na musamman ga mata da suka Fuskancin kalubale kwatankwancin irin nawa.
Da yakinin cewa suma za su samu Kyakyawan Rayuwa anan gaba kamar yadda na samu.
Sannan da fatan Mutane za su daina kyamarta irin mu da kaddaran kan fad'a mana sai a kiramu masu farar kafa ko wani abun da ba shi acikin Addini.
Su kuma san cewa wani abun ba Aljanu ko mutum ba ne, komai daga Allah ne, sannan duk wani abu da zai faru daman ya na bukatar SANADI kamar yadda ni Hasiya na zama Sanadin Rasa dukiyar Abubakar tare da Rasa lafiya a bangaran Salisu.
Sannan da kara ma zawarawa kwarin Gwiwan cewa suma mata ne, kuma masu galihu kamar sauran mata.
Da kuma nuna ma duniya cewa Zawarawa ba kilakai ba ne sannan ba Yan duniya ba ne, kuma ba'a son ransu suke zama zawaran ba da yawan mu kaddarace ta ke fad'a mana
*******
*MURFI.*
*BAYAN SHEKARA D'AYA.*
*BBC ABUJA.*
Assadiq ya rakoni ofishin BBC da ke Abuja inda suka kirani sun gayyaceni za su yi Hira dani.
Tare da Junior muka zo, sai kuma karamar jaririyar da na haifa ko arba'in ban yi ba wacce ta ci sunan Innani Hadiza muna kiranta Afra.
Sanye na ke da wani less golden Mayafin jikina da takalmin kafata duka Golden ne.
Ba kwalliya na yi ba tunda ban saba ba.
A shekara d'ayan da na Wallafa labarina na TSAKA MAI WUYA.
Ya Zaga duniya ya shiga in da ban taba Tunani ko tsammani ba.
Na samu kira kirayen waya akan matan da suka fuskanci Tozarci akan Zargin Farar kafa ba adadi.
Da wad'anda suke kan fuskantan haka, sannan na samu matan da sanadin zawarci ne suke fuskantar Tsamgwama daga mutane da cin mutumcin barin ma in suka samu miji saurayi ko wamda bai da shekaru zasu aura sai a rika kiransu masu kwacen maza.
Matsaloli ga su nan wasu su sakani kuka wasu kuma su tunasar da ni Rayuwata ta baya.
Lokacin da Ma'aikacin Bbc ya ke min tambayoyi, ya tambayeni shin da gaske ne wannan Labarin da na rubuta Labarina ne?
Ina Mirmishi nace"Tabbas Labarina ne, sai dai na Boye sunayen wasu da kuma sauya hallaya wasu da garuruwa ammh tabas ni ce wannan Hasiyar ta cikin Labarin TSAKA MAI WUYA, wacce ta fuskanci Tozarci da kyamar al'umma saboda Canfin ina da Farar kafa, kuma ni ce na fuskancin Tashin hankalin kirana da wasu suke yi da sunan Mayya da sunaye marasa dad'i.
Sannan ni ce wacce na yi aure har Biyu ta dalilina mazajen da na aura suka samu rasa lafiya da asaran dukiya, ni ce wacce duk wanda na Rab'a sai ya shiga Tsaka mai wuya sai na raba tashin hankalinn Rayuwata tare da shi."
Dan jaridan ya tambayeni yadda na rika ji in kirana da sunan mayya ko mai Farar kafa?
Sai naji hawaye sun kawo cikin idanuwana.
Cikin rawan murya nace"Na kan ji wani irin daci acikin zuciyata sai naji kamar duk duniya ba kowa sai ni kad'ai daga baya na fara Tsanar kaina da Tunanin gwara na mutu na Huta, abun ba dadi ko kad'an shiyasa na ke so mutane su sani su kuma kara sani _BABU WANDA YA ISA YA YI MA MUTUM ABUNDA ALLAH BAI TSARA MASA CIKIN KADDARANSA BA.
SAI DAI MUTUM YA ZAMA SANADI.
SANNAN MU YARDA DA ALLAH MU KUMA SAN CEWA FARAR KAFA ZENCEN MUTANE NE, BA WATA MACE MAI FARAR KAFA TUNDA MU ANNABIN RAHMA KAMBUN BAKA YA SANAR DAMU._"
Ya sake tambayata shin kuma bani da Aljanu?
Sai da nayi dariya kafin nace "Ba ni da Aljanu ko wata matsala, kawai ni na zama SANADI ne.
A Karshen Tambayoyinsa yace" Malama Hasiya daga karshe me ya baki kwarin gwiwan Rubuta Labarin ki sannan ki yad'a ma duniya?
Kai tsaye ina kallon Assadiq nace"ASSADIQ. MJIN HASIYA.! Shine tsanin da na taka kuma shine gwarin gwiwar da na samu wajen Rubuta labarina na tura shi ga duniya.
Kuma shine Mijin da ya aureni duk da lokacin ina cikin Tsaka mai wuya, kuma shine ya fara nuna min cewa ba ni da farar kafa ya kuma fara sanar da ni cewa BA ABUNDA YA ISA YA SAMENI SIYA SAI ABUNDA ALLAH YA KADDAROMIN CIKIN KADDARATA.'
Sannan ya aureni ina a bazawara ya zauna dani cikin Tsaka mai wuya sannan ya ji Tausayina ya tsaya min kuma ya kareni bayan ya zama garkuwata.
Kafin shi mahaifiyata ta jima ta na nuna min cewa nima watarana zan samu kyakyawan Rayuwa, sai da na had'u da Assadiq na gasgasta haka."
******
Muna tafe a motar Assadiq zamu koma gidanmu.
Ina gaba kusa da shi rike da Afra Junior kuma na kan jikinsa.
Sai faman mirmishi ya ke yi ya na kallona, na gaji da kallona da ya ke yi yana mirmishi.
Cikin yar dariya nace"Assadiq me ya faru?
Hankalinsa na wajen Tuki yace"Ina Tausayama Abubakar da Salisu, domin sun tafka asaran rasa mata kamar ki Siya."
Ina yar dariya nace"Allah sarki kasan da ya ganni a kasuwar kwari haka ya rika kallona ya yi mamakin ganina sosai."
Da ya ke watan jiya mun je kano gidan shahida suna ta haihu.
muka shiga kasuwa tare da su Anty Surayya sai gamu shagon da Abubakar ke yi yaron shago.
Ji kawai na yi ya kira sunana cikin mamaki na juya nima sai na gansa na kira sunansa.
Abubukar ya tsufsa duk ya yi wani iri, yace min matansa daya da yaro d'aya bai jima da aure ba.
Tunda ya rasani shikenan yaji aure ya fita kansa.
Lokacin muna tare da su Asim kuma ga ciki a jikina kafin na Haifi Afra ne.
Har kyautar kudi ya basu har kuma muka bar shagon nan bai daina kallona ba, ina gani ya na sharan kwallah.
Har ce min ya yi Hasiya ki yafemin don Allah.
Ni kuma nace bai min komai ba na yafe masa duniya da Lahira.
Salisu ne bamu kara had'uwa ba ammh duk sanda ya ga Ramatu sai ya ce ta gaisheni.
Har muka isa gida Hiran yadda Labarina ya karb'u mu ke yi da Assadiq.
Ima fad'a masa ko a yanzu Burina ya cika mata ire irena za su samu saukin Tozarci.
Muna isa gida na samu kiran wata itama daga Bauchi.
Tana kuma t gayamin itama ta yi aure ammh mijin ya saketa
Yace tunda ya aureta ya ke ganin Bala'i mutane sun ce ita ce mai kashin Tsiya da farar kafa karshenta ya saketa.
Kuma dalilin haka kowa yazo neman aurenta sai a bat'a abun ace ta na da Farar kafa wanda ya aureta ya auri bala'i da masifa.
Ire iren Labarai irin nata suna da yawa, ko da yaushe cikin kuka na ke yi ina kara godema Allah.
Assadiq ya zaunar da ni ya na lallashi na tare da cewa na godema Allah.
Tunda ga yadda Rayuwata ta mika.
Sai kuma naga gaskiya ya fad'a.
Duk da dai ba ka ce ka samu komai Dari bisa dari ba ammh a kallah ka samu daidaitan Rayuwa 70% sai ka godema Allah.
Kafi wani, wani ma ya fika sannan na Juya naga Ya'yana yanzu Hud'u sultana ke da Biyu itama, duk da har yanzu ba ma jituwa ammh tunda na san Halinta sai na ci mganin zama da ita.
Kowa ya daina Biye mata tunda bazata sauya ba.
Na duba naga hatta dangin Babanmu na Zariya ma sun daina kyamata ta tare da kirana da sunayen banza sun Fahimci ba haka ba ne.
Sun saduda sun koma ga Allah
Naga duka yan'uwana mijina suna sona da kaunata sai abunda ba'a rasa ba tunda bazaka ce ka samu kowa yadda ka ke so ba.
Yanzu haka Sajida ta koma gidan Mijinta sun daidaita.
Sannan Su Asim suna Gusau har an saka su makaranta.
Innani ma na nan da Ranta Har yanzu Lokaci bai yi ba.
Sai dai a kan wannan keken yanzu ta ke Rayuwa.
Na tuna Amma na can tare da ya'yan Adda, cikin kulawa da zaman lafiya sun kamata sun rike gam.
Har ta aurar da Badd'o mun je mun sha biki.
Sai dai mu je mu ganta mu gaisheta mu yi mata alheri.
Sannan a gefe d aya Assadiq tafiye tafiye ya ke yi, tunda yanzu shima a na turasa garin da suke aiki.
Sai ya yi wata baya nan ko sati uku, Sultana bata daina kishi da zargi ba, ammh dagani har Assadiq ba ma Biyemata muna kokarin nuna mata adalci.
Daidai gwargwardo ba bu abunda Assadiq ya rage ni dashi, Ya bani jari kamar yadda ya yi alkawari na had'a da kudaden hannuna na kafa kasuwancin saida kayan mata, irin su less, Atamfofi, mayafai, takalma, dogayen riguna, yan kunnaye, material komai na kayan Adon mata ina Saida su, mun had'a hannun jari ni da Anty Shahida da ke kano tare da Anty Surayya mun saka a manyan kantuna kasuwan kwari, sannan gefe daya muna tafiyar da harkan kasuwancin mu ta waya, burina ya cika na zama yar kasuwar da na jima ina fata da Buri.
Alhamdulillah.
Idanuwana suka kawo ruwa cikin sanyin murya nace"Hakane rayuwa ta na tafiya daidai, duk da ba yadda bawa ya so ba, ammh muna godiya da irin tamu Ni'imar da ya yi mana."
Rumgumeni ya yi ya na lallashima.
Ya sharemin hawaye yana fadin"Ko ke fa yar Zabiyar mata ta."
Na ture shi ina Dariya, zabiyar da ya kirani yasa muka Tuna da Tahir.
Shima Hauwa'u ta sauka Tsakanin mu ba nisa.
Sai da muka yi shirin kwanciya Assadiq na ganina da waya ya kwace ya kashe Lokaci d'aya ya na fadin"Siya yanzu fa Lokacina ne."
Dariya na yi kafin nace"Ni da safiya ne kasan ni ce babbar kawar Amarya, tun ana saura sati daya zan tafi."
Assadiq na hararata yace"Ko dai zaki tafi ne sai ta haihu sai ki dawo?
Kyalkyacewa na yi da Dariya sai ga Afra ta motsa.
Sai ya nuna min baki alamun na yi shuru yadda ya koma ya na lallashinta ne yasa na koma
Gefe ina masa Dariya, Sai da ta koma barci ya zo ta bayana ya kwanta yana fadin"Muguwa wato kina so ta hanani shagali, kinsan kuma Gobe gusau zani wajen Sultana."
Ina rike hannuwansa nace"Can ma ai zaka yi shagalin ko?
Kafad'a ya noke kafin yace"A'a yau romon Siya na ke so na sha, gobe sai na sha na Sultana."
Mintsinan Hannunsa na yi ina Dariya shi kuma ya cijeni a kunni.
Sai muka koma muna rama in rama.
Kaina ya hau yana fadin"Na sauka ne ki rama?
Sai na Boye kaina a saman kirjinsa ina Dariya.
Ban isa na hana Assadiq shan Romonsa ba.
ALHAMDULILLAH.
RAyuwa ta na tafiya daidai, duk da Assadiq ba zai zama mai arziki ba ammh yana zaune damu cikin Rufin asirin da Allah ya wadace shi.
Ya ci damu ya sha damu sannan ya biyamana Bukatanmu na alheri.
Daman bai zama lalle ka samu abunda ka ke so duka ba in ka samu mafi Rinjaye sai ka gode masa.
Kar'she.
*ALHAMDULILLAH. Nan na kawo karshen Labarina mai taken TSAKA MAI WUYA, nagode ma Ubangijina domin da ikonsa na fara na kuma gama shi lafiya, ina fatan abunda na Rubuta daidai Allah ya bani Ladansa, kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min, Dan adam tara ya ke bai cika goma ba, in ku ka ga wani kuskure ku dauke sa a matsayin ajizanci ne na Dan'adam.*
*Nagode ma Masoyana da suka biya kudinsu wajen bibiyan Labarin nan tun daga farko har karshe, Nagode Ubangiji ya albarkaci kasuwanci Allah ya bar zumumci ya kuma had'amu a Aljannah Firdausi.*
*Janafty*