Showing 33001 words to 36000 words out of 116366 words
sha Allahu zamu je Zariya gidan Baffanki da ya Daura muku aure na samu tabbaci."
Sai kuma ya Juya ya na kallon Sadiq kafin yace"Ka kira abokin ka Tahir ya taho shima muje tare da shi."
Cikin girmamawa Sadiq yace"To Abba , Allah ya kara girma."
Kai Tsaye Abba ya kalli Sauran ya'yansa kafin yace"ga wata yar'uwa nan kun samu acikin ku, sai ku marabaceta cikin Ilimi kamar daman kun saba, ke kuma Sultana ki yi hakuri Bamu isa mu sauya wannan kaddaran ba, Magajin gida zai zauna da ku dukkan ku a matsayin matansa In sha Allahu."
Umma ta mike a fusace kafin tace"Abban Siyama wannan wani irin Hukunci ne?
Mama na gefe tace"Gaskiya fa, wannan ai ba mgana ba ce."
Suma sauran nata kuskus, Surayya dai batace komai ba Sajida ne ke ta yi ma Sadiya rad'a suna Gulma.
Sultana kuma kamar da kasa sai kwai ta fashe da kuka.
Jin haka yasa kafin ma Abba ya samu Zarafin mgana Innani ta mike kad'an ma ya rage bata fad'i ba Saboda masifa tace"Ishunki Salamatu ai Sulaimanu bai isa ba, samman wannan Hukunci da ka yanke bai yi ba."
Abba ya sauke Numfashi kafin yace"Innani wani Hukunci ki ke so na yanke bayan wannan?
Innani na Huci tace"Ka yi masa fata fata na cin amanarmu da ya yi mana, bayan haka a gabamu ka saka ya saki kilakin nan a yi mata Korar kare shine hukuncin adalci Sulaimanu."
Abba yace"Subhanallah Innani, Magajin gida aure ya yi ba zaman Haramci ba, kuma shi da Niyyar taimako ya yi wannan abun, mun zauna da shi ya yi min bayanin komai kuma ni na aminta da shi."
Umma da ke tsaye tace"Kai ya yi ma bayani ai bai yi mana ba ko?
Abba ya kalleta kafin yace"Hakane to ku koma ku zauna, kai Sadiq juya ka yi musu irin bayanin da ka yi min dazu"
Sadiq da gabadaya yaji gwiwarsa ta sare, ni ya ke kallo ganin na dukar da kaina ina ta kuka komai fa zai Faru bazai bari a Tozartamai mata ba.
Cikin gyara zama ya fara bayaninsa haduwarsa da Hasiya da auransu sai dai kamar yadda Abba ya Bukata ya Boye wasu abubuwan.
Ya karishe da fadin"Kuma ni har Allah acikin zuciyata Tausayi ne, sai daga baya na Fahimci ba'a Tausayi in ba so, ina son Siya sannan Kuma ina son zama da ita har karshen Rayuwata Umma don Allah Ki Fahimceni."
Umma cikin harzuka tace"In naki na Fahimceka fa? Nace in naki na Fahimceka fa? Sai aka yi ya ya?
Kansa na kasa yace"Ki yi hakuri Umma, na yi kuskure kuma na yi miki alkwarin in sha Allahu hakan bazai kara Faruwa ba."
Kai Tsaye Umma tace"Abubakar bazan karbi wannan auran naka ba, sannan kuma Wallahi Tallahi sai dai ka zab'a ko Auran da muka sani ko wanda ka yi ma kanka."
Da sauri ya dago ya na kallon Umma kafin yace"Umma."
Hannu ta daga masa kafin tace"Abunda nace shi na ke nufi, kuma anan wajen zaka zab'a, gwara Tun wuri nasan matsayin da ka ijiyeni."
Sai kuma kawai ta Fashe da kuka, Innani ta yi zaraf tace"Kwarai mganar Salamatu haka take, gwara dai mu san matsayin mu."
Abba zai yi mgana Innani ta daga sandarta ta na fadin"Ka na cewa Tak Sulaimanu kagani in ban kwad'a maka sandar nan ba."
Duk da ana cikin Rudani ne, ammh bai hana wasu darawa ba.
Abba sai ya koma kawai ya yi shuru ya na kallon ikon Allah.
Sadiq ya rasa yadda zai yi ya tashi yaje gaban Umma ya duka ya na fadin"Umma don Allah ki janye kalamanki, duka ina son mata na kuma ina son zama da su bazan iya zabar d'aya na bar d'aya ba."
Umma na sharan kwallah tace"Sai dai ka zab'a, tunda har ka iya nuna ko ni mahaifiyarka ba ni da ta cewa acikin Rayuwarka Abubakar"
Yadda ta Juya masa Fuska ne yasa yasan ta riga ta yi fushi.
Mama ya kallah tun kafin ya yi mgana tace"Sadiq gaskiya ne fa gwara dai ka sahale ma kanka, kafin ma ta san irin bakin fentin da ke tare da matar da ka aura."
Ido ya kura mata ya na kallonta Umma ko da Sauri ta Juyo ta na fadin"Wani irin bakin fenti ne Suwaiba? Don Allah ki fad'amin."
Mama ta Juya ta na kallon ya'yanta su Sa'ima su kuma suka gyad'a mata kai alamun ta fad'a.
Surayya kuma Tsoro ya kamata sai ta kalli Sajida ita kuma sai ta ware mata ido alamun ni bansan komai ba.
Mama ta gyara zama ta na fadin"kunsan dai salima na auran danginta, Alhaji jibril da ke kanin babanta da kansa ya ke fad'a ma Salima Matar da Sadiq ya aura Farar kafa gareta, duk wanda ta rab'u dashi ko asaran lafiya ko na dukiya ko na rai, Sannan da bakinsa ya fad'a yace tunda aka haifeta iyayenta ke ganin bala'i har sai da ta yi sanadiyar karayar arzikin Ubanta daga karshe tayi ajalinsa, sannan Mahaifiaryarta ta fara ciwom da aka kasa gane kansa, komai na su ya kare sannan kowa ma ya gujesu har su dangin Uban nasu, Sannan yace auranta Biyu na Farkon shima sai da komai nashi da na iyayen suka kare daga karshe ma zaman garin ne ya gagaresa, na Biyun kuma ranar Daurin aure ya samu had'ari ance har yanzu bai warke ba ya nakasa ga asaran dukiya, Wlh ance duk zuru'ar da ta shiga sai ta tarwatsasu sun rasa komai na su in ba'ayi asaran rai da lafiya ba fa an godema Allah."
Gabadaya Falon sai ya Dauki salatin su Umma, Innani kam kamewa ta yi a zaune Tsabar tashin Hankali.
Surayya kanta ta yi kasa da shi tasan komai ya lalace.
Sajida kuma ta mata alama da Hannun cewa ba ita ta fad'a ba, sai yanzu ta tuna da Hoton da ta Turama Salima shi ya lalata komai.
Kafin kace me salima ta karbi mganar ta na kara maida yarda akayi sai nanata take yi wai ance auranta ma Biyu duka ana sakinta Saboda bakin Jinin da ke tare da ita.
Shahida ta saka salati Kafin tace"Sadiq yanzu wannan Annoban da kowa ke gudu kai ka kwaso mana?
Sadiya kuma tabdijan kawai ta ke fad'i kafin tace"Wlh Umma Canfi gaskiya ne, mun shiga uku."
Abba kuma na zaune yana jinsu, yana maimaita sunan Alhaji Jibril shi sai yanzu yasan Komai da mafarin lamarin.
Yana ganin kimar Alhaji Jibril tun bayan da suka had'a auratayya a Tsakaninsu, ammh kuma wannan Labarin da yaji sai yaji kwata kwata ya raina masa ta ina zaka Biye ma wannan Abun da baka da Tabbaci a kansa? Kawai sai yaji kamar ya raina masa kwata kwata Tunda a baya yana ganinsa mai ilimi ne.
Falon ya kaure da hayaniya Umma kuka kawai ta ke yi ta na Hango kilama ta kusa rasa d'anta.
Surayya bata da mgana Saboda su Shahida da Sadiya suna kara ma Umma Famfo kar ma Sajida ta ji labari.
Sadiq sai kawai ya koma ya Dukar da kansa ya na kuma neman mafita ammh acikin ransa Hasbullahi ya ke ta maimaitawa.
Ba wanda ya san lokacin da Innani ta tashi sai da akaji muryan Abba na fad'in"Subhanallahi Innani lafiya?
Sai aka juyo nan fa aka ga Inanni ta Daga sandarta zata makama Hasiya dake zaune ta na kuka.
Fad'i ta ke yi"Ka bari na Rafketa Sulaimanu, wannan ai bakar dakace ta Shigo Cikin zuru'ata na bani ina jin ma ko mayyace zata lashe kurwan Magajin gida, namiji kwara d'aya kwal da Sulaimanu ya mallaka in wani abu ya sameshi ai mun lalace, ni Dije ina zan saka kaina, yau naga Bala'i ganin idona da maita."
Ta ke fad'a ta na kuka ta na kokarin kwace sandar ta daga hannun Abba.
A tare Surayya da Sadiq suka mike, sai dai ya Rigata isa kaina, tunda Innani ta saki sandarta da Hannu ta saka ta kaimin Dundu sai gadon bayan Assadiq Tunda ya yi min Rumfa.
Bata ma Fahimci shi ta ke duka ba idanuwanta ya Rufe fad'i ta ke yi"Mayya Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu, kurwan jikana Qur wlh, fita ki barmin gidana ki kuma Rabu da zuru'ata gabadaya."
Ta ke fad'a ta na kuka, Sadiq ya Dago a fusace ya Rike Hannun Innani yana fadin"Kada ki kara kiran matata da Mayya. SIYA ba mayya bace itama Mutum ce kamar kowa."
Ya fad'a cikin Tsawa kafin ya wancakar da Hannun Innani ya Dagoni jikinsa ya Rumgumeni kamkam, ni ko ina ta kuka ina fad'in"Assadiq don Allah kada ka rabu dani."
Ya na rike dani yace"Babu wanda ya isa ya rabani da ke Siya."
Sai jin muryan Umma ya yi ta na fadin"Har ni nan Abubakar.?
Idanuwanta Jajir ya ke kallonta kafin ya mike ya rikoni nima na mike ya Rikemin hanmu gam gam.
Sannan ya fara takawa dani har gaban Sultana itama ya mika mata Hannunsa guda daya sai taki kamawa ta kauda kai ta na kuka.
Da kansa ya Duka ya Riko hannunta itama ya mikaar da ita.
Ya kuma Jimke hannunta acikin hannunsa na Hagu, muna gefe da gefensa cikin karfin gwiwa yace"Na karbi duka zab'in Umma, da zabin da kuka yi min da wanda Ubangiji ya yi min da siya, ni na aureta ba ita ta aureni ba Umma ki yi hakuri kada kice zaki Rabani da matana."
Gadan gadan Umma kamar kabubuwa ta isa gabammu ta warce hannun Sultana ta na fadin"Ita wannan Annobar ka zaba kenan?
Shuru ya yi ya kasa mgana Umma ta daka masa tsawa lokaci daya ta na fadin"Ka bani amsata mana."
Kai Tsaye yace"Umma dukkansu ina son su, bazan iya barin d'aya saboda daya ba, ki yi hakuri."
Umma sai taji kanta ma ya fara Juyawa, ta kure Sadiq da ido kawai ta na kallonsa ganin haka yasa na fashe da kuka ina fadin"Don Allah ki yi hakuri Umma"
Ganin haka yasa Surayya ta rike Umma ta na fadin"Umma mu bi komai a sannu don Allah, mu godema Allah aure ya yi, in kuma ba auren ba ne fa! Zaki so ace Sadiq lalacewa ya rika yi achan? Ko kuma wannan Rabon fa ina za'a same shi?
Ta fad'a ta na nuna cikin jikina, ni kuma sai kuka na ke yi ina kara Fadin"Ki yi hakuri Umma ammh don Allah kada ki saka Assadiq ya sakeni."
Shahida ta katse ni da tsawa kafin tace"Dilla Rufema mutane baki Annoba kawai, ke har kina da bakin magana? Rabuwa kuma ai ya zama Dole sai dai kuma ki bi wani sarkin ba kanin mu ba."
Sadiya ta karbe da cewa"Ahto muna zaman zaman mu kada tsiya ta Fara Bibiyan mu."
Sajida tace"Kuma fa kuna ji fa bazawara auranta biyu, wannan ai bai yi ba kwata kwata."
Sakeena ta Dorawa da cewa"To kuna dai ji su kansu dangin su sun gujesu Saboda ita, Sai shi zai rumgumota?
Innani na gefe a had'a kai da Gwiwa sai kuka ta ke yi, ta na fadin sai an yi Turaren maita tunda ko na bar gidan Tunda na kwallafa rai sai na Bibiya kurwan jikanta.
Abba ko na zaune bai yi mgana ba, so ya ke magajin gida ya tsaya ma matarsa da kansa, in ya yi hakan shi kuma sai ya tabbatar da nashi Hukuncin kamar yadda ya yi a Farko.
Kowacce sai fadin albarkacin bakinta take yi a kaina suna aibatani da fadin dukkan kalaman da suka Fito daga bakinsu a kaina.
Sun kirani da suna Annoba, da kuma mai bakin jini, mayya shi yafi Dagamin Hankali ba bazawaran da suke ta Jifana dashi ba.
Sadiq ya gama jin iya abunda zai ji, yaga abun nasu ya yi yawa sai kawai ya kara Damke hannuna sannan ya Daka musu tsawa.
Sai kowacce ta yi shuru suna kallonsu ya na faman zare ido.
Hannunsa d'aya yasa ya na nuna su, Tunda Umma Surayya ta maidata saman kujera ta zauna ta na sharan kwallah.
Sai da ya nuna su da hannunsa kowacce a saman Fuskarta sannan cikin Kaushin murya yace"Ya ishe ku, kun yi na kudin ku, kada wacce a cikin ku ta kara aibatamin mata Ya isa nace.!"
Ya karishe fad'a a Fusace Subai'a ce ta taso masa ta na fadin"Bai isa ba, nace bai isa ba me zaka yi, Wlh kayi kad'an wannan Annobar ta zauna acikin mu"
A fusace"Ina Ruwan ki? a kan ki zata zauna?
Nace a kan ki zata zauna ko mijin ki ne zai rike min ita ballatana abun ya Dameki?
Ya fad'a cikin kaushin murya, baki gabadayansu suka Bude suna kallonshi.
Sa'ima tace"Sadiq ba dai rashin kunya zaka yi ma Anty subai ba?
Idanuwansa sun kad'a saboda bacin rai ya sakar mata wani kallo kafin yace"in ma nayi mata ai ita taja, domin kun fara Tsallake abunda ba Hurumin ku ba, babu wacce zata gayamin yadda zan tafiyar da Rayuwata sannan acikin ku ban ga wacce na taba mata katsalanda a abunda ya shafi gidan auranta ba, Saboda haka kada na kara jin kun tsoma min baki, wannan mganace tsakanina da iyayena da abunda zuciya ta zaba ku fitar da kan ku aciki."
Ya karishe fad'a cikin Tsawa har kuma Lokacin bai saki Hannuna ba.
Sadiya ta saka salati kafin tace"Kai yanzu Sadiq akan wannan yarinyar mai kama da zubin mayu ka ke jayyayya damu? Wannan Shegen cikin na jikin nata ko shi ka sani bazmu karb'esa ba."
"SADIYAAA...!
Sadiq ya wani Kira sunanta a Firgice cikin Tsawa da yasa har Umma sai da ta Dago ta na kallonsa.
A fusace ya saki hannuna ya taka har gaban Sadiya ya daga hannunsa manuniya ya nunata da shi kafin yace"Kada ki kuskura ki ce zaki aibatamin mata sannan ki shegantamin gudan jinina, kada ki kuskura na gaya miki."
Kawai sai tace"In ba haka ba fa? Ance shegen cikin, waya sani ma cikin ba naka bane Tunda tayi yawon dakuna sannan an san dadin zawar..'
"Sadiya..!"
Sadiq.."
Alokacin da ya Kira sunanta ya Daga hannu zai kai mata mari, Surayya ta kira sunanshi itama a tsawace.
Sai ya dakata lokaci d'aya yana Dunkule hannunsa sannan ya naushi iska.
Cikin Tsabar Fushi da yadda Jijiyon kansa ke tashi Saboda bacin rai.
Surayya cikin bacin rai tace"Ka bi a hankali mana wannan wani irin hauka ne, kai da ka ke kokarin gyara kuskurenka sai kuma ka bata shi da sake yin wani laifin?
Ta fad'a cikin bayyana bacin ranta kafin ta kalli Sadiya ta na fadin"ke kuma Sadiya kin fara Tsallake iyakarki, in bazamu fad'i alheri ba sai mu yi shuru."
Kawai sai Sadiya ta saka kuka ta na fadin"Mu ne yanzu Saboda mace Sadiq kana kanin bayanmu kana gaya mana magana, sannan har kana neman daga hannu ka maremu?
Sa'ima ta karbe da cewa"Ko domin darajan mun girmesa ai ya raga mana."
A fusace ya juya ya na kallonta kafin yace"Naji kun girmeni, ammh ai baku Haifeni ba sannan baku halliceni ba Allah ne ya Halliceni kuma shi kadai nake jin Tsoro kuma garesa kad'ai nake ninka bibbiyata, cikin ku ba wacce ta taba Daukan Ragamar Rayuwata, Saboda haka ku Rufemin bakin ku ku yi min shuru anan wajen."
Cikin Kaushin Murya ya fad'a sai gashi sun yi shuru cikin sarkewar murya yace"Duk da ina karamin ku ina da girman da Ubangiji ya bani kaf din ku da Harkarina aka hallice ku, kuma iyayena Ubangiji bai ce na yi musu biyayya kan abunda nasan ya saba ma addina ba, kuma ina so na Fad'a muku wani abu game da Kaddaran Siya da kuke ta aibata ta akan haka to ku saurareni da kunnen basira ku ji wani abu."
Ya dan dakata sai da ya kallesu d'aya bayan d'aya kafin ya fara fadin"Dukkan ku nan baku da iko a cikin kaddaran ku, kamar yadda itama Hasiya ba ta da wannan ikon a hannunta. In da ace Littafin kaddaramu a hannumu ake bamu mu zabi kalar Rayuwar da muke so mu yi a duniya na rantse da wanda raina ke Hannunsa cikin mu ba wanda zai yi kansa a yadda ya ke, kema bazaki saka kanki a wannan matsayin ba, nima haka to itama Hasiya haka bazata taba saka kaddaranta a haka ba, to ina so ku gane cewa Littafin Rayuwarmu da komai namu ubangiji ne ya ke Tsara mana komai, Hasiya ba Mayya bace sannan ita ba Annoba ce ba, duk abunda ya faru da ita ba ita bace ta yi silar Faruwarsu ba, Face Ubangiji da ya shiryama kowa kaddaransa sai dai ace itace Sanadi, kuma ku sani kuna wasa da Tauhidi sannan kuma hakan da kuka nuna ya kara tabbatar min da cewa baku san Qur'ani ba."
Sai gabadaya suka fara kallonsa cikin mamakin kalamnsa.
Kai Tsaye yace"Eh tabbas baku san menene Qur'ani ba, Domin duk wanda yasan abunda Qur'ani ya kunsa bazai yi irin manganganun da kuke yi ba, tunda munsan cewa kashi na Farko na alqur'ani Tauhidi tare da Bauta kashi na Biyu kuma al'amaru wannahi Umarni da Hani, kashi na uku kuma yana mgana ne kan Alkillas Labaran Annabawa da Al'ummar da suka gabata."
Sai falon ya kara Daukan wani irin Shuru har da masu komawa ma su zauna, Abba na gefe ya na ta mirmishi hatta Innani da ke kuka sai da ta Dakata ta baza kunne tana Saurara.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya Cigaba da fadin"In da ace kunsan haka da duk baku fad'i mangaganun da kike fad'a a kanta ba, saboda haka ku sani Wani abu bai isa ya samu bawa ba face Abunda Ubangiji ya kaddara masa ko ina tare da Siya ko ba na tare da ita Wani abu bai isa yasa na Gujema kaddaran da ke cikin Littafina ba. Sannan karya ne babu Canfi acikin Addinin mu, kuma kauce ma abunda Addnimmu bai zo da shi ba Farillah ne,hakan kad'ai ya isa ku gane cewa aurena da ita na cikin Littafin kaddarana."
Ya sake yin shuru kafin ya kalli Sajida ya na fadin"Ke kuma da kike ta nanata ita bazawara ce? Miye illar bazawaran ko ita ba Mutum bace? Kada ki manta Annabi Rahma Sallallahu alaihi wasallam, ya auri Nana Khadija Ta na da shekara arba'in kuma a matsayin bazawara Annabin Rahma kuma na da shekara ashirin da Biyar, in da ace Haramcine da Annabi bai yi ba, ta nan ma ya kamata kusan zawara na cikin Tarihin musulunci, ke awa kice zaki aibata bazawara? Kina da tabbacin zaki Mutu a gidan mijin naki ne! Kina da tabbacin watarana bazai iya sakin ki ba ? Ko kina Tunanin watarana bazaki iya zama bazawara ba?
Sajida ta zaro ido ta na kallon Sadiq cikin Subutar baki tace"Allah ya kyauta na zama bazawara."
Kai Tsaye yace"Itama ai ba ita ta maida kanta ba Allah ne, kuma kema ina kara Tusanar da ke cewa Kema