Showing 30001 words to 33000 words out of 155892 words
yana jinsu amma bai tankamusuba, harsaida suka gama
Kb yace ya maidashi gida kafin suka dawo,
Ak'ofar Gida suka samu Dijah tana zaune Akan Dutsi tana rik'e da k'ananun duwatsu tana cillasu sama,
Tundaga can nesa Kabir yake k'aremata kallo harsuka iso, da ace wata yarinyance mai mutunci sai ya yaba ma kwalliyanta don shi yanason dressing d'in fulani yana masa kyau sosai,
Kayan fualanine irin farare tas d'innan Riga da zani anmishi ado da ja da green d'in zare tajera abun wuya farare sur wuyanta ga wani ta ke waye kanta dashi ya sauk'o har goshinta gashinta yasha gyara saidai har iyau fuskanta ba kwalliya,
Sani da yake atabayansa yana kallon irin kallon dayake wa Dijah itakuwa ta wutsiyan ido take kallonsu,
azahiri zakace batasan da wanzuwansu agunba, da gayya Sani ya turoshi gab da ita, dagangan ta d'ago wani k'aramin dutse kaman zata cafe shi yanda takeyi, kawai ta k'wala ma Kb a idon sawunsa,
Ya salam! Sani ya fad'a yana kallonta zabura tayi kaman da gaske ta kalli fuskan Kabir da yaciza lip d'inshi nak'asa dan ba k'aramin zafi yajiba, hanunta biyu ta had'a cike da shak'iyanci tace "dan Allah kayi hak'uri Gurgu d'an birni ban gankabane, ππΌπ°
Cikin zafin nama ya mik'o hanu da nufin damk'ota sai dai ina tuni ta mik'e har ta isa dai dai k'ofan da zai sada ta da cikin gida, ta juyo ta kalleshi ta kece da dariya har tana sunkuyawa k'asa tana rik'e cikinta, π€£
Sai da tayi mai isanta, sannan ta fara tafa Hanunta tana fad'i "Eh walale walale walale wa aka jefa wa yayi jifa Gurgu d'an birni, waya tab'o?
Dijahn Baffa waya gayamaka za ka iya? Eh jama'a kuzo kuga gurgu d'an Birni wai shi zai jah da Dijahn Baffa, kugayamasa yayi kad'an,
Tak'arashe wak'antan da wani irin dariyan shak'iyanci tana zaro harceπ
Duk yanda Sani yakai da son danne dariyansa dan kar yak'ara fusata Kabir abun yaci tura sam shi baisan shak'iyancin Dijah yakai hakaba sai yau,
Kanta Sani ya nufo kaman zai kamata ta arce cikin Gida aguje caraf Inna ta kamo Hanunta cike da tsoro da mamaki don sam bata tab'a tsammanin akwai wani abu tsakaninsuba, sam batayi tunanin Dijah zata musu Rashin mutuncintaba, kasancewansu bak'i agarinma baki d'aya, donko da tajiyota tana wak'a batagane dasu takeyiba sai da Bintalo ta gayamata,
Janta takeyi har sai da ta kaita gindin Bishiyan lallen da yake gidan tana k'ok'arin ciran bulala, don wannan karonka batajin zata k'yaleta duk irin abun da takeyi takan zuba mata ido,
Cab d'i Sai dai inaga dad'ewan da Inna tayi bata kama Dijah da sunan duka ba shiyasa ta mance halin Dijah awajen duka, sai dai yanzu tana ta tunamata, don kuwa wani iri k'ara da ihu da Dijah takeyi nema ya hana innan katab'us gashi ta rik'e bulalan, sai kururuwa takeyi don Allah inna kiyi hak'uri inna bazan sakeba wayyo na shiga uku wayyo idona wayyo wuyana wayyo jama'a innata zata kasheni inna kiyi hak'uri,
Alhalin ko kallon banza innan bata fara mata tukun, sai tsalle takeyi duk wanda yaji irin kukan da takeyi zai d'auka ana gab da kasheta tsaban duka,
Haka yake gasu Kabir da suke k'ofan gida duk irin haushin da tasa Kabir aciki jin irin tsalle da ihun da takeyi ba k'aramin tausayamata yayiba, gaba d'aya yaji jikinsa yayi sanyi musamman tunawa da yayi akan abun da tamishi innan take suburbud'anta duk sai yaji kunya takamashi,
Tofah kankace kobo mak'ota sun fara cika gidan inna sai dai duk wanda ya shigo sai yaga inna rik'e da hanun Dijah d'ayan hanun kuma tana rik'e da bula Dijahn kuma ta rik'e bulalan tana tsalle tsayawa kawai sukayi suna ba inna baki wasu kuma suna dariya inna kam ba abunda tace kuma bata saketaba dan tasha Alwashin sai ta suburbud'eta ahaka innansu Jebu ta shigo kai tsaye gurinsu ta nufa taje ta k'wace hanun Dijah acikin na inna, dai dai lokacin Baffa ya iso k'ofan gidan ai bai san lokacin da yayi wurgi da kekensa ba ya shige cikin gida ahanya sukayi kicib'us,
Cikin tashin hankali Baffa ya kwato hanunta ya koma ciki da ita abaranda ya tarar da inna,
Ko kallonta baiyiba yashiga d'aki da ita abakin gado ya ajiyeta yafara share mata fuska tayi jajazur da ita kallo d'aya zaka mata kazata tasha bugu har da na A'uzubillah, sai ajiyan zuciya take gaba d'aya ran Baffah ya jagule bayajin zai yima innan afuwa wannan karon donji yake kaman yayi kuka ya huce shiyasama ya wuto da ita d'aki don inyatsaya agun innan yasan baza'ayi mai kyauba,
Ruwa yabata arandan k'asa mai sanyi tasha sannan ya lakato zuma ayatsansa yasa mata abakinta talasa haka ya tayi mata har tayi bacci ya gyramata kwanciya ya fito,
Tofah inda yabar inna anan yasameta gefenta Bintalo ne k'irjinta sai bugawa yakeyi
( *domin da iyayenmu bak'aramin shakkan mazajensu sukejiba kodakuwa suna da gaskiyane basa nitsiwa in sungansu cikin b'acin rai sab'anin mu ayanzu dagangan zakiyi abu dan kib'ata masa rai kai wasu kama har sa insa sukeyi da miji "yar'uwa ko badon ki mallaki mijiba kibishi don shid'in Ajannanki wlh sai kin bishi kafin kishiga aljannah shi namiji yana da wani abu wlh zai iya rufe ido yaci mutuncinki akan abunda shi kansa yasan bayi da gaskiya akai ammma inkinyi hak'uri tun aduniya zakiga sakamako Allah yabamu ikon yin hak'urin bin mazajenmu*ππΌπ)
Tun kafin ya iso cikin dabara ta aiki Bintalo gidan Goggoji
( *don bai daceba kuyi magana na b'acin rai agaban yaranku*)
Cikin b'acin rai yafara magana wato Karimatu ni ban isa in hanaki ki hanuba? Sau nawa ina miki magana akan yarinyannan? Shine dan kin rainani zaki kama kimata irin wannanduka? Fad'a yakeyi ta inda yashiga batanan yake fitaba, har sai da yayi mai isansa kan inna yana k'asa badon batajin zafin kalamansaba don dai koda Dijah "yar rik'oce ba ita ta haifetaba bai kamata ya dinga mata hakan akantaba,
Daga k'arshe yace "ki kwantar da hankalinki tunda kin tsaneta zan d'auketa inbayar da ita agunda za'arik'emin ita da amana ba cutarwa, ai da gangan kike matsa mata dan kinga sunan uwa tace meyasa baki matsa ma Bintalo haka? Saboda sunan uwanki ce da ita, daga haka yajuya yafita, sam b'acin rai ya rufema Baffa ido yamanta da banbancin hali dake tsakani Bintalo da Dijah,
Bintalo takasance mai nitsuwa da hak'uri
Yayin da Dijah takasance mai tsananin fitina tun tana yarinya ga k'iriniya ita dai sauk'inta batacikayi ma babba Rashin kuntaba amma sam Dijah bata da dad'i,
Inna tajima awurin tana Addu'an yayewan bak'in ciki don maganganun sun batamata rai dayawa,
Tunda ta idar da sallahn isha'i taketayiwa Dijah Addu'an Allah ya shiryeta, ahaka har tajiyo shigowan Baffa tafito alokacin Dijah da Bintalo suna zaune ba mai cewa komi,
Da sallama tashiga alokacin yana zaune bakin gado kallo d'aya yamata yakau da kai duk da kwalliyanta yaburgeshi don inna ta iya kwalliya na hankali, wani lokaci inta tsara kwalliya bazaki tab'a cewa arugan fulani takeba,
( *nikam nace inna kodai kwalliyan ban hak'uri da Rarrshine?*) π
Ak'asansa ta zauna daf da k'afanshi ta jiye mishi damammen fura ta kalleshi malam ga fura ko har yanzu fushin kakeyi dani? To inma fushinne kayi hak'uri na tuba ka yafeni, tafara janmasa yatsun k'afansa
Janye k'afan yayi alamun har yanzu bai huceba ta marairaice to Malam inbaka hak'uraba kamin hukuncin da zakamin Amma don Allah kadaina fushi dani, ahasale yace hukuncin kenan bazaki sake ganin Dijah a idonkiba, tunda ba ki k'aunanta, murmushi tayi tace haba Malam ya za'ace bani k'aunan Dijah ai koban k'aunaceta don tana "yata ba zan k'aunaceta don kana sonta nikuma ai masoyiyarkace,
Don Allah kar son Dijah yasa katake gaskiya kasanfa irin hak'urin da nakeyi da yarinyannan tun bata kai hakaba, kafin kayankemin hunkunci Bincike yakamata kayi,
Saida tagayamasa maganganu masu dad'i sannan tagayamasa abunda Dijahn tayi ta d'aura da kuma wlh ko bulala d'aya banmataba duk wannan karad'in datayi,
Shiru kawai yayi najin kunyan matannasa amma sai ya wayance da aini dama kukantane banaso kinsanfa tana da matsala, don Allah kidinga rabuwa da ita kawai daga nanan dai saiga ma'auratan suna dariya daga baya kam ai sai zance yasauya tsakinn inna da Baffa nikam nace barin ππ½ββ
*Ummu fatima ce* π
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*Ummu Fatima*π³π¬
Don Allah mabiya Novel d'innan kuyi Hak'uri najin shiru dakukayi kwana biyu kumin uzuri kowani d'an Adam yanada uzuri,ππΌππΌββ
Wa irnda sukabini prvt damsu min text a inbox kai Maman Nabil kamma k'irata tayi, wai yataji shiru itafa tamatsu Dijah tashiga Hanun Dr Kb π
Kowa yacemata Dijah tana shakkan Dr kb? π€π
Kai Dukanku ina muku fatan Alkhairi acigaba dagashi insha Allah yanzu ba tsayawaπ€π»
π *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......π
*page* 1β£7β£
Washi gari da safe Dijah tazogaida Baffa kaman yanda tasaba,
Kallonta yaketayi
Haryanzu idonta akunbure yake sam baiji dad'in ganinta hakanba,
Har tamik'e yak'ira sunanta tadawo tazauna cikin lallashi yace "Mamata wai meya had'aki da Kabiru ne tun a Asibiti na fahimci kaman dawani abu tsakaninku sai gashi jiya Innan ku tagayamin abinda kikamasa,
Turo bakinta tayi tace Baffa shinefa ya wurgomin k'adangare jikina,
K'adangare kuma? Baffa yatabaya da mamaki,
Yayi murmushi "kenan kin ramane?
Ta gyad'a kai,
Jijjiga kansa yayi yace "inaga baisanibane Dijah bansanki da fitina da manyan mutane hakaba, karkisake kinji? Ta gyad'a kanta, alaman to,
Baffa yace "maza jeki kaimusu abun karyawansu, kizo ga wankina dakike tafitinan nabaki,
Ince kinyi musu? Tace "Eh nayi, Baffah kaciro wankin duka zan iyayi wlh kuma zaifita tas,
Ak'ofan d'aki tasamu Kb yana zaune akan kujeran Roba, yana Rik'e da Littafin Hisnul Musulum kallo d'aya yamata ya d'auke kansa,
Aransa yana tuna irin Ihun datayi jiya, sai yau da safe Bintalo take cemasa Innan badukanta tayiba, shidai yana manakin Halin yarinyan, Anyah bata da matsalan k'wak'walwa? Yatambayi kansa,
Tagefensa tabi tawuce tashige d'akin bayan ta ajiyemusu abun karin sunjima suna Hira da Sani awajen
har saida Kabir yashiga tamik'e tana mamakin ganin sa yana dogara sanda yana tafiya, yaushe ya warke haka? Tayi tambaya azuciyanta, tana ficewa,
Wanki takeyi nakayan Baffanta mai had'e da wasa, saida ta zauna tagama wasa da kumfan sannan ta tashi tacigaba, haka tayi tayi har tagama tana shanya taji ana rafka sallama tad'ago tana Amsawa tana kallon mai sallaman,
Wata Matace fara k'al da ita kyakkyawa, daka ganta kaga Bafulatanan Asali,
doguwar rigan shaddace lemon green ajikinta dayasha aiki tundaga Sama har k'asa da Babban mayafi kalan zaren da akayi aiki ma rigan golden takalmi da jakanta ma golden ne tana sanye da farin glass a Idonta, Mamy kenan, itanma kallon Dijahn takeyi fuskanta d'auke da murmushi Beutiful baby, tafad'a tana matso Dijah ganin haka yasa Dijah k'arasowa ta karb'i d'ayan trolin datake ja tana fad'in sannu da zuwa haryanzu Mamy murmushin takeyi, Dijah tanufi d'akin inna kicib'us sukayi da Inna lokacin tana fitowa da kaskon turaren wuta ahanunta ganin Mamin yasa ta ajiye kaskon da sauri abakin k'ofa tana d'an tafa hanu "Lale maraba da zuwa Hajiya sannu sannu kece da tsakar ranan nan? Tabarman Roba ta shinfind'a mata atsakar d'akin tana jeromata sannu,
Mamyn sai amsawa takeyi cike da fara'a,
Dijah kuwa tana fita batatsaya ko inaba sai shagon ilu ta dawo fa peur water mai sanyi ta shige kitchen ta d'auko plate ta juye takai gaban Mamy ta durk'usa ta'ajiyemata, Mamy tana murmushi
takamo hanun ta "Meye sunanki? "Dijah, tabata Amsa tana d'an Murmushi "Allah Sarki Khadijah tul kubra,
Kina zuwa makaranta kuwa? Ta gyad'a kai tana murmusawa, ajinki nawa?
"Ss1, very Gud islamiyyafa?
"ina islamiyya4 Haddah 3
"to Khadijah Allah yataimaka ko, daidai lokacin Inna tashigo da dammamiyar Fura da soyayyun zabi ta'ajiye agabanta, tana fad'in "Bismillah Hajiya karkibiye ma wannan surutacciyan, Dijah ta tashi tafita Mami tana dariya tace "Ayyah Inna kingg koremin ita, Ifna takwara tace?
"Mnn Bitalo ce tatafi kitso, d'azunnan,
"Ayyah ita nasani bantab'a samun Khadijah agidaba, duk zuwana biyunnan,
"Eh wlh baku had'uba kam, dake akan k'afanki kk komawa, Amma yaukam kwana zakimana ko?
"Eh inaga zan kwan in Allah yakai Rai gobe sai inwuce,
"to Allah yasa muna raye, Kici Abinci Hajiya Dan Allah,
Mik'ewa Mami tayi tana Ffad'in barin lek'a Marar lafiyannan tukuna indawo,
Can gindin Bishiya ta hango Dijah tana carafke tayafatota da Hanu, dasauri Dijah ta tashi tana kad'e Hanunta ta isota, Mami ta kama Hanunta "Haba Khadijah ba'asan student da wannan wasanba, Inna da take fitowa ad'aki tace "ai wannan student d'in sai ahankali, Mami tayi dariya tace "muje kimin Rakiya,
Tana rik'e da Hanunta suka shiga pert d'in da sallama Mami tad'aga labule, alokacin Kabir yana zaune da Lap top agabansa, Sani da Habib suna gefensa,
Suna Hira cike da Nishad'i Kallon Mamin yakeyi Fuskansa d'auke da bayyananne farin ciki, sam Habib bai cemasa tare da Mamin sukazoba,
Kujeran Roban dake gefen Kb Mami ta jawo tazauna, ture system d'in yayi gefe ya Matso ya d'aura kansa a gwiwowin k'afanta yasauk'e Nannauyan ajiyan Zuciya, Kaman uwar da taga d'an daya b'acemata tsawon lokaci,
Yakamo hanunta ya d'ora akansa, Dariya sosai Mamy takeyi tana shafa kanshi "My luvly son ya kk? Ya jikin? Wani farin ciki yakeji yana ratsashi gashi ga Mamin sa yad'ago yana kallonta "Mami da ga safe zuwa yanzu munyi waya yakai 3 times bakicemin kina hanyaba Why?
"dama naso inmaka suprise ne,
Amma naji dad'in ganinka my Son kayi kyau sosai, gaskiya Sani kana kula dashi da kyau, Sani yana dariya yanuna Dijah da ta daskare awajen dan mamaki aranta ko sai gulma takeyi "k'ato dashi yana ta wani sakalci itakuma sai biyemasa takeyi, "ga wacce take kulawa dashi nan Mami tadafa mishi wannan tadafamishi wancan ba dare ba Rana, yak'are maganan yana kallon fuskan Kb da yake hararansa, Mami ta dafa kan Dijah datake zaune ak'asa gefenta, tace "Ayyah Khadijah yarinyan kirki, bani da bakin musu godiya sai Addu'a,
"Mami ina su uncle ne? Kb ya tambaya don son b'atar da zancen,
"suna nan sunce ingaisheka, ba last weak sunzoba,
Nafisa fa baka tambayeni itaba karkaga yanda duk ta lalace wlh Kabir, kasan Yaya yahana asanar dasu cewa kananan har yanzu akan ba asan inda kakebane,
Kabir yad'anyi Murmushi yace "Mami kodai Sangaya zakiminne? Auren mata biyu lokaci d'aya, wancan yarinyanma kusan kullum sai ta k'irani, kuma tace kekabata no. na,
"Hakanma zaifi wlh Mami a auramasa su dukansu kinga ma shikenan wlh nanda nan zai taro sa'anninmu da sukajima da aure harda "ya"yan nan, Habib ya fad'a cike da zolaya,
Kb yabishi da harara "dallacan Malam wayasaka bakinka anan, Sani yace "to ai naga duk suna sonkane kb wazaka ki acikinsu ai kawai hakan shine mafita a auramaka su kawai rana d'aya musha Biki π
Murmushi kawai Mami tayi dan ta lura sun maida abun sakarci tace "karku damu koma dai ba amuku sangaya ba nasan yanda za'ayi, daku dashi ai duk kanwan jace,
Tamik'e rik'e da Hanun Dijah, Kabir ya Marai raice fuska Mami ina zaki je kuma? Kofa gaisawa bamuyiba,
Zanje mugaisa da maigidan Kabir ina dawowa,
Mami kam ba k'aramin yaba wa Baffa da iyalansa tayiba irin nanda nan da sukeyi da ita don tunda Baffa ya dawo yaganta Yake ta fita da shigan kawo wanan kawo wancan,
Da Daddare bayan Mami ta idar da Sallah ta je pert d'insu kb a waje ta samemesu zaune akan darduma tunda suka gama cin Abinci basu tashiba,
Itama agefensu ta zauna, Dijah ma tazauna agefe sun d'antab'a hira Habib yace ma Sani yazo sufita suga gari,
Sukafita yarage daga Mami sai kb da Dijah, kabir ya kalli Dijah yanda ta nitsu kaman wata mutuniyar kirki, had'e fuska yayi cikin tsawa yace ke dalla kiba mutane wuri, sunkuyar da kanta tayi tana shirin tashi Mami tarik'eta tana masa wani irin kallo, "yahaka Kabir? Me tatsaremaka anan?
"Mami zamu yi magana irin na d'a da uwa, "itama "yata ce Kabir ashe haryanzu kana nan da halinka, baka canzaba, ba ason ransaba Dijah tazauna agurin suna Hira, itama Dijah hakanan tajita kaman akan k'aya sosai takejin nauyin Mamin,
Sunjima suna tattaunawa Harsaida Mami taga Dijah tafara gyngyad'i sannan