Showing 27001 words to 30000 words out of 155892 words

Chapter 10 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

445

"Eh tace tana Amsawa, yanzuma tace agaisheka tana maka yaya jiki, "Nagode k'warai dai2 Lokacin Sani ya shigo ya zauna kan katifa gefen Kb ya tank'washe k'afa yana kallon Bintalo bako k'iftawa, kallon dayake mata ba k'aramin d'aureta yayiba har takasa bawa Kb Amsan tambayan dayake mata,


Ahankali Kb yad'ago ya kalleshi lfy kuwa malam?

Sani yad'an yamutsa fuska "da akayi yaya? Nalura wannan bata gaisuwa, "to ina Ruwanka da ita akan me zata gaisheka? Dallah can Malam kafitar mana anan Kb ya runtse idonsa yabud'esu akanta,
Yace shikenan inma kace ba Ruwana, Nidai nasan da Ruwana, kuma dole arink'a gaisheni, kamar yanda ake gaisheka,
Yak'arasa maganan cike da kwaikwayon yaranta,


Kb yaja k'aramin tsaki, ya kalli Bintalo datake ta b'oye Fuska, "Mama ta jeki abunki, Da daddare kizo muyi Hira kinji? Da sauri ta mik'e ta fita, tana gyad'a kai,

Sani yace Gaskiya Oga ba kyautaminba, Haka kawai ka koreta,

Yad'an gyara zama yana fuskantan Kb an
Gaskiya yaran Garinnan suna da kyau sosai kb,
Yad'an shafa sajensa yana lasan lips d'insa mai zai hana mud'auki d'ad'd'aya? Ni ind'auki ita wannan Babban kai kuma ka d'auke k'araman don naga naku yazo d'aya sosai wlh ni har kamannin ku nake gani,

Wata wayan caja dake gefen Kb ya d'auka yasaiti dai2 bakinsa ya wurgeshi da sauri Sani ya sunkuya cajan ta wauce ta bugi bango ya d'ago yana kallon Kb dayake Huci kaman macen zaki, Sani ya langab'ar da kai yana Murmushi, "Haba oga Kb? Meyayi zafi?

Kabir yaja dogon tsaki ya had'a giran sama dana k'asa "kar ka sake kasake Alak'antani da wannan fitinanniyan yarinyanba, ka iyama bakinka,
"Shikenan My friend nidai inason Fatima pls kataimaka min wlh jiya danaga tana Hira karkaji yanda naji, Kb ko kulashi baiyiba donyariga yab'atamasa Rai don daya had'ashi da wannan yarinyan gwanda yazageshi yafi mishi sauk'i,


Yau da gobe asaran mai Rai, cikin watanni hud'u Kafan Kb yastmu sauk'i sosai ayanzu har yana iya tsayuwa, ahaka wani zuwan dasu Mami sukayi sukazo masa da wail chair,

Yau juma'a ga Al'adan Mutanen Rugan Juma "yanmata da samaruka sukan sha kwalliya suje dandali, don ganawa da masoyansu,


Kabir nagano Zaune kan wail chair ak'ofan d'akinsu yasha kwalliya cikin fara k'ald'in shadda wanda Mami takawomasa da zata zo shadan sai maik'o takeyi da d'aukan ido yasanya Hula Ruwan k'asa da akamasa kwalliya da farin zare takalmansa half shaoe Ruwan k'asa bak'aramin kyau Kb yayiba jikinsa yayi lufluf sakamakon Hutu darashin shiga rana dayasamu arugan juma farin fatansa maid'aukan ido ga d'an siririn sajansa da yakwanta afuskansa gwanin sha'awa yau yafito a Dr Kbnsa badun rashin k'afaba, gawani fitinanen k'amshi dayake fitowa ajikinsa,
Yayi shiru ya k'urama Iro dayake wankemasa iner waers ido,
Dijah ce itada Jebu suka shigo tana rik'e da falaks ahanunta, daga Dijah har Jebu kusan suman tsaye sukayi daganin Kb dontunda yazo basu tab'a ganinsa cikin manyan kayaba, kallo d'aya yamusu ya d'auke idonsa, yana kallon Iro dayake shanya,


Dijah ta lakato Jebu, tana dariya k'asa2 tace "ke kalli Gurgu k'afa yafara samuwa, dukansu suka shek'e da dariya, yajisu sarai amma yayi kaman baijisuba yana sane da sunan da Dijah tasamasa kenan jifa jifa yakanji,


tagefenshi ta wuce d'akin ta'ajiye flaks d'in, tafito tana sa Takalmi wasu manya2 k'adangaru guda biyu suka fad'o daga sama,

arazane tayi tsalle takoma gefe dai 2 lokacin kuma suka razana sukaje jikin k'afan Kb Cikin zafin nama yasako k'afa ya wurgo k'adangaren jikinta, yafad'i akan kaf'anta, wani Razanannen ihu tasaka shikanshi sai da tabashi tsoro,

jin k'adangaren yana shirin hauramata ne yasa tayi kansa cikin kid'ima, tana tsala mahaukacin Ihu, da sauri yasa hanunsa ta baya yasuk'e wani k'arfe keken yayi baya dashi, agefenshi ta tsuguna ta kifa kanta akan gwiwowinta tana kuka, shi kuwa goganna ka ko ajikinsa saibin Jebu da take shirin fita yakeyi da harara har ta b'ace ma ganinsa,

Dai2 alokacin Sani yafito daga ba bayangida rik'e da bucket ahanunsa kallon KbYakeyi har ya iso ya ajiye Bucket d'in, aranshin kuwa mamaki yakeyi yarasa meyasa In Kabir da Khadija suka had'u sai ansamu Abu irin Haka ko tamishi ko yamata,



Matsota yayi yafara k'iran sunanta Khadija khadija nan ya sauk'e idonsa akan k'afanta yanda farcen k'adangaren ya. Karjeta sha'aninka da farar fata d'ansiririn jini ya gangaro ya taru atakani yatsunta, kallon Kb yayi yana danne2 waya, d'ki yashiga ya d'auko first aid box ya ajiye agabanshi yana gyaran murya Kabir ya kalleshi yana yatsina Fuska, da ido ya nunamasa K'afan Khadijah


Ya d'an tsorata daganin jinin wata zuciya tace to incizonta sukayifa mezakagaya ma iyayenta da suke d'awainiya da kai?

Ohonta ai ita tajawo, wata zuciya tabashi amasa,

"Pls Kb kayi treating k'afan kagafa jinine yake fita, Sani ya fad'a yana tura kekensa Gaban Dijah, kaman baziyiba sai kuma ko meya tuna? Ya d'auki auduga yasa hydrogen Dijah tana cikin rafsa kukanta taji wani Sabon rad'ad'i, afirgice ta d'ago tana tsala wani ihun,

Batasan lokacin data kama Hanunsaba da sauri KB ya fauce hanunsa yanamata kallon baki da hankali,

Sani ya tsuguna agefe yi hak'uri Khadijah awanke miki saboda jinin yatsaya, ko kallonsa batayiba taci gaba da kukanta,

Kb yasake miko hanu zai samata ai asab'in ta mik'e ta d'aga kwalban hydrogen d'in ta watsa masa ajikinsa ta bar wajen sai da taje k'ofan da zai sadata da sashinsu ta juyo tana share Hawaye tace "Gurgu kawai wlh ban yafeba,


Da sauri Sani yashige d'aki don ya fitar da dariyan da yake k'unshewa, anan yatarar da Iro ma yana k'yak'yata nashi,


Tafe suke shida Sani da yake turashi jifa jifa suna hira sosai yanayin garin ya burgeshi kasncewan yanayin farkon shigan daminane Hadirine ya had'u agarin ya baje sai yabar iska mai dad'i da k'amshin k'asa,


Jifa jifa kuma "yan mata da samari masu zuwa dandali suna wucesu Kabir yakan shagala sosai da kallon tsarin kwlliyansu musamman na "yan matan wani lokacin har yakan d'an murmusa, ahaka suka iso k'ofan gidan, agindin bishiyan dake k'ofan gidan yasa Sani ya ajiyeshi sabo da yanda yake jin dad'in iskan da yake kad'awa, yau cike yake da kewan Maminsa yagaji da raahin ganinta dukda yawan wayan da sukeyi akowani Rana,

Dafe hab'ansa yayi yana tuno Rayuwa step by step,

Hayaniya yaji abayansa ahankali ya juyo yana kallonsu "yan matane guda uku Dijah ce ta Hud'unsu ga dukkan Alamu fad'a sukeyi kuma ayanda ya fahimci fad'an Dijah ce ta arangamo sannan taja gefe tana bada umurnin yanda za'ayi,

Sani ne ya k'arasa wajen bayan yarabane ya tambayi Dijah abunda ya had'asu,

Abunda ya k'ara ba kb da yake sauraronsu mamaki shine ji Da yayi Dijah tace batasan ma me ya had'asuba sosai ya ware ido yana kallonsu agefe d'aya kuma yana mamakin Halinta ga iyayenta dukansu masu Hak'uri da sanin yakamata amma Su sun haifi hatsabibiya fitinanniyan yarinya,

Ajiyan zuciya yayi gami da gajeren tsaki ji yake inama ace a familyn Su take? Tabbas da yajima da karairayata, da b'ab'ballata,


Jerowa sukayi ita da Jebu da wata yarinya dukansu fuskansu yasaha fente2 kala2 banda Dijah don bako d'igon kwalliya afuskanta tun tana mitsila Dijah ta tsani kwalliya yanzu kuwa da ta girma intaga masuyi wani lokacinma dariya take musu, sai dai fa ran da ta tashi da iya shege takanyi haukan kwalliyan da yafi na kowa muni daf da zata shiga Gida taga Su Jebu sunwatse juyowanda zatayi da niyan tambayansu Ina zuwa?, caraf idonta sukayi karo da na Lado, yana murmushi yasha kwalliya sosai irin na gayun Rugan Juma dogon Riga yasa na wata yadi Ruwan k'asa da wando na jeans ya cusa Rigan tagaba acikin wando tabayan kuma yana reto da Hulansa da ake k'ira Rabin hula Kore mai hoton wata da tauraro,

Ga wani matsiyacin kambus da yasa jajazur fuskanshi sai k'yallin mai yakeyi Tabbas Lado yana d'aya daga cikin manyan gayun Rugan Kuma, wannan yana d'aya daga cikin abunda yasa yayi nasaran samun matsayin zamowa saurayin babban yarinya Dijah,


Don acikin Rugan juma samaruka da dama sun gwada sa'ansu agurinta amma basu daceba,


Dijah kam rasa yanda zatasa kanta tayi Don Lado yagama kamata ba halin gudu itakuma ba babban Abun kunya awajenta shine taganta face to face ita da Lado da Ranan Allah gwandama inda daddarene wataran intaga dama takan saurareshi,

Shikuwa Lado ji yakeyi yau ba Wanda yakaishi sa'a gashi ga abar sonsa, sai murmushin farin ciki yakeyi, kamo bakin mayafinta tayi ta rufe gefen fuskanta ta inda yake tsaye sai wasa da yatsunta takeyi kanta a sunkuye shikuma sai lek'o fuskantan yakeyi yana magana,


Kb kam duk yanda yaso ya mayar da dariyansa ya kasa Dan haka ya tallafi hab'anshi da bakinsa yana kallonsu ta gefe,


Sosai yacika da mamakin wannan Rainin Hankalin na Dijah yanda yanzu2 ta dawo kamar mutumiyar kirki,

Don bawanda zai kalleta bayi tunanin da gaske tana da kunyaba, wani k'arin dariyansa shine dressing d'in Lado sannan yagama marairaicewa shi adole yana gaban budurwa,


To wai saboda Allah wannan yarinyan har ta isa tsayuwa da saurayi? Yatambayi kanshi sannan yaja gajeren tsaki, "ai ko saboda tsaban rawan kantama zata fara tsayuwa da samaruka, ya fad'a aransa,



Duk maganan da Lado yakeyi Dijah bata amsa ko d'ayaba kanta yana k'asa Su na ahaka Jebu ta iso wajen ai ganin hankalin Lado ya koma wajen Jebu tasa Dijah tayi wuf tashige cikin gida,







*Ummu Fatima ce?*
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹



*DAMATA! DAMATA!! DAMATA!!! LITTAFIN YA FAD'AKAR YA GAMSAR YA MA'ANAR _SIS BATUL JIN JINA GAREKI πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ» NATAYKI MURNANA KAMMALA WANNA K'AYATACCEN LITAFI MAI SABON SALO ALLAH YAK'ARA BASIRA_*
Muna jiranki asabon buk karkidade kinji😰


πŸ‡³πŸ‡¬




🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 1⃣6⃣



Dr Kabir Yabi hanyan da ta shige da kallo yana murmushi,
Yadawo da kallonsa wajen Lado da Jebu da alamu Complain yakeyi akan Dijahn,
Tab'e bakinsa yayi ya mai da hankali ga wayansa da yake hanunsa,

Sunjima suna tattaunawa kafin suka jero da Lado inda Kb da Sani suke Lado ya gaidasu Sani ne kawai ya amsa, Kabir kam sai wani hura hanci yakeyi haka kawai yaji Ladon yana bashi haushi,
Nika nace "toko don yatsani Dijah ne?πŸ€”

Ganin irin shan k'amshin da yakeyi yasa Lado yin sallama ma Jebu ya wuce yabarta nan suna magana da Sani,
Kb kuwa yacigaba da latse2 wayansa jifa2 kuma yana kallon masu wucewa,
Can ya hango
Bintalo da Ma'au sun fito cikin kwalliya, suna tafiya suna tad'awa, ganin Kabir zaune cikin kekensa ne yasa Bintalo k'arasawa da murmushinta ta masa sannu, Shima cikin murmushi da sakun Fuska ya Amsa mata,

"Mamata wai yau me akeyine haka agarinnan naga kunsha kwalliya kuna yintanan yanuna Inda yaga "yan mata da samari suna yawan yin gurin da yatsansa, tana murmushi tace
"Dandali ake zuwa, Kabir ya marairaita Fuska kaman mai shirinyin Kuka "mamata shine baki gayyaci d'ankiba, zaki tafi kibarashi

Dariya Bintalo tayi mai sauti ta zaga tabaya tafara turashi "bansan kana son zuwaba ne da bazan tafi inbarkaba,


Sunzo daf da Sani zasu wuce yatare keken da k'afansa yana kallon Bintalo "ina zaki kaishi?

Kabir ya Harareshi "Dalla can malam kabamu hanya muwuce Dandalo zamuje muyi rawa, Jebu ta kwashe da dariya har tana rik'e ciki, "Inane kuma Dandalo?

Sosai Kabir yaji haushin dariyan datakemasa, donshi baima lura cewa bai fad'i sunan Dandalin dai2 ba tunaninsa itama "yar rainin Hankalice kaman k'awata shiyasa sam baya sakemata Fuska,


Cikin zafi yace ma Sani Remove ur Leg, matsa musu Sani yayi suka wuce Ma'u tanabiye dasu,
Suna tafiya suna tad'i duk abunda yagani sai yatambayeta Wani lokaci tabashi Amsa wani lokacinkuma Ma'u tabashi Amsan

Ahaka harsuka kai Dandali Nesa da gurin yasata ta'ajiyeshi agindin wani Bishiyan d'orawa,


Suna tsaye awajen Sani da Jebu suka iso, ganin Sani yazo ne yasa Bintalo tace ma Kabir tana zuwa, dama Ma'u kam tuni tashige dandalin,

Taku d'aya tayi ana biyu Sani yasha gabanta, yana mata wani irin kallo,
"yanzu duk tarin samarukanki da suke zuwa gida basu ishekiba? Harsai kinbiyosu nan?

Cike da mamaki Bintalo tazaro ido tana kallonsa,
Yad'an had'a fuska, gami da d'aga gira yace "yes abunda kuke zuwa yi kenan,

Cikin takaici Bintalo tace "duk wanda yacemaka abunda muke zuwa yi kenan yamaka k'arya kaje ka gani wasanni akeyi kala2 sannan kuma "yan wasu rugagen da basu kaimuba sukanzo ayi zumunci,

Had'e rai Sani yayi yace "to bazakijeba, waro ido tayi sosai ta kalleshi babu alamun da wasa yayi maganan,

Turo baki tayi ta kalli Kabir dayacika da tsananin mamakin Sani harwani karkace kai yayi yana lek'a fuskansa,

Dawowa tayi daf da Kabir tatsaya tace Likita inason inje wajen wata k'awatace "yar Rugan lelam,

Murmushi Kabir yayi yace Fatima kinason Sani?

Wara idonta tayi tamasa kallon kaima haka zakamin?

Murmushi yayi ya d'an sassaita muryansa "pls mamata Dagaske nake tambayanki, banison atakuraki inkina da wanda kk so Dole ya hak'ura,


Ahankali Bintalo tafara ja dabaya sannan tajuya cikin nitsuwa takama hanyan Gida, "Fatima!, Kb yak'irata ko juyowa batayiba, Sani ya juya zai bita Kabir ya rik'o hanunsa yace "kai sam baka da kunya wlh,

Sani ya langab'ar da kai yana kallon Kb "kenan tana nufin bata sona?

Kabir ya Harareshi "to meye imbata sonka?

Kaman zaiyi Kuka yace "pls Kabir kataimakeni wlh I really Love her,

Gajeren tsaki kb yaja yace "shikenan kaima kazamo d'an iska irinsu Habib,

Sani ya shafa gashin kansa yana kallon Jebu da take zuwa wurinsu rik'e da leda ahanunta, yace "Kb duk yanda zangayamaka bazaka fahimtaba amma wlh ina sonta sosai,

"Nidai nagaya maka ka daina mun irin wannan magana, inbanda iskanci ba abunda kuka iya kutak'ark'are kuyi ta maganan banza akan k'ananun yara wai kunason su,

Dai dai lokacin Jebu ta iso,
Ledan daya ke hanunta tamik'a ma Sani, ya bud'e yaga Rogo ne yana dariya ya d'auki guda d'aya "Nagode Zainabu har da tsarabane haka?

Murmushi kawai tayi ta mik'a ma Kabir d'aya ledan, kafe Ledan yayi da ido sannan ya tab'e baki yace "baniso d'azu ma wa kk dariyan Rashin kunya,

"Ayyah kayi hak'uri dandalo dakacene yabani dariya, gyad'a kanshi yayi yace nibana cin wannan abun jekici kayanki,
Yad'an lek'a bayanta "Kunyi fad'a da Aminiyanki ce? Naga banganku tareba,
"ai bama fad'a kuma bama rabuwa da Dijah sai awajen zuwa dandali, bata zuwa sai randa taga dama,

Ya tab'e baki meyasa?

"Ra'ayinta ne hakan sam bata jituwa da mutane daga inda mutane suka fi biyar to ita zama acikinsu matsalane awajenta,

Shiyasa ko biki taje bata wuce minti goma awurin zata koma gida,

"Mhmm ai saboda tsaban masifantane shiyasa bazata iya zama da mutaneba hatsabibancinta yayi yawa,

Jebu tace "aifa Dijah ba masifasiffiya bace saidai in mutum bai fahimcetaba, ita dai bata da hak'urine kawai amma bata shiga sabgan mutum, hararanta Kb yayi yace "Eh aibazaki fad'i laifintaba tunda kina tsoronta harkarb'a mata fad'a kkyi,

Sani dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login