Showing 54001 words to 57000 words out of 155892 words
bata hangoshi afalonba tayi Dariya ta rufo ma lya k'ofa ta fito tasha kwana zata shiga d'akin ta kena ta ji ta bugu da mutum a tsorace ta d'ago suka Had'a ldo dagashi sai singlet da dogon Wando Hanunsa Rik'e da goran Ruwa da cup da Alama a kitchen ya d'auko.
juye2 ta hau yi yatsaya yana kallonta ganin ba hanyan guduwane yasa ta juyo ta kalleshi tana zaro ldo muryanta na d'an sezing tace "Sannu da dawowa, ina Wuni, ta gefenta yabi ya wuce batare da yace komiba da gudu ta shige d'aki ta maida k'ofa ta rufe.
Washi gari da sassafe Dijah ta shige kitchen don yin abun karyawa kaman yanda tasaba wani lokacin suyi tare da Mami wani lokaci kuma kafin Mami tafitoma tuni tagama.
Yauma hakan Akayi kafin k'arfe 8:00 tuni ta gama duk abunda yadace tashiga wanka tunda tafito take kan Mirrow, duk da bawani shafe2 tayiba bak'aramin kyau tayiba, swiss less tasa Lemon green mai kwalliyan zare Orange sark'a da d'ankunnen ta dasu warwaro duk orange ta saka, takalmi da jaka Lemon green ta yafa mayafinta orange mai stones ba k'aramin kyau tayiba tafito sai baza k'amashi takeyi a falo ta sami Mami itama cikin shiri take karyawan ta kenan ta tashi zata shiga ciki,
cak Mami ta tsaya tana kallonta har tak'arasota ta duk'a tace ina kwana Mami d'agota mamin tayi tana Murmishi lfy 'yar Mami kinganki kuwa?
Kinyi kyau sosai kamar 'yar sarauniyan Engla, Duk na zuwa gidan Fatiman ne? Ai nazacikin manta tayi maganann da zolaya Murmushi kawai Dijah tayi.
"kin karya kuwa? Nasan ma baki karyaba, kikarya inkingama ina sama daga haka ta wuce.
Tea kawai ta had'a zallan sa ta dawo kan kujera a falo ta zauna, dai dai lokacin Kabir ya shigo cikin Riga da wandon dark blue d'in Jeans Rigan kuma shirt ne mai dogon Hanu light blue, kallo d'aya yamata ya zarce d'akin Maminsa, Abakin gado yasameta tana duba wani takarda, d'an gefenta ya zauna Fuskansa d'auke da Murmushi, ya gaisheta ajiye takardan tayi ta dawo kan kujeran da yake kusa dashi ta dafa kafad'ansa "ka Huceni? Kabir abun har da yaji?
" a'a Mami kinsan shirin bikin Habib mukeyi abunda yasa kika ga bandawo da wuriba kenan, muna can wajen tsara Venue,
"To meyasa ka kashe wayarka?
"Wlh Nafisa ce take son takura min shiyasa nakashe.
"Nayi zaton ko don auren kanne Kabir kamin yaji,
"Bahaka bane Mami yafad'a yana sosa kansa,
Kallonsa tayi da Alama da magana a bakinsa,
Murmushi tayi wata k'ila kanason sanin yanda akayi aka maka aurenko?
"Bahaka bane Mami Nafisa nake tunani yanzu za'a ajiye maganan Auren tanne?
"Meyasa za' ajiye? Ai in anmata haka ba ayimata Adalciba tsawon lokaci tana jiranka.
"Mami nasani zamu sha artabu da itane sam banson tashi hankali,
"Kabir kad'auki wannan aure naka a wani babban al'amari da Allah ya hukunta kasamwta kasanar da lta bayin ka bane.
"Mami to wai wacece yarinyan kuma yaushe aka d'aura Auren nazacima Nafisan tasani amma jiya maganan da tamin na fuskanci bata saniba, Mami mata Biyu basuyi yawa ba kuwa?
Murmushi Mami tayi sarai ta fuskanci lnda zancen nasa ya nufa.
"Kar kadamu Kabir zakasan matan lnlokaci yayi, aure kuma ma bakanan aka d'aura lokacin kana England.
Wani mashiriri cun Murmushi Kabir yayi jin maganan yayi kamar a tatsuniya cikin son yabasar yace "kai Mami ashe najima da angoncewa ma ni bansaniba, kaman zaki fitane ko?
"Eh zanje gidan Sani "ok lnkin shirya muje inkai ki.
"Khadijah nake jira ka dubota lntagama sai mutafi.
"To yace sannan ya fita bai sameta a faloba, D'an dube2 yashiga yi a kitchen yaji motsin Ruwa yashiga a lokacin tana jikin famfo tana wanke kup d'in da tasha tea, bayanta yatsaya yana k'are mata kallo, ta juyo da niyan ajiye cup d'in kawi taga mutum Wani lrin razannane k'ara tasake, gami da wurgar da cup d'in Da sauri ya matsota zai rik'eta Mami ta fad'o kitchen d'in a tsorace "lfy Kabir mai kamata? Tayi tambayan tana rik'o Hanunta.
Ya Harare Dijah da take ta muzurai Ba abunda namata Mami juyowa kawai tayi ta ganni.
"Gaskiya Mami yarinyannan tana da sercatref problem yakamata akaita Abinciketa, Hanunta kawai Mami takama suka fita.
Uziri pls kuyi Hak'uri da wannan π°
UMMU fatima
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*UMMU FATIMA CE*π³π¬
π *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......π
*page* 3β£2β£
Bayansu yabi sai wurga mata Harara yakeyi, aransa yana Mamkin Halin yarinyan sam lhu bayamata Wuya yanzu ta tatarama Mutane ba wani Abubane awajenta.
Afalo Mami tasake Hanunta, tace ta d'auko mayafinta taje wajen Motan tajirata.
Saida taje tayi ma lya sallama sannan tafito.
Atsaye tazo tasami Kabir ya jingina bayansa da Motan yana hard'e da Hanunsa ak'irji, d'an nesa dashi kad'an ta tsaya tana Amsa waya, zubamata ldo sosai yayi yana kallon yanda take Lumshe ldo da Alama tanajin dad'in Maganan datakeyi.
Cikin taku Na kamala da Nitsuwa Mami ta iso, tundaga nesa da Dijah ta hangota ta'ajiye Wayan ta nufota ta karb'i jakan Hanunta,
Baya Mamin tashiga sannan tamata Umurni da shiga gaba, suna tafiya jifa2 Kabir yanayi ma Mami tad'i har suka iso.
A k'ofar Gidan yayi perking, Mami ta kalleshi "meyasa kayi perking anan Bazaka shigaba? Yad'an yi Murmushi "Mami ince yanzu Zaki shiga ki fito, yafad'a yana Langab'ar da kai..
Murmishi kawai tayi suka shiga Khadijah tana Gaba Mami na biye da ita, a k'ofan falo Dijah tayi Sallama wajen sau biyu ana Ukun ne Bintalo ta Amsa ta fito tana Bud'e k'ofan Falo tayi tozali da Dijah ihun Murna sukayi gaba d'aya suka Rungume junasu.
gefe Mami taja zuciyanta cike da tausayin yaran dakuma tuhuman Kanta na Rashin Kawo Khadijah wuri "yar'uwanta, Tasani ba k'aramin kawaici tayiba dai2 da Rana d'aya bata tab'a nuna Alamun tanason ganin 'yar'uwan nataba.
"Mami kishigo Muryan Bintalo ya katsemata tunani, Murmushi tayi ta kalli Bintalo da take ta nok'ewa saboda Cikinta da yad'an fara Ture Riga,
K'asa tasakeyi da Kanta tace "Bismmillah Mami kishigo.
"kingama Murnanne Fatima? So kike ki karyamin 'ya ko? Tafad'a tana kutsawa ciki, Sai da tazauna akan Kujera kafin Dijah ta zauna ak'asa daf da ita, Bintalo tashiga Bed Room ta sako Hijabi, sannan ta shiga kitchen ta cika musu gabansu da kayan ciye2 da shaye2.
A gefe Bintalo ta zauna cike da Girmamawa tagaida Mami, "Kuna lfy ko Fatima?
"Eh lfy k'alau.
"To Alhamdulillah kina waya dasu Baffankin ko?
"Eh d'azunma muka gaisa.
"To yayi inda wata matsala dai nagaya miki Fatima kar kiji nauyin sanarda ni ko wace irice kuwa, kid'aukeni tamkar lnnan ki kinji?
Bintalo Ta gyad'a kanata tana wasa da yatsunta.
"Sannan shi zaman Aure Hak'uri yafi yawa acikinsa kaman yanda nake gaya miki kullum, Kibi Mijinki sosai Fatima duk da dai nasan ke yarinyace mai ladabi to kik'ara akan nna da.
Ya Makarantan dai lnce ba wata matsala?
"Babu Mami wlh Malam dakika had'ani da itannnan tana kirki sosai, tana taimaka min a kan karatuna.
"Ayyah nasan zatayi ai Hajiya Ameena ba laifi.
Mami ta kalli Agogon da yake mak'ale a hanunta Sannan ta kalli Dijah "Ni zan tafi Khadijah inada Meeting, sannan daga nan zan wuce gidan Uncle d'inku zuwa yamma zan turo ad'auke ki,
"To Mami kigaimin da Umma da Sauda.
"zasuji.
Tana k'ok'arin mik'ewa Bintalo ta langab'ar da kai "Mami bakici komiba fa zaki tafi,
"Sory Fatima Sauri nakeyi ta fad'a tana d'aukan goran Ruwa d'aya, ta mik'ama Dijah kaima Kabir nasanshi da shan Ruwa naga kuma bai d'aukoba,
"To, tace Sannan ta d'auka tafita yana zaune akan Mota yana waya da Nafisa, baya yabata dan haka sam bai gantaba, har sai da yagama, daga bayansa yaji Muryanta adak'ile "Likita wai gashi lnji Mami, wurga k'afansa kawai yakeyi daga saman Motan batare da ya juyoba, tad'an wuto gabansa tamik'amasa zuba ma k'irjinta ldo yayi batare da ya karb'i Ruwanba, cikin dakewa yace lna mayafinki? D'an juyawa tayi ta kalli k'ofan gidan "yana ciki.
"Yamiki kyau yafad'a yana maida kallonsa ga wayansa, ta turo bakinta "ba zaka sha Ruwanbane in maiyar?
Ya had'e Rai "zo ki bani abaki, ta karkace kai tana mishi wani Kallo ance maka ni 'yar lskace irin Wancan Banzan Nafisan?
Wlh ma ka jawo makanka, sai nafad'a Mami abunda naji yanzu kafad'a awaya wai ku had'u a aroma Hotel kaceko?
Cikin zafin nama ya dirk'o asaman Motan ai asaba'in ta yarda goran Ruwan ta arce da mugun Gudu, abakin gate sukayi karo da Mami, Mami tana shirin rik'eta tayi saurin komawa bayanta tab'uya, tana lek'owa.
"Lfy kuwa? Bintlo da tayi Rakiya ma Mami ta Tambaya tana kallon Kb dayake jingine da jikin Mota, Hanunsa soke a cikin Aljihunsa, barakatab'a cewa dashi Dijah take wannan gudunba.
Mami ta matsa gefe tana kallon su takalli Diijah ta kalli Kabir, badin sanin Haliba sai tace Dijah ita kad'ai ta kwaso wannan gudu.
"lfy Khadijah? Inji Mami.
Turo baki tayi Shine ai wai ln bashi Ruwa abaki.
D'an gajeren tsaki Mami tayi ta wuce ta shiga Mota.
Bintalo ta d'an Harare Dijah murya k'asa2 tace "Mai Hali dai baya fasawa, Allah ya shiryeki, Sannan tak'arasa bakin Mota, suka gaisa da Kabir d'in alokacin yana shirin tada Motan.
"Ya Kabir shine kak'i shigowa ko?
"Jiya fa iwar haka inacikin gidankinnan Mamata kokin Manta?
"jiya daban yau daban ai.
"kar kidamu Yau da daddare zan zo ind'auki aron Mijinki yamin Rakiya, yafad'a da zolaya, Dariya kawai Tayi ta kauce masa yaja Motan.
Suna komawa ciki Bintalo ta kamo Hanun Dijah tana k'aremata Kallo, tarik'e Hab'a "Dijah Haka kika dawo? Wlh banda namiki kyakykyawan sani bazan ganekiba, kinganki kuwa?
Dijahn kam da Mamaki take kallonta "yanzu Har zakicemin Na canja Bintalo? Toni Har yanzu kokonto nake anya kuwa kece?
Kinyi k'iba sosai ga wani Fari da kika k'ara Bintalo Meye wannan acikinki? Tafad'a tana zaro ldo gami da tab'a cikin.
Bintalo ta buge Hanunta tana Dariya tashige Bed Room.
Jim kad'an tafito "Dijah wai lnji Honey yana gaisheki, zaro ldo Dijah tayi "waye kuma Honey?
"yaya Sani man.
Jinjina kai tayi "dama yana ciki Shine yayi likimo yak'i fitowa?
"yafita waya mukayi nace masa kinzo mana kwana lnce kwana zakiyi mana.
"cab shida yace ba a kwana agidanku, ba abunda zai sani inkwana.
Bintalo tana dariya tace to sauko kici koda friut ne.
Sauk'owa tayi suka baje awajen suna Hiran abunda ya wuce suna Dariya, can Dijah tad'an yi shiru, Bintalo tace yadai?
Nan danan Hawaye suka fara zarya a fuskan Dijah "Binatalo Baffah na inason ganin Baffahna wlh inason inkoma gida.
Shiru Bintalo tayi aranta tana tunani ba ita kad'aiba hatta su Baffah insunyi waya sukan nuna mamakinsu na yanda Dijah tayarda ta zauna tsawan wannan lokaci a wani gurin.
Tayi abunda ba wanda yatab'a tunanin zatayi.
Bintalo ta nisa cikin son kawar da zancen tace "To indankuma kika shiga d'akinki na Aure fa ya zakiyi?
Rabuwa dasu ai yazamo miki Dole Dijah tunda Allah ya hallitoki Mace ba na Mijiba.
Tasa Hanu ta goge Hawayenta tanakallon Bintalo "ni bazanyi Aure awani Gariba, gani ga Baffa da lnnata kullum lna tunani yanzu waye yake d'ebo ma Baffana Ruwa?
Wa yake tayi lnna aikin gida?
Bintalo tayi wani Murmushi mai ciwo cike da tausayin lyayen nasu dan lrin tunanin da Dijah takeyi itama takeyi musamman yanda Rayuwa ya canza mata tana cikin jindad'i ga ababen More Rayuwa kala2 Bata da wata matsala, Rayuwa takeyi irin wanda bata tab'a Mafarkinsaba( Allah kenan) kullum kwad'ayinta inama ace lyayen nasu suma haka suke.
"Tace Dijah ki kwantar da Hankalinki indai wannan ne aidai dama da d'iban Ruwan da aikin Abincin duk dan muna nanne yake yawa, yanzu kuwa duk zai zo musu da sauk'i.
Wlh cikin k'oshin lfy suke duk lokacin damukayi waya sundinga Tambayana lnce dai bama cikin wata Matsala?
Dijah tace Don Allah kibani no. Baffah kinji?
Bintalo tayi shiru tana tunanin maganan dasukayi da Mami bayan ta koreta da wayon takaima Kb Ruwa.
"Mik'omin wayan gashi can abayanki ink'irashi Kugaisa kafin kitafi zan baki no.
Dasauri ta mik'o mata ta kalleta "Kimin Alk'awarin bazaki fad'a musu wani abunda zai b'ata musu raiba kuma ki share fuskanki kidai daita Muryanki inba hakaba bazan k'iraba.
Me Hali baya fasawa saida tad'an Harareta ta murgud'a baki kafin tace "wlh gaisawa kawai zamuyi.
Tana k'iranshi bugu d'aya yad'auka.
Jin Muryan da baiyi tsammani bane yasa shi sakin lallausan Dariya cikin farin ciki yace
"Uwata ta kaina
Uwata tafi ta kowa
Uwata maganin Kuka na.
Saida ta sauk'e ajiyan zuciya, tace
"Baffana lnason lnganka Baffah kullum sai nayi Mafarkinka,
"Zaki ganni Dijah na indai ina raye kina raye zamu ga juna dayardan Allah,
Hajiya tace min inkin sake samun wani Hutun anan zakiyi mana, ki kwantar da Halinki mamata kiyi karatunki kinji?
"To Baffah ina lnna ta? Innan ki tana gida nina fitane,
"Kaje d'ibo Ruwane ko Baffah? Ko lta ce? Tayi maganan araunance.
Baffah yayi dariya mai sauti "ki kwantar da Hankalinki Dijah bana Ruwa bana l tace.
.Baffah ina Jebu na? Tafad'a cike da shauk'i.
"Ayyah Jebunki ai kullum itake d'ibo mana Ruwa iro kuma ya d'ibo mana itce kullum tana wajen lnnanki tare suke aikin gidan bata da magana sai naki.
Cikin son Aminiyan nata tace lnka koma gida Baffa Zank'iraka ka had'amu da ita.
"To Dijah na Amna kin min laifi baki tambayi Takwarankiba, Goggoji ita kuwa kullum tana magananki,
Rufe ido tayi kaman tana gabansa tace Kayi Hak'uri Baffah wlh nayi Missing Goggoji na sosai ba kad'anba in munyi magana da Jebu zance takaimata.
Daga Haka Bintalo ta karb'e wayan suka gaisa, daga bisani sukayi Sallama ta kalli Dijah datake ta Murmushin farin ciki, "Ki tashi mushiga kitchen yau ke zakimana Abinci, Honey ya Huta tsaki Dijah taja daida Lokacin Sani yashigo.
Da Murmushi yake Kallon Dijah
"yau Khady Baby ce agidan namu? Lallai yau muna da babbar bak'uwa, yafad'a yana zama agefen Bintalo sannan ya kamo Hanunta yana Murzawa "Sweety yau Baki Har kunne gaki ga Khadijahnki.
Rintse ido Dijah tayi aranta tana tunani Dama haka aure yake duk wanda yayi sai yazama d'an lska?
"Khadijah yaya Gida?
"lfy ta Amsa kanta na k'asa dariya yayi sannan ya mik'e sweety Barin zo naga wannan Bak'auyuwar k'auyanci nata ya motsa, lna zuwa yanzu, yana fita Dijah ta dallah ma Bintalo Harara.
dai2 lokacin Mak'ociyarta Aysha ta shigo, da Sallamanta tazauna Kusa da Dijah tana kallonta tace "Aunty Fatima wannane Khadijahn ki ce ko?
"Eh itace,
"kai naga kama amma dai tafiki kyau.
"kai Aysha kiduba da kyau dai ta fini kyau? Ko tafini Fari?
"ah wlh kyau d'inma tafiki, lna sonki Mai kyau kusan Kullum sai Aunty Fatima ta bani labarinki kullum lna Allah2 inganki sai yau ya mutanen gidan?
"Lfy k'alau, tana gulmana dai ko?
"ah sam wlh tana dai bani lbrn kine kawai.
Aysha ta kalli Bintalo, "Aunty Fatima kinga jiya baki gannibako? Wlh sweety na ya rik'eni fir yahanani fitowa kin san jiya anyi d'an sanyi bai fitaba bai barni na fitaba, wlh ko Abinci sai da na lallab'ashi yayi bacci na d'ora ai yana farkawa aka faka girgi agefe, ta k'are maganan tana mik'amata Hanu suka tafa.
Nanfa Hiran matan Aure ya b'arke a tsakaninsu.
Saida sukayi mai lsansu Aunty Aysha ta mik'e barinje ingama ayyukana zan dawo intafi da Mai kyau Gidana.
Dijah dai tana zaune awajen kaman andasata ji take kaman ta nitse awajen Harara kuwa ta musu ba Adadi daga k'arshema tashi tayi tashiga kitchen.
Anan Bintalo ta sameta har ta kunna Gas tana fere Doya tana dariya tace "oh Khadijahn Mami sakwara za'ayi mana ne?
Barin dafa ma Honey indomie, mutuminki yak'irashi wai zasu lek'a Campaninsa Dijah ta tab'e baki tana mita
"wlh Bintalo kinshiga Ukunki daga zuwa Birni kinzama 'yar iska, nikam ba Ruwana kin had'u da wa incan matan sun koya miki lskanci,
Saida ta d'ora ta kalleta Ayyah Dijah am wanna matan abun ki mata godiyane zuwana gidannan kinsan ba abun da na iya ko Abinci mai kyau ban iyaba haka take shigowa ta koyamun komi da yanda zanyi amfani da komi Hatta zama da Mijin ma ba k'aramin jahadi tayi daniba
Ke wlh bani da bakin mata godiya sai Addu'a ta d'aukeni tamkar 'yar'uwanta.
"Eh daganan kuma sai ta koya miki Rashin kunya da maganan banza ko
Bata rufe bakiba sai ganin Sani tayi ya shigo ta baya ya rungumo matarsa Sweety zan tafi fa kinzo kinbiye ma Khadijah kin mantani.
"ah Honey na gashima yadafu ta juye a flate suka fita tare
Dijah kam mutuwan tsaye tayi taja gefe tana jinsu har yanzu bata daina mamakin Bintaloba aranta tana tunani inama ace a ldon lnna da Baffa take irin wannan abun tasan da sun tsinemata angama.
.
Sai da yamma Mami ta dawo gida lokacin Kabir da Habib suna zaune a Farfajiyan gidan kusa da pert d'insa magana sukeyi har Mami ta iso gurin basu luraba, saida tace "Sannunku kafin Suka kalleta, Kabir yace "Mami waya dawo dake?
"Ni da kaina nadawo, yad'an zaro ido yana kallon Motan, da kanki Mami? Yanzu kuma mukayi waya bakice min inzo in dawo dakeba "ah ai tunda kace min kai da Habib ne nace to barin barka kayi danna k'irjin da kyau.
Kabir yana dariya yace "Mami ashe Sauda ce Amaryan? ai dama baku b'oye mana wacece matarba.
Habib yad'an lakaci Kabir yana masa ldo.
"kingani ko Mami wai kar in fad'a Munafukai dama suna Soyayyansu a b'oye, lskancine kawai yasa basu nunaba inagama su Uncle sun ganene yasa suka had'a Mami tayi dariya mai Sauti tace