Showing 111001 words to 114000 words out of 116366 words

Chapter 38 - Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

344

mgana.
Da safe ita zata dafa musu abun karyawa kamar su tea, soya kwai ko doya ko dankali.
Da rana kuma nace ta dafa abunda ta ke so, in kuma wani abu zata sha ko goldemorn ko Cornfl sai ta jika ta sha, da Daddare kuma na kan nuna mata abunda zata yi ko ta Dafa shinkafa jalop ko taliya.
Sai dai ina gefe na toshe hanci watarana na wanye lafiya watarana kuma na yi ta kwarara amai.
Assadiq kan siyo Tuwo watarana da daddare in yaji sha'awan haka.
Wannan watan ganin Amna yasa yace zai je gusau ya Duba Sultana da su Umma nace yakamata.

Ranar jumma'a ya tafi da safe ya barni dagani sai Amna.
Ni fa kwanciya ce aikina kamar wata mai laluran barin jiki.
Wayar ma yanzu in ba kirana aka yi ba, bana bi ta kanta.
Kwana Uku Assadiq ya yi ya dawo ya kawomin Hotunan su Asim da Viedo da ya yi ta daukansu.
Sai suka karamin girma a ido, yace ko damuwa ba su yi sun zama yan gida.
Har Innani sai da tace ya'yan  magajin gida sun zo da alheri gidan nan.
D'an zagayen da suke yi a bangarenta tace yana deb'e mata kewa sosai.
Kuma yace da zai tafi ba su yi kuka ba har suna yi masa Bye bye.
Umma na cewa ba za su ku je wajen Mami ba? Suka noke a jikinta.
Ina dariya nace"Shikenan sai mu bar ma su Umma, mu ma zamu haifi namu Allah ya bani yar mace ina so Assadiq."
Yana kallon Wayarsa yace"Allah ya baki, mafi alheri siya."
Na amsa masa da Ameen.

Sai washegari da bai fita aiki ba baya jin dadi zazzabi ya kwana da shi.
Sai nace ya kwanta a gida ya huta sai dai ya kira can  wajen aikin su ya gayamusu.
Dani da shi ranar a daki muka yini, muna shan soyayyarmu da Hiran mu.
Muna kwance ya bani wayarsa ina kallon Hotona sai naa ga Ummi an Dauketa ta yi kiba kamar ba ita ba.
Sai na juya ina kallonsa ya na kwance ya Rufe ido ammh ba barci ya ke yi ba.
Tab'osa na yi kafin nace"Na manta ban tambayeka ba ya su sultana da Ummi?
Fata suna lafiya?
Assadiq ya yi shuru kafin can ya mike zaune da sauri yana dariya.
Cikin mamaki nace"Miya faru?
Cikin gyad'a kai yace"Sultana na can na kuka wai na yi sonkai na kara yi miki ciki ita ban yi mata ba."
Ido na zaro ina kallonsa shi kuma sai ya yi dariya kafin ya cigaba da fad'in"Wlh rigimar da naje tarar ta na yi kenan, tace ba na mata adalci ina Fitita ki a kanta, da farko cikin yan Biyu na yi miki ita kuma da ba na kaunarta d'aya na yi mata shine yanzu da son kai da rashin Adalci na yi miki Ciki ita ban yi mata ba to wlh itama bata yarda ba in ina son na zama mai adalci itama na yi mata ciki."
A tare da ni da shi muka Fashe da dariya cikin Dariya nace"Assadiq to kai baka yi adalci ba, me yasa ka dawo ba ka yi mata cikin ba?
Mirmishi ya yi kafin ya koma ya kwanta ya yi filo da hannayensa.
Cikin Tattausan lazafi ya kira sunana"Hasiya."
Na amsa masa sai ya mika Hannun ni kuma na kama ya jawoni jikinsa ya Rumgumeni na yi matashin kaina a saman kirjinsa.
Cikin Sanyin murya yace"Ina so na fad'a miki wata magana."
Cikin ba shi hankalina nace"Ina jinka. Sai ka fad'a"
Kai Tsaye yace"Kin san meyasa na gayamiki wani abu daya danganci sultana game da ni yanzu?
Sai na girgiza masa kai, yana shafa kaina yace"Saboda na nuna miki Sultana bazata taba sauyawa ba. Halinta ne haka zafin kishi zargi da kuma rashin son zaman lafiya, a baya  na damu da Fitinarta ammh daga baya da na zauna ma Fahimci halinta har ga Allah lamarinta ya Daina damuna, can u just imaging ta tasani gaba ta na min kuka wai sai na yi mata ciki in ina so na yi adalci.?
Ina yar dariya nace"To sai ka ce mata mene?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Me zan ce mata? Tun ta na bani mamaki sai ta dawo bani dariya da Tausayi, yanzu dai na lallasheta nace ta bari itama zan yi mata ciki tunda shi ta ke so"
Mirmishi na yi ban yi mgana ba shi kuma ya Cigaba da fad'in"Shiyasa na ke son na gayamiki ki yi hakuri da ita don Allah kin ji ko? Tunda mun san halinta mu zauna da ita a yadda ta ke"
Ina jinsa sai na gyad'a masa kai ina fad'in"Baka da matsala dani in sha Allahu"
Da bakinsa ya ke fad'amin wasu daga cikin Rigigiman su, wasu na yi ta Dariya sultana yar bala'i ce wlh.
Yace yanzu duk ta b'ata da su Sadiya aammh yasa ta ba su Hakuri.
Yace Har Umma fa in abunta ya tashi sai ta yi mata yaji tace an yi mata gori ko Umma ma nuna son kai.
Yanzu ma zuwan su Asim sai da tace Umma ta yi sonkai.
To itama Ummi zata kawo mata, Umma tace sai ta bari ta yayeta.
Ammh sultana bata ji ba sai ga shi ta had'o kayan Ummi ta kawo ta wajen Umma.
Ina Dariya nace"Kai to wannan jaririyar aka rabata da uwarta ai sai a dauki hakki."
Assadiq yace"Umma tace Shegantakan Sultana ya isheta wlh, sai da Abba ya shiga mganar yana ta lallashi yanzu dai tace itama ta na yayeta Umma zata riketa Tunda ta rike ya'yan kishiyarta."
Yana bani Labarin ina auna wasu abubuwan.

Nan take na kara tabbatar ma da kaina Sultana bazata tab'a sona ba.
Sannan ko kwanta mata na ke yi bazata bar kishi da ni da gasa dani ba.
Na fahimci duk wani abu da zata ganni da shi sai ta yi kokarin mallakan wanda ya fishi a Tunaninta ta fini, sannan ta na ganin Assadiq ya fi sona shiyasa ya ke nuna mata rashin adalci.
Alhalin adalci daidai gwargwado yana yi mata kishinta da Zarginta da Rashin mutumcinta yasa ta kasa gane komai.
Tundaga Lokacin na fahimci ita Rayuwa ba ta cika 100% bisa dari  in kaji dad'i a wani bangaren Dole ta wani bangaren asamu akasin haka.
Sai ka yi hakuri da yadda taka Rayuwar ta zo, haka kila kafi wasu wasu ma sun fika.
Cikin ikon Allah na Cigaba da Renon cikina Amna wajen wata uku ta yi min sannan ta koma gida tunda za ta shiga makaranta.
Saboda nuna godiya da ni da Assadiq muka maidata har gida tare da shatara na arzikin da Assadiq ya yi mata.

Mun yi mata sabbin d'inkuna kayan kwalliya littafan makaranta da jaka da takalma Assadiq har karaman Ipad ya siya mata saboda karatu.
Adda Rukayya na ta godiya da Mijinta Adamu dai kamar ba shi ba.
Ya zauna da Mijina suna ta Hira har yana kallona yace"Ikon Allah Hasiya ki yi hakuri da abubuwan da na rika aikata miki a baya, wlh sai daga baya na kara gane cewa duk zencen mutane ne, sannan naji wani wa'azin kwanaki da akace rashin yarda da Allah nw in wani ya samu bawa yana nuna mutum bai yarda da musulunci da ya ke ciki ba kenan."
Assadiq yace"Kwarai ma da gaske, ai acikin shikan shikan musulunci akwai yarda da kaddara mummuna ko kyakyawa."
Sai ga shi zamu tafi Amna na hawaye nima wlh na saba da yarinya mai kwazo ga hankali.
Assadiq yace ta bar kuka duk sanda ta samu hutu zai rika zuwa yana Daukanta.

A gidan mu na zariya muka sauka da ya sha kura, Allh sarki maman suhailat sun tashi d anta ya gina gida sun koma can wajen kabama.
Ummi ma sun tashi gidan duk bakin Fuskoki ne.
Dakin ma Assadiq yace zai sake shi, sai dai in ya samu kudi ko karamin gida ne ya gina mana in da zamu rika sauka in mun zo garin.
Wannan zuwan da muka yi Amma ta matsamin sai na ne gidan Baba Tanko tare da Assadiq muka je  har gidan Baba Saminu.
Sannan na kaisa gidan Goggon kona itama suka gaisa sai kuma jin kunya, suna ta kame kame a raina nace ku kuka sani ta bakin Amma tace mu mun riga mun sauke hakkin zumumcin da ke kanmu.
Kuma Assadiq ya yi musu alheri suna ta Tambayan yan biyu nace suna Gusau.
Hatta wasu daga cikin yayansu masu zagina da mugun baki na gansu, sai kunya da sunne kai.
Mugun abun da suka Rika jefani da shi ya koma musu.
Tunda cikin ya'yan Baba Tanko akwai sakakkiya auranta uku baya zama ta na gida, nidai nace alhakina ne ya kamasa da ya rikamin mugun baki in ma na yi aure bazan zauna ba Tunda na zama bakar Annoba gobara daga kogi mganinta sai Allah ba.
Daga zariya ne muka je Gusau nan  muka yi jima Tunda Lokacin hutun karshen shekara ne.
Su Asim sun zama yan gusau ina wuri ma kamar ba na nan Umma da Mama ne iyayensu yanzu.
Muna garin Siyama ta haihu har aka yi shagalin suna.
A sunan ne su Anty Sakeena  ta yi ma Sajida tsiya lokacin da bazawarinta ya kirata a waya.
Sai a lokacin naji ashe wani Tsohon saurayinta da ya nemeta tun tana Budurwa ne ya Dawo kuma abun mamaki bai yi aure ba shi har yanzu.
Saleema ta zo sunan itama da Cikinta Tunda sau biyu ta na samun b'ari.
Ita kuma asibiti ta ke zuwa Tunda in dai ta samu ciki sai ya zube.
Duk ta rame ta zub'e ba wannan gayun sai a hankali.
Shahida ke bada labari a wajen suna irin yadda Baba Jibril ya rika nuna ko Salimar ne ke da wani Laluran a jikinta? Kamar ya na nuna shi fa matsalan daga wajen salima ne ya manta Allah ke kashewa da Rayawa.
To ina Baba Jibril yasan Allah shi ban da neman duniya ai bai saka ma komai gaba ba.
Don ma Saboda Abba ne yana karuwa ta bangarensa da Tuni salima ta wulakanta kuma domin mijinta na sonta.
Ammh in akace Salima ta yi b'ari suna asibiti ji ya ke yi kamar kud'insa ne za su yi kuka ya yi ta mganganun rashin Takwalli.
Ni tausayi ta bani, ina auna irin yadda Rayuwar mata ke fuskata a wannan zamanin Allah dai yasa mu dace
Ya kuma cika zuciyoyin mu da Takwalli da yakana.

Wannan karon a Abuja na Haihu ammh kuma a Gusau aka yi taron suna. Kuma na haihu da kaina batare da an sake Farkani ba
Ban samu macen da na dinga kwad'ayi ba namiji na kara haifa.
Assadiq kuma ya saka masa suna TAHIR.!
Tahir ya yi murna Farincikin da ya Hauwa'u ta yi min sati a Gusau ta kuma zo min da kayan arziki daga Takwaransa Tahir Yusuf Daura.
Tahir da ya zo barka ya Dauki takwaransa ya rike cikin Farinciki yace"Abokina me na yi maka da na Cancanci ka Tsallake sunayen mutanen da suka fi daraja ka saka ma d'anka sunana?
Kai tsaye Assadiq yace"Da taimakon ka na auri Siya, Tahir ka yi min komai da  bani da bakin da zan gode maka."
Tahir kamar ya yi kuka yace"Me na yi maka! Ni da na rika adawa da auran ina ta cewa baku dace da juna ba, ashe muna namu Allah ya gama nashi ashe ashe har Takwara ma yar Zabiyar matarka zata Haifa min Nagode kwarai Allah ya raya Junior Tahir yasa ya Biyo mai halinsa."
Assadiq na jijjjiga kafad'ansa yana fad'in "Ameen ammh dai ka kara sani sunan Matata Hasiya ba Zabiya ba."
A tare duk muka saka musu dariya ni da Hauwa'u.
Kowa yaji sunan yaro sai yace Tahir ya cancanta.

A gusau na yi jego na Umma da Mama na Tsaye kaina suna kula da ni.
Sai dangina suka zo nan gusau karon Farko da su Adda Fati suka tako gidan su Assadiq.
Wajen kwanansu hud'u sun kuma ga karamcin da mutuntatawa.
Ramatu ta zo har da Inna Talatu itama Habiba ce bata zo ba tunda ta jima wajen Amma.
Bani da matsalan komai ina Bangaren Assadiq Sajida na shigowa ta zauna dani mu yi ta hira kamar bamu tab'a fad'a ba.
Assadiq kuma na tare da matarsa yar Rigima, Sultana dai bata samu ciki ba ta gama rigimamta ta Hakura.
Ammh har yau har gobe ba wani jituwa tsakanina da ita.
Ni kuma in muka had'u ni ke fara gaisheta ko da bazata amsa ba.
Daga baya da taga ina tura mata Aniyarta sai ta dawo tana gaisheni in muka had'u ammh shima ba koda yaushe ba.
Wannan karon na tada ma Amma Rigima sai da tazo har Gusau ta ganni ita da Matar Hamma Isuhu da Habiba da Badd'o
Umma ta yi musu kyakyawan karb'a.
Sai anan taga kammanina da Amma.
Ta ga inda na Dauko hasken Fatata kamar ita jajir.
Duk da yanayin Rayuwa da yasa Hasken Fatan Amma ya dishe ammh har yanzu da haskenta sannan Zanenta na Fulani na nan a gefe da gefen bakinta.
A bangaren Umma ta sauka nan Taga su Asim sun girma da suka ganta sun manta da ita sai da suka kara ganinta sannan suka fara yarda da ita.
Umma da ta kai Amma bangaran Innani tace mahaifiyata ce.
Innani na saman kekenta ta rika sakama Amma albarka ta na fadin ni alheri ce ga Rayuwar magajin gida.
Amma bata so ta jima ba kwana Biyu ta  sobsu yi su koma na lallab'eta ni da Assadiq ta amince zata yi sati.
Anty Surayya ta zo ta gaida Amma kuma har girki ta yi ta aiko mata dashi.
Ana gobe Amma za su tafi, yan'uwan Saurayin da ya ke son auran Sajida suka zo har gida har Falon Umma suka yi tijaransu.
Da sunan cewa su dan'uwansu bazai auri bazawara alhalin bai bata aure ba ita kuma Sajidan suka ja mata kunnin ta rabu da d'anuwansu ruwa ba sa'an kwando ba ne.
Tana bazawara sai ta makale ma Saurayi tace zata aura ko kunya bata ji ba?
Umma da ta yi musu magana tace ai hakan ba Haramun ba ne.
Wata cikin su ta kalleta kai Tsaye tace"Malama Rufe ma mutane baki, kinsan da haka nan da d'anki ya auro miki bazawara ki ka tada tsiyan sai ya saketa? A she wanzami baya son Jarfa ita wato ba yar ki bace tunda yanzu yarki ce kin ce ba Haramun ba ne mana."
Sai Umma ta yi shuru ta koma ta na kuka Sajida ce tace su bar musu gida in Allahu ta rabu da Isma'il tunda abun ya zama haka.
Har da Amma a masu ba ma Umma hakuri tunda suna wajen aka yi ni sai daga baya Sajida ta zo ta na fad'amin.
Umma ta yi ta kuka ta na fadin alhakina ne ya kamata.
ta tozartani da Farko gashi itama abunda ta aikata ya na dawo mata a kanta.

Har Amma ta yi ta bama Hakuri akan abubuwan da ta had'a kai da ya'yanta suka yi ta min harda na korana Lokacin da na ke da cikin su Asim.
Amma tace mirmishi kafin tace"Ni Hasiya ba ta tab'a gayamin kun yi mata wani abu ba, koda yaushe alherinku ta ke fad'amin na rantse da Allah ban da yanzu da kike fad'amin da bakin ki bansan da Labarin abubuwan da suka faru ba, ta Boye sirrin auranta ta zauna lafiya mu ma ta bari zukatanmu sun zauna lafiya."
Umma ta yi ta mamakin halina ta kuma ta yabona a gaban Amma.
Har Amma tace mata"Hasiya ta dabam ce acikin ya'yana mai Raunin zuciya ce ammh kuma mai kirki daga da yakana daga cikinta."
Sajida ke ta maimata komai ta karishe da fad'in"Yanzu kina nufin har koran nan da muka yi miki ba wanda kika fad'amawa?
Tab a gaisheki Hasiya."
Ina mirmishi nace"To miye amfanin na yi ta gaya? Yanzu ba ga shi komai ya wuce ba, da ace na yi ta gayamusu duk wani abun da ya faru da ni sai na yafe muku su kuma su rika ganin ku da abun su kuma kasa mantawa."
Sajida ta jinjina kai kafin tace"Hakane na dauki wannan dabi'ar in sha Allahu ina na samu na yi wani auren zan zauna lafiya da mijina sannan na Rike sirrinsa kuma na daina kokarin shiga Rayuwar auran wasu."
Sai hawaye ni na zauna ina ta bata baki da komai taga ya faru daga Allah ne.
Sai ranar da su Amma za su tafi Sultana ta zo gaisheta kuma Assadiq ya gayamata ta rika cewa saboda makaranta.
Kuma Naja fa ta na wajenta Saboda Sultana Assadiq ya nemi alfarma aka basu ita har sun sakata a makaranta.
Amma ko a fuska ba ta nuna ma Sultana wani abu ba.
Ta dauki Ummi ta na yi mata wasa har da Goyo kunya yasa sultana ta kasa mgana.
Ta ga duk rashin mutumcin da ta ke yi min uwata ta zo ta na wahala da Yarta.
Shiyasa na ganta cikin masu Rakiya Abba ya ba da Mota aka kaisu har Zariya Umma ta bata atamfofi harda Hijabai Mama ta yi musu alheri Abba kuma 20k ya ba su.
Naji dadi sosai bakina yaki Rufuwa abun akwai dad'i kaga an yi ma naka wani abun alherin.
Zariya Amma ta wuce sai da ta kara kwana Biyu sannan ita da matar isuhu da Badd'o suka koma gida.
Hankalin Amma ya kwanta na samu Rayuwar da ta ke yi min Fata Fiye da Fatan ta ma da Tsammaninta.
Ni kuma wajen wata Biyu na yi a gusau sai Junior ya fara wayau sannan naje Zariya na yi ziyaran yan'uwana da kawayena.
Daganan na wuce naga Amma na kwana d'aya na wuce Abuja daganan
Tunda Assadiq ya rigani tafiya shi ya tafin ma da wasu kayan.
Ina da sati biyu da dawowa muka je katsina gidan Tahir muka yi musu wekeend naji dadin zuwana katsina sosai.

Mun zo har Daura na gaida Hajja Tana ta tambayan Innani Assadiq yace tana lafiya.
Na tuna sanda Assadiq ya kai mata Tahir Lokacin da aka haifeshi ta shafa kanshi tace"Ka yi ma Attahiru takwara saura ni Magajin gida, in ka kara samun mace ka saka mata suna ba Hadiza saboda ko bayan raina ku rika ganinta kuna tunawa da mai suna na"
Innani ita gani ta ke yi mutuwa zata yi ko Rasuwa aka gayamata daga Yan'uwa a shinkafi sai tace sai mun zo Allah yasa mu dace.
Sai da muka dawo daga Katsina muka yi mgana da Hajiya Surayya deee na tura mata kudin ta aikomin da tsumi da kuma kazar had'in uwar gida.
Ta kuma had'omin da saiwowin maganin Sanyinta Sadidan masu kyau da inganci +234 803 277 3332.

Da ya ke Umma ta ba ni wasu na sha acan Sannan Anty Sakeena ma ta kawomin gumba na sha da Nono kuma na yi amfani da su.
Shiyasa da Assadiq ya rab'eni yace Romon siya ya kara zak'ak'wai.
Madallah da Surayya Dee madallah da Saiwowon Kazar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login