Showing 135001 words to 138000 words out of 155892 words
🦋 🦋 🦋
*UMMU FATIMA CE*🦋🦋
🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......🖊
*Wai dan Allah yaushe za'a daina niman _Dijah Qayah_ daga farko ne? Har yanxu Kusan kullum sai na samu masu bina wai inbasu daga farko ko daga 37* 🤔🤔🤔
*Jinjina gareki Dougterna 'yar Albarka Hauwa ta kaina manajar Dijah Qayah ina godiya gareki tare da yawun dubbannin ma biya wannan buk da baki gajiya da basu duk page din dasuka nima* 😍😘👍🏻
*Gaisuwa gareki Maman 4 ta gidan Huguma* *Masoyiyar Dijah da marubiciyan Dijah*
*My Hannah Rabi'u ma tana jinjina gareki tare da mik'o gaisuwarta gareki*
*Ummu Fatima conversation group wannan page gaba d'aya nakune ku dukanku wlh inayinku Nagode matik'a da irin so da k'aunanku gareni* 😍😘😘😘😘😘
7⃣1⃣
Tajima tsaye bakin k'ofansa cikin fargaba kafin ta k'onk'osa, tsawon lokaci tana k'onk'osawa taji anbud'e k'ofan ba tare da anyi maganaba,
D'aure yake da Towel iya kunkuminsa yayinda wani k'arami ke rataye a kafad'ansa, Ruwa na tsiyaya ajikinsa da Alamun daga wanka yafito yanzu, ganinta tsaye yasa yad'an yamutsa fuska yana kallonta alamun saurara,
Tayi saurin sadda kanta k'asa tanajin wani abu na mata yawo acikin jikinta,
Murya asark'e tace "Mhhmm dama Mamice taxo tana son ganinka, shiru yayi kaman mai tunani, Sannan ya maida k'ofan ya rufe ba tare da yace komiba,
Ta juya a sanyaye ta koma,
Mami tana zaune cikin kujera Bakinta d'auke da Addu'o'i kala2 Dijah ta shigo,
"Mami yana wanka, kai kawai Mamin ta gyad'a Tace kawomin Cup,
Tashiga kitchen ta d'auko mata ta bata,
Mami ta d'auko Ruwan Zam2 ajakanta ta bud'e ta juye a cup d'in, ta shiga karanto ayoyi tana tofawa aciki, har tagama ta ajiye Kabir bai shigoba, Mami ta tashi ta d'auki Ruwan zam zam ad'in takalli Dijah, "Muje ki kaini wajen nashi,
Dijah tana gaba Mami tana biye da ita,
Cikin kasada da k'undunbala, Ta tura k'ofan ta shiga ba tare da ta nimi iziniba, yana zaune a saman Kujera sanye da Jallabiya Ash ma dogon Hanu, Nafisa tana zaune kusa dashi ta d'ora k'afanta a kan cinyansa,
A zabure ta Mulmulo wani K'aton Ashar ta wurgoma Dijah ta d'aura da cewa "Ke iskancinkin har yakai haka? Yuashe Rashin kunyankin yakai har nan?
Da zaki shigomin d'akin miji kai tsaye haka,
Dijah ta wurgamata wulak'ancaccen kallo ta juya ta kalli Mami, "Bismillah Mami shigo,
Mamin ta shigo sannan Dijah ta maida k'ofan ta rufe ta Kujeran da yake Fuskantansa Mami ta zauna, Dijah ta zauna kusa da k'afansa ak'asa, Murya k'asa2 tace "Honey kasauk'o ka gaida Mami, a hankali ya zamo k'asa ya zauna kansa ak'asa,
Mami ta mik'o masa cup d'in da ta shigo dashi "karb'i wannan kasha Kabir kafin mugaisa, Dijah ta karb'a ta mik'a masa rai ahad'e ya karb'a zai kai bakinsa Dijah tayi saurin rik'ewa "Likita bakayi Bismillah Yayi Bismllahn sannan yasha duka ya mik'amata cup d'in,
Yadinga ajiyan Zuciya akai2
Nafisa taja Dogon tsaki tace "aikin Banza aikin wofi,
Ko kallon indatake Mami batayiba, ldonta naKan Kabir da ta lura nitsuwa ya d'an shiga jikinsa, Cikin wani irin yanayi kansa ak'asa ya fara gaidata Bata Amsa gaisuwanba, tace "Kabir kayi sakaci da Rayuwanka, kabari shaid'anu suna k'ok'arin yin nasara akan ka,
Ahankali ya d'ago ya kalleta, "Bahaka bane Mami,
"Hakanemana Kabir Kana karanta Qur'ani kowani Safiya kaman yanda kasaba?
"Wlh Mami yanayin aikinane da ya canza sam bana samun zama, Bancika karatunba Gaskiya,
. Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un Mami ta dinga fad'a tana nanatawa har sau Uku,
"Kabir yanzu a duniya akwai wani abu da zai d'auke hankalinka har ka ajiye karatun Qur'ani saboda baka da lokaci? Ka kasa waran 5 Minuts cikin time d'inka ka karanta Qur'ani? Yaushe Rabon da kayi nafila kuma koda raka'a Biyu ne?
Yad'anyi Shiru yanason tuna ranan,
Mami ta Girgixa kai "Bakada gata ko wani kariya da ya wuce Qur'ani Kabir, daga inda ka nisanta kanka da Qur'ani to ka nisanta kanka da Ubangijinkane, Inko hakane komi na iya faruwa da kai,
Kana da Mak'iya da miyagun Mutane Mushirikai masu niman duniya ahanun wanin Allah bai kamata kayi sakaci da Rayuwanka hakaba, kabari suna shirin cinma mummunan k'udurinsu akanka,
Nafisa tace "Gaskiya Ni inma wannan maganganun dani ake Allah zai sakamin dan nasan so ake kawai a rabani da mijina dan Munafunci, A fusace Kabir ya zabura yayi kanta, Mami tayi saurin dakatar dashi,
"Ko dawasa Kabir banyardaba, Karma ka fara, jikinsa na k'yarma ya nunata da yatsa, "Wa Mahaifiyar tawa kk wannan Lafazin Nafisa?
"Yafa isa nace maka tashi karakani ni zan wuce, a tare suka tashi gaba d'aya suka fita sukabar Nafisa anan zuciyarta fal tsoro ba dai a sirin har ya karyeba?
A jikin mota Mami tayi ta musu fad'a gami da Nasiha na sakaci da Azkar da sukayi, Sannan ta Sallami Kabir, yana tafiya ta kalli Dijah,
"Ke kuma Khadijah Meyasa da kika al'amuran Gidanki sun canza baki sanar daniba? Anyah Khadijah kin d'aukeni a matsayin Mahaifiyarki kuwa?
Cikin Muryan kuka Dijah tace "Allah Mami Bahakabane Banson ind'agamiki Hankaline nazaci wani laifi namasa ya dawomin haka, nayi zaton in ya huce zamu dawo Normal,
Mami ta sauk'e ajiyan Zuciya, Jeki d'auko hijabinki kizo, ba musu ta juya ta d'auko suka fita tare,
Cikin tashin Hankali Kabir ya samu Nafisa tana ta niman wayan Mamanta tarasa, tana ganinsa ta tashi ta fad'a jikinsa ya rungumeta yana shafa bayansa,
"Sory Babyna Banso b'atamiki raiba, Anma abunda kika fad'a agaban Mami Kuskurene dan Allah kar kikuma kiniji?
"Anma kai bakaji me take gayaminbane?
"Rabu da ita kinsan Mami yanzu sai ahankali ta fara tsufa,
***********
Mami suna fita basu tsaya ko inaba sai Gidan shiek Aminu wani malamin Ahlisunnah, Ba b'ata lokaci tamishi bayanin Abindake tafe da ita,
Cikin k'ank'anin Lokaci ya had'a musu magunguna da ganyen Magarya dasu zamzam, Ya mata bayanin yanda zasuyi Amfani dashi, suna fitowa Mami tayi waya ma Sani tace yazo Dijah ta gayamasa duk abin da bata dashi ya kawo mata,
***********
Washi gari Dijah tana zaune a palour sai Ga Binta da Sani, ba k'aramin dad'in ganin 'yar'uwar nata tayiba,
Nan tayi bayani Ma Sani na duk abunda take buk'ata, Ba b'ata lokaci ya je ya kawo duk abunda ta gayamasa, Bintace ta tayata suka gyara stor d'in suka shirya komi, suka shiga Bed room Dijah tace tana son sujuya gadon ta jima bata juyashiba,
Nan suka fara k'ok'arin juya d'akin Suka d'aga katifa, a firgice Dijah ta saki salati ganin layoyi a jere a k'asan katifanta, ba k'aramin firgita sukayiba dukansu Bintace tayi k'arfin halin samun leda tayi Bismillah ta taresu guri d'aya tasa acikin ledan ta k'ulle ta wurga ajakanta, a tsorace Dijah tace Aunty Binta meyasa kika a cikin jakanki baki tsoro?
"Zan tafi dashi gidnmu ink'ona Dijah ba abunda zai sameni da ikon Allah,
Cikin sanyin Jiki suka gama gyaran D'akin fes suka gyara ko ina, Dijah ta banka hayak'in habbatus sauda maganin Shaid'anu, Sai da akayi la'asar Sani yazo d'aukan Binta, a tare suka fito da Dijah,
Can suka hango Nafisa da Meena suna k'usk'us, Har jikin mota ta rakata saida taga fitansu ta jujo,
"waini Nafisa mekikeyi agidannane Kika bar wannan yarinyan har tana shirin koranki agidan?
"Cike da masifa Nafisa tace "ta koreni fa kikace To bari kiji wannan ita da babu yanzu d'aya suke agidannan, Kuma d'an lokaci kad'an nake jira tayi gaba,
"Mhmm nidai banga alamaba tunda gashi kinbarta ta rab'u miki da Miji har ya d'irka mata ciki,
Azabure Nafisa ta tashi tsaye "ci... Me? Wlh k'aryane ba cikibane bata isa tayi ciki a gidannanba sai dai shege ke wlh bazaima yiwuba, zakisa inshak'eta yanxu ta mutu,
Gaba d'aya ta fita a hayyacinta ta fara sambatu dan itama tun fitowan Dijahn ta hasasu cikin,
Meena ta rik'e Hanunta "Ke Nafisa ki dawo hayyacinki, ki d'auki mataki dan ciki kam cikine ajikin Yarinyannan,
A kid'ime Nafisan tayi kan Dijah sai dai kafin takai wurinta ta b'ace maganinita tsaban kid'ima batama lura ina ta shigaba,
A gigice ta dawo ko takan Meena bata biba ta shiga mota ta fice agidan,
********
Dijah kuwa tana shiga ta d'auki Had'in Maganin KB tayi sashinsa zaune ta sameshi ya rafaka tagumi ga Qur'ani ahanunsa, cikin nitsuwa take takunta ya kafeta da ido har ta isoshi, ta d'an durk'usa kusa dashi,
"Honey na barka da warhaka, yau baka sha maganinkaba ta fad'a tana mik'amasa, ya ajiye Qur'anin agefensa ya karb'a yayi Bismillah ya fara sha idonsa na kanta yayin da ita kuma ta zuba ma T.V ido tana kallonsa da gefen ido,
Yanagama sha ya ajiye cup d'in ta kalleshi, gami da mik'omasa na shafawan,
"Inshafamaka ko zaka sahafa?
Kallonta kawai yake tayi tayi murmushi tafara shafamasa, caraf ya kamo hanunta yana shanshanan Hanun,
Ta zuba masa ido tana kallonsa kawai tanajin wani abu na tsargamata,
Cikin wani irin Voice yace "Khadijah me yake faruwa da Rayuwana??
"Me kagani?
"nakanjini kaman baniba zuciyata sai ta dinga min zafi game da duk wanda nake alak'a dashi mussamman ke da Mamina, Nakanyi k'ok'arin cire hakan araina anma sai ya gagara, sai dai kwannan nan Naji sauk'in hakan araina,
Dijah ta d'anyi Murmushi cikin tausayi tace "Komi zai wuce insha Allah, ta mik'e zata tafi ya mik'a hanu zai kamota tayi saurin kaucewa ta wuce yabita da ido, har ta b'ace ma ganinsa ya sauk'e Ajiyan zuciya ya jingina bayansa da kujera ya cigaba da karatunsa,
***********
Cikin k'araji Nafisa taketa rafka k'ira ma Mamanta, har ta isa gareta,
"Mama yarinyannan cikine da ita wai yaushe za'agama wannan case d'inne? Nagaji wlh,
A rud'e Maman ta tashi "Ciki????
"Wlh mama cikine da ita, wlh yau sai na kashe yarinyannan cikin dare kowa ya huta,
"Kar kiyi haka Nafisa barni dasu wlh wlh i har na haifu cikin uwa da ubana sai naga k'arshensu su ayau d'innan zan sa azubaar da cikin daga nan akashe shegiya mu huta da matsala,
Ta sure gyalenta "Natafi wajen Boka na Hanyan Jos,
Nafisa tabi bayanta suka fita tare ga dubu Hamsin ki k'ara da na Hanunki in anzo aikin ahad'a harda Maminnan, dan naga tanaso ta kawomin rainin Hankali,
"Barni dasu duka nasan yanda zanyi dasu, Daga haka Suka rabu, Nafisa ta tafi gidanta Mamanta ta nufi Hanyan Jos wajen Boka,
Tana shigowa gida kai tsaye d'akin Dijah ta nufa ji take kafin Boka ya kashetama yau zata kasheta, ko tahalin k'ak'a
*Ummu Fatima ce* 😘
[10/12, 2:58 AM] Ummu Fatyma: 🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋
*DIJAH* *QAYA*
🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋
*BY ASMA'U GALADIMA*
🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿
🦋 🦋
🦋 🦋 🦋 🦋
*UMMU FATIMA CE*🦋🦋
🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......🖊
*Ina kike Mariam Tijjani Adam (Admeen na Taurarin Mata Group)*
Keda *My Aminiya Khady Pinky* 'yar Amana (Maman Sirikata) 😍😘❤❤❤
*Na sadaukar muku da wannan page gab'a d'ayansa kuda Members na TaurarIn Mata gaba d'ayansu* Luve U oll😘❤
7⃣2⃣
Dijah tana kitchen tana shirya lafiyayyen Abinci ma Mijinta dan ta lura yunwama yataka Muhimmiyar Rawa wajen Raman da ya bayyana a jikinsa,
Kaman daga sama taji ana Bubbuga k'ofanta kaman za'a karya, Gami da aikomata Manya2 Ashar,
Daga farko ba k'aramin Razana tayiba, afirgice ta fito daga kitchen d'in, saidai daga Baya da tafahimci Mai aikata hakan sai kawai tad'an Murmusa ta k'arasa jikin Window ta zuge Glass ta lek'a, cikin Kwancacciyan Murya tace *"Subhanallahi Allahumma Ajirni fi Musibaty Hazah* Aunty Nafisa lfy? Wa..
Kafinta k'arasa Nafisa ta matso Window "Dan Ubanki inkin isa ki bud'e k'ofannan wlh kasheki zanyi, yau badai ki kwana aduniyaba
Dijah tayi Dariya mai sauti tace "Haba Aunty na Kinsan kuwa Hukuncin wanda ya kashe d'a'uwansa Musulmi a Musulunci?
Na farko inkin kasheni Duk laifin dana aikata a doron k'asa Yana wuyanki,
Allah S.W.T *"yace Duk wanda ya kashe Mu'umini da gangan, Sakamakonsa Wutan Jahannama har Abada"*
Mutuwa Dolene tanan mak'ale dani idan wa'adina yayi xan mutu ko baki zamo sanadinaba, ki kwantar da hankalinki,
Inanima miki tsari da aikata wannan Mummunan aiki fatana dani dake Muyi tsaftacacciyar Rayuwa a Duniya Mu muta mushiga Aljannah tare da Mijinmu Auntyna,
Wani irin Kallo Nafisan tabi Dijah dashi da Alama Maganan ya d'an shiga jikinta, jikinta yad'anyi Sanyi kad'an, tayi k'uta ta gyad'a kai "Wlh zankamaki Zaki gane dani kikeyi, ta juya fuuu ta shiga sashenta,
Dijah tayi Murmushi tana gyaran Glass d'in Windown tace "Aunty Nafisa Manya Allah ya sassautamiki tsananin kishin dake damunki, Kaman yanda ya Sassautamin nawa,
Ta koma kitchen taci gaba da aikinta, tana gamawa ta Salla wanka tayi gayunta cikin Doguwar Rigan Atamfa mai k'aramin Hanu, ta yane kanta da d'an k'aramin gyale iya Wuyanta, sai baza k'amshi take mai dad'in shak'a,
Ta jera Abincin Acikin Basket ta k'ofan pert d'inta tashiga sashin KB, Yana kwance Luf cikin tree seater Hanunsa Rik'e da Littafin Addu'o'in da Mami ta Bashi d'azu da yaje Gidanta, d'aya Hannunsan kuma yana kan
Cikinsa da yake masa k'ugin yunwa,
Tunda ta turo k'ofa ya kafeta ido har ta k'araso gareshi,
Sannu ta mishi bai amasaba, bai kuma daina kallontaba, ta duk'a ta ajiye Abincin agabansa sannan ta zauna ta d'auki plate ta zubamasa, Ta d'an Kalleshi Asanyaye tace "Likita Bismillah ka tashi kaci Abinci,
Wani irin Kallo yabi Abincin dashi, ya Lumshe idonsa ya bud'e aransa yana Mamakin halinda ya tsinci kansa aciki,
Yanzu idan bai gantaba kewanta yakan isheshi yaji yana matik'ar Son Ganinta, idan yaganta sai yayi ta kallonta kaman ya tashi ya Rungumeta,
sai dai datamishi Magana sai yaji kaman ya shak'eta dan Haushi,
sab'anin da dako tunota yayi sai yaji Kaman ranshi zai fita dan tsananta da yakeji na yawo cikin jikinsa, ya k'ara Lumshe ldonsa gam yana Addu'a.
Cikin wani irin kasala da Sanyin Jiki, Ta mik'e Idonta taf da Hawaye dan ta lura baya ko Son Ganinta, tadinga d'aga k'afanta Ahankali tana tafiya kaman mara laka, xuciyanta namata zafi,
Ya zubama Bayanta ido kaman ya tashi ya kamota, Har sai da takai k'ofa ta juyo ta kalleshi dai2 lokacin kuma hawayen dake mak'ale a idonta ya gangaro, Ahankali ya girgizamata kansa yana mata alama da Hanu kancewa tayi HAK'URI,
Tayi saurin bud'e k'ofa ta fita, tana shiga palournta tafad'a kan Kujera tasaki kuka mai sauti, sai da tayi Mai isanta Sannan tayi shiru dan kanta,
Ta tashi ta zauna tana tuna Maganan da yar Jamila tamata jiya dasuka kawomata Katin Auren Jamilan,
Matan tana kallonta tace "Baiwar Allah inbazaki damuba zangayamiki wani Magana, Cikin ko inkula Dijah tace Bismillah fad'i inajinki,
Matan tace "Kinacikin wani Hali mara dad'i dan anyi Mummunan ajiya ajikinki, Dijah ta zaro ido, "Niii!!!?
K'warai kuwa inbazaki damuba ki bani Had'in kai zan taimakamiki In ware wannan k'ullin da akamiki, Dijah tayi shiru tana tunanin Maganan,
Matan taci gaba, karkiyi sakaci da Rayuwanki bak'aramin Sihiri akamikiba wanda ke Hatta cikin dake jikinki inba an ware Sihirinbane bazki haifeshiba haka zaki ta zama dashi ajikin ki.
Buga k'ofan da akeyine ya katsemata Tunaninta, ta tashi da Sauri ta lek'a Mami tagani tsaye dan haka tayi saurin Bud'e k'ofan tana mata Sannu da Zuwa,
Har zata juya dan nimomata abun sawa abaka, Mamin ta dakatar da ita "Dawo Khadijah Daga gida nake bana buk'atan cin komi yanxuma zan tafi, na dai zone inga yanda kike dan nasan kad'aici nadamunki, abunda nayi tunanin kuma shi na tarar, dama nace inba sa'aba zakiyi ta kuka, dan nasan halinki, sai kuma na tarar da hakan,
Kiyi Hak'uri Khadijah wannan Rayuwa da kika ganta ba komi acikinta sai K'alubale kala2 da jarabawa iri2 ki gode ma Ubangiji da irin wannan taki jarabawan Wlh inkinga na wata Khadijah sai kinmantama ke wacece,
Babu wani Rayuwan Auren da mata ba sa fuskanta jarabawa acikinta, sai dai kowa da irin nata, wata takan samu matsalane da Dangin Mijinta, wata Kishiya wata mak'ota wata yaran Mijin, kai wata shi kansane Mijin take fuskanta Jarabawa kala2 na zamantakewa dashi, anma inkik'ayi hak'uri kika mik'ama Ubangiji lamarinki sai komi ya wuce kuma shi hak'uri ba'ayinsa abanxa dole yana da sakamako mai kyau, kiyi Hak'uri Khadijah am Ki sani auren shi kansa ibadane, Tabbas Rashin kulawan Miji ga matansa abunda ciwo,
sai dai kisani wani halinsama kenan da Allah ya halicceshi dashi yin oho da ko inkula da iyalansa,
Babu wani tattausan lafazi da zai shiga tsakaninsu inba fad'aba wata zata dage tana iya bakin k'ok'arinta anma sam baya gani bare ya yabamata,
Wani abun takaicinma zaki iya samun wani namiji da wlh keda babu duka d'aya kuke awajensa anma abin takaici sai kisamu yana Nuna kulawansa ga wata mace a waje inma wacce yake so da aure