Showing 9001 words to 12000 words out of 116366 words

Chapter 4 - Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

309

da kaina na rage huld'a da Saliha, tunda itama taga ta na bi na ina basar da ita sai taja baya, duk da Assadiq yace mu cigaba da mu'amalan ba karya ba ne ni matar kaninta ne, ammh ni ce a karan kaina na kasa, sai na ke ganin kamar za'a samu matsala.
Ammh lokaci bayan lokaci mu kan gaisa ta waya ko ta chart.
Assadiq ya raba mana kwana ni da Sultana Tunda dukkanmu ba ma zaune waje daya da shi, sai yace duk bayan sati biyu zai fara zuwa ya sauka wajena, in ya koma ya yi sati daya, satin sama kuma sai ya sauka Wajen Sultana haka ya raba mana Tsarin kuma na amimce tunda sai da ya yi shawara da ni.

A koda yaushe in na yi masa maganar Lokaci fa na kurewa yasan hanyar da zai fad'ama su Umma game dani sai yace na kara masa lokaci har yanzu yana Tunanin ta wacce hanya zai saukaka Lamarin, ni kuma gani na yi cikina na kara girma ina Tsoron nan gaba abubuwa su kara Tsami.
Shi kuma Sadiq ya buga duka Hanyoyin samun mafitan ya kasa samu ne, kunya da wani irin nadama sun gama dabaibayeshi.
Ba zai iya taran su Umma da mganar ya auri wata matar shekaru uku da wattani batare da sanin su ba.
Ya zauna ya yi tunanin duk ya kasa samun mafita, Kuma ga shi ba abokin shawara, Tahir ne kuma yanzu yaja baya da shi ranar dai ya kirasa ammah a Dakile Tahir ya rika amsa masa shiyasa shima ya fita batunsa.
Tunanin abun yasa har rama ya fara rashin natsuwa ta fara bayyana masa a fuska.
A cikin irin Tunanin da ya ke yi sai ya yi tunanin Big sis Surayya, duk cikin yan'uwansa ya fi shakuwa da ita, kuma ya na mata kyakyawan zaton zata Fahimcesa, da yakinin zuwa ya gayamata abunda ya faru yaje gusai a satin, sun had'u a gida yace mata zai zo wajenta akwai mganar da za su yi, tace sai yazo anan ma agaban su Umma tace duk ya rame da Farko dai ya fara kiban Amarci.
Mama na wajen tace wahalan zirga zirga ce na jeka ka dawo, Umma ta yi karaf tace sultana na gama makaranta ya sama mata muhalli ta bisa chan sai dai bayan wattani in sunzo ganinsu.
Shi ko har ga Allah baya so Sultana ta bishi Abuja in hakan ya faru Hasiya fa? Kuma ga shi kad'an ya rage ya gama Masters dinsa shiga zariya zai yi masa Wahala  gaskiya.
Ana gobe zai koma Abuja ya shirya da Daddare da niyar tafiya gidan Surayya  ai Sultana na ganin zai fita ta makale masa sai yaje da ita, ba shi da zabi ya sakata a gaba suka je.
Duk yadda ya so ya yi mganar sai kuma yaji ya kasa, duk da Sultana ta ba su waje, ammh kuma guilt din abunda ya aikata yaki barinsa ya fad'ama Surayya komai sai kawai ya Bige da fad'amata in ya koma Abuja zai kirata a waya.

Kuma da ya koma sai ya kasa kiranta tunda ya rasa ta ina zai fara, sai gaahi ta kira da kanta , ta na mai tuni kan maganar da ya ce za su yi kai tsaye yace in zai gayamata zai kirata da kansa, Daga baya ma data matsa masa sai yace mata bakomai.
Ita kuma duk sai ta Damu, saboda tafi  kowa Sanin kanin na su ta tabbata akwai abunda ke damunsa.
Har ta fara Tunanin ko sun samu matsala da Sultana ne? Ta shirya taje har gida ta turketa ta tambayeta Sultana ta rantse mata suna zaune lafiya cikin soyayya, daganan sai ta sare sai Tunaninta ya bata ko daga wajen aiki ne?

Har megidamta ta yi ma mganar suka Tattauna shi yace koma menene kada ta matsa masa ta yi masa addu'a yadda ta ke da Sadiq ya tabbata da kansa zai zo ya fad'a mata da Damuwarsa.
Da shawaransa ta yi amfani ta kyalesa sai dai ta dukufa yi ma kanin nata addu'an koma meke damunsa Allah ya kawo masa mafita ta alheri.
Bata sani ba Allah ya amsa addu'arta sai dai kila mafitan ta yi jinkirin samuwa ko bayyana.

A satin da zai je zariya wajen Hasiya ya samu wayar Umma cewa Innani ba ta da lafiya, ta zame ta fad'i acikin Falonta yanzu haka ta na asibiti.
Hankali tashe ya kira Hasiya ya gayamata yace ta yi masa Hakuri ya je Gusai yaga innani, itama duk ta damu fadi take"Ka gaisheta Assadiq. Allah ya tashi Kafad'un Innani."
Ya rika amsawa da Ameen Hankalinsa ya tashi da wayonsa bai san Lokacin da innani ta kwanta asibiti ba, ko ciwo ta ke yi ta gwammace ta yi ta shan jike jike.
Yaje ya iske innani an dawo ma da ita gida, bayanta ne wato kugunta ya Bugu, zai zazzabi a jikinta likitoci sun ce a daina barinta ita kad'ai Tunda jikinta na Tsufa ne ta na Bukatar wani mataimaki.
Sai ga Innani kwance shuru baki ba mgana, sai ido kawai ta Saduda ta ga mutuwa.
Sadiq shi ya yi ma Abba mganar ko cikin ya'yan Su goggo Husai ya Dauko daya daga cikin su ta dawo nan da zama a sakata makaranta.
Wacce zata rika kwana da Innani ta na kula da ita.
Shawaran Magajin gida ita tayi aiki, Mutanen Shinkafin daman sun zo Dubata, Da Abba ya yi mganar da Dan'uwansa  sai yace akwai Autar Hussai, Farida ta na jss2 ne yasan zata iya kula da Innani.
Haka ko akayi ana mgana Hussai tace ta ba su Farida har abada, Kwana daya Tsakani ta had'o kayanta ta dawo Gusai da zama.
Cikin Sati daya aka sama mata Gurbin karatu a makarantar da su Sultana ke zuwa,kuma tare a ke kaisu Direba kuma ya Daukosu.
Sultana ita gidanta ta ke tafiya ita da Siyama mai tayata zama, ita kuma Farida ta na shashen Innani.
Gata ba ta da kiyuwa, ga son aiki da kazar kazar Umma da Abba sun yaba da ita sosai.
Innani duk masifarta sai da ta ragama Farida ganin yadda ta ke hidima da ita, sai dai suna tafka tsiya in Tace zata yi ma Innani Jagora ko zuwa daki ko makewayi.
Sai Innani ta fara fad'an ita ba makaunniya bace kada Farida ta raina mata wayau mana.
Ita ko sai tace to in ke ba mahaukaniya bace ki cire gilashin mana kuma ki yi tafiya ba sanda mu gani.
Da Innani taji haka sai bakinta ya Mutu, tasan Faridan na taimakonta kuma duk inda Mutum ya ke Rahama ne, ta na jin dadin jin motsinta kusa da ita ballatana da tare suke kwana su tashi, bakin Innani ya Bude hira chau cau, labaran tsoffin garin shinkafi ba wanda Innani ba ta bata ba, har da Labarin kakarta da irin kishin da ta yi da Innani, yo ina ruwan Innani watarana ma cikin zencen har Hussai din ta ke zagewa in yan tsiyanta suna wajen
An dai samu ta Rage tsine tsine ammh fa watarana in aka tabota yini zatayi Allah ya tsine ma uwar barawo tun ballatana in ta ajiye abu bata gani ba, wani Lokacin kuma manta inda ta ijiye take yi sai ta fara jan Hanci ta na Tsine ma barawon da bata gani ba da Danginsa gabadaya.




*Janafty*
*TMWBK3003*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/IhAz8h8nRy250ZnGGXwM65

Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641


*Bayan Wattani Uku.*

Wattani ukun da suka shud'e na yi su ne cikin farinciki tare da tsananin kulawa ta bangaren Assadiq da yan'uwana, Tunda a yanzu cikina na cikin wattani na shida da kwanaki ne har na fara Awo a asibitin musulmi. duk da Assadiq yaso na sauya asibiti, ni nace ya barni anan saboda Cousin din Safiya Sister Zainab, mun saba da ita sannan ta na kula dani, tare da bani shawarwarin da suka kamata.
A yanzu haka mun samu Hutun First Semister ina gida in da Allah ya taimakeni kenan, saboda Cikina ya yi wani irin girma na ban mamaki kamar ya na cikin wata na tara.
Ban yi kiba ba, sai dai na Kumbura kafafuwana da hannayena tare da Fuskata, komai ada da ya ke karami yanzu ya koma Babba.
Na zama wata katuwa sai Ciki mai Tsini ta gaba, ga uban nauyin da cikina ya ke yi, ina jinsa har a jikina Da Kafafuwana kuma har a asibitin na yi Korafi suka tabbatar min da komai lafiya namiji suka gani shiyasa na ke jin nauyin cikin a jikina.
Tuni na daina Amai, sai dai na kan yi in naci wani abun da cikina ya kasa karb'a Miyau kuma na daina ammh wani Lokacin sai na kasa had'iyam miyau sai na Tofar da shi.
Zazzabin dare shima ya tafi, sai kananun cuwuka da ba'a rasa ma su Ciki da shi.
A baya na dauka cewa iya son da na ke yi ma Assadiq ya isa ya rikeni ni da shi a zaman auren mu, Sai daga baya na Fahimci nima ina bukatar Soyayyarsa, Kuma sai a lokacin na kara tabbatar ma da kaina Assadiq ya na sona kuma zai iya komai Saboda ni. Kuma ya na son cikin jikina ya na kuma Burin samun Tsatsso daga bangarena.

Gatan duniya da Miji ke yi ma matarsa Assadiq na yi mini shi, Har fiye da zato na da Tsammanina, Ko da yaushe cikin kira na ya ke yi yaji Lafiyata, in kuma ya samu sarari ko ba ranar zuwansa Zariya ba ne zai samu lokaci ya zo ya ganni ko da bazai kwana ba.
Bai taba bari na yi kukan wani abu ba, Duk abunda na ke so kafin nayi mgana ya riga ya yi min shi.
Kayan abinci wani baya karewa ya ke tarar da wani, komai na Bukatar macen kwarai a gidan mijinta Allah ya bani shi ta bangaran Assadiq ta ko'ina Rayuwata ta inganta.
Kudi bani da matsalansu har ma ina taimaka ma yan'uwana, Amma ma dagachan bangaran ina taimakon su da iya abunda na ke da shi.
Sun zo kwanaki ita da Adda suka Dubani ba su dai kwana ba ne, Amma daman bazata iya kwana a wajena ba, da ma dai gidan Adda Fati ne, gidan Adda Rukayya daman Saboda Mijinta ba ta cika ganin baki ba.
Bangaren Maman Suhailat itama Tsakaninmu sai godiya sosai ta ke kula dani, in dai ta na gida sau ukun nan zata lekoni taga lafiyata shiyasa da Assadiq ya yi mganar kayan Haihuwa da nawa nace ita zan bamawa ta Siyomin ta na da kirki.
Nasan yadda zaman gidan haya ya ke, ana samun mutanen kirki da na banza ita dai maman Suhailat ko da ta na da wani halin to kirkinta duk ya shafe wannan.
Ramatu da tazo ta ga irin gatan da na ke ciki sai da ta kara dawomin da mganar da ta tab'amin shekarun baya.
Ta kalleni da tsinin Cikina a gaba kafin ta yi mirmishi tace"Kawata daman ai na fad'a miki watarana Zaki ji dadin Rayuwa kamar kowa koma fiye da kowa."
Na kalleta cikin mirmishi kafin nace"Hakane wlh gashi komai ya wuce sai dai Tunawa."
Ramatu tace"Kin tuna na sha gayamiki Daga salisu har Abubakar ba su ne gwanayen ba  gwanin in  yazo Shine yardaddaje har a wajen Ubangiji ki ka yi ta min musu kina ganin kamar haka bazata faru ba, yau gashi kin samu fiye da zaton da na yi miki Fata Hasiya."

Sai na kasa yi mata mgana ina ta shafa Cikina ina jin wani farincikin zamowa uwa a cikin raina.
Yau ga shi ni Hasiya da na cire rai ga aure ma, ni ce dauke da cikin Haihuwa lalle Allah ne abun godiya
Rayuwata daidai ta ke tafiya sai dai abu d'aya ne na ke tunawa ya sakani Fargaba  shine na rashin sanin gobena a cikin Ahalin Assadiq tunda har yau ba su san da zamana ba.
Ramatu ce te katsemin Tunani da cewa"Ke na manta ban fad'a miki ba, ranar na shiga anguwan su Salisu na had'u da shi"
Cikin mamaki na dago ina kallonta kafin nace"Haba? Me ki ka je yi?
Ramatu tace"Makociyata din nan, Maman Basma mahaifiyarta ta rasu naje mata gaisuwa sai naga ashe kusa ne da gidan iyayen Salisu, aiko ina fitowa sai ga shi mun had'e da shi, shi da Musabahu."
Cikin wani yanayi nace"Allah Sarki? Ya kika gansa? Ya warke?
Ramatu tace"Ya warke, sai dai har yanzu ya na dan d'ingishi, sannan ya na Dogara karamar sanda."
Sai na yi shuru na kasa mgana acikin raina ina jin wani iri, kenan har gobe in aka kalli Salisu Bakin Fentin da na yi ma Rayuwarsa bazai taba goge masa ba.
Kila Ramatu ta Lura da sauyin yanayina ne, kuma tasan saboda mganar ne, yasa da sauri ta dafani ta na fad'in"Kinga ba na gayamiki ba ne saboda ki shiga damuwa ba, na fada miki ne saboda sai da ya tambayeni ke, yace yaji an ce kin yi aure nace masa Eh! Sai yace in mun had'u nace ya na gaisheki"
Kai kawai na kad'a kafin nace"Ayya Ramatu ina amsawa! Ammh dai ko da ya warke, akwai wannan tabon a jikinsa in shi bai kirani bakar Daka ba, yan'uwansa baza su taba mantawa dani ba."
Ramatu cikin wani yanayi tace"To ai ba ke bace Allah, ke dai kawai kin zama Sanadi ne Hasiya, ki kara godema Allah domin kin cinye jarabawarki."
Sai kawai na gyad'a kai kafin nace"Hakane ina Labarin Abubakar? Ya dawo garin ko ya na chan kanon?
Ramatu tace"Anya? Kinsan bansan kowa daga bangaransa ba, ko ya dawo kila dai ya na chan, ko kilama ya yi auransa."
Da Sauri nace"Allah yasa."
Daga haka muka saki maganarsu muka kama wata, sai dai har ta tafi abun na cikin raina.

Yanzu Fargabata d'aya yan'uwan Assadiq ta yadda zasu karbi' mganar auranmu daga sama, ni abun da ke damuna in suka ji Bakin fentin da ya bata Rayuwata dakyar su amince Assadiq ya cigaba da zama da ni.
Ga cikinsa a jikina in har ya barni bansan kuma wani Hali zan shiga ba.
Da farko farko na dauka in ma yace baya son cikin ni kad'ai zan iya renen Cikin har na haifesshi na bashi Soyayya da kulawa, sai daga baya na Fahimci wani abu ni kad'ai bazan iya ba. Assadiq shi ne ginshikina ni kuma ni ce mahad'in Rayuwarsa da Rayuwar abunda ke cikina gabadaya.
Ko da yaushe cikin Tuna ma Assadiq na ke yi akan ya yi ma yan'uwansa maganata su san da ni, ammh sai yace na kara masa Lokaci in sha Allahu zai sanar da su, abunda na lura shine tsoro ya ke ji, kuma ya rasa ta hanyar da zai iya fad'a musu kuma Lokaci na ta tafiya, Tsoro na d'aya in har na Haihu wlh abubuwan za su kwabe mana yadda bamu yi tsammani ba.
Kuma in har na Haihu nasan yan'uwana za su bukaci ganin Dangin Assadiq rashin ganinsu zai iya fassara karyan da na yi musu.
Ammh bayan wannan fargaban babu abunda ya tab'a Rayuwar auran mu, cikin Farinciki mu ke zaune tare da Soyayya da kauna da Tunanin Dorewa na har Abada.

In ya zo min weekend kashe wayoyinsa ya ke yi, sai zai kira Sultana ko gida sai ya kunna ya yi mgana da su, Lokacinsa da komai nawa ne, ba na girki sai dai ya Daukeni a mota mu fita mu ci a waje, mu ne wajen shan Ice cream mu ne wajen cin abincin da cin kayan kwalama, ba kowani zuwa ya ke zuwa da mota ba, wani Lokacin sai ya biyo ta haya.
Ya sauyamin waya ya siya Wata Samsumg Sabuwa, sannan ya siyamin wata karamar Tap mai kyau, har sai da na yi masa mgana baya gajiya da siyan computer, ko wani Lokaci sai na gansa da sabuwa ? Sai ya yi dariya kafin yace min sana'ar Abba kenan ya na shigo da su daga china, india zuwa Gida nan Nageria.
Daganan na yi shuru Tunda abun na masu uwa a gidin Murhu ne, Karamin Tap din sai na ke zuwa makaranta da ita babba kuma sai na rika barinta a gida na kallo na ko yin game da Sauran abubuwa.
Saboda gudun a samu matsala ko Hotona ba na Dorawa a waya Tunda Saliha na da lambata, sai dai in muka yi Hotuna na adana su a wayata, shima baya Turawa saboda gudun a samu matsala  sai dai ya kan dauki wayata mu yi ta Hotuna da shi.
Akwai wani zuwan da ya yi lokacin cikina ya shiga watansa bakwai kenan ya kara girma da tsini.
Zamu fita ne zuwa gidan Ramatu daganan mu je gidan Adda Fati, na saka bakar Abaya na yi Rolling din mayafin shi ya ma nad'amin shi, shi kuma ya sanya Farar shadda har da Hula sai ya zama wani babban mutum kwarjinsa ya kara bayyana.

Rikeni ya yi ta gefen Damarsa ni kuma sai na kwantar da kaina saman kirjinsa, shi ya Dauki wayata ya yi mana Hoton ni na dago ina kallon wayar shi kuma ya na kallona dukkanmu muna Dariya aka yi Hoton
Farar Fuskata da ta kara wani haske ta bayyana acikin hoton shima Saboda Hutu ya kara fari da kiba sai muka yi wani irin kyau kamar Wasu Taurari acikin Wata.
A mota ma ni na kara yi mana wasu Hotunan ya na Tuki ina faman Sauke kaina saman kafad'ansa ina yi mana Hotuna har da Vedio.
Mun yi kyau sosai shima da muka Dawo gida na nuna masa yace Hotunan  sun yi kyau na ijiye mana watarana zai saka a wanke mana Babban Frem dinsa.

Abunda bansani ba Shine ni dai nasan ba wanda ke Daukan wayana shiyasa ban taba Tunanin Samar ma Hotunanmu muhallin sirri ba, na manta Safiya na Daukan wayata, a satin da muka yi Hoton muka koma makaranta a chan ne Safiya ta karb'i wayata ta na gani sai ta ga Hotunan nan Sai ta fara santin mun yi kyau, Daman kuma tasan Assadiq tunda sun taba had'uwa yafi sau biyu.
Bayan Hotunan mu ina da littafan Hausa a wayata, wanda na kan samu a groups din novels, su ne su ke debemin kewa in Assadiq baya nan, duk da karatun ba sosai na ke yi ba su Safiya tace min zata Tura bansani ba ashe ta had'a da wad'anan Hotunan ta Tura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login