Showing 81001 words to 84000 words out of 116366 words

Chapter 28 - Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

26 Oct 2025

326

zai sakata a Mota ya maidata shinkafi.
Tunda ta raina Umma itama yanzu bata da kima acikin Idanuwanta.
Shima Sultanan ta fadi na shi laifin maganarta daya ne baya sonta yafi son Matarsa a kanta kuma yana yin mata kaza itama baya yi mata.
Mgana dai duk na zarge zarge da kishin Tsiya.
Surayya dai nan shima ta nuna masa ya gyara sannan tace kada ta kara jin ya kara kai hannu Fuskar Sultana matarsa ce ba Jaka aka aura masa bq shima ya ce ya yi kuskure bazai kara ba kuma ya bata Hakuri a gaban Anty Surayya, sannan shima yace ta ja mata kunne ta daina zagin masa mata yadda bazai bari siya ta zageta ba shima bazai bari Ta zageta a gabansa ba.

Nan dai Surayya ta zaunar da su gabadaya ta yi ta musu nasiha itace sai Goma na safe sannan ta koma Gidanta bayan ta tabbatar ta gyara barakan dake Tsakanin su.
Ta dai yi kokarin kebewa ita da Sultana ta gayamata gaskiya ta daina Biye ma zugan kowa sannan kuma ta Rike sirrin mijinta ko Tambayanta akayi tace bakomai..sannan ta yi masa Biyayya ta daina ja inja da shi sannan ta gyara kanta da jikinta har maganin gyaran jiki tace zata aiko mata da shi don Allah ta gyara.
Ta kuma yi mata alkwarin zata gyara sannan tace ta shirya taje ta ba ma Umma Hakuri, ta yi fushi da ita.
A lokacin ta yi kuka ta nuna Nadamarta.
Kuma tana da tabbacin in taji shawaranta bazasu kara samun matsala da Sadiq ba, in kuma bata ji ba komai zai iya Faruwa.
Yanayin mganar Sadiq tasan da gaske ya ke yi ya gaji.
Kuma gajiyarsa daidai ya ke da Faruwar komai.

Sannan Surayya ta sakata ta karb'i lambar Hasiya a wajenta ta kirata ta bata Hakuri Hasiya tace ita bakomai bata riketa ba, kuma a gaban Sadiq din aka yi, sannan shima tace kada ya sake Doguwar waya in dai yana tare da d'aya daga cikin su Saboda a zauna lafiya.
To kamar dai Abun ya Dore Sultana ta gyara ta koma kamar Farkon auransu, sai ga shi har kwana ya kara sai Ranar Monday ya koma Abuja.
Sannan sun je tare ranar lahadi da Daddare ta ba ma Umma hakuri.
Umma tace ta yafe itama ta kara yi mata Fad'a sosai.
Kamar taga uwar bari ne tunda ko su Sajida sun kirata su ji Labari su kara zugata sai taki gayamusu komai.
Ammh fa kishin Hasiya da tsanarta na nan acikin ranta sannan Babban Burinta yanzu ta samu ciki itama ta Haihu.
Har ta fara damuwa auransu ya fi shekera ba ta samu ciki ba, shikuma sai yaga kamar abun ya fara taba mata Tunani sai ya koma yana lallashinta duk sanda yazo, ko kuma suka yi mgana ta waya.
Yana nuna mata Haihuwa ta Allah ce itama bai manta da ita ba ta yi ta addu'a zai bata.
Har fa asibiti ta saka sukaje aka auna su likita ya tabbatar da suna lafiya sannan ta yarda lafiyar kalau lokaci ne bai yi ba.
Saboda ta rage damuwa yasa ya matsa mata ta siya jamb ta zana kuma ta samu Score mai kyau.
Nan take ya nema mata Gurbin karatu a jami'ar Gusau.
Ta fara karatu a tsangyar B.A English.
Sai karatun ya fara Dauke mata Hankali da wasu abubuwan ammh kishi nan da zargi bata daina ba tadai rage da kuma nuna an yi mata ba daidai ba.
Shi kuma ya sha zaunar da ita yana fad'a mata tafi Hasiya zama acikin gata, ni acan a gidan haya na ke zaune, da ire iren mganganunsa yasa ta fara Fahimtar gwara ita tunda tana cikin gidan sa ne.

********
Ni kuma a lokacin har mun gama TP mun koma makaranta muna karishe Sauran Semister mu.
Su Asim na da watani bakwai a lokacin Tuni har sun fara zama, karatu yasa ban kara komawa Gusau ba Tafiya ma sau daya na yi.
Amma ciwon ta ya tashi har asibiti ta kwanta mukaje na kwana daya na dawo.
Koda yaushe korafin su Umma yaushe zan zo na kawo musu su Asim?
Sai dai nace zan zo in sha Allahu makaranta ce ke boye ni.
Assadiq yace min Siyama ta samu mijin aure lokacin Bikin zai yi daidai da mun gama jarabawa sai naje daga biki na jima acan.
Assadiq bai taba gayamin zai tafi dani Abuja bayan na gama makaranta ba, na fi ma Tunanin gusau zai maidani da zama, zan so haka Tunda yanzu bani da matsala a wajen dangin mijina.
Masu matsalan ma kalilan ne.
Siyama a garin Gusau ta samu miji wani likita ne zata aura ba'a kuma saka Lokaci mai Tsawo ba..wattani Hudu aka saka Shiyasa Shirye shirye ya tashi Gadan gadan.
Ni ma kuma ina ta shirina Tunda Assadiq yace zan jima acan daga Bikin Siyaman.
Biki ya rage wata daya muka gama Jarabawar karshe muka yi bye bye da makaranta sai jiran sakamako.
Assadiq ya shiryamana Tafiye tafiye a shekaran yace har Daura zamu je garin su Tahir zamu je shinkafi.
Tahir an saka masa ranar aure Wata Hauwa'u zai aura yar cikin garin katsina.
Ammh saboda yana gini shekara a ka saka, kuma agarin katsina zai zauna Saboda Siyasar da tafi karfi a cikin garin katsina.
Turaren Wuta na siya ma Siyama Gudummuwa tare da kayan gyara na Saiwowin Dahuwar kazar gudiyo wajen Marubuciya Surayya dee, aika musu da shi na yi ta Hannun Anty Surayya Tunda itama na gayamata ingancin kayan ta fara amfani da kayan gyaran Surayya Dee takwaranta.
Ku gwada ku gani kayan gyaran Surayya Dee masu kyau ne da inganci ni Hasiya tabbaci na ke baku ba yakini ba.+234 803 277 3332

Mama da kanta ta kirani ta na min godiya nace bakomai, Assadiq sai dak yaji nayi yan'uwansa abun alheri ba na gayamasa shiyasa nima daidai gwargwado ban taba neman wani abu na rasa ba.
Ko su Adda Fati sai dai na Taimaka musu, ko Adda Rukayya da ta ke ganin mijinta na da hali bata kama kafata a jin dadi da saka Suturu ba.
Mijinta ya sani ni yanzu na sha kwana domin mun taba haduwa kwanaki a gidan Adda Rukayya.
su Anma na fama da su Asim ba ni kadai ba har ya'yana haka ya rika kallo yana mamaki
Da na gaishe shi ya amsa yana kara tambayar Adda Rukayya ni ce na koma haka?.
Ita ko tace nice mana ta na bashi Labarin mijina da Danginsa.
Sai mamaki ya ke yi, daman abunda ka ke zaton bazai Faru ba shine ke faruwa.
Labarin Haihuwata har a kunnen Sahura da yan'uwan Salisu tunda na had'u da kanwarsa.
Har gidanmu na samaru da muka zauna suke zuwa tambayansu  Maman boy da gaske ne na Haihu yan Biyu? Su kuma su ka tabbatar musu.
Har da karin cewa wai shima mijin nawa ya yi hadari Allah ne ya yi kwanansa na gaba.
Maman salihi da ke bani Labari tace sun ce musu da gaske ne, abunda Tunda shi ya yarda ba mai yi sai Allah suna nan tare da juna cikin Soyayya.
Ramatu na gayamin Salisu ya kirata a waya yace ta tura masa lambata ya Kirani tace bazata tura masa ba ni matar aure ce sai ya nuna mata Hakuri zai bani tace ai Hasiya bata rike ka a ranta ba.

Ni kam in inajin Labarin nan sai naji kamar komai bai Faruwa ba, sai nake ganin abun kamar al'amara Allah Sarki Rayuwa Abubakar ne bani da Labarinsa gwara Salisu duk ana tare a anguwa daya sannan indai zan Tuna Halin Tsaka mai wuyar da na Shiga bazan manta da Salisu da Abubakar acikin Rayuwata ba.
Kawayena guda Biyu da Assadiq ya Sanni da su daga Ramatu da ta kara Haihuwa kwanaki sai Safiya da Sanadin makaranta muka Kulla zumunci yayarta ta yi aure khariyya na yi mata kara sosai kamar yadda nima take yi min in Sha'anina ya tashi.
Anko wajen kala uku suka Fitar akwai na walima sai na yinin biki sai kuma na Sister day.
Duka kuma Assadiq ya siyamin acan kuma aka d'inkamin.
Nima ta bangarena na siya Sabbin mayafai da jaka da takalmi.
Sannan na Dage da Sabaya nan ina Damawa ni da yara muna sha ganin Tsotso duk ya kara Tsotesni gani daman ba auki ba.
+234 706 548 1260
Cikin Lokaci na ciko na yi bul bul dani gwanin ban sha'awa.
Tun ana saura Sati daya na tafi Gusau motar haya na shiga sai tashar Golf na yi Assadiq ya turamin kud'i yace Saboda yara gwara mu samu sarari.
A dakin Umma na sauka kamar yadda Mijina yace.
Sai dai ban san cewa itama sultana ta dawo wajen Umma da zama ba sai da naje na ganta kwance duk ta rame sai fama ta ke yi da Amai.
Ashe ciki gareta kuma yana saka ta  laulayi mai zafi.
Tana ganina ta fara gulma gulmace kakaro Amai da Sanabe kala kala wai ita mai ciki yara ko su Asim tuni suna hannun dangin Ubansu har Rubibin Daukansu ake yi.
Kusan nice bakuwa ta farko data fara sauka dagani sai Saliha sai Anty Saddiqa.
Tare dani aka yi sauran shirye shiryen su Sajida har Lokacin ba su min mgana in na gaishesu sai sun ga dama suke amsani.
Ni da Umma kam sai son barka, bata kara nuna min wani Tsamgwama ballatana Tsana ba.
Ya'yana ko sun zama abun so acikin Dangi, ni kaina na had'u da su Saliha da Anty surayya na shige cikin su ban maida kaina bakuwa ba.
Gyaran kai da kunshi duk a Gusau na yi shi tare da su Anty Surayya.
Sultana ta so ta yi, ammh ba hali duk da tanq babban kawar Amarya Laulayi ya hanata Burinta ya Cika ta samu Ciki.
Iyayin da ta ke yi da wannan cikin sai wanda ya gani, tun ballatana da ta gani sai abun ya karu.
Ni a dakin Umma wannan karon na sauka na barta dakinta da na sauka wanchan karon ni bata gabana.
Sai dai ina gaisheta kullum da safe ta amsa tana wani yamutsa fuska.
Tun kafin nazo daman an yi amarya Jere, saura kaya kawai ake kaiwa can gidan
Innani na nan sai dai yanzu jikinta yaki dadi yau lafiya gobe ciwo kuma taki yarda aje asibiti, innani dai Jikin Tsufa kawai da Shekaru ne sai dai kawai Allah yasa Tafiya ta yi kyau.
Mutanen shinkafi duk sun iso suma, da na cikin garin Gusau Dangin Mama.
Assadiq sai ana Gobe Daurin aure ya iso da yamma, lokacin muna gidan Surayya gabadayanmu inda ake Walima.
Sister Day sai ranar lahadi a gidan Amarya za'ayi yinin biki kuma a gidan Abba.
Sai kirana ya yi a waya yace ya zo bai ganni ba.
Nace muna wajen walima matsamin yayi sai na dawo tunda su Asim na wajen Umma sun fara kuka.
Ana mangariba Anty Saddiqa ta Tukomu zuwa gida.
Sultana ta rarrafa taje walimar ammh muna dawowa taga Assadiq sai ta koma ta narke ta ce nan ke mata Ciwo tace nan ne
Ni dariya ma take bani a raina nace lalle yarinyar nan bata san ciki da Haihuwa ba ne shiyasa.
Washegari aka Daura auran Siyama da angonta Saleem.
Gida ya cika da mutane kaf dinsu ba wacce bata zo ba, mun sha ankon yinin biki mun yi kyau gwanin sha'awa.
Assadiq ma yaci Fararen kaya shi da Tahir tunda ya zo masa Daurin aure Abba kuma na can da bakinsa abokan arziki irin su Alhaji Jibril da ya yi ya kusheni a wajen Abba ya kasa samun nasara.
An sha Hotuna sai wansda ya gani, ni ban Tusa kaina ba sun dai sun karbi su Asim suna ta Hoto da su ni kuma ina gefe sai da Surayya ta jawoni cikinsu tana fadin nima ai na zama yar cikin Family din SS SHINKAFI.
mun sha Hotuna kuma kowanne Hoto sai su ce duk na Cinye su.
Ammh fa su Sajida ina shiga suka Fita daga Hoton ba kuma wanda ya Damu da su.
Assadiqa ma ya yi Hoto da yan'uwansa Sultana da ta sha kwalliyarta harda makeup ta Lafe masa suna ta Hoto shi kuma yana Dauke da su Asim.
Saliha ce tace nima na shiga a yi mana ni ba domin sun matsa ba, ba zan Tusa kaina ba.
Zuwa la'asar aka yi haraman Tafiya da Amarya tunda an ci an koshi.
Mu bamu tafi a ranar ba sai washegari Lahadi tunda za'ayi Sister Daya.
Kuma abun yi yi kyau Sosai sai wanda ya gani an ci kuma an sha, sai aka kara gyara gidan Amarya mai kyau da shi  ni da da gidan Anty Surayya.
Muka bar Amarya a gidan tare da Fatan Zaman lafiya na har Abada.
Da daya da daya baki suka watse suka barni a gusau.
Assadiq har ya koma Abuja yace sai na yi wata a gusau in yazo sai muje Shinkafi.
Umma da taji Labari tace tare zamu je shinkafi itama ta kwana Biyu bata je ba, Sannan har Gummi zamu je a kai ma mallam Zakari Asim ya gansu
Jin haka yasa yace shikenan na Shirya mu tafi da Umma.

Sultana kuma ba Halin tace zata ga Laulayi ga makaranta dole ta na ji ta na gani muka tafi muka barta.
Shinkafi muka fara zuwa can naji abun mamaki,ana ta cewa Sultana tace ita yan biyu zata Haifa.
Umma tace bata sani ba, Cikin da bai yi kwari ba ne har ta san yan Biyu zata haifa?
Ni kuma har a raina sai na yi mata Fatan Allah ya bata, ni bata san na gada ba ne, iyayen su Amma kakkaninsu tagwaye ne kuma asalin Zuru'rsu suna haihuwan Tagwaye
Ita kuma Sultana saboda ni ne ta ke son ta haifi Tagwaye ita a dole sai ta yi kwacen son da ake yi ma ya'yana ya dawo a kanta.
Tab ni ko a raina nace iska na wahalar da mai kayan kara.!






*Janafty*
*TMWB3K016*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/IhAz8h8nRy250ZnGGXwM65

Kwana Biyar muka yi a shinkafi Daganan muka wuce Gummi ni da Umma, naji dadin garin Shinkafi sosai ba in da Umma ba ta kaini ba. Sai dai kiji ana nuna ni ana fad'in nice matar da Abubakar ya aura a Boye kafin ya auri Sultana.
Kuma ba tsamgwama ba Wulakanci gidan baba Sammani muka sauka nan muka yi kwanakin mu har muka tafi, Su Asim sun sha jagwalgwala kamar me, ba su wannan gidan ba su wannan gidan.
Da zamu taho kuma suka had'o min da kayan arziki, ni Alkalama suka bani da shinkafar Tuwo sai gyad'a aya da sauran tarkace sukace na had'a ma su Asim kunu ne, daga ganin yadda jikinsu ya yi fresh da kiba kunin alkalama na ke ba su.
A gummi ma mun samu kyakyawan Tarba Mallam zakari daman tun zuwan mu na Farko nasan halin kirkinsa.
Ya yi ta kara ce ma Umma ko ita fa? Ganin mu tare kad'ai ya kara sanyaya masa rai ya yi ta fara'a da murna ni kaina ya yi ta sakamin albarka tare da Nasihun zaman duniya.
Matansa ma alhamdulillah sun karramamu, Barin ma Inna mero ita Umma mahaifiyata ta Dade da rasuwa sai sauran matan mallam da yan'uwanta masu aure a garin duka mun ziyarcesu sun gani sun kuma ga su Asim sun saka albarka.
Anan dai kwana hud'u muka yi muka Dawo gida, Daura ne bamu samu zuwa ba, Assadiq yace na bari in Bikin Tahir ya tashi sai mu tafi gabadaya Umma na jin haka tace itama da Farko da taji zamu je sai ta ce mu bari mana Tunda ga Bikin Atrahiru na matsowa.

Wasa wasa fa na share watanni biyu da wani abu a garin Gusau kuma a dakin Umma Tunda har Lokacin Assadiq bai ce min na koma ba, ni kuma ban gayamssa na gaji da zama zan koma ba.
Daman kuma ya fad'amin na dauki kaya masu yawa tunda zan jima acan, sai dai jimawar ne ban dauka zata kai wattanin haka ba.
Sai da na zauna da Umma na kara ganin Tabbacin Abunda Anty Surayya da Assadiq ke fad'amin a baya a kanta.
Hakuri, sanin ya kamata da kyakyawan zuciya Umma ta na da kirki sosai da ba ta da bakinciki ko kyashi na yi mata Uzuri ya fi sau Saba'in Tunda na Fahimeta.
Na kuma san a irin  Labarina da yanayin auren mu ya kasance da Assadiq a matsayinta na uwa na Tsammaci abunda yafi haka Daga bangarenta.
Duk da ba zama muke yi mu yi Hira sosai ba daga gaisuwa sai abunda ba'a rasa ba. Mganar su Asim ma tafi had'amu Tunda ni dai tun zuwana ban san wahalarsu ba Umma ce da Mama sai Farida ke ta wahala da su ni kam sai in suna kuka a kawomin su na basu Nono, sai kuma in zamu kwanta da Daddare.
Ni iyakata in na tashi da Safe, mai Musu aikace aikace sai da rana take zuwa kafin tazo na gama gyara bangaren Umma tas tun Tana cewa na bari har tagaji ta kyaleni.
Ni na riga na saba da aiki Shiyasa ban iya zama, hatta Abun karyawa da Safe ni na kan yi, Har Abba ya sha cin girki na Wani lokacin da rana ne mai aikin kan Dafa ammh har na Dare in ya kare da naga Umma zata Daura sai na karb'a na Dafa.
Sultana kafin ta koma sai dai taci ta kwanta ita a dole mai laulayin ciki Alhalin in hira ne da yini ta na rike da waya ta iya shi.
Tayi wani abu da ya bani mamaki bayan Bikin Siyama.
Tunda taga Assadiq ya dawo bayan Bikin ta mike ta nuna taji sauki ta warke, Umma tace ya dauketa su koma Gidansu.
A lokacim ban Fahimci abunda ta ke nufi ba sai da ya gama kwanakinsa ya tafi tsakanina da shi sai gaisuwa ko tambaya game da abunda yara ke Bukata.

Ranar da ya koma Abuja ta kwaso kayanta ta dawo ma Umma wai bata son kamshin gidan sannan komai taci sai tayi amai ta barta ta zauna a wajenta kafin Assadiq ya dawo.
Mamaki ya kamani hatta Umma sai da ta Fahimceta kuma daga haka ta Samu sara da ya dawo zata koma gidanta yana barin garin zata Dawo wajen Umma har sai da Umma ta mata Fata fata tace ta zauna gidan mijinta bata son iskanci in abinci ne za'a rika aika mata da shi.
Tunda tana gani ta ji sauki har makaranta ta na zuwa ta kuma yini waya da charting sai taga mijinta ya Dawo ta narke masa su koma gidansu.
Kuma duk Saboda kada ya samu Sararin kebewa dani ne tunda ina Gaban Umma.
Ni bata ma sani ba, ko yana gari ban cika nuna kwad'ayina a kansa ba.
Wani lokacin ma nafi zama a bangaren innani da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login