Showing 75001 words to 78000 words out of 116366 words

Chapter 26 - Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

318

Bud'e mana muka shiga.
Yadda na gane matar gidan bata maraba dani, shine har wutan dakunan takashe ko'ina Duhu sai da ya kunna Haske ya gauraye.
Nice na ke ta bin ko'ina da kallo shi kam yana rike da Asif shi ya shigar min da akwatinana dakin da ke yamma da falon.
Shima a kulle ne sai da ya saka makulli ya Bud'e.
Bakomai a dakin sai gado sai wardrope akwai kuma Tiolet aciki sai Cafet sai dai gadon karami ne ba babba ba.
Kamar yadda na lura gidan Bedroom guda uku ne, biyu suna waje daya Daga yana bangarensa na Dabam.
Yadda bai ce min komai ba nima ban ce masa komai kan Sultanar ba.
Shi ya taimakamin na yi musu shirin kwanciya.
Da yake da yamma Mama ta sake yi musu wamka tun a gidan ma suka Fara barci, nima sai yace na yi shirin kwanciya ya duka ya sumbaci kuncin su Asim sannan nima ya duka ya Sumbace.
Lokaci daya yana fadin"Sai da Safe Matar Assadiq.'
Nima ina mirmishi nace"Sai da Safe Mijinsiya."
Yana mirmishi yace na Rufe kofa kuma sannan na yi addu'a kafin Fitarsa har A.c da fanka sai da ya Tabhatar da ya kashe min.
Ni kuma sai na Shiga Tiolet na kama Ruwa na zo na yi shirin kwanciya bayan na yi addu'a na Tofe jikina da na ya'yana na Rumgumesu bayan na Rufe kofar da key ta ciki..ban ksshe wuta ba Saboda su Asim na motsawa suka ga Duhu za su fara rigima.
Barci na sha sosai sai Asuba na Farko ko da Assadiq yazo yana bugamin kofa a lokacin ina sallah ne.
Bayan na idar na tashi naje na Bude kofar na dawo, yaran nan sun yi barcin Dare ammh da Asuba nan suka fara kuka duk suka rikani.
Asssadiq kuma bai Dawo daga masallaci ba, kukansu har haraban gidan nan Ammh Sultana bata Fito ba.
Shine ya dawo masallaci yaji kukansu ya Shigo da gudu dakin yana Tambayar Ba'asi.
Cikin gajiya nace"Bansani ba, kawai a tare suka farka suka fara kuka."
Allah Sarki Assadiq haka ya Rikenin Asim da Asif a tare yace na had'a musu madaransu.
Ba ruwan zafi shi ya ce na fito muje kitchen ya nuna min komai yace na Dafa Ruwan zafi.
Haka ko akayi ya jirani na Dafa ruwan Dumi na Dama musu kowannen na cika masa Fidansa, falo muka Fito ni da shi Saboda yadda suka Rikitamu da kukansu shi yana ba wa Asim ni kuma ina rike da Asif ina bashi.
Bamu san Fitowarta ba sai ganinta muka yi a saman kan mu.
Kere kere tana kallon mu, ko Darajan yana mijinta bata gaishe shi ba sai nice na gaisheta ta yi kamar bata ji ba ta wuce ta shiga kitchen ta na sakin karamin Tsaki.
Kallona ya yi rai bace kafin yace"Kada ki kara zubar da  girman ki, ki gaisheta in bazata gaisheki ba ta bar shi."
Cikin nuna komai ba komai ba nace"Haba bakomai ai ni nazo gidanta."
Bai kara mgana ba ammh Daga gani ranta ya baci, muna zaune ta fito ta koma dakinta d'auke da Mug a Hannunta.
Allah ya taimakemu suna sha suka daina kuka daman rigima ce da Yunwa kuma.
Ban dauka Haka Sultana ta yi nisa da Tsanata ba sai Ranar, ko Abun kari bata yi mana ba ballatana Ruwan zafin da zan yi ma yara wanka Tunda Tanki ya lalace ruwa baya zuwa ta makewayi.
Bansani ba ko yaje ya yi mata mgana ne, naji tashin muryansa ya na yi mata mgana ammh ni ban ji nata muryan ba.
Sai da ya shigo ne na gansa ransa a b'ace yace ko zan shirya ya kaini gida ne can sai na karya nayi wanka suma yaran su yi?
Ni kuma sai nace haba ni zan iya yin komai indai yabani izini.
Shi ya rikemin yaran na shiga kitchen na Dafamana Ruwan Tea da Soyayyen kwai da Buredi da shi muka karya sannan na saka Ruwan zafi na yi ma yaran wanka yana tayani.
Bayan na shiryasu ya rikeminsu nima na yi wankan na shirya shima kuma sai yaje ya yi wankan ya shirya cikin manyan kaya tunda yanzu naga ya rage saka kananun kaya.
Har muka bar gidan nan Sultana bata fito ba, yana ijiye ni bai ko shiga gidan ba ya juya yace akwai inda zai je.
Naga ransa a bace ya ke na yi kokarin jansa da Hira ammh bai saki Jikinsa ba.

Ni dai bakina kanin kafata ban gayama kowa abunda ya faru acan ba,  bangaren Umma na sake sauka sai dai naje na gaida mama da Innani da ta yi ras da ita na dad'e a wajenta muna ta Hira Sai Abba shima da na jima a bangarensa muna gaisawa.
Sai can da rana sai ga Assadiq da Anty Surayya ta kawomin sinasir da miyar Naman rago.
Shi a lokacin yace zai kama hanyar Abuja ya kirani har mota ya ce min kada na rika biyema Sultana Don Allah kuma tunda baya nan na rika Tafiya da Siyama in gari ya waye sai mu dawo gidan su Umma.
Ni kuma sai naga ai wahalace cikin Sanyin murya nace"Ni dai ka barni wajen Umma Assadiq don Allah."
Cikin Fushi yace"To ni sa'anta ne da zan ce ga abunda za'ayi tace a'a."
Ni kuma ganin ya harzuka sai na Shiga lallashinsa ina nuna masa bakomai ya barni na zauna a wajen Umma sai yace min itama Surayya haka tace.
Dakyar ya amince na zauna wajen Umma, sannan anjuma na aika Farida da Siyama su daukomin kaya nace to.
Ko da Umma taji nan wajenta zan karishe kwanaki bata damu da Tambayar ba'si ba a tunaninta ko kila Saboda tafiyar Sadiq ne.
Ni kuma sai hakan yafi min kwanciyar Hankali Tunda ni bani son abun Rigima ko kankani.
Sai na koma kwana bangaren Umma komai yi min ake yi, hatta wankan su Asim kayansu sai dai a kawomin su an wanke su tas.
Ni ce ma ke yi ma Umma shara da wanke wanke da gyaran dakinta.
Shima tayi ta cewa na bari nice ban saba zama ba.
Sai gashi Umma har sai ta tambayeni me zan ci? Nace duk abunda aka bani zan ci.
Yara kuwa sai in suna kuka a kawoni na basu nono, madaran su kuma su Siyama sun iya had'awa bani da matsala.
Anty Surayya ta rakani da Umarnin Umma naje gidajen yan'uwan Assadiq, gidan Anty sa'ima da Sakeena sai gidan Anty Sadiya da Anty Sa'adatu har gidan Sajida mun je.
Ita dai sai wani yamutsan fuska take yi shiyasa bamu dad'e ba.
Washegari kuma ta zo gidan ta yini a bangaren Umma tana ganin komai.
Tana tashi daganan ta Biya wajen Sultana tace mata sai ta zauna bata Haihu ba  ga Umma can ya'ya yasa Hankalinta ya koma kaina ta fara ji dani kamar kwai a miya.
Aiko itama Sultana sai gata tazo gidan Ahalin tunda muka zo bata zo ba har sai da Umma ta mata tsiyan idonta kenan?
Sai tace wai bata jin dad'i ne.
Taganin ma Idonta ganin Umma ta goye Asim ta na ta kuma lallashin Asif da ke hannunta.
Gidanta ta yini kuma bata min mgana ba nice ma na gaisheta ta amsa kamar bata so.
Yara kuma ba ta taba Daukan su ba.
Tsaraban da na zo mata da shi na Humra na Dauko a gaban Umma na bata ta amsa a wulakance
Da farko ma kin amsa tayi sai da Umma tace"Karb'i mana Sultana."
Shiyasa ta karba ko ta gode batace min ba, nima ban nema ba tunda domin Allah na yi.
An kira sallar la'asar Daga ni har Umma muna salla, ni ina cikin Daki Umma kuma a falo take sallarta su Asim sun yi barci ta kwantar da su.
Shine suka fara d'aya na fara kuka d'aya ya saka kuka.
Suka fara yi kamar jiniya  Sultana na gefe kafarta daya kan daya ko ta daga kai balle ta Kallesu.
Cikin Tausayi Asim saboda kuka ya fad'o daga kan kujeran.
Umma na salla tunda suka fara kuka take Ihin ihim ammh ko ajikin Sultana.
Ni kuma na sallame ammh kunya ta hanani fitowa.
Inajin sanda wani cikin su ya fad'o ya Tsandara Ihun da kowa a gidan sai da yaji.

Umma bata idar da salla ba ta yanke ta Dauki Asim da Sauri ta na jijjigashi sai ga Mama itama da Gudu tana tambayan taji kukan su Asim lafiya?
Umma na kallin sultana cikin bacin rai tace"Ina salla ne, uwar ma ina jin sallar take yi. Sultana na zaune inda take nan ammh yarinyar ko a jikinta ballatana tasan suna yi har Asim ya fad'o daga saman kujera bata daga daga inda take ba sai ni ce na katse sallar na Daukesa."
Mama na kallon Sultana lokaci daya ita ta Dauki Asif ta na fadin"Ke kam sultana baki kyauta ba, ina Ruwan kishi da yaro kuma?.
Umma tace"Sakarci mana, yara ne fa kuma kada ki duba komai ki Duba suma ai ya'yanki ne."
Kai Tsaye Sultana ta mike tace"Ni ba ya'ya ba ne. A bari in na haifi nawa sai ace musu ya'yana."
Mama ta kama baki Umma kuma da ranta ya baci, Ga Asim yaki barin kuka yadda take jin yaranan har ranta.
Cikin Tsawa tace"To mun ji mara kunya, sai kije ki haifi naki shashasha kawai."
Kawai sai Sultana ta saka kuka ta Dauki mayafinta da Jakarta ta Fice da gudu tana kuka
.
Mama ta koma ta zauna Rike da Asif tana fadin"Kai sultana taki yin hankali."
Umma tace"Kar ma ta yi, ai na daina saka baki a kanta in Sadiq din ya gaji ya saketa tunda bata san mutumci ba, yarinyar nan nasan iskancinta ya hana Maman yara nan zama gidan mijinta yace ta dawo wajena  ko da bai gayamin ba na Fahimci haka kuma da sanin Halin sultanan."
Mama tace"uhm ai nima na saki da Lamarin Ubangiji Umma, ki duba da ashe rabon yaran nan ne komai ya faru, ni kwanakin nan Naji labarin Yaron nan abokin wasan mu da kwanaki na taba fad'a miki an ce bazai auri yarinyar da ya ke so ba?
Umma ta gyad'a kai Mama ta cigaba da fadin"To wlh ya auri zabin uwar tasa, ammh fa ya ribace yarinyar nan sun lalace a waje karshenta dai an haifa mata Shege a waje."
Umma ta zaro ido kafin tace"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un.
Kai Allah ka rabamu da mummunan kaddara, to ina dad'in shi don Allah."
Mama tace"Ina fa dadi ai Sadiq ya yi Tunani sosai."
Umma ta yi shuru jikinta ya karayin sanyi.
Mama kuma ta cigaba da bata Labarin dalilin haka uwar ta fadi ta samu Mutuwar barin jiki.
Umma sai salati take yi, ta na kallonsu a Asim.
A fili ta furta"Sai yanzu naga Ribar auran Yarinyar nan, sai kuma yanzu na yadda da mgamar Abban siyama da yace tunda akwai Rabo a Tsakaninsu in da ba su aure ba to fa ta hanyar  banza za su samu duk Rabon da Allah ya Tsaga a Tsakaninsu."
Mama tace"Shiyasa na saki komai,suma yaran nace wlh su bar adawa da Hukuncin Allah."
Kukan su Asim ne ya hansu hiran dole Mama ta kwalamin kira na fito sai Umma ta kalleni ta na fad'in"Kina jin yara na kuka kin ki fitowa Hasiya?
Cikin jin kunya nace"Ban ji ba ne Umma."
Mama tace"Zo ki basu su sha, balle Asim da ya sha kasa."
Kasa ba su nono na yi a gabansu sai na Rika karbansu d'aya bayan d'aya ina Shiga da su ciki.
Mama ta kalli Umma tana fadin"Wlh tana da kunya, ta fa ji kukansu kawaici ne kawai."
Jinjina kai kawai Umma tayi, itama taga kunya a tare dani sai dai ta wannan tabon da ke gareni ne ke damunta duk da ta fara Fahimtar Allah ne fa sarkin kowa.

Washegari Lahadi tun safe muka yi shirin tafiya Umma taso mu kara kwanaki Assadiq da suka yi mgama ta waya yace zan fara Tp shine Dalili sannan Saboda Haihuwa har aka tafi Hutu ban fara zuwa ba.
Ni kaina naji kewarasu bako Rab'a akace, Umma ta siyama su Asim kaya Mama kuma ta siya musu kayan wasa ni kuma Umma ta bani leshi mai Tsada da Takalmi sai wata Atamfa da tace na kai ma Mahaifiyata.
Abba kuma ya bani kudi, Innani ma ba'a barta a baya ta bama su Asim 500.
Anty Surayya kuma ta bani kyautar Mayafi da takalmi masu kyau da tsarin sun yi min sha tara na arziki.
Direban Abba ya kaini har gida abun sai Godiya na kira Assadiq ina gayamasa abunda aka yi min a Gusau.
Shima cikin jin dadi yace"Kema ai kin yi musu abun alheri baki gayamin ba, sai da Umma ta gayamin to kada ki damu domin sun rama ma kura Aniyarta."
Sai kawai nayi Dariya, Nayi Farinciki sosai kuma shima ya Fahimci haka.
Tun a ramar muka yi waya da su Umma nace mun sauka lafiya.
Tace a gaida mata mazajen su ita da mama.
Ina dawowa na kira Habiba tazo Saboda ta tayani gyaran daki da kula da yara.
Na kira su Adda ina ba su Labarin naji dadin zuwana gusau da abun alherin da suka yi min.
Amma ma na kirata nace an yi mata kyautan zani ta na ta godiya.
Da Safiyar Litini tare muka fita da Habiba, ta wuce makaranta ni kuma ma tafi inda na ke Tp.
Na basu uzurin ba na nan sukace bakomai sun bani aji Hudu, sannan akwai Nanny mai kula da yara ita sukace na rika bar mata su Asim kafin a fita break, in anje Break sai nazo na gansu na basu nono.
Sai abun yazo min da Sauki ganin na jima ban fara ba, sai na saka Pressure ballatama da akace Supervisor d'in mu suna kan hanya Tunda bai wuce wata daya da wani abu mu gama Tp din ba.
Ina jin dad'in malaman makarantan Sosai harda mai makaranta ga sauki kusa da gida bani da wata matsala.






*Janafty*
*TMWB3K015*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*


https://chat.whatsapp.com/K3rO5UonX4GDVxtQbA5mZl
PAID ADVERT✅

Assalamualaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu!!! Wannan group din dai na komai da komai ne. A taiqaice
*Farashin mu na daban ne compared to sauran Yan kasuwa
*Kaya masu kyau da quality. Abinda kika zaba shi za a Baki
* Swift delivery.watau waybill a sauqaqe da Yardar Allah
* Muna sake New Arrivals ka fin su cika Gari
* Muna iya duba maku kaya a good price ko da ba namu ba ne idan kuka Aiko da hoton kayan
Allah sa mu qaru da juna Ameen


*BAYAN WATTANNI BIYU.*

Wattanin Biyun da suka gabata duk ba su zo ma Sultana cikin Dad'i ba.
Domin ta yi su ne cikin Kunci Tsananin kishin Hasiya da ke cinta a ranta ya haifar mata da Zarge zarge na banza da wofi.
Bata da aiki sai kunci da kuka, ita gani ta ke yi duk abunda ake yi mata ba aldaci ake yi mata ba Yaya Sadiq yafi son Hasiya a kanta sannan Umma ta fara karka akanta daga karshe ma har Gorin Haihuwa ta yi mata Saboda Kaunar da ta ke yi ma Ya'yan Hasiya.
Kuma saboda wauta irin nata ta samu duk ya'yan Umma da ke zugata ta fad'a musu Umma ta daina sonta har Gorin ma Haihuwa ta yi mata.
Magana kuma taje kunnen Umma daya sa Ranta ya baci tace a gayama Sultanan ta yi mata gorin Haihuwa in taji hauahin Gori gobe ta ganta da Ciki.
Shikenan Sultana ta kwazzabi kanta ita sai ta yi ciki saboda ta Haihu, ita ma Umma ta fara kaunar ya'yan da zata Haifa ta daina kaunar su Asim da ta Tsane su su da uwarsu gabadaya.
Kuma in dai ta Fahimci baka Goyon bayanta a zagi Hasiya ko kuma taga kana bayan Sadiq sai ta janye jikinta dakai.
Yanzu Sadiya ne da Sajida abokan shawaranta sai Salima da ita ce ke kiranta ta na kara nuna mata bakin Hasiya a wajenta, tunda Salima ina ne bata taka a dangin su Hasiya ba? Labarai sai wanda tace bata so, haka ya'yan su Baba tanko da su Baba Saminu ke bata wasu labaran in sukaje Zariya wasu ma Labaran duk na karya ne.
Su ukun nan da kamashon su wajen kara tabarbarewan zaman aure Tsakanin Sultana da Sadiq, tunda shi ya kasa gane mata tun bayan bayyanar Sirrin da ya Boye na auransa da Hasiya.
Duk sanda zai zo mata weekeed ba sa Rabuwar dad'i duk iya kokarin da ya ke yi sai Sultana tace ita yana Danne mata hakki sannan ya fi son Hasiya akanta har tunanin cewa ita fa a budurwa ya aureta ya kamata ya fi sonta ba ya rika nuna ya fi son Hasiya da ya aureta a bazawara ba.

Kuma duk Sajida ce ta saka mata wannan Tunanin na cewa hasken Fata kawai Hasiya zata nuna mata ammh jikin mata ta fita komai da ilimi da komai ita Hasiya Jahilar banza ce.
Sai daga baya take jin Hasiya da iliminta Tunda har Karatun Nce take yi a yanzu shima sai da ta tada masa Rigiman itama makaranta zata koma.
Shi ko yaso ya tafi da ita Abuja Tunda mganar Loan din gidan da za'a basu ya tabbata.
Tunaninsa sai taje can ta cigaba da karatunta ita kuma Hasiya sai ya dawo da ita nan Gusau, ammh Zargi da kishi suka rufe ma Sultana ido ta kafa masa kahon zugan Tunda Hasiya na karatu itama karatu zata koma shi kuma ba tashin hankali yace Allah ya bada sa'a, in an fara saida Jamb ta yi masa mgana ya siya mata sai ta Rubuta shi ba shi da matsala.
Duk irin abubuwan da ta ke yi masa bai taba daga baki ya kai karanta gaban Umma ba, gwara ma wani Lokacin ya na yin mganar da Big Sis, ita kuma sai ta rika Tausan shi da yarinta ke damun Sultana ya yi mata Uzuri, shi kuma abubuwa da dama ya ke dubawa ciki harda in yace zai Dauki mataki a kanta Umma ya ke ji, sannan mutane za su ce saboda Siya ne ya yi haka kenan zai goga ma Siya abunda bata san faruwarsa ba.

Ita kuma Surayya ta san harda Zuga ke dawainiya da Sultana kuma tasan masu zugata bata so ta gayama Sadiq ne tunda akwai yar matsa tsakaninsa da su Sajida har gobe bayan gaisuwa wata hira da ke shiga tsakaninsu a baya yanzu ta kare..shi ya riga ya tsame su gefe suma kuma suna ganin suna gaba da shi, shi ya kamata ya bi su. shi kuma ta bakin shi yace ba su Haifeshi ba sannan su suka Tsallake Hurumin da ba na su ba.
Kuma su dai suna iya bakin kokarin su wajen gayamata gaskiyan ta kwantar da Hankalinta ta zauna lafiya da mijinta watarana sai labari, ammh sai take ganin kamar ba gaskiya suke fad'a mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login