Showing 90001 words to 93000 words out of 155892 words
da kayanta, da k'arfi ya ciremata kayan yasamata Rigan baccinta, ya kwanta yajawota ya kwantar da ita kanta yana kan k'irjinsa yadinga mata susa tundaga Kanta har gadon bayanta, tuntana mutsu2 har bacci yayi gaba da ita,
Basu suka farkaba har wajen 12:00 na Rana, wayan Mami ya farkar dashi, ahankali ya mik'a hanunsa ya d'aga yakara akunnensa, "Hello Mami,
Mami tace "Haba Kabir wannan wani irin Baccine? Kusan sau uku ana kawo muku abun break, anyi knocking anyi knokcing shiru? Ina Khadijah? Ahankali ya zare jikinsa acikin nata yatashi yazauna yana fad'in Wlh Mami jiya bansmu nayi bacci isasshe bane, nace "ina Khadijah? Yad'an kalli inda take tana motsi alaman zata tashi, yasa Hanu yana wasa da gashin kanta, yace "inaga tana falo Mami, batanan, Jinjijina kai tayi ta kashe wayan,
Ya gangara da Hanunsa ya shafo k'irjinta, dai2 lokacin ta farka, ta tashi ta zauna,
"Mn jeki ''had'a mana Ruwan wanka, hijabinta ta zira sannan ta shiga toilet, ta had'a tafito, narkewa yayi dole saida ta rik'eshi ya tashi, suka shiga bayan gidan tana k'ok'arin fita ya rik'ota "aike zakimin Wankan ni bazan iyayiba, zaro ldo tayi waje
"Ni kuma? Wlh bazan iyaba,
"To inbakiyiminba wa zaimin? Tunda kikazo jinya aikomi ya hau kanki,
"mnnn to barin cire hijabina, kar yajik'e
"to yace gami da saketa, tafara kiciniyar cire hijabin tana matsawa da baya tana zuwa jikin k'ofa tayi saurin bud'ewa ta fice da gudu ta rufo k'ofan,
kai tsaye bayan gidan falo tashiga tasa key sannan tahad'a Ruwan wanka tashiga tajima aciki kafin tayi wankan tafito, afalon tasameshi rik'e da remote yana kamo tasha, yasha kwalliya cikin jeans da Ash d'in shirt, sai baza k'amshi yakeyi, ta wuce, kwalliya tayi sosai tasa Riga da sket na jan Material, mai bak'in flawers, fashion din jajayen sark'a da abun hanu tasaka, bak'aramin kyau tayiba, tana zaune akan stool tana fesa turare kb yashigo, kallonta yakeyi har ya iso gabanta ya tsaya rai ab'ace yace "kar ki kuskura kisake shiga toilet d'in falo, kinajina? Yanzu inda kin fito kinsamu wani afalonfa? Ko bakijinane bazaki amsaba?
Ta dago Ido araunane ta kalleshi, tace "Naji bazan sakeba,
"Gud yafad'a ya juya har yakai bakin falo, yajuyo yace ana nocking, kizo kije ki bud'e, daga haka yafice,
Saida tasa Hijab taje ta bud'e mai aikin Mami ce ta gaida tare da tambayanta mai jiki, ta mik'o mata abun kari,
Tana ajiyewa tashiga kitchen ta d'auko cups,spoons da plates, ta dawo, ta zuba ta tura masa gabansa, ya kalleta "what do you mean? Aike zaki bani baby yafad'a yana d'agamata Gira, zatayi magana ya jawota jikinsa, ya mik'amata spoon ba yanda ta iya haka tayi tabashi kaman k'aramin yaro, sannan ya karb'a ya mannata a k'irjinsa yayi tabata,
Bayan sungama ta gyare pert d'in gaba d'aya, tasa turaren Wuta sai k'amshi ke tashi,
Ta dawo kusa dashi ta zauna kallonta yayi da Alaman magana abakinta ya jawota ya d'orata akan cinyanshi, yasa hancinsa wajajen wuyanta yana shak'an k'amshin dake tashi ajikinta, idonsa alumshe, yace "What is ur wrong baby?
D'an zamewa tayi daga cinyansa tayi k'asa tana kallonsa, shima kallonta yake yana lumshe ldo kaman wanda bacci mai tsanani ya kamashi,
Cikin marairaicewa kaman zatayi kuka tace "kace da safe zakasamu Mami kamata magana inkoma, shiru yayi na lokaci suna kallon juna, can ya nisa yana d'an yatsina fuska ya lalumo wayansa, yace "ba Mami bace ta creating Maganan, su Uncle ne barin k'irashi, yana danna waya, asanyaye, ta dafe Hanunsa idonta taf da hawaye, tace "Dan Allah kar kakira Uncle,
"To yaya kkson anyi? Dole shine zai san abunyi,
Ta girgixa kai hawaye nabin kuncinta, nasan Halin Uncle bazai barniba,
Hanunta yakama yana murzawa, "to meye na Kukan Khadijah? Indai bakison ak'irashi to kik'ara hak'uri mana, nan da 'yankwanki za'a d'aura Aurena, ana auren nasan zai sallameki tunda inada Mata, da sauri ta k'wace Hanunta acikin nasa, tasaki kuka mai sauti, k'irjinta sai bugawa yakeyi,
Jawota jikinsa yayi yana kissing d'inta tana zillewa, yasa bakinsa a kunnenta, "Tsaban kin tsaneni shine bazaki iya jiran wannan lokacinba?
Tureshi tayi tace "Bazan jiraba mezai hana yanzuma ta dawo ta zauna da kai?
"ina kikaga antab'ayin haka?
"kukan kunsaba har abunda yafi haka kusan ini takeyi ad'akinnan, kai zan iyacewama kwana akwai randa naga tafito ad'akinnan cikin dare ina duba agogo naga 1:19 na dare,
K'uramata ido yayi har takai Aya, yasauk'e ajiyan zuciya yana mamakinta, ya tuna Ranan da akayi hakan, Nafisance ta masa waya cewan takasa Bacci sabida tsananin ciwon ciki da takeye na piriod, yace mata ta bari da safe yamata Allura anma tak'i tazo ta dinga masa knocking dole ya bud'e k'ofa yamata, aggagauce yamata baiko bari ta zaunaba yace ta tafi dare yayi,
Wato yarinyannan takan samasa idone aduk al'amuransa? Ko kuma tsakaninsa da Nafisane kawai take masa hakan? To meye dalilinta nasamusu ldon?
Ganin tana shirin tashine ya jawota yazaunar da ita,
"Khadijah meyasa kike da zargi? Da kinga abu sai ki fassarashi yanda ba haka yakeba, Why? Meyasa kike min Mummunan zato, ban tab'a kusantan abinda kike zargina dashiba, inason wannan yazama Rana na K'arshe da zaki daina Zargina da Nafisa, Ya k'arasa maganan yana sharemata Hawaye, "Sannan idan dan zamanki ananne bakiso to ni nasan hanyan dazanbi ki koma wajen Mami, Amma sai kin kwantar da Hankalinki kin nuna ma kowa da son ranki kike zaune dani sannan kinbi duk Umurnin da nake baki,
Kisani duk irin son da Mami take miki indai kika fito fili kika nuna mata bakison Kabir tofa son datake miki acikin kashi d'ari zaki b'arar da Hamsin, dan haka ki kwantar da hankali, nan ba da dad'ewaba zaki tafi abunki, koda cuta zata kasheni cikin dare zan san yanda zanyi,
Sosai Jikin Dijah yayi sanyi da lafazinsa na k'arshe shima ya lura da hakan, dan haka ya jawota jikinsa suna shak'an numfashin juna,
Can sukaji ana niman order, d'agata yayi daga jikinsa yace ta d'auko Hijabinta taje ta duba,
Tana bud'ewa taga Sauda da Habib da murna suka rungume juna, Nan Habib ya wucesu yana Murmushi, sai da suka gama Murnansu suka shigo ciki, kusa da Habib Sauda ta zauna ta gaida Kabir, Dijah kuma kitchen ta wuce kawo musu abun tab'awa, sai da ta cikasu da fruit da drinks ta zauna ak'asa d'an nesa dasu ta gaida Habib,
Sauda ta d'auki kankana ta kalli Habib Honey ga mutuminka bakinsa ya mik'o tasa masa, yana sha, wani mummuna kallo Kb yajefesu dashi, da sauri Sauda ta b'oye Fiskanta abayan Habib, fito da ita yayi yana Hararan Kb "yi shiru abinki my Soul bud'e bakinki bud'ewa tayi ya d'ago kankana zai samata, Kb ya d'auki goran Ruwa da d'an sauran kad'an aciki ya wurgeta dashi, Habib yayi saurin cab'ewa yana Zaro ido, "Haba Man inda kasametafa?
"Ke tashi kifitamin anan, banson Rashin kunya kinaji?
Shagwab'ewa tayi "yaya Kb sakamakon zuwa gaishekan kenan?
"Eh bana son gaisuwan, "Allah daga yau konazo bani k'ara shigowa nan, "Naji tashi kifita karkisake shigowa, kuma inkika sake wani magana anan zan tashi intakaki, inkina gadaran aurene dake da auren da Mijinkin sai intakaku, Habib ya kwashe da dariya wlh Baka isaba yaya Kb, Sauda kam mik'ewa tayi ta kamo hanun Dijah da tayi Mutuwan zaune tana kallon ikon Allah, "muje mugaida Mami,
Suna fita Sauda ta kwashe da Dariya, "wai meke faruwane Mutumiyar naga duk kin wani diririce?
"mhhm Aunty Sauda wai dama kowa tayi aure sai tazama mara kunyane?
Dariya ta kuma kwashewa dashi "Rashin kunyan me Khadija? Ai dama zama da na miji sai da Rashin kunyan indai wannan shine Rashin kunya, to ai baki ga komiba, inyi kikayi sake yanzu sai wata can ta k'wace miki Miji,
Dijah ta tab'r baki "mhmm Allah ya kyauta,
Sauda ta rik'o Hanunuta "Khadijah yakamata ki tsaya ki fuskanci rayuwan aurenki wannan game d'in yatsaya haka, kinci wsan taurin kaine kawai irin naku, Dijah ta turo baki, "Ni bawani zaman aure da zanyi kina ga har yanzu yanakan bakansa na auren wancan Banzan, nidai badani za'ayi wannanba,
"Waya gayamiki za'ayi auren? Kuma ma in anyi sai me? Ai zamanta daban naki daban, kowa tata ta ficceta, ai zama fa kishiya ba wani abu mai tsananibane illa yakansa mace ta k'ara k'aimi wajen niman Alajannanta, "nifa bazan iyayin abun da kike saninnanba wlh,
"zaki iya harma fiye da hakan muje mufito yau zan baki wani Assigment guda d'aya tak, dai2 lokacin suka shiga ciki, da sallama d'akin lya suka fara shiga,
[8/4, 4:50 PM] Ummu Fatyma: πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*UMMU FATIMA CE*π³π¬
π *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......π
*Jinjina da Godiya gareku mai tarin yawa,* ππ»π€π»
*Group d'in Mum Meenat* _(Mijin k'waila)_
*Batul Adam Jatko* _Damata Group_ 3β£
*Aysha Ali Garkuwa* _Fans Group_
*Huguma Conversation* _Group_
*Sawwama AG* _Group_
*Zuwaira UmmuMaryam* _Group_
*Dijah Qayah* _Fans Groups_ π
_And oll *Kainuwas groups Fans* π
_Sosai nake jin dad'in zama acikinku_ π€π»π€π»π€π»π€π»
_Allah yabar so da k'auna_ ππΌπ
4β£9β£
Basu sami Mami a faloba dan haka kai tsaye d'aki suka nufa, zaune take a bakin Gado tana duba wani littafin Addu'o'i, Nan ta musu lzinin shigowa, tun shigowansu Dijah take ta sinne kai k'asa,
har suka zauna idon Mami na kanta, Dijah ce ta fara gaisheta tana nok'ewa, Mami ta rik'e Baki "yau Khadijah nikike kunya? Ko me?
"Mami Fushi nakeyi,
"Fushin me kuma Khadijah na?
"Bake bace... Sai kuma tayi shiru tana turo Baki,
"Bani bace me? Mami Ta fad'a tana d'an Murmushi, sannan ta dubi Sauda dake Gaisheta, suka Gaisa, Hira ta d'an fara jan Saudan dashi,
Khadijah ta cire Hijabinta "Mami meza'adafane?
Mami ta kalleta "Na hutar dake da aikinnan Khadijah aikin pertd'in kuma ya isheki, kedai kar kibari Kabir ya koyamiki wannan Baccinsa, tun yana d'an k'ank'ani yake fama dashi har yau baidainaba, tun inatunanin baida lfy ne har nagane d'abi'arsace inaga sai yafara tara yara hayaniyansu zaisa yarage,
Kina idar da Sallah inkingama Azkar d'inki ki tashi kifara ayyukanki, Sannan ki tambayeshi in akwai abunda yakeso sai kidafa masa, inkuma yaci Abincinmun shikenan, yanzu tunda kinshigo kuje Sauda ta tayaki, ku masa Cuscus da kayan lambu,
"To Dijah tace sannan ta mik'e tana tattauna Maganganun Mami, tana tuno Abunda kb yace *Duk irin son da Mami takemiki, inkika nunamata bakison Kabir Acikin kashi dari zaki barar da Hamsin* nayarda tafad'a k'asan mak'oshinta,
Acikin Mintuna kad'an suka shirya k'ayataccen jalof d'in Cuoscous gami da Kunun Aya dayaji kayan had'i kwakwa, soyyayiyar gyad'a, kankana, Dabino, da Cucumber, k'ank'ara tasa aciki, ta ajiye a frich, Sauda ta kaima Mami, Dijah kuma su Kb, tadawo ta kaima lya nata, zaune tasamu lya tana kallo ta'ajiye agefe ta haye cinyanta, zaro ldo lya tayi "Ke kina haukane zaki k'arasani? D'agani ko yanzu inyik'iran Uwanki, tafad'a tana Mutstsininta, Dijah ta tashi tana sosa inda ta mutsineta tana dariya, "lya Ashema baki da k'arfin sisi Ranan kikace in anhad'amu tsere zaki wuceni,
"To kisa kud'imana ja'ira natabbata zan baki Kunya, Malam ma da in muna tsere dashi acikin Gida wuceshi nakeyi bari kiji, Dijah ta zaro ido "lya wai tsere kukeyi da Malamd'in?
"Mezai hana ancemiki ni bak'auyuwace irinki? Anaso anakaiwa Kasuwa, yo innice da Malam baida lfy k'ofa takashi bani takawa, inan jikin Mijina da yamotsa zance mekakeso? Shiyasa kinganmu muda bamusan Hawan Jiniba, saboda munsan yanda muke tattalin mazanjenmu, basa bamu matsala, sab'anin ku yanzu da sam bakusan yanda zaku zauna dasuba, shiyasa abu kad'an kaga yarinya k'arama wai da Hawan jini, Kidaina nok'enok'e kibi mijinki kinaso kina yauk'i
Dijah ta turo Baki "ni bance mikiba lya kinga banso, kuma wayace miki wani hawan jini wani kesawa? Ciwone daga Allah,
Iya ta kamo Hanunta, "Tom zo kixauna inbaki Misali da kanki,
Yanzu gaki da Mijinki agida d'aya tsawon Lokaci baki tab'a nuna kulawa akansaba matsayinsa Na mijinki, yaci Abinci bai ciba? Ba Ruwanki, yafita aiki ya isa bai isaba? Baidamekiba, Ranshi yab'aci waya b'ata masa? Bakisaniba, Magana mai dad'i baya shiga tsakaninku, bare irin d'an kirsannan na Mata, maijan ra'ayin Namiji, Anma Kullum kina jikin Window kina lek'enshi da wata, duk lokacin da kika gansu tare sai k'irjinki ya buga, kwanan nan naga yabar wayansa a falo kika d'auka kina masa bincike, to gayamin meke haddasa Hawan Jinin? Kicemin sa abun b'acin rai a zuciya, to Amma da kinbishi kin koyamasa Sonki azuciyansafa? Zai saurari wata? To koma zaiyi bazai bari kiganiba, dan gudun b'acin Ranki, anhallici Zuciya akan son Mai kyautatamata, kizauna dai sakarcinki ya kaiki ya baro, tafad'a tana tashi, kinga ni barinyi Sallah kar ya k'ure in kunne yaji,... daga haka tashige toilet,
Mik'ewa Dijah tayi akasalance ta fita, tsaye ak'ofa ta iske Sauda tana sauraransu, Hanunta Sauda takama suka k'arasa cikin falon suka zauna, Nafitomana da Abinci, naga shiru baki dawo daga d'akin lyaba, nabi bayanki, Wlh Khadijah Iya kad'ai inzaki d'auki abunda take gayamiki, ina mai tabbatar miki Baki da sauran wata Matsala dan yanzu nima na k'aru a cikin Magananta,
Assigmentd'in da zanbaki Khadijah k'waya d'ayane tak, Shine kizamo mai biyayya cikin duk abunda yaya Kb zaisaki duk abunda yace kiyi koda ranki baisoba, Wannan kad'ai nabaki, Sauk'e ajiyan zuciya Dijah tayi tafara cin Abinci tana sauraran Sauda,
Hira sukeyi cikin Hikima Sauda take nusar da ita har suka gama cin Abincin Sauda ta kurb'i kunun Aya ta kalli Dijah "Kai anma Kunun nan yayi dad'i Khadijah Sosai Khadijah, "Kin kuwa san sirrinsa? Kai Dijah ta girgiza,
Ke duk Macen da tajuri shan wannan wlh ba'ita ba had'a hanya da kishiya ko sun had'a ko zata rainan kanta, Ke wlh ko Nononki bazasu zube, Dijah kam sauk'e kanta k'asa tayi dan ita kam har ga Allah irin wannan Maganan yana bata Kunya,
"Waya koyamiki?
"Bintalo, ai Aynty Binta inkinje gidanta kullum zaki samu a frich d'inta,
Sauda tayi Murmushi, wato har yanzu bakinki bai daina cewa Bintaloba ko?
"Wlh, amma dai yanzu nafara Mance Sunan, sai kuma tayi raurau da idonta,
Sauda tace lfy?
"Baffana Aunty Sauda da lnnata ina matik'ar son Ganinsu, yanzu kusan kullum sai nayi mafarkinsu, ta share k'wallan da ya gangaro mata, Sai kuma tad'anyi Murmushi da kuma Aminiyata Jebu abokiyar k'iriniyata, inason zuwa Ruganmu, inafama da kewansu, tafad'a araunaniya,
Cikin tausayi Sauda tace "ki kwantar da Hankalinki Suna cikin k'oshin lfy, zakije kisamesu, Khadijah saura kwana kad'an kigama Makarantanki nasan Mami zata kaiki tunda tamiki Alk'awari, dai2 lokacin wayan Sauda ya hau ruri tad'aga "Helo my Honey, Ayyah Honey kabarni sai can yamma kazo kad'ukeni, Haba mintuna nawane dazakace baka iya zama baniba, can kuma tace shikenan gani fitowa wlh kai kafai daru,
Dijah dai tattare wajan tahauyi tana sauraranta, takai kitchen ta wankesu ta ajiye, ta fito dai2 lokacin Sauda da Mami suka fito suna sallaman juna, Dijah tashige d'aki ta d'auki hijabinta tafito suka fita a zaune suka tarar dasu a k'ofan pert d'in, Habib yana fad'in "kokak'i ko kaso Malam yarinya ta maka Game over, tirjewanka na banzane, kuma wannan furucin ko k'aramin yaro yaji yasan fad'a kakeyi,
Tsaki Kabir yaja "kaima kasan ban tab'ayin magana biyuba, ince no indawo ince yes,
Mik'ewa Habib yayi yana dariya, su Dijah suaka shige ciki dan anan Sauda tabar jakanta, suna shiga ta d'auka suka sake fitowa, Da Gayya Sauda tada'an kwantar da Kanta ajikin Habib da suke magana da Dr Kb, "Honey Mutafi kaji? Hanunta ya kamo suka juya da ido kawai Kb ya rakasu, ya kalli Dijah datake gefen Sauda zata musu Rakiya, yace "Ke Khadijah! Tsayawa sukayo dukansu, suka kalleshi, "dawo yafad'a da gadara (kunsan Kabir) d'an jim tayi, sannan tayi baya, Aunty Sauda sai anjima mungode daga haka ta shige ciki, Habib ya ja Sauda suna dariya suka tafi, yana zaune agun ya sak'a wannan ya kwance, yana kallon wayansa da k'iran Nafisa ke yawo akai, kaman bazai d'agaba, dan so yake ya hukuntata da zaman gidan Meena da takeyi a yanzu, d'auka yayi ba tare da yace komiba, har ta gama magananta, "ok kawai yace yakashe ya tashi ya shiga ciki, Zaune ya samu Khadijah, a falo ta sha kwalliya cikin English wears bak'ak'e Riga da sket masu santsi gami da kwalliyan Net ajiki, sai wani addababben k'amshi takeyi hanunta rik'e da temot tana canza tasha, yi tayi kaman bataga shigowansaba, yatako ahankali ya kwanta gami da d'ora kansa acinyanta, yana kallonta, yana shak'an k'amshin dake tashi ajikinta, ahankali kuma yafara karanto d'an damuwa afuskanta, yamik'a Hanu yana k'ok'arin sawa cikin Riganta, da Sauri ta rik'e Hanun sai alokacin ta kalleshi idonsu ya had'u,
"Danna hanaki raka wa incan marasa kunyanne kike fushi? Girgiza kanta tayi to meye? Bakiso dawowa nanbane ko? Girgiza kai ta kuma yi, "tam gayamin meke damunki?
"Kainane yake ciwo,
"Bake bace kikak'i yin bacci jiyaba,
'Dan Murmushi yayi "wai kam tsoron me kike ne Khadijah,
"Ni banason duhune yau a falo zan kwana,
"olright da jiyanma falon kika fito kika samu kikayi Bacci ai dayafi miki, yatashi yasauk'a k'asa, yana kallonta, fuska ad'an had'e "Banci Abinciba, yunwa nakeji, ta tashi ta nufi dining ta d'auko kayan Abincin, ta kawo gabansa ta jera, ta zuba masa, da ido ya mata alama da tabashi abaki, saida ya cinye ta