Showing 21001 words to 24000 words out of 116366 words
kwana achan kawai in dare ya yi."
Saddiqa na daukan wayanta da Jakarta na Hannu tace"Zan dawo Umma ai Bamu gaisa da Abba ba."
Ba'a son ran Umma Saddiqa ta tafi ba ta na fita Haraban suka had'u da Mama zata zo shashen Umma suka gaisa itama da tace mata zata je gidan Surayya sai da ta kalleta kafin tace"Da daddaren nan Saddiqa? Allah yasa lafiya"
Saddiqa tace"lafiya lau Mama, bari dai naje ba dad'ewa zan yi ba."
Daga haka suka rabu, adaidaita ta samu zuwa gidan Surayya, Daman sun yi waya dazu da rana lokacin suna hanya ba ta riga ta iso ba.
Surayya na falonta zaune ita da yaranta suna homework sai ga Saddiqa cikin mamaki ta mike ta na fad'in"Saddiqa"
Cikin irin nayi mamakin ganinki a yanzu.
Saddiqa ta samu kujera ta zauna yaran Surraya suna gaisheta, karamar ta dauka saman jikinta Lokaci d'aya ta na fad'in"Ban dad'e da isowa ba, nace sai nazo ina so mu yi mgana, big sis ta na zamu fara kamo bakin zaren wannan maganar nan?
Surayya ta kalli yaranta lokaci d'aya ta na fad'in"ku shiga ciki khalil."
Sai da suka shiga cikin sannan ta mike ta na fad'in"Bari na kawo miki lemu da ruwa."
Saddiqa tace"Bar ruwan nan Big sis, ki zo mu zauna mu yi mgana."
Ba musu surayya ta dawo gefen Saddiqa ta zauna ta na fad'in"Ina jinki Saddiqa, ta ina ki ke ganin zamu fara?
Saddiqa na fuskantar ta lokaci d'aya ta na fad'in"big sis ni a shawarata ta inda aka hau ta nan za'a sauka."
Surayya tace"Kamar ya?
Saddiqa ta gyara zama ta na fad'in" Nufina anan shine Sadiq ne ya jawo komai saboda haka shi sai ya zo ya sanar ma su Umma da bakinsa, in muka Shiga fad'an da babu ruwan mu fa? Kuma abun haushin ma ba da bakinsa ya fad'a mana ba, shi har yanzu bai samu lokacin sanin bai kyauta gamw da abunda ya aikata ba."
Surayya ta yi shuru kafin tace"Ban ki ta mganarki ba, ammh ni a shawarata tunda kin zo, ni da ke zamu tara su Umma mu sanar da su abunda ke faruwa."
Saddiqa ta zaro ido kafin tace"Mu kuma?saboda mene?
Surayya ta gyara zama lokaci d'aya ta na fad'in"Saboda Sadiq kanin mu ne."
Saddiqa ta katsesta da fad'in"Kina so ki nuna min zamu kare Sadiq a wajen su Umma? Zamu karesa big sis ki ke nufi duk a irin abunda ya aikata? Tabdijan wlh in muka yi haka ma gobe sai ya kara ya ma raina mutane wlh"
Saddiqa ta karishe fad'a ta na Nuna bacin ranta kafin ta cigaba da fad'in"kuma suma su Umman ai su gani, tsabar soyayyar da suka nuna ma yaron nan da Abba da Innani, suna Fifita mganar Sadiq a saman ta su, ba dole ya je ya aikata abu mai girma haka bada sanin kowa ba, ya na Tunanin babu abunda zai faru ne shiyasa kika ga ya yi shurunsa ko ajikinsa fa."
Surayya ta yi mirmishi ba ta yi mgana ba, Saboda ta na Tunanin ba lalle in ta yi mgana kowa ya fahimceta ba.
Sanin tsakaninta da Sadiq yanzu sai ace shi ta ke goyama baya.
Tana cikin wannan Tunanin taji Saddiqa na kara fad'in"Nasan dai tsakanin ku da Sadiq akwai kauna, kin fi shakuwa da shi duk da yana namiji, ammh bai kamata ki goyamasa baya ba, tunda duk yadda ku ke bai iya samun ki ya fad'a miki ba."
Surayya ta kara yin mirmishi kafin ta muskuta ta na fad'in"Ke ma kina Tunanin ina Goyon bayan abunda Sadiq ya aikata ne?
Saddiqa tace"Haka ne mana, tunda kina so ya na chan kwance mu mu yi masa yakin a nan."
Surayya tace"Ba shi zamu yi ma yaki ba, Adalci zamu nema ma Hasiya."
Saddiqa ta yi karamin Tsaki kafin tace"Wacece wata Hasiya kuma? Chan ita ta sani, me ya kaita auran wanda bata sani ba?
Surayya tace"Kada ki manta itama ya yi mata karya, in zamu kalli abun ta fuskar adalci itama bai kyauta mata ba. Kuma ni wlh tallahi bazan kare Sadiq ko na minti d'aya a gaban su Umma ba, Hasiya da na yi ma alkwarin komai zai yi daidai ita zan nema ma adalci.
Saddiq sai kawai ta tab'e baki ta na kallon Surayya kafin tace"Ni bangane manufar manganunki ba, yanzu kina so mu je ma su Umma da mganar sannan mu tsaya ma matar da Sadiq d'in ya aura ko me kike nufi?
Surayya tace"A'a abunda na ke so mu yi shine, mu sanar da su Umma saboda su san halin da ake ciki."
Saddiqa tace"To shi me yasa in ya gane ya yi ba daidai ba bai zo ya fad'a da kansa ba? Ko ba shi da baki ne?
Surayya tace"Sadiq na cikin Tsaka mai wuya, ko ni duk yadda mu ke da shi wlh saddiqa ya kasa fad'amin, nan yazo ya zauna ammh ya kasa iya fad'amin komai."
Saddiqa zata yi mgana Surayya ta yi saurin Dafa kafad'arta ta na fad'in"Ki yi hakuri na yi miki alkwarin ko sau daya bazan boye laifin Sadiq ba ammh ni dai ki tayani sanar da su Umma komai."
Saddiqa ta kalleta a kaikace, itama sai ta langwabar da kanta ta na kara fad'in"Ban san ki da haka ba Saddiqa."
Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace"Shikenan domin kin matsa ne, ammh wlh ni naso ki bari sai matar ta Haihu, naga yadda zai kare, yaro karami ammh ya iya raina ma mutane Hankali."
Surayya ta yi dariya ta na fadin"Ba yaro ba ne karami, namiji ne shi kada ki manta."
Saddiqa tace"Hakane yanzu na Tabbatar da haka."
Sun cigaba Tattauna yadda gobe surayya zata zo domin su sanar da su Umma Halin da ake ciki.
Maganar Dauko Hasiya kuma Saddiqa ta ba da shawaran su dakata su yi mgana da su Umma su gani, yadda suka karbi mganar ta yanayin da za su samu mafita kenan.
Surayya ta gyad'a kai alamu gamsuwa kafin tace"To shikenan Allah ya kaimu, ina fatan komai ya daidaita in sha Allahu."
Saddiqa tace"Ammh ki kira yaron nan, mu zamu kwanto masa kuran da ya Daure, sai ya zo ya san yadda zai yi ya sake Daureta."
Surayya ta saka Dariya kafin tace"Zan kirasa ai mganar boye boye kuma ta kare masa."
Sun cigaba da Tattaunawa har Mijin Surayya ya Dawo, shi kanshi da ya ga Saddiqa ya sha mamaki har yana yi mata tsiyan hausanta ya koma na Sokkatawa.
Karfe goma da wani abu Surayya da Mijinta suka dawo da ita gida ba su shiga ba a kofar gida suka sauketa suka rabu akan sai gobe.
Umma sai da ta ga Saddiqa ta dawo ta ga ba wani abu sannan Hankalinta ya kwanta.
Yadda Saddiqa bata ce mata ba, itama bata matsa mata da mgana ba.
Abba ma sai da safe taje ya ganta suka gaisa saboda a daran Mama ke da Turaka kuma dare ya yi shiyasa bata shiga ba ammh tasan tabbas yasan da Labarin zuwanta.
Da safen ma da taje gaishesa sai da ya tambayeta lafiya ko?
Tace masa lafiya Lau tazo ganinsu ne, ta jima a wajensa suna Hira, saboda Abba mutum ne da ke sakewa da ya'yansa.
Daganan sai shashen Mama, itama sun jima suna Hira da ta ga falon wayam ne ba kowa yasa tace"Shikenan gida ya zama tsit, Siyama ta zama yar gidan Sadiq."
Mama na dariya tace"Wlh gida fa ya yi tsit ba kowa, to sai farida ita kuma ta na barayin Innani, in kin ganta anan sai in aikota ta yi Siyama ai sai Sadiq ya dawo ki ke ganinta a gidan nan, in kuma baya nan sai dai su zo tare da sultana."
Saddiqa tace"Itama Allah ya kawo mata miji nagari ta yi auranta."
Mama ta amsa da Amin sun cigaba da Hiran Salima wacce Mama ke fadin yanzu bata zama sosai tunda ta fara karatun nan.
Sai da Saddiqa ta koma Shashen Umma sannan ta kira Surayya, nan ta ke fad'a mata ta kira Abba tace kada ya fita zata zo akwai maganar da ta ke so su yi da shi, sai yace daman yau ba da wuri zai fita ba sai an juma.
Sun Tsaida mganar Daga Umma sai Abba sai mama da Innani za su yi mgana daga baya in komai ya daidaita sai mganar ta fita ga sauran yan'uwa.
Tunda Surayya ko Sajida bata nema ba a wannan karon ba Hurumin su ba ne.
Da wuri Surayya ta zo gidan Umma dai mamaki sai ya kamata tun ballatana da taga sun kule a daki ita da Saddiqa, da kuma sun ganta ta shigo sai su yi tsuru tsuru, Umma dai ta na kallonsu a ranta ta tabbatar akwai wani abu, tunda ta shiga su gaisa da Abba ya ke gayamata wayar da suka yi da Surayya.
Gabanta ke fad'i fatan ta d'aya Allah yasa ba wani abu na mara kyau ya samu d'aya daga cikin yaran ba.
Zuciyar Uwa duk sai ta firgice zullumi ya shiga ranta duk sai ta kasa sukuni.
Surayya da kanta taje Bangaren Innani bayan sun gaisa sun taba Hira, Innani na bata labarin Farida mai kirki ga ba ta da kiyuwa ba kamar su Siyama ba.
Har Innani na fad'in ba ta yi Halin uwarta ba, Surraya dai na jinta ta na faman dariya.
Da ta ga Hiran ta ki karewa ne yasa tace ma Innani zata rakata bangaran Abba za su yi mgana ne.
Innani ta karkace kai kafin tace"Shi Sulaimanun ne don zai yi mgana da ni, sai na je da kaina?
Surayya sai ta kasa mgana Innani ta fara masifa ta na fad'in"Shi kuma Sulaimanu lalacewa ne ko bakin duniya ce ta fara kamasa da ni ina uwarsa zai ce sai naje da kaina har bangaransa? Naga dai daga shi har matansa nan suke zuwa su tarar da ni, ko da suna da mgana da ni."
Sai Surayya ta Fahimci kuskurenta da Sauri tace"Yi hakuri Innani , bari mu muzo sai a yi mganar a nan bangaren."
Innani ta tabe baki kafin tace"Da dai yafi muku."
Dole Surayya ta koma ta fad'ama Saddiqa yadda suka yi da Innani, sai Saddiqa tace ba matsala sai ayi achan din.
Surayya ce tace ma Umma su je bangaren Innani su yi magana, Umma bata ce komai ba illah tace to kawai, Ita Mama Saddiqa ta je ta fad'a mata itama cikin mamaki tace lafiya? Saddiq tace suna fatan haka.
Abba daman ba shi da matsala shi ya fara ma isa bangaren Innani, ko da su Umma suka zo sun iske su suna Hira na Tsakanin uwa da abunda ta Haifa.
Ga dai Umma ga Mama ga Abba sai Surayya da Saddiqa ga Innani a gefe wajen mintuna goma falon ya Dauki Shuru ammh tsakanin Surayya da Saddiqa an rasa me fara cewa wani abu.
Sai da suka zo gabansu Umma suka ji sun sare, barin ma Surayya da ta zo da kwarin gwiwanta, Saddiqa kuma Daman tace ita bazata fara mgana ba tunda Surayya ta karb'i fad'an ita zata san yadda zata yi.
Innani ta gaji da zama sai ta kawai ta gyara zama ta na fadin"Wai me ya faru ne? Naga kowanne ya zauna ya yi shuru ko an yi mutuwa ne?
Abba ya yi gyaran murya kafin yace"Innani daman Surayya ce ke son magana damu kan wani batu da bamu sani ba"
Innani ta yi karamin tsaki kafin tace"Shine kuma ta taramu kamar wasu sa'anninta ta tsaya ta na kare mana kallo?
Da Sauri Mama tace"Ki yi hakuri Innani, ke kuma babbar yaya muna sauraranki Allah yasa lafiya, ni wlh kada ku kasheni da zullumin me ke faruwa?
Umma ta kad'a kai kafin tace"Wlh nima baki ji zuciyata ba, gabadaya na kasa sukuni don Allah ku fad'amana Abunda ke faruwa."
Surayya ta kalli Saddiqa itama ta kalleta, Saddiqa ta tsinguleta alamun ta fara mgana, Dakyar Surayya ta iya jarumtar fad'in"Umma Abba, Mama Innani, magana ce a bakina sai dai yadda zan fad'eta ne kuma ku fahimceta shine Fargabata."
Mama tace"Topha? Muna sauraranki in sha Allahu kuma zamu Fahimceki."
Surayya ta Sauke ajiyar zuciya kafin tace"Dama. dama akan maganar Sadiq ne."
Gabadayansu a tare cikin firgici suka Had'a baki wajen kiran sunan Sadiq.
Cikin tashin Hankali Abba yace"Me ya faru da Abubakar din?
Umma kuma da jikinta ke rawa da Sauri tace"Surayya ki fad'amin me yasamu Sadiq ne kada zuciyata ta Buga."
Mama kuma sai salati ta ke yi, Innani kuma kuka kawai ta saka ta na fadin"Mun shiga uku mun lalace wani mugun abun ne ya sama mar min jika na? Namiji kwara d'aya da Sulaimanu ya mallaka magajin wannan gidan mijin sulsana mun shige su, me ya same shi? Ko mutuwa ya yi ne ku ke boyemana achan Habujan?
Innani ta karishe fad'a cikin Ihun kuka.
Jin maganar Mutuwa da kuma yanayin Rudewarsu yasa Da Sauri Saddiqa tace"Ba fa maganar Mutuwa ba ce ko wani abu, Lafiyan Sadiq kalau babu abunda ya same shi."
A tare Umma da Abba suka Sauke Numfashi mama ko sai da tayi hamdala.
Innani ne ta tsaya da kukanta ta na kallon su Surayya ta cikin gilashinta na wani lokaci kafin a fusace tace"To karya ku ke yi, in ba wani abu ya sameshi ba uban me yasa baku fad'i abunda ya faru ba tun dazu? Kun tsaya kuna ta raina mana wayau.'
Ta karishe fad'a cikin masifa, Abba dai jikinsa gabadaya ya yi sanyin da ya kasa mgana.
Umma kuma zuciyarta ne taji ya na gudu sosai kamar dai wacce wani abu ya sameta.
Cikin karfin hali tace"Zaku fad'a mana ne, ko kuwa sai mun mutu da zullumi.?
Da Sauri Saddiqa tace"Sadiq ne ya yi aure Umma."
Gabadaya sai falon ya yi shuru kowa na auna mganar Saddiqa.
Innani ce ta yi tsaki kafin tace"Ji wani shashanci daman ai kowa yasan magajin gida ya yi aure, daman dalilin dayasa ku ka taramu anan kenan? Kai sulaimanu yi tafiyarka sabgoginka yara nan wasa za su yi da Tunanimmu."
Surayya ta sauke ajiyar zuciya kafin tace"Innani ba wannan auren ba, kafin.. kafin ya auri Sultana to daman ya auri wata achan zariya."
Sai falon ya kara Daukan Shuru Surayya kawai a ke kallo.
Umma ta sandare a zaune, Innani kuma har gilashinta ta cire ta kara maidawa ta kara gyara kunnuwanta kafin ta kalli Abba ta na fad'in"Sulaimanu ko dai kunnuwana sun samu matsala ne?
Me nake ji Ana fad'a na wai?
Abba ya yi shuru bai ce komai ba, Mama ce ta kalli su Surayya cikin rawan baki tace"Ku yi mana karin bayani, bangane ba wani irin aure kuma?
Surayya kanta na kasa tace"Aure ya yi a garin Zariya tun Lokacin ya na bautar kasa, shekaru uku da suka wuce."
Mama ta Bud'e baki cikim mamaki kafin tace"Da gaske ku ke yi? Wani irin aure kuma ni Saratu?
Saddiqa ta gyara zama ta fara ba su labarin yadda akayi suka ga hoton Sadiq da Hasiya da yadda suka Bincika suka gano gaskiya da zuwan Surayya zariya ita da Sajida. Da kuma karin tabbaci daga bakin Hasiya tare da Shaidar ma cikin jikinta.
Mama ta koma ta yi zaman dirshan a inda ta ke maimaitawa ikon Allah kawai ta ke yi.
Umma kuma kanta na kasa bata Dago ba, ammh a cikin kasan ranta mamaki ne da al'ajabi Abba kuma ba wanda zai iya cewa ga yanayin da ya shiga.
Innani kuma shuru tayi kamar bata ma afalon Inaga tsabar Mamaki ne ya hanata mgana wannan karon.
Abba ne ya yi gyaran murya kafin yace"Shi Sadiq din baisan kun san labarin ya yi Auran ba?
Surayya tace"Eh Abba, ya yi kokarin ya fad'amin ammh kuma ya kasa, daman tunda abun har ya fallasa naga ya kamata ku fara sani."
Abba ya jinjina kai kafin yace"Ita matar tace Tahir ya san da mganar auran?
Surayya tace"Tabbas haka ta ce ya sani"
Kafin Abba ya yi wata magana Umma ta d'ago ta na kallon Surayya cikin wani yanayi kafin tace"Shi Sadiq din da kansa ya yi aure batare da sanin mu ba?
Tsakanin Surayya da Saddiqa sai aka rasa me bama Umma amsa.
Mama ce ta rike hab'a kafin tace"Ni kaina ina ta mamaki, Sadiq fa? Me yasa Sadiq da hankalinsa da Tunaninsa da iliminsa sai ya aikata haka? Aure fa kuka ce? Kuma kun ce an dade ma tunda su Surayya sun je sun ganta har da ciki"
Kafin kowa ya samu zarafin mgana sai sai ihu da kurruwan innani suka ji, har ta na wani tuma da kafafunta kamar karamar yarinya.
Cikin kuka ta ke fad'in"Wai daman da gaske kuke yi Magajin gida ya auri wata matar kafin sulsana? Yanzu Amana ta zai ci ya yi ma Jikata kishiya? Magajin gida ina ganinsa mai Hankali ashe maci amana ne, mara Mutumci to billahillazi bai isa ba, ya yi kad'an jikata ta zauna da kishiya ni da Magajin gida baram baram ko ya saki wacce ya aura ya zauna da jikata ita kada'i ko kuma ya sakar min jikata, sannan ya yi ta kansa nima na yi ta kaina.".
Sai kuma ta kara fasa kuka, har da majina ta na kara fadin"Tsakaninmu da wannan yaron sai Allah ya isa."
Lalle lamarin ya lalace tunda innani ke auna ma Sadiq Allah ya isa.
Umma ta yi kokarin danne abunda ke ranta kai tsaye ta kalli Surayya kafin tace"meyasa tunda bai so mu sani ba ku ke sanar damu yanzu? Na dauka Tunda ya yi auransa a boye baya so mu sani ne, sai mu bar shi a haka tunda shi a wajensa haka ya zab'a."
Surayya tace"Umma saboda matar ne, itama ya yi musu karyan ba shi da kowa iyayensa duk sun rasu."
Mama tace"Shi Sadiq din?
Saddiqa tace"Shi fa, ai Sadiq ya bani mamaki ban taba Tunanin haka daga bangarensa ba."
Mama tace"Ni kaina, ina ta mamakin wannan lamarin, abu kamar almara."
Umma ta had'iye abunda ke ranta kafin tace"Ni banzan ce komai ba, ramar da yaso mu sani zai zo ya fad'a mana da bakinsa"
Daga haka ta mike zata fita, Da Sauri Surayya tace"Umma kunsan matar fa."
Da sauri Umma ta Juyo cikin mamaki kafin tace"Mun santa?
Ta fad'a ta na kallon Mama, itama ta na kallonta.
Cikin karin mamaki Mama tace"To wacece?
Kafin Surayya ta yi mgana Saddiqa tace"Ina kawar saliha da tazo mata Biki daga zariya? Wace tace sun hadu da bikin salima a kaduna yar'uwan mijin salima wata Fara haka.".
Umma da Mama suka yi shuru suna Tunani, nan da nan suka ganeta Tunda ai sun ganta.
Saliha har falon Umma ta kaita suka gaisa, mama kuma a shashenta ta kwana ta gane, kuma kammninta ba shi da bacewa a fuska.
ita Umma ma har a kaduna ta tuna ganin da ta yi mata Lokacin da ta fito neman Innani.
Cikin mamaki Umma ta kalli Surayya kafin tace"Kuma kikace itama ya yi mata karyan ba shi da kowa? A