Showing 6001 words to 9000 words out of 116366 words
na kashe, sannan karamar wayata ta bace a sha'anin nan na rasa duka Lambobin su Adda Ballatana na kira su naji Lafiyan ki, sai dai ina da yakinin guda daya da cewa kina lafiya, na tabbata da wani abu mara dad'i ya sameki da zan samu labari, da wannan Tunanin na samu kwanciyar Hankalin komawa wajen aikina sai dai tare da Nadama mai Dimbin yawa da kuma alkwarin zuwa na same ki na baki hakuri, sannan na gayamiki komai game dani, kuma ki tambaayeni abunda baki sani ba na amsa miki."
Shuru ya biyo bayan maganarsa kowa da abunda ya ke tunani, ni ina Tunanin wannan Satin dayan da ya yi tare da Sultana amarci suka sha? Kamar sai naji idanuwana sun ciko da kwallah, kishi Halitta ne ina son Assadiq, kuma nasan Sultana itace zab'insa da zabin Danginsa Dole zan ji ciwon abun in dai na tuna ko da Sunanta ne.
Shi ko Sadiq a cikin ransa ya ke wani Tunani, Hasiya itace matarsa ta farko, kuma ya aureta ba'a a matsayin budurwa ba, Sultana kuma Budurwace, Zai iya ba da shedar shi ya fara saninta a y'a mace, akwai wani sirri da dukkansu suke da shi, sannan kuma sirrin na su ya yi tasiri mai girma a tsakaninsa da su, ya bar ma ransa Muhimmanci da kowaccensu ta ke da shi a Rayuwarsa, ya na son Siya, kuma ya na son Sultana ba ya kinta, Shiyasa komai zai faru bazai Rabu da d'aya Saboda D'aya ba.
Kamar daga sama ya ji na jefo masa tambayar yanzu shi daga ina ya ke? Naga kuma wannan karon bai zo da mota ba?
Assadiq ba shi da wani zabi illah na Boye wata gaskiyar domin ya kara gina wata gaskiyar.
Sai kawai yace daga Abuja ya ke, alhalin Daga Gusau ya ke, tun ranar jumma'a ya isa da yammah, ya gaji da tuki ne sai kawai ya hau ta haya, tunda ya tafi sultana ke damunsa a waya da Shagwabar ta yi kewarsa ita dai ya dawo ta gansa, daman dakyar ta barshi ya tafi, ta na ta kukan wai bata warke ba zai tafi ya barta.
Duk da yasan ba wani Rauni ya yi mata Sosai ai shi ba karamin mutum ba ne yasan mace, ya bi da ita a Hankali sai dai yasan yan'uwansa ne suka sakata ta yi ta shaye shayen magungunar da ya sa ya makalemata a satin da suka yi armaci ba karya ta Gurzu a hannunsa shiyasa ya ke Tausayinta, kuma ya kasa kwabe shagwabarta a garesa, duk da yaso a wannan satin ya zo yaga Hasiya.
Ba shi da mafita sai ta fara zuwa Gusai yaje yaga Sultana, itama ba domin Hasiya na ransa ba zata iya Rinjayansa ya koma Abuja batare da yazo Zariya ba.
Haka suka rabu ta na kukan shagwaba, duk da ta na kusa da gida, kuma in baya nan Siyama ke zuwa ta na tayata kwana.
Ga shi ta koma makaranta so ba ta da wani kadaici tare da ita, kawai Sakalci ne da Shagwaba na yaran zamani.
Ba na son mganar Sultana Shiyasa na kauda maganarta a tsakanim mu cikin Sanyin murya nace"Tambayata itace me yasa tun farko ka yi mana karya baka da kowa sai kakar ka?
Mirmishi ya yi kafin yace"Bansani ba, nima kawai naji ina fad'a ma Amma hakane, sai dai daman duk wanda ya had'u da ni ba lalle ba ne kafin mu rabu ya san wani abu game dani ba, ina bambamta Rayuwata ta gida da kuma Rayuwata ta waje."
Dagowa na yi ina kallonsa kafin nace"Kowa na sonka a gidan ku, sannan naji ana kiranka da wani suna ko magajin gari ko?
Dariya ya yi kafin yace"Magajin gida ne Sunan Siya? Kina so kinsan waye mijin ki?
Sai na gyad'a masa, kai tsaye ya maida kaina saman kirjinsa ya kara gyaramin zama sannan ya shiga bani Labarinsa haihuwarsa karatunsa Asalinsa da komai da komai yawan yan'uwansa mata, gatan da ya ke da shi Soyayyar da Mahaifinsa da kakarsa su ke yi masa da Dalilin da yasa a ke kiransa Magajin gida, da kuma labarin wacece sultana? Alkwarin auran da ke tsakaninsu tun tana yarinyarta da alakarsu.
Ya karishe da fad'in"Ni a gida mu ba bu da'n gata irina, ni kad'ai ne namiji sauran yayyena duka mata ne, kanwata guda d'ayace Autarmu Siyama, Sai Sultana da ita daman alkwarin aure ne Tsakanina da ita, Ina daraja mata guda Biyu a Rayuwata mahaifiyata da kakata bani da kamarsu, Abba ba shi da wata Damuwa ya ma fi fifita Ra'ayina akan na shi Ra'ayin, Siya ina jin wani nauyin acikin zuciyata nauyin cin Amanar yardansu da na yi, na aure ki batare da sanin su ba."
Ya dakata lokaci d'aya ya na sauke Numfashi, ni kuma ina jikinsa nace"To me yasa ka aureni in dai baka sona?
Kuma me yasa ka aureni ba tare da sanin iyayenka ba?
Cikin Wani irin yanayi yace"Bansani ba Siya, abu daya na sani naji Tausayin Amma sosai, kuma naji Rauni ya shigeni da naji Labarinki, maganar gaskiya ba so ba ne yasa na aureki Tausayi ne, ammh daga baya sai na Fahimci shi So dabam ya na iya Farawa da Tausayi sai ya Rikide ya koma Soyayya Allah ne shaidata Hasiya, Ina sonki kuma ina kaunarki kuma ina son na Dauwama tare da ke har Abada, in da ba na sonki a yadda na ke cikin Tsaka mai wuyar nan da Tuni na Rabu da ke., Maganar kuma meyasa na aureki ban sanar da Ahalina ba? Ina da dalilaina na Farko bani da Lokaci, na Biyu kuma in har na je musu da maganar ina da yakinin ba za su amince ba, ko da ma Abba ya Amince Umma da Innani ba za su amimce ba, sannan a lokacin na yi niyar na sakeki bayan na baki jari mai Tsoka, shikenan in na bar zariya na koma gida komai ya kare, ashe ba haka ba ne, Allah bai aura ma na juna Domin mu rabu ba, saboda ke na rika Dojema auran Sultana har na Tsawon shekara uku, saboda ke na fara masters a zariya sannan kuma ke ce Dalilina na karb'an aikin kamfanin da na yi Bautar kasa a zariya Siya kin Sauya Rayuwata, Saboda ke na zama mai karya kuma na iyata, Saboda ke ma ke wata Boyayyiyar Rayuwar da na san Cin Amana ce ga Ahalina."
Ya na mgana ina jin zuciyata na kara narkewa cikin soyayyarsa, ina jin na gama yarda da shi, ko da baya so na to ina da matsayi mai girma acikin Rayuwarsa.
Abu daya na ke so na kara sani, shine me yasa ya kaini aka sakamin Implanta? Tunda yace ya na sona meyasa ba ya son had'a zuru'a dani?
Kai Tsaye ya Dago ni muna kallon juna, sumbata ya ke shirin yi na yi saurin kauda kaina ina nuna masa bakina da ya fara cika da miyau.
Sai ya yi dariya ya mikamin ledan da har miyau ya fara taruwa ya taramin na Zuba, ina kallonsa ya ijiye ledan a gefensa ko kyamkyami ba shi da shi.
Cikin mamaki nace"Baka kyamkyamin Miyau Assadiq?
Cikin sauri yace"Ina da kyamkyami mana, Sai dai ke ce ban isa na yi kyamkyamin ki ba, abunda ke sakaki miyan ai ni ne na Digasa ko?
Zai sake rikoni na yi saurin kwace kaina ina fad'in"Ka bari na wanke bakina."
Ya na dagamin gir yace'To miye?
Ban kulasa ba na shige ciki da gudu sai da na sake yin brush sannan na dawo, kuma bai yarda ba sai da ya kama Fuskata muka sumbaci bakin juna na wani lokaci sannan ya kalleni ido cikin yace"Siya soyayyarki ce taja min duk abunda na zama yanzu, Wallahi kin ji Rantsuwan musulmi ban taba kyamatar komai da zai Fito daga Tsatson ki ba Hasiya, a lokacin bani da mafita ne, sai ta hakan dalilina shine ba na so ki samu ciki har ki haihu iyayena ba su san da ke ba, ba na so abunda zamu haifa ya zo ya Fuskanci laifin da ba shi ya aikata ba, Daman ina da niyar in komai ya Daidaita na gaya miki da kaina sannan na kai ki a cire miki, ammh har ga Allah har acikin zuciyata Siya bani da wata manufa ta sharri ko kin had'a zuru'a da ke daga bangarena."
Ya karishe fad'a ya na kallona nima shi na ke kallo ammh na kasa mgana.
Zuciyata daga chan gefen ta na gasgasta shi, wata kuma na Kokarin nuna min ba haka ba ne.
Ganin haka yasa ya kara rike Hannayena ya na fad'in"Ki yarda dani Hasiya wlh ba karya na ke fad'a miki ba, ki Fahimceni."
Sai na lumshe ido kafin na bude ina kallon yadda ya marairaicemin kamar wani maraya, lokaci daya kuma ya na shafa Tafin hannuna cikin wani irin Salon da ya sa, sai da tsikar jikina ya tashi.
Bani da zabi illah Aminta da Assadiq domin nan duniya bani da wanda ya fisa cikin gyad'a kai nace"Na Aminta da kai Assadiq, na kuma Fahimceka na kuma yarda cewa baka na gudun had'a zuru'a dani saboda Canfi da ke kaina ba ne"
Da Sauri yace"Astagafurullah.! Kada ma ki kara wannan Tunanin, ni ban yarda da Canfi ba , sannan ina da ilimin addini nasan Allah ke yi ba Mutum ba."
Sai na yi masa mirmishi ina jin zuciyata na samun natsuwa kafin na koma saman kirjinsa na kwanta ina Fadin"Assadiq ya kamata ka yi saurin sanar da iyayenka mganata kafin na haihu ko?
Ya na shafa kaina zuwa bayana yace"In sha Allahu, zan sanar da su kada ki damu."
Sai na jinjina masa kai shuru muka yi kafin ya muskuta ya na fadin"Daman Alhaji Jibril baffan ku ne Siya?
Sai na Dago ina kallonsa kafin nace"Na kaduna?
Sai ya gyadamin kai, cikin mele baki nace"Eh kanin babanmu ne, ammh da ya ke sanadina yasa tunda babanmu ya rasu ba su duba bayansa ba, a cewarsu duk wanda ya rabemu shima zai iya rasa komai na shi."
Shuru ya yi kafin yace"Mutane yanzu sun saki Allah sun kama boka da mallam, da kuma Canfe canfan banza da wofi, mutane ba ikilasi ba Tauhidi, sun manta da Allah shi ne Allah, komai baya faruwa sai da cewarsa da kuma Umarninsa."
Ina jikinsa har a Lokacin idanuwana suka kawo kwallah kafin nace"Farkon Rayuwata na taso cikin Farinciki, Daga baya ta juye zuwa kunci da bakinciki na shiga Tsaka mai wuyar da kai ne ka fitar da ni acikinsa Assadiq don Allah ko da iyayenka ba su karbeni daga Farko ba, kada ka Juyamana Baya ni da cikin da ke jikina."
Sai kawai na fashe masa da kuka ina Rokon kada ya zabi sultana ya rabu dani kai tsaye yace"Kamar yadda Saboda ke ban barta ba, ke ma kuma saboda ita bazan barki ba Siya".
Sai na kara kamkamesa ina ta kuka, shi kuma ya na aikin lallashina.
Daganan kuma daga lallashi sai kuma ya fara kokarin nuna min yadda ya yi kewata.
A nan saman kujera mun kasa ko shiga ciki komai ya wakana, ni kaina nasan na yi kewar mijina, shima haka ballatana ga cikin jiki, Sai dai muna Samun natsuwa na mike da gudu sai Tiolet naje zubar da miyau shi na bari da tattara mana kayanmu, ni daga nan tubewa na yi na tsabtace jikina.
Ko da na fito ya shigomin da akwatuna ciki tare kayanmu da muka yi falati da su, shima wanka ya shiga ya Tsabtace jikinsa.
Dagani har shi ba ma jin yunwa, nad'ewa muka yi a gado muna sake Sabon Hira ya kashe wayarsa gabadaya Saboda yace yanzu lokacina ne.
Muna kwance a kan filo daya fuskokin mu na kallon Rufin Dakin, hannayemmu sarke a waje d'aya, Juyawa na yi na rab'i da rabin jikinsa na kira sunansa"Assadiq?
Da sauri yace"Uhm SiyaAssadiq."
Ina shafa gemunsa nace"Ya ku ka kare kai da abokin ka din nan? Domin nasan yasan har yanzu muna tare.?
Assadiq ya yi shuru saboda baya so Hasiya tasan a kanta sukayi fad'an da ba su taba yi da Tahir.
Sun rabu zukata ba bu dadi kuma Daga Lokacin ba su kara neman juna a waya ba.
Ba kuma wani abu ya had'a su ba, sai Tahir da ya ke jifan Hasiya da kalmar Annoba sannan ya na rainata Saboda ita bazawara ce, kuma ya na kokarin nuna masa ya saka Rayuwar Ahalinsa a bala'i tunda ya kasa rabuwa da Hasiya.
Yasan ya yi kuskure da ya yi masa karya ammh Hasiya matarsa ce kuma Sirrinsa bazai taba bari wani ya ci zarafinta ba Shiyasa ya yi ma Tahir Tsawa akan kada ya kara aibata matarsa in kuma ya kara sai ransa ya baci, shikenan Tahir yace yaje tunda ya zabi hasiya sama da shi, ya bar shi duk sanda ya gane kuskurensa ko ta kwabemasa yasan zai nemesa.
Shima a lokacin ransa ya baci shiyasa har yanzu bai ko nemesa ko ta waya ba.
Sai da yaji muryata ina kara fad'in"Uhm ka yi shuru?
Da Sauri yace'Na fad'a masa gaskiyan cewa muna tare yanzu."
Kai Tsaye nace"To me ya ce maka?
Ajiyar rai ya sauke kafin yace"Me kuwa? Abokina ne fa ba Ubana ba Hasiya, ba shi da ikon zab'a min Ra'ayina"
Sai na yi shuru na kasa mgana,Ammh na Fahimci shi da abokin nasa ba su yi Rabuwar dad'i ba.
Gudun kara Tabarb'arewan al'amarin yasa na yi shuru da bakina.
Sai dai na kara lafewa a jikinsa ina fad'in"To ka na Tunanin a yanzu bazai gayama kowa ba?
Sadiq yace"Da zai fad'a da Tuntuni ysa fad'a, nasan Tahir bazai taba fad'an komai a kan ki ba, sai dai in dan ni ne na Bukaci hakan."
Ajiyar rai na sauke kafin nace"Allah yasa komai ya zo da Sauki Assadiq."
Cikin jinjina kai yace"In sha Allahu Khairan Siya ta."
Daga haka ya Rumgumeni yace mu yi barci ya gaji, kamar wasa sai ga shi barci ya kwashemu dagani har shi, sai dai ni miyau ne ya rika tadani da na mike daman ya san miyau ne ya cika bakina.
Muryansa cikin barci yace"Miyan nan ba shi da magani ne Siya?
Ina kara kwanciya ajikinsa nace"Likita yace for now dai babu, ammh yace zuwa gaba zai rage."
Kara rikeni ya yi cikin barci barci yace"Ya na takura min mata ne Shiyasa."
Sai bayan azahar muka tashi muka yi sallar, shi ya fita ya siyo mana abinci da kayan marmari, ni kayan fruit din kadai na sha suma ba'a wanye lafiya ba na yi ta amai, ya hadamin Tea shima na sha na yi amai, Tuwo nace ina so yaje ya siyomin Tuwon Semo miyar karkashi shi naci ya zauna a cikina.
Duk wasu kayan kwalama sun daina Burgeni, Da daddare kuma Tuwon shinkafa ya siyomin miyar kubewa da ganda, sanda naci lafiyata kalau ammh kwana na yi ina ta faman Amai da miyan yanzu ya yi yawa, shi Assadiq yadda na ke ta bushewa ne damuwarsa da kuma Aman da na ke yi yasa da Safe ya tasani gaba muka koma asibiti ganin Likita.
Bai yarda ba sai da likita ya karanta masa sai hakuri in cikin ya fara girma duk zan daina Aman sannan miyan zai Ragu, Ramar da na ke yi kuma kila Sanadin cikin ne, ammh zuwa gaba in na fara cin abinci sosai zan maida jikina.
Bai bamu komai ba, sai magungunan karin jini na masu ciki ya sake Rubamin, Yace maleria ya rabu dani zazzabin dare da na ke yi cikin ne ya na Tunanin in ya yi kwari duk zan dawo Normal.
Haka muka koma gida, ina kwance jiya da yazo da karfin jikina ammh washegari sai na kwanta kamar ruwa, kuma gashi gobe da Safe zai koma wajen aiki, maganarsa shine bazai barni ni kadai ba, gwara na koma gidan Adda Fati na zauna ko kuma Habiba tazo ta zauna dani.
Ni kaina ina son na Huta sai nace zan je gidan Adda Fati na yi ko sati ne daga baya in zan dawo sai na Dawo da Habiba.
Ga makaranta ma, da ya ke ya kunna min wayata, Safiya ta kira mun yi mgana tace an fara Test ya kamata na zo makaranta, shi kuma yace komai sai da lafiya na bari ko an wuceni na yi Difaring ni ko ina zan bari Yan ajinmu su yi gaba su barni.
Da kansa ya had'amin komai da zan bukata washegari da Safe sai da ya kaini gidan Adda Fati ya kuma barmin isassun kudi sannan ya hau Motar haya Zuwa Abuja.
Ita kanta Adda Fati taji dadin haka Tun ballatana irin ramar da ta ga na yi, sannan taga laulayin nawa mai zafi ne.
Tunda Assadiq ya tafi a rana ban san adadin sau nawa ya ke kirana yaji lafiyata ni da Baby ba, kullum cikin cewa ya ke da naji wani abu na koma asibiti, ni kenan kullum tuwo da tsaki, Komai baya min dadi, kuma ban daina amai ba ga miyau, maganar gaskiya ina Laulayi mai zafi sosai.
Sati daya na yi gidan Adda Fati ta had'ani da Habiba muka dawo daganan Wajena ta ke zuwa makaranta.
Bayan tafiyar Assadiq sai da na yi sati Biyu sannan na fara farfadowa, na rage Amai sannan na daina zazzabin dare, kuma yanzu zan ci abinci ya tsayamin acikina na wani lokaci a satin ya baro Abuja bisa adalci ya sauka a gusai, ya gayamin ban nuna wani abu ba, Tunda itama matarsa ce kamar yadda na ke da Hakki a kansa itama ta na da Hakki a kansa.
Bai zo zariya ba sai da ya koma Abuja sai weekend Ranar jumma'a ya zo ya ganni, ranar da yazo Habiba ta koma gidan Adda shi kuma ya cigaba da kula dani.
Duk da dai naji sauki sosai, ni kuma na matsa masa ranar litini da ya tafi da Safe ni kuma na Shirya na koma makaranta naje na iske Uban Assigemt sannan an yi abubuwa da dama ba na nan, Sai dai Thanks to Safiya duk ta min wasu abubuwan sannan komawata ta na kokarin koyamin abunda ya wuceni.
Kullum da minti da cingam na ke yawo a jakata ko da kunzo Saboda Miyan bakina, ina shiga cikin jama'a akwai cutarwa saboda wani ya na da kyankyami.
Ramewa kawai na ke yi, sai dai na fara cikar Fuska dagani In ji Adda zan yi girman ciki mai kumburi Domin tun cikina na wata uku da wani abu ya bayyana ajikina, ga shi dai ina da Tsawo ammh Tsawo na bai shanye girman cikina ba, in na saka Hijabi in ban saka hannu na kare ba sai ya bayyana.
Ni