Showing 99001 words to 102000 words out of 155892 words

Chapter 34 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

472

ya shige motansa yana hararansa, yace "tsaban karaianani anan ne zaka tareni da irin wannan maganan, mts yaja tsaki gamida yi wa Motansa key kamanzai bankeshi ya bad'eshi da k'ura yayi gaba,


Murmshi kawai Kb yayi ya shige motansa yayi gida, dan tun ba yauba yasan tsatsan dake Ran Baffan nashi,

shi kuwa Alhaji Ya'u da k'yar ya iya kai kanshi gidansa, zuciyansa sai zogi take masa,


Wurgi yayi da Sallahyan hanunsa yana bankamata harara, sosai ya lura da ita yanzu sam bata mutuntashi ko dan taga yanzu baya da Kud'ine?

Cikin zafin rai ya kalleta, "banga kina wani shirin bikin Nafisa a gobe ba, ajiye rigan da ta d'ago zata ninke tayi, tana kallonsa da Mamaki dan daren jiya ba irin artabun da basuyi dashiba akan maganan auren anma fir yak'i yace Bazai ba da 'yarsa ga Mara kunya irin Kb ba,

"Na lissafa nayi shawara naga bai kamata ace duk mun taru mun Rasa abunda muke soba, ni nakasa mallakan dukiyan kb, sannan tilon 'yata ma ta rasashi amatsayin mijin da takeson aure,


Ya furzar da iska yaci gaba "Naji sunyi shiru basu ce komi akan maganan bikinba, hakan ya nunamin daga shi har Uwarsa da 'yan'uwanta basa son auren kenan, to Wlh muddin ina numfashi sai anyi kuma a Goben zan cika ma Nafisana Burinta, inyaso su had'iye ransu su mutu, kuma banga wanda ya isa ya hana wannan aurenba, ya k'arashe cikin k'araji yana ciza hak'ora, sannan wata Murmushi mai ciwo, "Kuma bazan bar farautansaba koda 'yata tana hanunsa,


Maman Nafisa tashi tayi tsaye cikin wani irin Farin ciki dandama tana shirin tagama abun da takeyine ta k'ira Nafiasan suje wajen boka, yabata maganin da zai yarda ayi bikin dan dahakan ta lallab'a Nafisan bayan tagama kuka kaman ranta zai fita,


Hanunsa ta kama ta zaunar dashi tana washe baki "Zauna nana muji dad'in yin batun, nagode ma Allah daka fahimceni inbanda abunka ai indai Nafisa ta auri Kabir mun warke ina mai tabbatar maka duk k'udurinka akan Kabir zaka cinmasa, ba b'ata lokaci, Sannan Dukiyanmu zai farfad'i ta Hanunta, zata Dinga Amsarmana da dabara, ta kuma washe baki,

" karkaga yanda tad'aga hankalinta datasamu lbrn kace anfasa bukin, yanzu zan k'irata in sanar da ita, wayyo Nafisana yau zatayi kwana zaune dan farin ciki, saidai wani hanzari ba guduba, Shin yaza'a b'ullo ma iyayen nasa? Tunda kaga har yanzu case d'innan ba agama bincikenba,


Wani uban tsaki yaja yana zabga mata harara, "yo duk ba ke bace da k'aramar k'wak'walwanki kika shirya wannan shirmen, Kabir d'an kazane? Dazaki shirya wannan shirmenki yayi tasiri? Wlh nagaya miki kisan yanda zakiyi ku cigaba da b'oye meena inba hakaba duk randa aka ganta aka bincika ba ta da hanu wajen samasa poising d'in to dole agano gaskiyan magana ananne kuma zan fito inwanke 'yata wlh saidai a hukuntaki ba itaba,

cikin firgici take tasharan zufa duk da taji zafin maganganunsa, ta dan zai Rina, takuma san tabbas Meena bazata cigaba da b'oye kantaba duk randa aka ganta kuwa gaskiya zatayi halinta, aranta tace "ai wlh kuwa xa'ayita dan kaima zan maka tonon tsilili bazan shiga risky ni kad'aiba.


Mik'ewa yayi yana zabgamata harara ya fice shi kad'ai yake sambatu amota yana tafiya gidan Abban Habib, "Barin je musu ta mutunci insunk'i wlh ayita ta tsiya tsiya ko sunk'i ko sun so sai anyi wlh, banga Shegen da ya isa ya hanaba, mtssss yaja dogon tsaki yana shiga layin Gidan.

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Tunbayan da ta gudu ta shiga d'aki ta fad'a kan gado tana Dariya, tanajin ya rufo k'ofan Falo, ta tashi ta yaye labulen Window tana kallonsa sai sauk'e ajiyan zuciya takeyi har yashiga mota ya fice agidan ta rufe labulen tana Murmushi, ahankali ta furta "yana da kyau kuma ya iya d'aukan wanka, tafiyansa mai kyau, muryansa mai dad'i, hatta sautin dariyansa mai dad'i, tana murmushi ta tashi ta koma kitchen ta cigaba da aikinta ita kad'anta sai smiling takeyi tana wassafo kammaninsa, har tagama ta shirya komi akan dining ta fad'a wanka tunda ta fito take kan Mirrow ta dinga tsara kwalliya nagani na fad'a tagama ta tace kanta ta tufke da k'aton Ribon ta jima tana niman kaya can ta zak'ulo wani code lace maruum mai azabann kyau fiten gawn mai kwalliyan zare Golden ajiki, tasaka cif yakamata kaman ajikinta aka d'inka ta d'auko head d'insa Golden ta sa akanta, d'an kunne da sark'a gami da warwaro duk na gold tasaka, ta kalli kanta a mirrow tadinga murmushi dan tasan tayi kyau Sosai, mami ce ta fad'o mata arai tasan itace kawai zatace tayi kyau, tayi ta yaba mata, gurin takalmanta ta nufa ta d'auko wani dogon takalmi mai azaban tsini yana da igiya kaman sandal golden colour ta saka bayan tagama feshe jikinta da turaruka masu tsaban k'amshi ta fito, kitchen ta shiga ta d'auko kayan Abincin da ta had'a nasu Mami a Bascket ta nufi k'ofan fita,
, Tana mik'a hanunta zata bud'e k'ofan, taga Handle d'in na Motsi alamun ana k'ok'arin bud'ewa ' daga waje mai da hanunta tayi tad'anyi baya gami da zuba ma k'ofan ido,

Ahankali ya turo k'ofan tun kan ya shigo k'amshin ta ya daki hancinsa, yana d'ago ldo yayi tozali da ita tsaye da alamun wai jira take ya wuce itama ta wuce kallonta yake ba ko k'iftawa ya jawo k'ofan ya rufe gami da jingina bayansa ajiki ya zuba hannayensa cikin aljihun rigansa, yana cigaba da kallonta zuciyansa sai hawa da sauk'a yake, sauk'ar da kanta k'asa tayi tana kallon yatsun k'afanta, taku biyu yayi ya k'araso gabanta yana murmushi ya d'ago hab'anta yana kallon fuskanta, ahankali yace "inazakije? Ta d'ago idonta suka had'u da nashi tace "zankai wa su Mami abincinsu ne, ya kamo Bascketa d'in ya ajiye ak'asa ya rik'o hanunta suka k'arasa tsakiyan falo ya zauna akujera ya zaunar da ita kan cinyansa suna kallon juna yace "Bana hanaki shiga ciki ba lullub'iba?
"Tabayafa zanbi, ta amsa kaman mai shirin kuka,
Ya lumshe idonsa ya bud'esu akanta yace "duk da haka mami mai mutanece zaki iya shiga kisamu wasu aciki,

Yanzuma dasu Habib muka shigo suna can sunje gaisheta, in sun gama zasu shigo nan, wai me kika giggirkane?

"suna da yawa,
"Ok Su hud'une Zai ishemu?

Tad'aga kai Alamun "Eh
Ya rungumota Jikinsa, yana sansanan wuyanta idonsa a lumshe yace "Baki da baki ne kike d'aga min kai?



Ad'an tsorace cikin sanyi murya tace ina dashi,

Ya d'agota yana kallonta yace "ma wa da wa kika zuba Abun dad'in?

"wa Mami da iya,
"Kai Khadijah duk wannan k'amshi da ya dinga bule "yan gidan wa iya su Mami kawai kika bayar? Gaskiya in kinyi abun dad'in irin haka kidinga sa ma masu aiki komin kashinsa a mik'a musu, kinji? Kai ta d'aga ya kuma Rungumota yana kissing, "Banace kidinga amsamin da Bakiba?
"to to ta fad'a ajere dai2 Lokacin sukaji ana nocking da k'arfi, tsaki yaja ya sauk'eta yana rik'e da Hanunta yashigar da ita d'aki ya zaunar da ita abakin gado, "kar ki yadda ki fito ko gaishesune, daga haka ya juya ya fita,

Ya bu'e k'ofan falo yana hararansu

"Wannan wani irin buga k'ofane sai kace Gidan kurame kukazo?

Sani yace "yo ba gara kurameba da ku, Habib yace "kabarshi kawai, zai raina wa Mutane hankaline kaifa ka gayyatomu, mu gaida Uwarmu mukazo, kace mu shigo shine za'a wani shanyamu,

Dr Na'im yace kai kubishi ahankali ba sonsa bane kunfa san halin Giyan Angonci ba k'aramin bugarwa takeba, ya fad'a yana dariya

Sani ya rank'wafo kunnen Habib ya masa rad'a, Habib yad'an lek'a k'asan wuyan Kb, ya lakato jambaki ya nunama dai2 Fuskansa "Kai gurgu d'an birni meye wannan? Fisabilillahi da girmanka da ajinka aganka da irin wannan? kaiba yaroba, gaba d'ayansu suka tuntsire da Dariya harda rik'e ciki, Hanu kb yasa inda Habib ya lakato jambakin, cikin waskewa yana sharewa, Naser wanda tun isowansu yake binsu da kallo baice komiba, sai murmushin da yakeyi, yace "wlh ku 'yan Mugun sa ldone, Abokina kayi a hankali, dasu duk 'yan iskane,

Kb na murmushi ya mik'o masa hanu "Rabu dasu abokina sun zaci nima na iskancene kamansu, Bismillah mu shiga, ku kuma inkungama iskancin naku sai ku juya bana gayya iskanci, gaba d'aya suka kutsa kai suna dariya, "ai munshigama angama,

Habib ya kalli daining da mamaki, "wai dama wa mu aka shirya wannan d'in ko munzone akan gab'a? Dariya kawai sukayi suka fara savice,

Dr Na'im yana kai loma yace "wai Dr Matan kannan 'yar Bauchi ce? Kasan Matan Bauchi kusan ince sunfi 'yan kowani jiha iya girki da rashin k'iwuyan girki, (😜😜)

Bazan tab'a manta wani Abincin da naci a Bauchi ba, yasake kai loma, zai kuma cewa wani abu, Kb yana dariya shima da lomansan abaki, ya tab'a bayansa, "dad'in abundai akwai weji abayanka, sai alokacin Dr Na'im ya Ankara da yafara sake layi yana sosa kai yace "kai banson lskanci bafa santi nakeyiba, gaba d'aya suka kwashe da dariya,

Ba k'aramin dad'i Kabir yaji aransaba, yanda yaga sun tashi da Abincin gaba d'aya da Drinks d'in, sai magana suke mai kama da santi, "Khadijah tarinig d'in Mami ya fad'a aransa,


Habib yajingina da kujera yana share hanunsa da tisue, yace "Wai baza ka k'irata ta gaishemu bane? Hararansa yayi "Yace tana Bacci, Sani yace "Fatima ta ban sak'o inbanta,
"To sai ka bari sai randa kuka had'u kabata, Nasir yace "wai tunda kunzo kun cika cikinku da garan girki ina Ruwanku da matan Gida,

Kb yace "Rabu dasu Munafikaine,

Dr Na'im ya kalleshi "kai Dr Kb mungaisa da Mami take cemana wai har yanzu kak'i fara zuwa aiki duk sonka da aikinkannan intamaka Magana sai kace inkagama jin dad'in jikinka zakaje, kuma dai naga kullum kana zuwa sai dai uban lattin da kakeyi,

Habib ya kwashe da dariya yace "ai wato mutumina akwai wani abune ak'asa bakaga ina ta maka idoba kar ka fallasa, Kabar Mutumina da sabuwar ciwon mara suka kwashe da dariya harda tafawa,

Tashi tsaye Kb yayi yana kallon k'ofan bed room kaman mara Gaskiya, yace "Duk kutashi ku barmin Gida, na sallameku, Banzaye 'yan air, "ko baka sallame muba dama yanzu zamu tafi iyalanmu suna jiranmu, har bakin mototinsu ya rakasu suna ta barkwanci,


Khadijah tana jin fitansu ta fito ta fara tattare wajen, tana kitchen tana wanke2 ya shigo, tabayanta ya rungumota yasa kansa ta jikin wuyanta yasa hanunsa ta k'asan Riganta yana shafa cikinta, yace "Yunwa nakeji, ta juyo tana kallonsa "Bakaci Abincinbane? "iyi duk sun cinye sun barni ya fad'a yana Rangwad'a kai kaman k'aramin yaro, ta d'auki towel paper ta goge hanunta, ta d'auko wani cooler da plate da spoon ta kalleshi Muje na zuba maka,
Yace

"wannan d'in na waye?
"Da nazuba zancine,
"Mhm yanzu kinfasa cine?
"Eh dama banajin yunwa, anjima zan sake Girki,
Ak'asa suka zauna ta zuba a plate zata tashi yakamota ya zaunar da ita ajikinsa, ya d'ibo zai samata abaki tace "Kaci na k'oshi, da ido ya mata Alamu da takarb'a, bata ya dingayi, sai da ta k'i karb'a tace "wlh Likita na k'oshi da yawa, kace kana jin yunwa kuma bakaciba, yana murmushi yace "Ai duk nafisu cin Abincin cikina kaman zai fashe nake ji,

Zata tashi ya kuma jawota, tace "Abincin su Mami,

"Nakai musu ai tayi tasamiki Albarka, na barotama ta fara ci dama bak'inta duk sun cinye Abincin pert d'in, mutuniyar kice dai take ta surutu wai duk abunki bazaki k'wace mata Mijiba, yafad'a yana kallon k'wayan idonta, yi tayi kaman bata jishiba. Dan ta lura da wani sabon salo da ya koyo tsakanin jiya da yau.




Da misalin 9:00 na dare Mami na hango, zaune a bakin gado sai jujjuya wayan hanunta takeyi cike da damuwan sak'on da Abban Habib yagama gaya mata yanzu, Gaba d'aya hankalinta ya gama tashi, sak'a da warwara take tayi awajen daga bisani ta tashi ta nufi d'akin iya ranta tana fad'in "barin je insami lya inji me zatace, oh ni Fatima naga ta kaina da wannan lamari,


Zaune tasamu iya a kan Sallahya tana lazimi tun bayan idar da sallahnta, kallo d'aya tayi ma sirikar nata ta karanto damuwa a fuskanta, gefenta tasami ta zauna, lya ta nad'e k'afafunta da suke mik'e tace "Yadai Fatima me ke faruwa? Mami ta sauk'e ajiyan zuciya tana kallonta, Tace "Iya yanzu Abban Habib ya k'irani yake cemin wai maganan Auren Kabir da Nafisa Ya'u yaje yasameshi da zancen, yaso yace masa abari tukun agama case d'insu yace amma ya hango fitina da Ya'un yake nima shiyasa kawai yace to shikenan tunda anriga da dama antsai da Rana, angama komi gara ayita ta k'are magana yak'i ci yak'i cinyewa, lnyi hak'uri kawai inraka da Addu'a,


Iya tasauk'e ajiyan zuciya tace "to ke meye shawaranki fatima?

"Iya ba wai k'in Nafisa da Kabir nakeyiba, hasalima tun farko ni nayi ta k'arfafa abun nayi ta lallashin Kabir akan ya amince, amma wlh lya yanzu banaso ba kuma Nafisance bansoba Wasu Munanan hali da naga ta koyane banaso, narasa waya d'orata kan munan d'abi'u tana k'araman yarinyanta,


Iya tad'anyi Murmushi irin na Manya tace "Na fahimceki nakuma san abinda kike gudu, Ki kwantar da Hankalinki Nafisa ba a k'asa ta d'aukaba zan iya cewa tagada kuma tasha anono, haka nay ta gwagwarmaya da kakarta har Allah ya rabamu ba wani abunda ya tab'a tasiri akaina da ikon Allah, Haka Ubanta yayi ta fama da Mahmud amma bakigaba saida Allah ya kasheshi kafin ya mutu? Dama nasani zai dawo kan Kabiru saidai akullum ina gode ma Allah da yamallaka ma Kabir ke amatsayin Uwa ta gari mai jajircewa da lbada da Addu'o'i ki dage sosai ki kwantar da Hankalinki ayi, ba abunda zai faru sai Alkhairi,


Mami ta jinjina kai "Kuma lya ni nafi tunanin 'yar Mutane da take tsakninsu, kinsan yaranna bakaman kai babba da kasan ciwon kankabane suna da sakaci da Addu'a, sannan tana da wauta da yaranta har yanzuta,

Iya tace ba wani Wauta tare da Khadijah goyone kawai na lura Baffantanan da take yawan k'ira ba dare ba Rana ya sakaltata da yawa, sannan kema kikazo kika d'ora daga inda ya tsaya, Barta kawai tsaf zata ware kirakasu da Addu'a kawai.


"Shi Kabir d'in ince yasan da goben zai zamo mijin Mata biyu?

Mami ta tab'e baki "Oho masa ko yasani ko baisanibama ai yariga da yagama komi, naga har kati sun raba, shi Adole zaiyi auren so,

Iya tace k'irashi awaya yazo yanzu adad'a shaidamasa, bawani auren so dazaiyi tirsasa ma kansa yakeyi, bawani so,



Mami tad'aga waya ta k'irashi, alokacin suna ta dramansu da mutuniyarsa, tun fitowanta daga wanka yake binta da kallo har tagama shiri yarasa wani irin turare haka take amfani dashi,

Mai tsaban sauk"ar da Kasala, bayan ta zira rigan baccinta tana shirin sa hijabi akai kaman yanda ta saba ko da yaushe yayi caraf ya jawota ta fad'a jikinsa, yad'an b'ata rai, Yace "Malama jirankifa nakeyi kimin tausa, turo baki tayi

"nifa ban iyaba bansanma yanda akeyiba, tom zo inkoyamiki da sauri ta janye "a'a zan maka, "Ok to Bidmillah nagaji ne, ya d'an rumtse ido, sai da ta harareshi sannan takai hanu ahankali kaman mai shirin tab'a wuta tafara matsa masa k'afa kaman zatayi kuka, bud'e ido yayi ya sauk'esu akan hanunta, da sauri ya kamo hanunta yana kallon zoben dake jikin yatsanta, ya kalleta waya baki wannan zoben?
Akan mirrow na d'auka,
"Mhmm kinsan zoben waye da kika d'auka?
"Nasani Na Goggojina ne da tabaka, a ruganmu ta fad'a tana murmushi cike da shauk'in rugan nasu,
"Ok ashema kinsan agabanki ta bani kuma kinji abunda tace min kan zoben shine kika d'auka?
Turo baki tayi tafara hararan gefe, saboda ya tsareta da ido bayanda za'ayi ta harareshi,
Ya d'an matsa yatsunta acikin tafin hanunsa, sai da tayi k'ara yace gayamin abunda tafad'a,
Ta b'ata rai tace "cewa tayi inka auri matar da kakeso kasamata,
"Ok shine bari kiriga matar da nakeson sawa? To awani dalili kikasa?
Ta fincike Hanunta tana fad'in ai sai kanimi wanda zaka sakamata badai Zoben kakataba, wlh bazan bayarba kaje kasuwa kasayo mata, tafad'a cikin b'acin rai tana k'ok'aerin tashi ya kamota, "Malama kizo ki cireumin zoben Masoyiyata tun ranki bai b'aciba, har ni zakiyi wa gorin kaka? Ai naga tana kallonki anma taban inbaiwa Nafisa na,

Wani irin kuka ta fashe dashi da yabashi mamaki, ya Rungumota yana Rarrashi sai zamewa takeyi ya kama hanunta zai cire ta tusa hanunta tsakanin cinyoyinta ya fara mata Cakulkulkuli, ta dinga da mutsu2 tana dariya har da hawaye, Nan k'iran Mami ya shigo Wayansa, saketa yayi ya d'auki wayan da sllama, tana Amsawa ta d'ora da kasameni yanzu ina d'akin lya,


D'an jim yayi cikin tsoro yana kallon Dijah da ta kwanta luf ak'asa tana maida numashi, a hankali ya mik'e ya d'auki jallabiyansa ma guntun Hanu ya zira, ya juya zai fita,

Ahankali Khadijah tace "Likita! Juyowa yayi ya kalleta, ta tashi ta zauna tana kallonsa, "lna zakaje?
"Kaman bazaiyi maganaba yace Mami ce ke k'irana, ta tashi da sauri ta d'auki himar d'inta, tana zirawa tace "zan bika, d'an had'e rai yayi yace "ki zauna yanzu zandawo, tayi rau2 da ido kaman zatayi kuka, "dan Allah zan bika "wlh tsoro nakeji, juyawa kawai yayi tabi bayansa a falo yatsaya ya had'iye k'wayoyin da yake sha na danne sha'awa tun zuwan Khadijah pert d'insa, sannan suka fita, duk tunaninsa Mami zata k'wacetane,


Suna shiga ta zauna a falo tana kallo shi kuma ya shiga d'akin lya,


Kusan Mamin sa ya zauna rai a d'an jagule, ya musu sannu,


Mami takaleshi tana b'oye damuwanta, tace "Ni Kabir naga Gobe d'aurin aurenka banga kana wani shiriba duk da dai kunriga kungama, ahanzarce ya d'ago ya kalleta k'irjinsa na bugawa, yace "Mami na zaci ai and'aga sai na k'ara samun lfy, Mami ta zaro ido tana kallonsa, "Wani lfy kuma Kabir? Bayan wanda kake da ita yanzu, kumama ko baka da lfy ai bazai hana d'aurin aureba, dambe akace kayi bare kace?


Mhm kaifa da kanka ka k'ak'alo aurenka da kanka Kabir Gobe dai in Allah yakaimu za'a d'aura aure da 11:00, sai kayi waya tun yanzu ka k'ira masu aikinin gidanka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login