Showing 69001 words to 72000 words out of 116366 words
masu dadi da lemuka.
Tuwon shinkafa miyar a gushi da Tokfish, da ganda sai zobo da kunin Aya.
Allah yasa yau su Asim naji abun arziki ba su yi min rigima ba Tunda na yi musu wanka suka ji ruwan zafi sai barci.
Har ya dawo ba su tashi har sai da ya yi wanka ya ci abinci sannan ya tada su da kanshi yana yi musu wasa.
Yara nan kamar su san babansu ya Dawo ba su yi mana kukan dare ba.
Suka bar Babansu ya sha Shagali.
Da asuba ne suka fara kuka sai na Dauke Asim na fara bashi Nono shi kuma sai ya Dauki Asif yana lallashinsa.
Ni ce ina dariya nace"Yara nan sun bani mamaki, ko kukan daren da suka saba mana yau ba su yi ba."
Na tuna ranar da ma kai su allura irin kukan da suka kwana suna yi mana.
Mirmishi ya yi kafin yace"Yaran albarka kenan, baza su takurama Abban su ba"
Yaso ranar muje gaida Amma, ammh sai na rokeshi in ya kaimu ya barni na kwana biyu a wajenta shiyasa sai ya bari sai Ranar litini ya kaini daganan ya wuce Abuja.
In na gama kwanakina sai na dawo, kuma hakan ce ta faru weekend din nan tare muka yi shi, ni da mijina da ya'yana.
Shi ya ke tayani Renonsu kamar kada ya tafi, ina jinsu wani Lokacin suna waya da Sultana, ni ma kuma ina waya da su Anty Surayya Anty Saddiqa da Saliha.
Sai Anty Sa'ima da Umma da tafi kowa kirana yanzu Saboda Darajan su Asim.
Muna hanyar zuwa wajen Amma ya ke fad'amin yaushe ya kamata na Shirya tafiya gusau.? nace masa kafin dai a koma makaranta Saboda Tp na
Sai yace wannan ba matsala ba ne sati daya dai ai bazai zama abun damuwa ba.
Mun isa da wuri tunda da safe muka kama Hanya Suprise na yi ma Amma sai dai kawai ta ganmu kamar daga sama.
Ta yi murna sosai ta rasa ina zata sakamu Saboda Farinciki, Barin ma Assadiq da ta rika yi masa barka da arziki.
Shima dalilin yi mata gaisuwan Adda yasa ya zo, sannan da kuma kawo mu ni da yara bai wani jima ba ruwa kawai ya sha ko lemun da Hamma Isuhu ya kawo masa bai sha ba.
Ya yi ma Amma gaisuwa tare sallama sannan ya tafi, 10k ya ba ma Amma ta yi ta godiya ita ai ganina cikin Farinciki ya isheta komai.
Na rakasa har mota su Asim na barci sai dai ya yi musu Rumguma daya bayan daya da Sumbata.
Nima haka ya rumgumeni ya sumbaceni cikin kauna kafin mu yi sallama da cewa sai mun yi waya.
Daganan Abuja ya wuce tunda Hanya ce.
Ni kuma ya barni wajen Amma ta da naji kamar an sakani a cikin aljannah.
Amma tunda muka zo ita ke wahala da su Asim Allah sarki sai fadi take yi"Allah ya sa ina raye gashi ina Goya ya'yan Hasiyata a bayana. Allah ya jikan Adda ta sha fad'amin kema watarana zaki ji dadin aure kamar kowata mace."
Sai ga Amma na hawaye sai na koma lallashinta.
Na zo mata da Sabulan wanka da na wanki da su omo sannan cikin kayan sunan da na samu na kawo mata leshi daya da Atamfa.
Amma na ta godiya tana kara godema Allah Hasiya ma ta samu Farincikin da ta ke mata fata.
Kwana Biyar na yi a wajen Amma sannan Hamma Isuhu ya kaini tasha ya sakani a motar zariya.
Ina mota ina Tunanin Hirar mu da Amma, ni na bata labarin irin yadda Umman Assadiq ta ke kirana saboda su Asim sannan yanzu ma ta matsa sai na je gusau.
Ammh tace na shirya naje, Sannan daman ta jima tana kai kukanta ga Allah, akan Allah ya dora kaunata a zukatan yan'uwan mijina ko Saboda Darajan yaran nan kuma tana ji a jikinta Allah nee ya amshi addu'arta.
Ta bani shawaran na yi hakuri na maida kaina wajen biyayya ga Mijina, sannan na bi yan'uwansa sau da kafa sannan in zan je na je musu da wani abun saboda alheri da kyautatawa na da dad'i.
Da wannan na fara Tunanin abunda zan kai ma Umma da Abba ga Innani ga Mama, Amma tace har Sultana in naje na yi mata alheri bakomai taci Darajan Abubakar.
Washegarin ranar da na dawo Assadiq ya kirani yace min yau gusau zai je, saboda haka na shirya sati mai zuwa zai zo ya Daukeni zuwa Gusau achan sai barni na yi koda sati daya ne
Ban yi musu ba nace Allah ya kaimu, daman tunani makaranta ne, sai kuma na lissafi naga a satin ne za'a koma zan iya zuwa na dawo kafin karatu ya kamkama.
******
Gusau.
Kamar yadda ya fad'ama Hasiya Ranar jumma'a ya baro Abuja zuwa Gusai, Ya samu kyakyawan Tarba wajen Sultana kamar yadda ta nuna ta sauya shima sai ya nuna mata ta na da fa da matsayi itama a rayuwarsa.
Cikin Farimciki suka kwana da Safe tare da ita suka je gaida su Umma suka dawo kuma tare.
Abunda ya lura ta rage fara'a saboda tun suna falon Umma da taji Umma na tambayan yaushe Twins za su zo mata ne taji shuru, yace sati mai zuwa zai je ya Daukosu Umma ta fara washe baki tana fara'a.
Abunda ya bama sultana Haushi Umma yanzu hankalinta na kan ya'yan da tace ba ta so, ammh yanzu ita ko damuwa da ita bata yi, har complain taje ta yi mata da cewa ko za su je asibiti ne ciki har yanzu ita bata samu ba, Umma tace wai ta kara Hakuri yaushe duka duka ta koma?
Sai kuma daman su Anty Sajida suna gayamata Umma yanzu son ya'yan nan ya Rufe mata ido bata ganin bakin Hasiya yanzu ta ma daina Zaginta.
Shiyasa tunda suka dawo ta ke masa cin mgana shi kuma sai ya kyaleta bai biye mata ba, shi ke janta ma da Hira ta na wani basarwa.
Sai da rana da ta yi musu abinci tunda yanzu tana gida sun gama jarabawa.
Suna kan Dining suna cin abinci ya kalleta yana fad'in" Siya zata zo kawo ma su Umma yaran nan su Asim saboda haka zata sauka anan Acikin dakunan ki. ki zab'a mata guda dayan da zata sauka aciki."
Cikin Mamaki sultana ta kallesa kafin tace"Nan gidan wai ka ke nufi?
Cikin shima mamakin tambayarta ya kura mata ido kafin yace"Eh nan gidan na ke mgana, ko ina da wani gidan da ya wuce nan ne"
Sultana ta tura bakinta gaba kafin tace"Tabdijam ni ai bani da masaukinta a gidana."
Hancinsa a bude yace"Bangane ba? Gidan ki naji kin ce?
Kai Tsaye sultana tace"Eh mana tunda ai saboda ni Abba ya baka kyautar gidan saboda haka da gidan da abunda ke cikin gidan duka mallakina ne"
Tsabar mamaki ya hana Sadiq mgana, kallon Sultana ya ke yi yana kara jinjina karfin halinta.
Cikin dan mirmishi yace"Oh ko Mallam shitu ne ya siya miki gidan sai kika taimakamin na ke zaune nima aciki?
Sultana bata taba tunanin irin amsar da zata fito daga bakin Yaya Sadiq ba kenan.
Cikin mamaki tace"Ni? Mahaifina ka ke zagi Yaya Sadiq a kan wata banzar bazawar..!
Bata karisa ba taga ya mike da sauri ta matsa baya.
Shi kuma da hannu ya nunata yana fad'in"Kul din ki, kin manta kashedin da na yi miki a gaban Umma? Da gaske na ke bazan dauki reni ko zagin cin mutumcin matata ba, baki isa ba ta na gaba da ke awajena ita na fara aura kafin na aure ki to ya kamata koyi girmamata, ya rage naki ki kiyaye ko karki kiyaye ni dai nace miki kul d'in ki yarinya."
Kawai sai Sultana ta fashe da kuka ta na fadin"Yanzu ni kayi ma gorin gida saboda matarka? Saboda ka fi sonta dani shiyasa ka kira sunan Ubana kai tsaye ba ka ji kunyar haka ba."
Yana jinta ammh yasan in ya Biye mata za'a iya yin mara kyau..shiyasa ya mike daga kan Dining din, ko abincin bai gama ci ba ya kama hanyar fita daga Falon lokaci d'aya yana fadin"In kin daukeshi a matsayin gorin to bazan ce miki ba haka ba ne sultana, gorin ne"
Yana jiyo kukanta ya yi kamar bai ji ba daman da key din motarsa a jikinsa ya shige motarsa ya bar mata gidan.
Gidan Big sis yaje suka sha Hiransu, yana gayamata zuwan Siya tare da su Asim.
Surraya tace"Kace Umma zata yi sallarta kenan."
Yana dariya yace"Umma na son yaran nan fa, ni fa ina ganin su za su kwace sunan magajin gida."
Surayya ta saka Dariya lokaci daya tana Fadin"Umma ai ina tsoron Allah ne ya fara kamata saura su Sajida."
A gidanta ya ci abinci ya koshi shima har mangariba sallah kawai ke fita da shi.
Ya baro gidanta kenan bai ko biya ta gidan Su Umma ba ya sauka a gidansa ya wuce sai ya tarar Sultana bata gida.
Da ya tambayi megadi sai ya gayamasa yana fita ba dadewa itama ta fita.
Sai ya kada kai yasan kila tana gidan wajen Umma, sai dai yana zuwa Shashen Umma ya ga bai ganta ba.
Sai ya tambayi Umma.
Ita kuma cikin mamaki ta kallesa kafin tace"Au ba ta koma gida ba?
Cikin mamaki ya ke kallo Umma kafin ya yi mgana ta cigaba da fad'in" Tazo min nan da rana haka tana min kukan wai kace Matarka a gidanta zata sauka don tace gidanta ne wai shine ka yi mata gorin gida ka kuma kira sunan mahaifinta ka zaga."
Cikin dage gira yace"Ita sultanan tace haka?
Umma tace"Eh ni dai na bata hakuri nace gidanka ne kana da ikon zabar inda Matarka zata sauka, to ta dai fita ni wlh na dauka gida ta tafi."
Sadiq ya yi huci kawai bai yi mgana kafin ya mike yana fadin"Umma ki kyaleta ina tunanin tana gidan su"
Umma tace"Bari dai na kira ta naji."
Nan take Umma ta hau kiran Sultana ammh sai taki Dauka.
Sai ta kira mallam Shitu bayan ya Dauka sun gaisa ta tambayeshi Ko Sultana tazo?
Cikin bacin rai yace"Ta zo shashshan yarinya Butulu, tazo min da wata mganar banza na Fattaketa nace komai Dare bazata kwanamin a gida ba, kuma in bata kwana gidan mijinta bq sai na ci mutumcinta."
Umma sai ta fara bashi Hakuri cikin jin kunya yace shi ya kamata ya basu hakuri yarinya tana neman gagaransu.
Su da suka riketa suka yi mata komai a Rayuwa.
Sadiq bai jira Umma ta gama waya ba ya fice bai shiga bangaren Abba ba, saboda Mama na wajensa sai kawai ya Shiga mota ya wuce gida ammh ya Tsaya a masallaci sallar isha'i.
Ya na komawa gida megadi yace masa Hajiya ta dawo sai ya gyad'a kai.
Yana Shiga ya ganta zaune a falo ta na kuka.
Ya dad'e tsaye yana kallonta kafin kawai ya kad'a kai ya wuce cikin Dakinsa.
A ransa yana jin bazai lallasheta ba Tunda shi dai bai yi mata wani abu ba, itace ta dauki Lamarin da Zafi.
*Janafty*
*TMWB3K014*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
https://chat.whatsapp.com/IhAz8h8nRy250ZnGGXwM65
*BOJUWA HERBAL'S BY SURAYYA DEE*!
*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Gaban ayu*.
*Hakkin daka gangariya*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
*Ana dafa GIMBIYAR KAZA da tattabarun garari*.
Kwanciyarsa ya yi, ko abinci bai Nema ba tunda ya ciko cikinsa a gidan Big sis ba shi da damuwa.
Shi abun na Sultana yanzu ya daina mamakinta in ta yi wani abun.
A baya yana kallon wani abun in tayi a matsayin yarinta sannan ya na yi mata uzuri ashe ba haka ba ne ta girmi Tunaninshi.
Yana nan kwance sai ga kiran mallam shitu, sai a lokacin yaji yar kunyar sunan da ya kama nashi kai tsaye duk da bai daukesa gori ko cin zarafi ba.
Cikin jin nauyi ya dauka suka gaisa kamar yadda suka saba, mallam Shitu ya tambaye shi ko Sultana ta dawo? sai Sadiq yace gata can a falo.
Mallam Shitu ya cigaba da fad'in"Ka yi hakuri Abubakar, sai dai zan baka Umarnin duk wani shegentaka da yarinyar nan zata kawo maka ka yi mata Hukunci daidai da abunda ta aikata Tunda bata da kirki, shashasha ce."
Sadiq yace"Bakomai Mallam, Yarinta ke damunta zata bari in ta kara mallakan Hankalin kanta."
Mallam Shitu yace"Wani hankali? Yarinyar da ta wuce ashirin ka ke kira yarinya? Kanenta ga su nan ai baza su aikata irin sakarcinta ba. Nan ta zo ta na gayamin wasu sakarcin mganganu ban Saurareta ba na Fattaketa ko zama ban bari ta yi ba."
Sadiq ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Kuma ni duk abunda tace na yi mata ba gaskiya ba ne, ina iya bakin kokarina wajen kwatatan adalci a Tsakaninsu."
Mallam Shitu yace"Haba ai ba sai ka Fad'a ba kowa ya san komai, ni ban saurareta ba kai ma ina baka Umarni in ta kawo maka wani shegentaka ka yi mganinta."
Da haka sukayi sallama, ya kwanta ya yi shuru yana tunanin Rayuwa.
Tabbas ijiye mace Fiye da d'aya ba abu ba ne mai sauki.
Ita Sultana duk bata ga abunda ya ke yi ba, ba zata taba godema kokarinsa ba.
Rayuwa yanzu ta yi tsada ko man da ya ke konawa wajen jeka ka dawo tsakanin gusau da Zariya kad'ai ya ishesa.
Kada ma a saka Labarin sauran Hidimdimunsa da na su da ke kansa, duk ita bata gode ba sai kokarin tada rigima take yi, shi kuma Saboda Darajan su Umma yasa bazai Biye mata ba.
Sultaana kuwa har kara jiniyan kukanta ta ke yi a tunaninta ko Yaya Sadiq zai fito ya duba ta ya lallasheta.
Sai dai hakkanta bai cinma ruwa ba, har ta gaji da daga murya ta koma ta na kukan zucci.
Abu daya yafi bata mata rai yadda Umma taki goya mata baya kiri kiri tace wai ta koma ta yi hakuri ta bar Yaya Sadiq ya sauki bazawarar matarsa a gidanta ai hakan ba adalci ba ne.
Shiyasa batare da shawara da kowa ba ta kama hanya sai shinkafi.
Ai ko ta na zuwa sai da ta yi nadamar zuwa ko kad'an babanta bai Saurareta ba, balle yaji irin abunda aka yi mata ko minti talatin bai bari tayi a gidan ba ya fattaketa ya na kiranta butulu Tunda har zata zo ta na kawo mganar wad'anda suka riketa suka Rufama Rayuwarta asiri.
Ko ruwa bai bari ta sha ba yace ta koma Gidan mijinta, sannan kuma kada ta kawo dawo masa gida matukar ba alheri ya kawo ta ba.
Kukan da take yi duk rabinsa na kishi ne, bakinciki take yi da Hasiya ganin har tazo ta haihu kuma ga shi kamar Umma ta fara son yaran nan..shiyasa yanzu ido rufe ta ke so tayi Ciki itama yan Biyu ko Umma zata Daina son yaran nan.
Saboda jin Hauahinsa a d'ayan bedroom d'inta ta kwana, da Safe kuma ta yi kwanciyar ba ta yi abun karyawa ba Sadiq ko bai ko Tsaya ba ballatana ya wulakanta
Da kansa ya shiga kitchen ya Dafa Ruwan zafi sannan ya soya kawai yazo ya had'a Tea ya sha da Kwai tare da Buredi.
Yaso ya kai gobe da Safe ammh ganin iskancin Sultana yasa ya yi shirin komawa Abuja a ranar.
Bayan ya gama karyawa ya koma daki ya kira Siya suka yi ta waya suna shan Soyayyarsu sai sha Biyu ya tashi ya yi wanka ya shirya ya Dauki Mota ya fita daga masallaci ya shiga gida ya gaida su Umma, Ko alokacin sai da Umma ta kara tambayarsa Yaushe su Asim za su zo? Yace sati mai zuwa.
Sai ga Umma cikin Fara'a ta na fad'in"Ma sha Allah, ammh za su kwana Biyu ko?
Kai Tsaye yace"Eh sati nace za su yi, ko ba na nan sai direban Abba ya maidata gida tunda ga yara."
Umma tace"Eh hakane kam,"
Suka yi shuru na wani lokaci shi yana Duba wayarsa ne.
Tahir ne ya ga kwana Biyun nan gabadaya in dai ba abun siyasa ba gabadaya post dinsa na Soyayya ne, to ya fara zargin wannan karon Tahir ya fara soyayya gaskiya ya daina yaudaran ya'yan mutane.
Hankalinsa na kan wayarsa yaji Umma na tambayarsa can gidan Siya zata sauka in ta zo kenan?
Sai ya maida wayarsa aljihu Lokaci daya ya na kallonta kafin yace"Eh haka nace Umma, tunda ina da gida bai kamata ta rika sauka gidan big sis ba."
Umma ta jinjina kai a zuciyarta kamar tace to ta sauka a waje na mana Saboda su Asim ammh sai ta kasa mgana shi kuma ganin haka yasa ya kara kallonta yana fad'in"Ko hakan bai yi ba Umma?
Da Sauri tace"Ah ya yi sosai ma, Allah ya kawo su dai lafiya."
Ya amsa da Ameen Ameen daganan yace mata yau zai tafi, bata masa mganar Sultana ba sai da taji yau zai koma cikin mamaki tace"Yau kuma? Sultanan bata dawo ba ne?
A dakune yace"Ta dawo mana, ina da ayyuka a office ne gobe da Safe."
Nan dai ta yi masa Fatan alheri ya sallameta daganan ya shiga bangaren Mama ya kara yi mata gaisuwa duk da har gidan gaisuwan yaje.
Daganan da ya fito sai ya shiga bangaren Innani ya iske ta tare da Farida da Siyama suka gaisheshi.
Innani na ganinsa ta washe baki ta na yi masa kirarin baban yan Biyu.
Bai jima a wajenta ba ya yi mata sallama ta shiga kwarara masa addu'a tun ballatana ma da ya bata kudi.
Yana jinta yan Biyu da mamansu sun sha addu'o'i.
Abba baya nan sai dai ya kirasa ta waya, Umma ce ta kirasa tace in bai tafi ba ya dawo tana son ganinsa.
Da sauri ya koma bangarenta ta na zaune inda ya barta.
Shima sai ya koma ya zauna inda ya taahi Lokaci d'aya yana fad'in"Umma lafiya kuwa?
Kai Tsaye Umma tace"Daman saboda na yi maka mgana ne, kana ganin bai kamata matarka ta can zariya ta dawo nan da zama ba? Gani na yi kai ma ya kamata ka Huta zirga zirgan zai yi maka yawa kaje can kazo nan."
Sadiq ya yi shuru kafin yace"Zata dawo Umma, ammh ba yanzu ba."
Cikin mamakinsa Umma tace"Bangane ba? To meyasa?
Kai Tsaye yace"Saboda ta na karatu, ammh ta kusa gamawa, nima ina Tunanin in tagama ta dawo nan da zama ko can inda na ke aiki."
Umma da sauri tace"A'a ba can ba, nan din dai, in can ka ke so sai dai ka tafi