Showing 150001 words to 153000 words out of 155892 words

Chapter 51 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

448

hanyan Gidansune, ta shagwab'e Fuska, " Mami muje gida can, Mami ta d'an sassauta Tafiyan, "kina nufin Gidanki ko Gidana?

"Gidanki zan koma Mami wlh tsoron can gidan nakeji, yanzu ni kad'ai akebarina, tayi maganan kaman zatayi kuka, Mami ta juya kan Motan zuwa Gidanta,


Misalin k'arfe Tara na dare ta fito daga wanka ta tsala kwalliyanta, tana zaune ak'asan Capet tana waya da Bintalo,

Kabir ya bud'e k'ofan ya shigo, ya zauna a k'asa kusa da k'afanta yana kallon k'afan sun kunbura sumtum, ya jawo pillow ya kama k'afan ya mik'ar dasu akan pillown, yana d'an matsamata su, wayanta taketayi abunta, can anjima ya rik'o Hanuta ya amshe wayan ya kara a kunnensa, "Helo Aunty Binta, ina wuni, ya Boy? .... Masha Allah, saida safe zamu k'iraki, ...OK .. Ya kashe wayan ya ajiye, yana kallonta,

"Khadijah bana hanaki dogon waya hakaba, karkiyadda ink'arajin kinyi wayan da ya wuce 10 minutes,


Ta langab'ar da kai, " OK my luv zan kiyaye, ya maijikin?

"Mhhn wa nakama?
" Ni wlh,
Dan Allah kayi hak'uri, ta fad'a da iya shege,

"Mhmm hukuncinki sai a Bed yarinya, tashi mu koma gidanmu, dare nayi,

"A'a Likita Mami tace in zauna sai Aunty Nafisa ta samu sauk'i ansallameta sai mukoma tare, lokacin ka samu nitsuwa, wlh tsoron Gidan nakeji,

" OK haka kika shirya? To ai sai muzaunamata duka agidan, ya k'arashe maganan yana cire Riga, ya tashi yaje Yayi wa d'akin key, yazo yajata sukayi Gado,

(nikan dai fita nayi ta window da gudu) πŸ™ˆ

Washi gari mutanen Maiduguri sukazo gaisuwa da Jaje, daga cikinsu harda lya, aranane kuma jikin Nafisa yadad'a zafi, duk Wanda yaganta sai yakaraya,

Tana kwance Har yanzu bakinta bai rabuwa da istigfari,


Wasu daga cikin dangin Mamanta da kuka suka koma gidan Mami, anan akabar lya, da Dare Iya ta d'agata da k'yar tasata tad'anci Abinci, ta mik'amata maganinta tabata Ruwa sannan ta zauna ta maida hankali ga kallon T.Vn da yake kunne ad'akin, tace "kisha Maganin, ki kwanta Nafisa, yau ki hak'ura da Sallahn Darennan kisamu kiyi Bacci haka, kinga Likita yace damuwa da Rashin Bacci sun miki yawa, Nafisa tad'an Murmusa, tace" lya wai ina d'an kalatane ko Allah zaiji tausayina, lya kinsan yanda Na gudanar da Rayawuta, ina tsoron had'uwana da mahaliccina lya!

"Allah ya kasance mai Rahma Nafisa insha Allah zai gafartamiki ki kwantar.... Photon da aka nuno a T.V yahana ta k'arashe maganarta,


*" Jama'a masu kallonmu da sauraro ajiyane dai aka tsinci gawar wannan Baiwar Allahn da kuke ganin photonta a T.V, akan Hanyar Shiga wani k'auye can cikin Maiduguri, ayashe akan hanya, Wanda akezargin wasu 'yan mafiyane suka satota, sakamakon samun pert pert d'in jikinta da a kaga babu, Anan k'auyen kuma aka binneta, saboda wari da tafarayi, Dan haka gidan TVn na Maiduguri suka kawo mana wannan Rahoto ayad'a ko ina, kasancewan ba'asan daga inda tafitoba,.......

Innalillahi wa inna ialaihirraji'un Kalman da iya tayi ta maimaitawa kenan, har Nafisa da tayi suman zaunema tasamu daman karb'an kalman itama abakinta, kafin ta b'arke da wani irin kuka mai cin rai, lya kam tagumi ta rafka tana kallonta cikin tsantsan tausayi, ta rasa da wani kalma zata bata Hak'uri,

Sai da tayi kukan har tarasa yanda zatasa Ranta,

Iya ta shiga bata baki, Gami da Nasiha mai ratsa zuciya da gangan jiki,

kusan raba dare sukayi ahaka, kafin Nafisa ta Rarrafa tashiga bayi ta d'auro Alola tafara jero salloli kaman yanda ta saba tun zuwanta Asibitin, Ahaka har gari yawaye, bayan tayi sallahn Asuba da karatun k'ur'ani, ta haye Gado, idonta a rufe yake anma hawaye na gangarowa, can anjima taji 'yan uwanta na Maiduguri sunzo,

Tanji sukayi ta jajanta irin Mutuwan Mamantan tun tanajinsu sama sama har Bacci ya d'auketa,

Can Bayan an sauk'o daga sallahn juma'ah kasancewan yau juma'ane kusan la'asar Hayaniyan Abbanta, ya d'agata daga Bacci, da wani irin zazzab'i mai tsanani ta farka, da k'yar ta iya tashi ta zauna tana kallonsa,

"Yauwa Nafisa kinajina ko? Kinga Mahaifiyarki ta Rasu ko? To zaman garinnan bai kamamuba, tafiya zamuyi, zan canza shiri, dan haka dole zamu bar garinnan, yanzu haka su Kila suna hanu, na tabbata idan aka matsa suna na zai fito a cikin case d'in, gwanda mu canza dabara,


Cikin Kuka Nafisa tace " Dady kayi Hak'uri ka ajiye wannan halin, kayarda haka Allah ya k'addaro maka Rayuwarka baka isa sauyata ba, Dace dabara, hikima, ko mugunta nasa ayi arzik'i da yanzu duk dukiyan Kabir na hanunka, Dan Allah Dady kaji tsoron Allah kanimi gafaran mahalliccinka ka nimi gafaran Kabir da Mahaifiyarasa, Ka canza halinka, Mutuwa fa bata sallama ma bawa duk lokacin da aka aikota zuwa kawai zatayi,

"Ke Nafisa bana son shirmen banza kina nufin in k'ask'antar da kaina agaban Kabir da Fatima? Sannan inbada kaina ga Hukuma, ba zai yiwuba, Dan haka ki shirya kawai Gobe zanzo mutafi, ya juya da sauri ya fita, ta d'aga Hanu tana k'iransa "Dady Dan Allah ka tsaya kaji, kar katafi, ta rushe da kuka gami da wani irin tari,

Dai dai lokacin Kabir ya shigo da takardan sakamakon gwajin da akayimata, fuskansa a birkice yake yana duba takardan, Sam bai kula da Dijah da take shigowa ta d'aya k'ofanba,

Yazo ya dafa gadon Da Hanunsa duka biyu yana kallonta akwance,

" me kikasa aranki haka Nafisa? Bana ce kidaina yawan tunani hakaba, kinga sakamakonki kuwa,

Bakinsa kawai Nafisa take kallo cikin wani irin yanayi ta kamo Hanunsa ta damk'e a cikin nata tad'an saki wahalallen murmushi, murya a shak'e tace "Yayana Dama kana sona?

Ya k'ara matsota yana kallonta, cikin karyayyen murya mai sanyi, yace " Ina sonki Nafisa, wlh ina sonki, ban tab'a k'ink'iba, ko dama halinki nake k'i ayanzu kin sauya Nafisa, ki kwantar da Hankali ki samu sauk'i zaki gaskata cewa ni Masoyinkine,

"Bakasona yaya Khadijah kakeso da bakinka kagayamin,


"Kece masoyiyata Nafisa Khadijah masoyiyar Mamice, ko kinmanta Mami ce ta auramin ita, kece wacce nazab'a kuma na Amince da kaina zan aura, me kikeson inmiki dan ki gaskatani?,

Nafisa tasa d'ayan Hanunta ta share hawayen da yagangaromata, tace " ba wannan lokacin, na yarda da kai, nima da Soyayyarka zan mutu, ta mik'a Hanun ta kamo Hanun Dijah data iso, ta had'e Hanun dana KB ta d'aura akan k'irjinta ta danne d'aya Hanunta, tana kallonsu cikin kuka, ta fara magana a sanyaye, "Khadijah kinyi sa'an samun Nagarcaccen miji mai Sonki da k'aunanki, ki rik'eshi hanu biyu, kimasa biyyaya, ki nimi Aljannanki da gaske, Nagode da yafemin da kukayi, dan Allah Ku cigaba Damin Addu'ah, kar kumantani a rayuwanku, Ina muku fatan Alkhairi, Allah ya k'ara kareku yabaku zuri'ah mai Albarka,

Ji tayi hawaye na d'iga d'is d'is akan Hanun ta da ta had'e hannayensu, ta d'ago ta kalli Dijah da fuskanta yagama had'ewa da zufa da hawaye, ta d'ago hanu ta sharemata tana girgiza kai zatayi magana kenan tari ya kamata, iya ta taso tazo jikin gadon ta tsaya, a sanyaye ta fara salati,

*La'ilah ha 'illallah Muhammadur Rasulullah sallallahu Alaihi wasallam,*

Fad'a take tana maimaitawa, can Anjima sukaji Nafisanma ta cafa, tafara, tana zuwa k'arse su kaji kaman an finciketa a hanunsu, kanta Yayi k'asa,


*Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati Hazihi wakhlifhni khairan minha,*

Kabir ya fad'a gami da share k'ollahn da yangangaro cikin gemunsa, ya zare Hannunsa cikin nasu da ta had'e Dana Dijah, yasa Hanunsa a cikin Ruwa ya rufemata idanunta, yaja zanin da ta rufe Rabin jikinta dashi ya rufeta kirif, da k'yar ya d'aga k'afansa ya juya, Dijah da tayi suman tsaye, tayi saurin rik'oshi cikin kuka tace "Likita bangane ka rufeta har fuskantaba, meye hakan yake nufi,?

Kabira ya dafa kafad'anta, " Khadijah Nafisa ta rigamu gidan gaskiya tabarmu da sauran barka Sai dai muyi fatan Allah yamata Rahmah mukuma yabamu sa'an taddata,

*Innalillahi* Dijah ta fad'a cikin k'araji ta sunkuya ta rik'e maranta, ta saki k'ara tana dafe da mara, lya da take gefe tana sharan k'0llah ta k'araso da sauri zata rik'eta Kabir ya rigata, yana fad'in Subhanallahi Khadijah, dai dai lokacin Mami ta shigo, hankalinta yana ga Gadon Nafisa da taga an rufeta, Sai da taje ga gadon ta bud'e fuskanta tagani, sannan ta juyo ga Dijah,

Cikin kuka tace "Kabir kaita Labour Room,

Cikin sauri ya ciccib'eta Yayi Labour room da ita,

Ya dawo ya jingine kansa da bango yarasa me zaiyi, wani irin zafi da gumi yakeji a cikin jikinsa,


😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭


*Ummu Fatima ce* πŸ˜πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ¦‹πŸ¦‹



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


_Naga wasu masu katsalandan sun cigaba da Rubuta wannan littafin bansan dalilinsu nayin hakanba Gaskiya banji dad'iba, Da kun barni nida kainma zan k'arasa kayana, har ga Allah bakumin adalciba, kun raba ma fans d'ina hankali,_


Jinjina ga *wannan shaharriyar k'ungiya mai Albarka _kainuwa dashen Allah da duk d'aukancin marubutan cikinta nabaku wannan page kyauta_ Allah yak'ara hazak'a da Basira*

Bazan mantakuba *ANATARE* WRITERS Kuna Birnin Raina jinjina gareku Baki d'ayanku, anatate🀝🏿

7⃣9⃣

Rayuwa kenan duk Wanda ya d'iba a da zafi, Bahaushe yace bakinsa, lallai Duniya Duk wanda ya baza kolinsa ya manta ranan kwashewa, ya gafala, babu komai cikinta sai jarabawa kala kala, Da danasi mai tarin yawa,



Kabir Yazuba ma masu fita da Gawan ido, Rayuwar Nafisa tun tana yarinya sai dawomasa yakeyi, ya dinga jiyo sautin muryanta kala kala, a k'wak'walwansa, da Muryanta na Wal wala, Dana fad'a Dana shagwab'a intasoyi, Ya tuno irin gayu da sanya tufafi masu tsada da takeyi yau gata acikin farin yadin da kud'insa bai kai ya kawoba, Da irin motan da take burin kullum a sayamata ta hau, yau gata a cikin motan d'iban ice da kayayyaki, tayi Rayuwa cikin makeken Gida Da gadonta da Katifa ga shifid'a mai taushi, yau cikin k'asa zata kwana, ba ko tabarman da kake ganin kafi k'arfin kwana akanta, bare Pillow, za'aje a sakata acikin k'asan da ko juyi bazaka iyaba, babu komi cikinta sai abunda kikazo dashi, inkinga fari dashi kika zo inkinga bak'i da kayanki kikazo,


Yasa Hanu yana share k'wallan da yagangaromasa, ya dafa k'irjinsa, nashi ranan mutuwan yahaue tunawa, nima ina hanya Nafisa ko yau ko gobe, ko yanzu, ko anjima, zan biyoki,



Yaji gaba d'aya komi na Rayuwan ya fitamasa akai,

Lallai Mutuwa wata wa'azice da aya ga Bayin Allah, anma sai Wanda ya lura da Hakan,


Uncle Musa ya dafa kafad'ansa, "Kayi Hak'uri Kabir, kaje ka rakata makoncinta, ko wani mai rai abunda yake jira kenan, Allah yabamu sa'an taddata,


Ba musu yanufi motan Gawan, A tsakiyan Habib da Sani ya zauna, Gaba d'ayansu sun rafka tagumi acikin motan sun k'ura ma gawan Nafisa ido, kaman wasa kaman gaske, kaman amafarki suke kallon abun,

(ahaka suka binne Nafisa cikin Gidan da yake jirana yake jiranki mai karatu) 😭




"Mami da gaske Aunty Nafisa ta rasu? Dijah tayi tambayan cikin zubda k'ollah,

Mami tayi wani Murmushi mai d'auke da alhini kala2, ta maida kallonta ga santaleliyan Babyn da take Hanunta, mai kama da Mahaifinta kaman Yayi kakinta,


" tsakaninmu da Nafisa sai Addu'ah Khadijah, sai kuma jimamin ta inda tamu zata riskemu, Rai d'ayane inyafita shikenan ba waninsa, Allah yasa hakan yazamo izna garemu,



Khadijah tasa Hanu ta toshe bakinta, Dan wani irin kukane taji na shirin kufcemata, Mami ta girgiza kanta, "kinsanifa Khadijah tsananta kuka ga Mamaci Haramunne,

Hak'uri yazamo mana Dole, Duk Duniya bayan Kabir ba Wanda na zauna da shi muka shak'u da ya wuce Nafisa, ba yanda muka iya Allah baya barin wani Dan wani, Kowani mai rai sai ya d'and'ana zak'in mutuwa,


Dai dai lokacin Kabir suka shigo da lya, Jikin gadon Dijah ya iso kai tsaye, ya Dubeta fuskansa d'auke da d'an Murmushin k'arfin Hali,

" Sannu Khadijah yaya jikin?
"Da sauk'i tace tana d'an Jan hanci, "Allah ya k'ara sauk'i, yanzu meye matsalanki?
" Babu,
"Ba inda yake miki ciwo?
" Eh,
"OK, Babynfa?
Shiru tayi batace komiba, ya d'anyi murmushi ya matso wajen Mami da take tabinsa da kallon tausayi, jiya jiya kawai, anma yagama fita a hayyacinsa, duk ya rame,

" Sannu Mami, ya fad'a yana mik'a Hanu abashi babyn, ta mik'amasa ita tana fad'in
"Sannu Kabir, ya k'arin Hak'urin?
Allhamdulillah Mami, ya me sunankin lafiya take ko?

Mami tayi murmushi, " Mai sunana kuma? Har kamata Suna? Nazaci Zakasa Nafisa Kabir,


"No Mami wannan da Sunanta tazo, sai agaba Khadijah zatayima Nafisan mai Suna, ya fad'a yana mai da kallonsa ga Khadija cikin zolaya, Dihah kam kanta yana k'asa, tana matsa yatsunta,


Iya tace " Kai Kabiru baka da ta idofa, Murmushi kawai Yayi yana mik'ama Mami babyn,


"Mami inba wata matsala barin sa Asallameku kukoma gida, saboda masu zuwa ta'aziyya, dai2 lokacin Sauda da Bintalo suka shigo, shikuma ya fita, ya mufi of is d'insu,




Allah mai girma da d'aukaka, Randa Kabar Duniyannan aranan wani zai shigota,

A yau Nafisa ta cika kwana 7 a Cikin k'asa, a yaune kuma aka sha bikin Sunan yar Gidan Dijahn Baffah wacce taci Sunan Mami, wato Fatima Zarah, ba'ayi wani Bidiri sosaiba saboda mutuwannan,


Hidimane akayi na Girma da Alfarma, ba'a tsanantaba, Mai jego da jaririya Sun zama tamkar sabon wata, had'uwa iya had'uwa sunyi,duk ta inda suka gifta Ido nakansu,Hotuna kuwa Dijah rasa na wa zata tsayama tayi,



Washi Gari kuwa Mami ta shirya k'ayataccen walimah daya had'a y'an'uwa da Abokan arzik'i, Kabir da Khadijah nagano sanye cikin dakakkiyar shaddah marum kala, yana rik'e da baby Zarah da itama aka shiryata cikin marum d'in baby Gawn mai ratsin fari,


Fuskansa d'auke da murmushi, ya d'an rank'wafo jikin Dijah yana mata magana, abundai sai Wanda yagani,


Anci ansha ba acewa komi, ahaka aka waste, a washi gari y'an rugan juma suka d'auki hanya da tsaraba kala2,



Sannu ahankali rayuwa take juyawa, kwanci tashi ba wuya a wajen Allah, ayau Dijah take da kwana arba'in da biyu da haihuwa, Zarah ta girma sosai tayi wayo,

Ayaud'innekuma take ta shirin zuwa ruga kaman yanda Mami tamata alk'awari,


Cikin farin ciki da d'oki ta gama shirinta tsaf cikin popul d'in lallausan leshi mai ratsin milk da Gold colour, ta fito da mayafinta milk da takalmi da jakanta Gold, tana Rungume da Baby Zarah da aka shiryata cikin Riga da wando Gold and Milk colour,



Mami ta kallesu cikeda murmushi itanma murmushin takeyi tace Mami mungama,
"To Khadijah 'yar gidan Baffah, yau kam kanwa ta kar tsami k'warnafi ya kwanta,

Yau gaki ga Baffanki, Dijah ta sunkuyar da kai k'asa tana murmushi,


"To Allah ya kare Khadijah, Dan Allah ki kulamin da Zarah, ko wani safiya ki dafa kanta kimata Addu'ah, Dan Allah karki shagala kinji?


Cikin jin kunya Dijah ta gyad'a kai, tare suka fito haraban gidan Mami tana rik'e da Zarah har jikin motan da aka shak'e da tsaraba kala2 Dijah ta shiga ta zauna kafin Mami ta mik'omata Zarah tana musu fatan Allah ya kiyaye hanya, gami da k'ara nanatamata sak'on gaisuwanta gasu Baffah da sauran jama'ah,


Tana tsaye tana d'aga musu hanu, har motan ta fice agidan, ta juya cikin sanyin jiki, ji take zatayi kewansu ba kad'anba Gida yamata sayau da yawa dukda Iya tana nan,


Ummu fatimace πŸ˜˜πŸ˜πŸ€πŸΏπŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ¦‹πŸ¦‹



🌈 *KAINUWA WRITTERS ASSOCIATION*.......πŸ–Š


πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š

*Dasunan Allah mai Rahma mai jin k'ai*

*Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah*

Komai Yayi farko yana da k'arshe, nagode ma Allah mad'aukakin sarki da yanunamin wannan Rana na k'arshen wannan Littafi,

Don Girman Allah duk Wanda ya karanta wannan labri yaji dad'insa, ya nimamin gafaran mahallicinmu ya yafemin kurakuran da nayi a cikinsa, na rok'eku badan halinaba, Don Girman mahaliccinmuπŸ‘ 😭😭😭😭😭😭😭

Duk Wanda kuma yaga wani kuskure acikinsa Don girman Allah yasanar dani ta hanyar da ta dace, cin mutunci da muzanta musulmi bana musulmibane, Dan Allah 'yan'uwa mukula, wlh ni ashirye nake na karb'i gyara daga gareku, ta kykkyawar fuska,


Inaji daku masoyana ina k'ara niman gafara gareku ina kuma Addu'an Allah ya gafartamana baki d'ayanmu, nida na Rubuta daku dakuka karanta,



Dafatan zamuyi amfani da Abubuwan ciki masu amfani muyi watsi da shirmen dake cikin,


Ku tareni cikin littafina mai Suna
❀ *ABINCIN ZUCIYATA*❀

Littafin yazo da salo kala kala, maraici, tausayi, nishad'i ta k'awa kirsa da zazzafan Soyayya, da sauransu karku manta

*Abincin Zuciyata* yana nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login