Showing 12001 words to 15000 words out of 116366 words

Chapter 5 - Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

335

cikin wayarta.

Wad'anan Hotunan su ne za su sillar fallasa Sirrin da Assadiq ya jima ya na Boyewa.

********

Saddiqa da ke aure a Jahar Kebbi yar kasuwa ce sosai, ta na kasuwanci saida atamfofi lesuka da Sauransu, sannan a cikin Family ko biki za'a yi ita kan fito da anko kuma ta Dauko.
Shiyasa ta na harka da yan kasuwa yan'uwanta daga mabambanta garuruwa.
Kuma harkan ta yafi yawa ne ta Kafafen sada zumunta, ta na da mutane sosai ma su kallon Status dinta, da kuma wad'anda ta ke huld'a da su.
Da safiyar ranar wata Laraba bayan ta gama abunda ta ke yi ta sallami yara da megidan ta dauki wayarta, akwai kayan data siya daga kano ta siya kayan za'a tura jigawa, ta na so ta yi mgana da mai shagon taji in har an gama had'a kayan gabadaya.

Ta na Bude data sakonni suka yi ta Tururuwan shigowa, Sai da ta bari suka gama shigowa sannan sai taga ma agent din yaron shagon ma ya yi mata mgana sai ta Bude ta na gani.
Vioce ta yi masa bayan ta ga hoton kayan da daukan mata, akwai sauran kudin da zata tura musu, sai da ta gama duba komai taga sun yi, sannan ta sauka ta tura musu Ragowan kudin, ta dauki Trancsation din ta Tura masa tare da lambar wacce za'a aika ma kayan Tunda su za su ba da akai tasha a saka a motar jigawa.

Ta na ganin ta gama da wannan bangaran, sai ta fara duba Sakonin mutane ta na ba su amsa bata ma gama ba, ta tafi kallon Status din Sauran mutanenta.
Har ta wuce Status din Khairiya Ahmad, sai ta dawo saboda ta na saida y'an kunnaye ma su kyau ta na so ta siyan ma yara, sai ta shiga ta fara Dubawa, ta santa tunda suna harkan kasuwanci tare ba su dai tab'a ganin juna ido da ido ba sai a hoto.
Ta dai san kamar Khairiya ta tab'a Fad'a mata ita yar zariya ce.
Kamar wasa ta na gama ganin Hotunan y'an kunnen sai tayi Tagging din na karshen ta yi mgana.

"Salam Khairiya wannan akwai na yara irin shi?

Sai kuma ta kara da cewa"Au bamu gaisa ba ina kwana ya kasuwa?

Sai ta fita ganin kamar ta na Online ammh kuma kamar ba ta kusa da wayar.

Ijiye wayar ta yi itama ta je kitchen domin ta saka ruwan zafi ta na dafa Indomie ne, yau yaran da megidan Plantai suka ci da Tea ita kuma ba ta cika son plantain ba.
Sai da ta gama Dahuwarta ta dafa kwai sannan ta Zubo a filet ta fito da shi falo ta ijiye saman Center table din da ke falon.
Wayarta ta dauka sannan ta fara cin abinci, ta na ci ta na duba wayarta, Khairiya ba ta duba sakonta ba sai tayi tunanin kila har yanzu ba ta zo kusa da wayar ba.
Sai ta koma Bangaran Status sai kuma taga sunan khairiya alamun ta kara saka wani Status  har ta wuceta sai kuma ta dawo ganin kamar Hoto taga ta saka, sai ta dawo ta Bud'e.
Abunda ta gani ne yasa sai da  cokalin hannunta ya subuce ya fad'i kasa.
Da sauri ta mike jikinta na rawa har ta barin Ruwan da ke karamin kofin Tangaran a gefenta.
Cikin Firgici da rawan baki tace

"SADIQ."

Hannunta na rawa ta kara Zooming din Hoton domin ta kara tabbatar ma da Idanuwanta shin abunda ta gani gaskiya ne?
Sadiq ne ta ke gani tare da wata mace da ciki, sannan a yanayin Hoton cikin Halin da mata miji ko farka kan kasance ne a ciki.
Saboda Tsabar Rud'ewa ta manta da Duba abunda Khairiya ta saka a kasan Hoton sai da ta dauki Hoton ta koma kan wayarta ta kara Duba shi da kyau.
Tabbas wannan Sadiq ne to Sadiq din ne bata sani ba Allah na Tuba ko cikin Duba sai ta iya Cire kanin na su.
Zama ta koma ta yi Saboda jin wani jiri na Dibanta.
Da Rawam jiki ta kara komawa ta Duba Status din khairiya sai alokacin taga abunda ta saka a kasan Hoton.

"Jama'a See Love don Allah? Mu ma Allah ya aurar da mu"

Tare da saka Emojin kunya da Love.
Saddiqa sai ta kasa ma wani Tunani, kada ta ce ba ta da tabbacin ba Sadiq ta gani ba domin shi ne ta gani a wannan Hoton tare da wata?
To in shi ne ta jikin Hoton wacece?
Sai ta kasa ba ma kanta amsa lokacin da wani shashe na zuciyarsa yace"Karuwar sa mana."

Tunda dai mace daya garesa itace Sultana to in dai ba Sultana bace wacece? Kuma a yanayin da suke a tare tabbas in ba mata da miji ba to su farkan juna ne.
Hankali tashe Saddiqa ta lalubo lambar Surayya ta doka mata kira ammh har ta gama ringing bata dauka ba, Sai zuba Zufa ta ke yi lokaci d'aya ta na fad'in"Ki daga mana, ki daga mana Big sis."
Ta ke fad'a ta na faman zagayen falon cikin tashin Hankali.
Kiran da ta yi ma surayya yafi goma ammh bata daga ba, sai ta yi tunanin Tabbas bata kusa da wayar.
Ta rasa wa zata kira, Surayya ce babba kuma kafin umma taji wasu matsalansu ita ke fara ji, kuma ta tayasu warware shi cikin sauki.

Ta yi Tunanin ko kiran Sa'ima ammh kuma sai ta fasa, in kuma ba shi ba ne fa? In har maganar ta fita Sun zubar ma kaninsu kima da Darajarshi da sauran suke gani.
Rashin Daukan wayan Surayya yasa ta kara komawa ta na ta duba Hotunan nan, ta na kara Zooming tuni idanuwanta har sun ciko da kwallah, sai a lokacin ma taga kamar tasan yarinyar jikin Hoton ammh ta rasa inda ta santa.
Sake komawa Chart din ta yi sai taga Khairiya ta sauka daga online da gaggawa ta kirata, kuma ba sa ma kiran juna in ba kasuwanci siyan wani abu ya had'a su ba.
Itama sai da wayar ta kusa katsewa sannan ta dauka.
Bayan sun gaisa Saddiqa tace"Khair na yi miki mgana ta chart baki Duba ba."
Dagachan Bangaren khairiya tace"Sorry na ijiye wayar ne muna mgana da Mama? Lafiya ko wani abu ki ke so ne?
Saddiqa tace"Eh na yi miki mganar wasu y'an kunne ne ko akwai na yaran su?
Khairiya tace"Ok in na duba zan miki mgana, Nagode"
Har khairiya zata sauke Wayar Saddiqa tace"Amh Khairiya ni ko nace ba, hoton da naga kin saka dazu amaren sun yi kyau, sai naga kamar kuna kama ko kanwarki ce? Mijinta ne?
Khairiya tace"Wacce? Wai HASIYA?
ba kanwata ba ce kawar kanwata ce Safiya a wayarta nima naga Hoton sun yi min kyau sai na Tura shi a wayata shine har na yi status da shi Eh mijinta ne."

Saddiqa cikin mamaki tace"Allah sarki! A nan zariyan su ke kenan?
Khairiya tace"Eh anan zariya su ke"
Saddiqa sai ta rasa kuma abunda zata ce, kiran wayarta taji ana yi, ta na Dubawa sai taga Surayya ce kiranta da Sauri ta yi ma khairiya sallama.
Ta daga kiran Kiran Surayya.
Wacce ta na dagawa tace"Ke lafiya naga uban kira Rututu?
Saddiqa ta sauke Numfashi kafin tace"Big sis ki zo online zan tura miki wani abu yanzu nan."
Dagachan Bangaran Surayya tace"Miye? Lafiya ki ke kuwa? naji muryanki ta yi kasa ne."
Saddiqa tace"Big sis ki je ki ga abunda ya sakani firgici don Allah"
Jin haka yasa Surayya tace shikenan Hankalinta ya tashi ganin kiran Saddiqan ba adadi.

Da sauri ta Bude data, Daman dazu wayar na daki ne ita kuma suna falo megidanta na karyawa sai da ya gama ta rakasa ya fita aiki shine da ta dawo dakin taga kiran Saddiqa ba adadi.
Ta na bude data ba ta tsaya sauraran kowa ba sai sakon Saddiqa da ta jira ya shigo ta na shiga sai taga Hoto ne.
A kasan Hoton Saddiqa tace"Don Allah Big sis wa ki ka gani cikin Hoton ga?
Sai da ta Bude hoton, irin razanar da Saddiqa ta yi, Surayya ta fita shiga tashin Hankali domin sai da wayar ta subuce daga hannunta ta fad'i saman Cafet Saboda gigita da Dimauta.
Sai da ta kara Dauko wayar ta sake bin Hotin da kallo, ai ba ta bukatar ta yi zooming ko mutuwa ta yi ta dawo zata iya shaida kaninta a cikin Dubban Mutane.
Wannan ai Sadiq ne! Sadiq shinkafi ne kaninsu to shi da waye?
Ita yarinyar ta rika kallo ma, sai ta ke ganin kamar tasan fuskarta cikin jikin yarinyar shi yafi komai jan Hankalinta
Saddiqa na ta turo mata mgana ba ta Dubawa.

"Big sis Sadiq ko? Ko ba shi ba ne?

"In da naga Hoton, tace wai mata da miji ne?
Sadiq na da wata mata ne bayan Sultana?

"Kin yi shuru?

'"ni macen Hoton ne na ke ganin kamar na santa."

Sakon Saddiqa na karshe yasa Surayya ta kara Duba Hoton macen da kyau, Tabbas tasan wannan Fuskar, kuma kamar a gidansu ta taba ganinta, zama ta yi ta na kallon Hoton ta na so ta tuna inda ta taba ganinta Momorig lokacin na Shiga kanta.
Kamar an Tuna mata sai taji ta tuna a da inda ta tab'a ganinta kawar Saliha da ta zo bikin Sultana.

Da Sauri ta kira Saliha tace ta Hau chart zata Tura mata wani Hoto.
Gudun abunda zai je ya dawo sai ta yanke Hoton Sadiq ta Tura mata na Hasiya sai da ta tabbatar ta gani sannan ta  kara kiranta
Ta na Dauka Surayya tace"Saliha kamar kawar nan ta ki ko?
Saliha tace"Kwarai HASIYA ce. Ba ta zo min bikin Sadiq ba? Kin manta wacce na ce muku a kaduna muka had'u yar'uwan mijin Salima ce fa."
Surayya sai jinjina kai ta ke yi cikin Tsananin mamaki kafin tace"Na tuna ta wata tfara haka  har ma kika bani wayarki na yi muku Hoto ko?
Saliha tace"Kwarai ashe baki manta ba, bari na tura miki hoton ki kara gani, anan ta yi kiban fuska ne kila Saboda cikin jikinta ne, ni ban ma san ta na da ciki ba, kwanaki dai da muka yi waya tace min ta yi ta fama da Zazzabi."
Surayya sai ta kasa mgana ji ta yi zufa na keto mata ta saman goshinta, duk da AC Din da ke falon.
Cikin wani yanayi Surayya tace"Da bikin sun had'u da Sadiq ne?
Saliha ta yi shuru kafin tace"Gaskiya bazan iya tunawa ba? Hala me ya faru?
Da Surayya tace"A'a bakomai, wata kawatace naga ta  saka a status sai na ke tunanin inda na taba ganinta."
Da haka ta shanshantar da mganar Saboda kada Saliha ta fahimci wani abu.

Sai gashi kafin ma ta tambayeta Saliha ta fara gayamata Hasiya ta ja baya da ita, ba kamar farkon fara kawancen su ba.
Surayya ta koma ta zauna Dafe da kai bayan sun gama mgana da Saliha a waya.
Jikinta gabadaya ya saki bata so ma ta yi wani Tunani sai kawai ta fara maimaita"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un" a cikin zuciyarta.
Wacece wannan yarinyar Tare da Sadiq? Me ye alaqarsu da za su yi Hoto rike da juna haka?
A ina zata samu amsar Tambayoyinta?
Kiran Saddiqa ya katse mata Tunani da Sauri ta daga kiran ta na fadin"Saddiqa Sadiq ne a wannan Hoton."
Saddiqa tace"Innalillahi Sadiq ne?
Surayya tace"Ba tabbaci gareni ba, yakini ne da cewa shi ne Saddiqa"
Saddiqa ta share zufa kafin tace"To in dai shine to miye alakarsa da wannan yarinyar?
Surayya tace"Sunanta Hasiya, kuma yar'uwar mijin Salima ce, itace kawar da Saliha ta yi a kaduna, ta kuma zo bikin su Sultana Shiyasa ki ke Tunanin kin santa"

Saddiqa ta saki baki kafin tace"Tabbas an yi haka sai da kika fad'a na gane? Wacce Saliha tace ta tafi ba ta yi mata sallama ba?
Surayya tace"Saddiqa ki bar mganar nan a tsakanin ni da ke, zan yi yadda zan yi na binciko komai  ammh kema ta bangaranki ina so ki samo min address din in da yarinyar ke zaune."
Saddiqa tace"Big sis Khairiya tace min fa matar aure ce kuma a yadda abun ya ke, Sadiq shine mijinta wai"
Surayya tace"Duk da haka muna so mu san inda ta ke, ki kace a zariya ko?
Saddiqa tace"Eh haka tace"
Kawai sai Surayya ta yi wani Dariya takaici kafin tace"No wonder"
Daga haka ta katse wayarta, ta fara safa da marwa a tsakar falonta.
Ta na sake maimaita sunan Hasiya da Zariya.
Sai kawai ta fara Tunano yadda Sadiq ya nace ma karatu a zariya, ya gama yace bautar kasa, ya gama yace aiki zai yi achan sai ya fake da karatu, ta tuna ya na yawan ambaton wata ASIYA da sunan abokiyar aikinsa, kenan in ta hasaso daidai su Sadiq ya maida kananun yara ya ke wasa da Hankalinsu?
Koma wacece wannan yarinyar akwai alaqar da ta yi karfi a tsakaninsu wacce ba su sani ba, ita ko kadan bata bari Tunaninta ya bata wani mugun abu Sadiq ya ke yi ba, Tunanin ya fi karkarta kan abunda Sauran ba su hasaso ba.
Wayarta ta sake Dauka da Sauri ta Kira Salima ta na tambayanta ko ta na ina? Sai tace mata ta na makaranta.
Kai Tsaye Surayya tace"Salima me kika sani kan wannan yar'uwan mijin naki kawar Saliha?
Salima tace"Wacce Big sis? Ban ganeta ba?
Surayya tace"Wacce suka had"u lokacin bikin ki, ta kuma zo bikin su sultana.".
Salima da ke tare da Zahra'u a makaranta domin ta fara karatu a kasu, kaduna State University.
Tace"Oh na tuna me ya faru da ita?
Surayya tace"Kinsan ta sosai ne?
Salima tace"a'a ni ban kara ganinta ba, hala me ya faru?
Surayya tace"Taimako na zaki yi, ina son sanin labarinta ne, ko shi Mubark din ki tambayeshi mana."
Salima tace"Ok!
Sai Surayya tace zata Tura mata Hoton ta, Tunda ta lura kamar Saliman ba ta maida kai kan mganar da ta ke yi mata ba.
Da Sauri ta Bude data sai ga Hotunan Saliha ta Turo mata harda wanda ta yi mata ita kad'ai Tabbas wannan yarinyar ce.

Da Sauri ta Dauka ta Turama Salima, ta kuma kara kiranta tace ta bincika mata da Sauri don Allah.
Jin haka yasa Salima cikin Tunanin to lafiya? Ta dai san me ya had'a Big sis da neman Labarin wata!?
Sai dai sanin kawar Anty Saliha ce sai bata damu ba nan ta ke ta Bude datan ta, ta shiga ta ga Hoton da Big sis ta Turamata sai a lokacin ta kara gane Matar da ake mgana a kanta.
Zahra'u ce ta leka ta na ganin Hoton sai taga Hasiya da Sauri tace"Hala wannan ai Hasiya ce"
Salima sai ta kalleta kafin tace"Eh itace kinsan ta ne sosai?
Sai zahra'u ta girgiza kai kafin tace"Gasiiya ba sosai ba, ni ma da Bikin ku ne na santa, da ya ke Baba bai cika barin mu, muna zuwa zariya ba, sai dai su zo"
Sai salima tace"To ki tambayan min ko Baba ne kin ji ko?
Sai Zahra'u tace to shikenan zata tambayan mata, ammh sai da tambayeta me yasa ta ke son sanin Labarin Hasiya? Sai tace kawar yayarta ne ita ke son karin sani akanta.
Sai zahra'un ta gamsu da maganar Salimar kamar yadda, itama Salima ta gamsu da cewa dalilin da ya sa Big sis din ke son ta sani kenan.

Ita kuma ta bangaren Surayya, sai da ta gama Tunaninta gabadaya sannan ta daga waya ta kira Sajida tace anjuma tazo gidanta ta na nemanta.
Sajida kuma daman uwar son jin mgana ne da zence, ba jimawa sai ga ta tazo, itama Hoton Surayya ta nuna mata tace ko ta gane waye?
Da sauri ta Mike ta na kwalalo ido Lokaci daya ta na fadin"Mun shiga uku, kamar Sadiq?
Surayya tace"ai ba kama bace shine."
Sajida ta dafe kirji da karfi kafin tace"Shi ne? To ita wannan macen da ke tare da shi fa! Wacece?
Surayya tace"Shi na ke son sani yanzu, ki kara kallonta dakyau zaki ganeta, kin taba ganinta kawar Saliha da ta zo bikin sultana wacce tace yar'uwan mijin salima ce."

Sajida sai ta kara zooming din Hoton ta na gani kafin tace"Tabbas ba musu itace, kinsan ai fara ce sosai shiyasa na ga neta. Big sis sadiq me zai ja mana? Ba dai ya koma Bin matan aure ba ne?
Ta fad'a cikin tashin Hankali, Surayya ta Girgiza mata kai kafin tace"Ba na wannan Tunanin Sajida, a sanin da na yi ma Sadiq mutum ne mai ilimi da sanin ya kamata, ba zai aikata haka ba."
Sajida ta koma ta zauna da yarta a hannu lokaci d'aya ta na fad'in"Big sis kaina ya Daure? Ko da bikin ne suka had'u da juna?
Surayya na kallon wani gefe tace"Ba'a lokacin ba ne, sun jima da sanin juna Sajida."
Sajida ta yi shuru kafin tace"Big sis wlh na shiga Rud'u, me ke shirin Faruwa ne?
Surayya ta koma ta zauna gefen Sajida Ta na fadin"Koma wacece to alaqar da ke tsakaninsu ba ta haramci ba ne."
Sajida tace"To alaqar uwar menene tunda ba aure suka yi ba?
Surayya ta kalleta kafin tace"In kuma ace sun yi auren fa? In kuma ace ita din MATARSA CE.!"
SAi Sajida ta zabura kafin tace"Matarsa?
Cikin Dimuwa, surayya ba ta sami zarafin magana ba, kiran Saddiqa ya shigo wayarta da Sauri ta Daga.
Mirmishi kawai ta ke yi na dacin zuciya da takaici, Saddiqa na gayamata ta tura mata adireshin inda Hasiya ke zaune, kuma har da karin Shedar mijinta ma'aikaci ne a garin Abuja.
Surayya ta yi ajiyar zuciya kafin tace"Saddiqa mu bar mganar nan a tsakanin mu uku, bayan mu kada najita a waje, ni da Sajida gobe in sha Allahu zamu tafi zariya domin mu kara Tabbatar da zargin mu."
Saddiqa tace"Gaskiya ya kamata, ni wlh duk na Rude, Umma kawai na ke tunawa, fata na Allah yasa ba Sadiq din mu ba ne"
Surayya bata ce komai ba ta katse wayar, a ranta ta na tunanin suna ma yaudaran kansu ne in suka ce wai ba Sadiq din su ba ne.
Sadiq ne shine ajikin wannan Hoton ba wani ba.
Sajida ta katse mata Tunani da fadin"Me zamu je yi a zariya?
Surayya ta mike ta na fadin"Sanin gaskiya, da kuma sanin abunda ke Boye game da Rayuwar kanin mu da bamu sani ba Sajida."
Sajida sai ta kasa mgana itama har taji idanuwanta ya kawo kwallah.
Me sadiq ya ke aikatawa ne a wannan garin? Daman shiyasa ya nace ma garin, har Sa'insa ya fara yi da su saboda haka ashe ashe.

Allah yasa ba abunda suke zargi ba ne Allah ma yasa kama ce ba shi ba ne.
Surraya tace bayan su uku kada wani yaji wannan mganar sai ta gama Bincikan gaskiyan Lamarin
Sannan tace ko Sadiq kada su bari ya Fahimci wani abu.
Za su je zariya kuma zasu tono abunda Sadiq ya dad'e ya na Boye musu.
Daman kuma ta Fahimci hakan Tuntuni, rashin Hujja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login