Showing 87001 words to 90000 words out of 116366 words
nesa ba kusa ba ni a Budurwa Yaya Sadiq ya aure ni ke fa? Bazawara sauran wani, kuma ma kin ji kunya mai kwacen mijin wasu kawai."
Ta karishe fad'a cikin Rashin kunya, ina jinta sai dai ban tanka mata ba.
Mirmishi kawai na yi na dago ina kallonta kafin nace"To nagode sosai."
Na maida kaina kan wayata a karo na Biyu.
Sai ta ji haushin ban Biye mata ba, cikin kara Tusamin haushi tace"Uhm ki kara ma Bokan ki kud'i, tunda aikinsa ya yi kyau ga shi Yaya Sadiq zai tafi dake Abuja, sai dai ina so ki sani wlh Tallahi yana can ne ammh zuciyarsa na tare dani, in a baya kina Fariyan saboda ya'yan da kika haifa ne nima cikin gareni kuma nima in sha Allahu yan Biyu zan haifa sai naga karyan Tsiya, har Umma da ke sonki yanzu sai ta daina da ke da ya'yanki dama a rashin uwar daki ta yi na kishiya."
Saboda na kara Tusa mata haushi sai na kara Dagowa ina fad'in"Allah ya baki yan uku ma in dai Alheri ne ina miki Fatan haka."
Ta murgud'amin baki lokaci daya ta na shafa cikin jikinta tace"Ohon miki dai, kyaji da munafunciki."
"SULTANA..!"
Mukaji muryan Assadiq daga sama a tare muka juya muna kallonsa yana Tsaye a kofar dakin sanye da Shadda Tazarce har da hulansa na bakar Dara.
Bamu da masaniyar ya dad'e a wajen, kuma yaji duka maganganun Sultana ko daga yadda ya ke bin Sultana da wani kallo na zaki gane kuran ki.
Shigowa dakin ya yi a Fusace lokaci d'aya yana fad'in"Sannu rasa kunye beran tanka, nace sannu da aiki."
Kanta na kasa ta fara fiki fiki da ido na alamun bata da gaskiya.
Ni kuma muryata a kasa nace"Sannu da zuwa.'
Kallo daya ya yi min ya kauda kai cikin kaushin murya ya kalli Sultana Lokaci d'aya yana fadin"Kada ki manta ba ke na fara Aura ba, ita na fara aura kuma a bisa al'ada itace Uwargida tana gaba da ke a wajena sannan a shekaru ma tana gaba da ke, ban ce ki sota ba, saboda daman ba ke ce daman ya dace ki sota ba. Ni ne ya dace da na sonta Tunda ni na ijiyeta. Ammh ki sani ya zame miki Dole ki koyi girmamata matukar kina son zama lafiya tare dani, in kuma baki so ki Cigaba da tozarta ta, ni kuma na yi alkwarin kare darajarku gabadayan ku, bazan kuma lamunci d'aya na cin mutumci d'aya ba."
Ya karishe fad'a yana nuna Sultana da yatsa.
Cikin gwaron Numfashi ta kwaso magana ya dakatar da ita da cewa" Bana son jin komai, na riga naji komai malama, ki fita ki bama mutane waje kawai."
Ya fad'a ya na nuna mata Hanyar Fita, ai sai gata sumu sumu ta fice ta na wani sunne kai kamar mutuniyar kwarai.
Ganin yadda ya Harzuka yasa na kallesa ina fad"in"Ka yi hakuri Assadiq"
Cikin kuramin ido yace"Ba hakuri zaki bani, ke ce zan gayama gaskiya ni ban ce ki zauna tana miki tozarcin da taga dama ba, ki rike girman ki yadda zata gane kina gaba da ita."
Kai na gyad'a kafin nace"In sha Allahu, ni ban ma Biyre mata ba."
Kai Tsaye yace"Kin yi kyan kai, kayan kin gama had'awa?
Ya fad'a yana kallon akwatuna da ke tsakar dakin, sai na gyada masa kai sannan nace masa Eh.
Bai ce komai ba ya kwashi akwatunan zuwa Haraban gidan Lokaci d'aya yana cemin na shirya yanzu zamu tafi.
Ganin tafiyar da gaske gaske tafiyar ne sai duk jikina ya yi sanyi, Na je bangaren Innani na yi mata sallama ta rike hannuna ta na fadin"Yar nan ina jin dadin zama da ke kuma zaki tafi?
Farida na gefe tace"Innani kuma Abuja fa Anty Hasiya zata koma inda Yaya Sadiq ya ke aiki."
Innani tace"Shi magajin gida can Habujan zai tafi da ke?
Sai na gyada mata kai kafin nace"Eh Innani haka yace"
Innani ta ja numfashi zata yi mgana sai ga Assadiq ya shigo tare da su Asim dama nace ya karbo su su yi sallama da Innani.
Hannuna ta saki ta rike nasu tunda Assadiq ya zauna a gabanta ya rike mata su.
Sai ga Innani na hawaye ta na shafa kansu, suma kamar sun sani suna ta jan hannunta.
Innani ta kalli Assadiq kafin tace"Tare zaku tafi da su can Habujan ne magajin gida?.
Cikin Sauri yace"In sha Allahu, ,Ammh yanzu Zariya zan kaita akwai abunda zata karisa sai zuwa nan da Sati biyu zan koma na Dauketa mu koma can gabadaya."
Innani tayi shuru kafin tace"ita sulsana nan zaka barta kenan?
Yace"Eh innani zata zauna tare da ku, zan rika zuwa ina ganin ku in sha Allahu."
Cikin gamsuwa Innani ta jijjiga kai kafin tace"Shikenan, da dai zaka yi hakuri ka bar min yan yara nan suna Debemin kewa magajin gida."
Assadiq ya yi mirmishi kafin yace"Innani ai suna shan Nono, ammh ki yi hakuri na yi miki alkwarin in aka yayesu nan gidan za su dawo hannun Umma."
Sai Innani taji dadi ta rika shafa kansu tana saka musu albarka.
Harda 500 ta kwance a hannun zaninta ta ba su, nima ta na ta sakamin albarka.
Har sai da Assadiq yace"Innani kwata kwata yanzu kin daina sakamin albarki d'in nan."
Innani na gyara gilashinta tace"Ai yarinyar nan sai dai Allah ya saka mata, nan ta ke zama tare dani duk abunda na ke bukata shi ta ke yi min dole kaji ina saka mata albarka matar taka yar kirki ce, ka riketa Amana da gaskiya Allah ya yi muku albarka gabadaya ya baku zaman lafiya da Zuru'a dayyiba, ya kuma raya muku ya'yanku cikin Addinin musulunci ya Had'a maka kan matanka gabadaya."
Ni da shi muke ta amsawa da Ameen Ameen.
Sai da na yi hawaye da Innani ke ta fad'in"Allah yasa mu gana.".
Ni kuma sai nace"In sha Allahu akwai rabon gwanawa a gaba Innani."
Ba ni kad'ai na yi kuka ba har Umma da Mama sai da suka yi hawaye Anty Surayya ma sai ta zo muka yi sallama
Umma ta had'amin sha tara na arziki kaya sabbi ta dinkamin su Asim kuma kaya sai dai su ba ma wasu, ga kayan wasa sannan Umma ta ce min duk abunda nake Bukata na yi mata mgana.
Abba kuma ni da su Asim kyautar 50k ya yi mana, ina ta godiya ina hawaye Asim ya fara kuka Asif ya kama kamar su san tafiya zamu yi, Allah Sarki har muka dauki hanyar Tafiya kuka suke yi sai dakyar suka yi shuru bayan na basu Nono na kuma had'a musu da madara
Sultana bata bani mamaki ba, ko da zamu tafi kowa ya fito ammh ita ko lekowa ta na shashen Umma kishinta baya Boyuwa a kaina.
Sai da muka yi nisa ne Assadiq ya kalleni yana fadin"Siya kada ki karamin abunda kika yi min yau, ba na so, nace ga Hukumcin da na yanke ke kuma ki ce a'a. Ban san ki da Gaddama ko ja'in ja ba."
Kai Tsaye na amsa laifina na kuma ba shi hakuri, shima kuma yace ya yafemin
Muma tafe muna hira su Asim daga kuka sai barci, tun da safe daman na kira Adda Fati nace Habiba taje gida ta karbi key hannun maman Suhailat ta gyaramin daki sannan ta yi min girki yau zamu dawo tare da Assadiq.
Ina ga kuma da Sassafe ta je, domin muna isa wajen biyu saura na rana muka iske ko'ina tas da shi har girkin ta gama yana tashin kamshi.
Maman suhailat bata nan taje kano sai yarta ne ke gidan Ummi kuma ta na makaranta.
Duk sai naga dakina ya Sauyamin, wattani uku ba kwana uku ba ne.
Habiba nata santin su Asim sun girma sun zama manya ga wayau sannan taga har sun fara tatan tafiya.
Ba ta dade ba, tana ganin mun dawo ta shirya ta tafi bayan Assadiq ya bata 2k yace ta Hau mashin.
Muna yi sallah ban ko tsaya cin abinci ba na kira su Umma na ce mun sauka lafiya.
Anty Surayya ma na kirata na kara mata godiya ta bani kayan kwaliya da dogayen Riguna da Maryam's Egyptian Abaya.
Ranar Saboda gajiya yini muka yi a daki da daddare ne ya fita ya siyo mana kaza da Tsire muka ci tare da shan Youghourt muka koma muka kwanta sai dai mun ci Amarcin wannan Daren ni da Assadiq an dad'e daman ba'a had'u ba.
Sannan ko da ni ke can ban yada manganunan gyara na Surayya Dee ba, na ma gani a status dinta tace zata Fara Dahuwar kaza na yi mata mgana ina so.
Kafin tafiyarmu Abuja zata aikomin da shi, in ma na koma can duk ana tare tunda dai na aminta da ingancin kayanta suna da kyau da Tasiri sannan su dad'e a jikin mace ba su daina aiki ba.
+234 803 277 3332
Sai washegari maman suhailat ta dawo ta zo har daki tana min maraba da sauka tace tayi kewana ni da su Asim.
Na dibi kayan kwalliya na bama yarta ita kuma na bata atamfa cikin wad'anda Umma ta bani ta na ta godiya.
Ban fita ko'ina ba tunda Assadiq na nan waya kawai muka yi da Adda Fati sai Ramatu da nace musu na dawo.
Sai Litini da Safe Assadiq ya tafi da niyar sai bayan Sati biyu zai Dawo ya tafi dani.
Nayi masa maganar kayan daki yace na barsu anan acan Abuja komai na kayan more rayuwa an saka bani da matsalan komai, kl daki kuma zai kara Biyan haya na shekara, in na zo garin zan samu wajen sauka.
Shi da ya ke yanzu ba shi da wani abu da garin Zariya ni ce daman kuma yanzu zan koma kusa da shi.
Sai Masters kuma tuni ya gama project ne ma yaso ya bashi matsala ammh daga baya ya shawo kan matsalan.
Saboda Hakkin Zaman tare Maman suhailat da Ummi na fara gayama zan koma Abuja, suka yi min Fatan alheri.
Maman suhailat kuma tace zatayi kewar mu ni da Asim.
Adda Fati kuma da kaina naje na gayamata ranar da naje na kaimata Tsabaranta ita da Habiba.
Ta tayani murna kwarai da gaske Adda Rukayya kuma sai a waya na gayamata.
Ta kwashi gud'a kafin tace"Allahu Akbar yau ga Hasiyan Amma a garin Habuja."
Ina ta Dariya, haka ma Ramatu ta yi da tazo min sannu da zuwa na gayamata suna ta cewa mahakurci mawadaci.
Ina shirina a sannu sannu sannan naje gidan su Safiya itama na kai mata Kayan kwalliya na gaida mamansu, daganan kuma ta rakani makaranta na fara Sreenning.
Kuma Alhamdulillah kwana hudu na yi muna zuwa ma gama gabadaya sai Jiran sakamako..
Itama tamin murna jin zan bi mijina zuwa Abuja, sannan ta yi jajen zan tafi na barta.
Ni kuma nace Allah ya bata miji ma'aikaci a garin Abuja sai tazo can mu had'e tace Ameen.
Assadiq ya Turamin kudi saboda siyan wasu abubuwan sannan yace Adda Fati ko Adda Rukayya cikin su wata ta shirya muje su ga inda muke ko Saboda gaba.
Amma na fara gayamawa, Tunda ita na fara gayama zencen komawata Abuja, ita tace na gaya musu cikin su wacce ke da Sarari sai ta rakani ammh tace a madadinta Inna Talatu ta bi ni itama ta saka albarka.
Haka ko akayi, Adda Fati taso taje ammh Adda Rukayya na ji tace ita zataje sai ta bar mata.
Inna talatu kuma da kaina naje na gayamata tace ta na ta fama da kafa sai dai daga baya zata zo taga inda na koma sai kawai nace Ramatu da Habiba su shirya mu tafi tare.
Mijin Adda Rukayya da tace masa zata rakani Abuja mamaki ya rika yi.
Har yana kara tambayan kuma muna zaune lafiya da mijina ba abunda ya same sa?
Adda Rukayya tace ba gashi har zan koma Abuja inda ya ke aiki ba, kuma ita da kanta da tazo gidana ta ke fad'amin.
Ni sai ya ma ba ni dariya, ni kaina nasan mutane da dama suna can suna shan mamakin jina shuru a gidan aurena a karon da aka Fidda min rai a kan zaman aure.
Adda Fati na ba ma kudi ta siyamin su kuka kubewa, Daddawa, Kuli yaji kayam kamshi sannan na saka aka dakamin garin kunin Alkalama na ke dama su Asim da ni kaina.
Sannan har Fulawa sai da na siya, saboda Dankwake da kayan miya Bushasshe da Tumatur na dai siya duk abunda nasan zan iya nemansa acan.
Kuma daman yace kayan wasan mu kadai zan dauka, ni da Zariya ba yanzu ba in ma munzo sai dai katsina Bikin Tahir sai in kuma wani abu ya faru mara dad'i wanda ba'a fata.
Kayan gyaran jiki kuma na siya wajen Surayya ta aikomin da shi har da Dahuwar kazar Uwayen gida tare da Tsumi da maganin sanyi.
Ni bana wasa da shan maganin Sanyi,ta dalilina na had'a ta da mutane sosai ciki harda yayyen mijina.
Adda Rukayya ma na yi mata Ciniki kuma itama Saboda ingancin mganinta yasa ta kawo mata Mutane sosai.
Sati biyu na yi Assadiq yazo Ranar jumma'a ya kwana Asabar muka dauki hanyar Abuja
Duk wani abun da zai lalace Adda Fati na ba mawa da sauram kayan abincin mu.
Maman suhailat harda hawayenta ammh tace tana shiga Abuja zata nemeni.
Ni dai nace su yafemini in na yi musu ba daidai ba Ummi tace Babu abunda na yi musu Allah ya yafe mana gabadaya.
Nima nace na yafe musu duniya da lahira, har makota ma da muke huldar arziki. Sannan har makarantar da nayi Tp sun so su rikeni na musu koyarwa su rika Biyana lokacin ma zamu tafi gusau to bayan na dawo ma sai da suka kirani nace musu zan koma Abuja da zama ne.
Da wuri muka fita shiyasa muka isa da wuri, ni ce a gaba tare da Asim sai Adda Rukayya da Habiba da Ramatu a baya tare da ya'yansu da Asif.
Gidajen suna nan a kusa da ma'aikansu a 24 Aminu Crescent Abuja.
Kuma 3bedroom ne da Falo guda biyu sai kitchen sai Tiolet a kowani dakuna sai Kuma haraban wajen ijiye mota.
Kowani gida da nashi Aparment din daidai kowa bazai shiga Hurumin kowa ba.
Kuma duka duka Gidaje Goma ne a waje d'aya a jere acan kuma gefen shima goma can gaba Wajen dai gidaje talatin ne.
Muna sauka shi ya fita ya barmu muna gyare gyare Adda Rukayya da Ramatu nata santin gidan komai Sabo.
A albashin mutum za'a cire har kud'in Furnitures.
Sai yamma ya dawo ya kawo mana abincin da ya yi mana Takaway.
Lokacin mun gama gyara gidan Tunda har mopper mun zo da shi na Zab'i dakina da na Assadiq.
Shima na kawo masa wasu kayansa , kuma yace zai kwaso sauran kayansa a inda ya ke zaune.
Kwana daya su Adda Suka yi min suka koma Zariya Habiba kuma Saboda makaranta, Da zai fita Office ya Daukesu zuwa Tasha ya saka su a motar Zariya bayan ya ba su Cikakken kudin mota.
Ni kuma ranar ni kadai na yini dagani sai yara kamar mayya, ban fara girki ba tunda ba kayan abinci da rana da ya fita lunch ya je ya yi min Takeway ya kawomin.
Da daddare ma haka, washegari kuma sai da ya dawo aiki muka fita kasuwa muka yi siyayyan kayan abinci sannan bayan mun dawo gida ya koma yaje ya kwaso kayansa a inda ya ke zaune.
Tare dashi muka jera komai a muhallinsa,
Shi wannan gidan akwai kayan kallo har da Firiza da A.c komai lafiya lau.
Ana ta kirana ana yi min Fatan alheri.
Umma da Mama duk sun kirani, Kaf yayayen Assadiq sun kirani illah ban da Salima da Sadiya da Sajida.
Bansani ba ko shi sun kirashi, ni dai ban matsa kaina ba, ballatan nace masa basu kirani ba.
Muka fara shimfid'a kyakyawan Sabuwar Rayuwa tare da Assadiq da ya'yana.
Mu kad'ai muka fara tarewa a Estate din nan , kullum in Assadiq ya fita ya barni dagani sai ya'yana muyi ta burumtu a cikin gidan.
Ba bu abunda na nema na rasa sannan ga wayata ina waya da yan'uwana tare da yan'uwan mijina.
Ni kaina in na juya naga yadda Allah ya maida Rayuwata sai na daga hannuwa sama na yi ma Allah kirari da Hamdala
Sannan nace"Alhamdulillah."
*Janafty*
*TMWB3K017*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk
Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan.
Sultana dai ta gama makircinta da kokenta kokenta na kada Assadiq ya tafi dani Abuja hak'anta bai cin ma Ruwa ba.
Na dauka daga wannan Lokacin ta Saduda ashe ba haka ba ne, ta fito da wani Sabon Tsirfa ko nace tsohon ya yi da ba wanda bai san irin wannan abun na masu kishi ba.
Addabarmu ta fara yi sai muna cikin barci ance dare mahutane ga bawa ammh ita a wajenta bamu isa mu huta ba.
Karfe biyu na dare uku haka zata rika Kiran Assadiq kullum kuma mganarta daya ne, abunda ke cikinta sun hanata sukuni sun hanata barci.
Ko tace ta kasa tafiya maranta na Ciwo, karya dai da makirci iri iri sai kuma ta kira ta na kuka.
Kuma abunda ya bani mamaki tana wajen Umma ne ammh ba ta rabo da korafin wani abu na Damunta.
In yace aje asibiti sai tace ba na asibiti ba ne, da farko ya fara Biye mata sai da ya kira Umma ya gayamata ita ta yi masa fad'a tace ya fita Batun Sultana sakarci ne ita bata taba sanin wani abu na Damunta ba, balle kuma har tace Cikin jikinta ya hanata barci sai kace ya yi watanin haihuwarsa.
Ashe bayan Umma tayi mgana da Assadiq sai da ta sameta har daki ta yi mata fad'a akan abunda take yi.
Shikenan Sultana ta saka kuka tana fadin ita ba'a son abunda ke damunta ba kuma anzo ana cewa karya ta ke yi.
Nima ranar ina zaune kusa da Assadiq Umma ta kirasa na so na tashi ya hanani, anan naji yadda Umman suka yi da sultanan a raina sai da na yi Dariya ita abun nata harda yarinyata ko rashin Hankali ne bansani ba ta na wani abu kamar wata yar fari.
Duk karshen wata ya ke zuwa Gusau in ya tashi dawowa Umma ta bashi abubuwa na amfanin girki tace a kawomin wanda dai tasan zai