Showing 15001 words to 18000 words out of 155892 words

Chapter 6 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

444

abubuwan dazai buk'ata,
"Sani ya kalleshi cike da zolaya "Mami tana ta mita wai ita kam ta gaji da halinka kullum sai ta tsaya akanka kake shiryawa kaman k'aramin yaro ita kam aure zatamaka ta huta,
Da k'afa Kabir ya wurgoshi da wani cup, Sani yakauce da sauri yana dariya
Atsaye yasamu Mami tana kallon agogo, tana ganinsa tazabga masa harara, kansa ak'asa yana murmushi yak'arasa wajen dining yaja kujera yazauna, tana zuba abincin tana tura mishi gabanshi, tana mitan k'in yarda dayayi yatafi ajirki, "mmn Mami nifa nafison intafi amota indai k'asannane, yafad'a yana mik'ewa to Allah ya kare Kabir kayi Addu'a kuwa?
" Eh nayi,

Tana rik'e da hanunsa kaman wani yaro d'an shekara uku, har sukafito Sani yana tsaye rik'e da murfin mota, cikin kulawa Mami ta amsa gaisuwansa, tad'ora da Sani kunyi Addu'ah? "Eh Munyi Mami, tajuyo tana kallon KB da shima ita yake kallo ko k'yafta ido bayayi ta rik'o hanunsa taturashi cikin mota tana takoro musu Addu'a, moto ci biyarne hud'u cike da sojoji biyu agaba biyu abaya na Kabir a tsakiya Sani yana tuk'awa harbakin gate Mami ta rakasu tana kallonsu harsai da suka b'ace ma ganinta, ta koma cikin gida, ji tayi gidan yamata fad'i dayawa gashi yauba aiki, dahaka ta k'ira wayan Hajiya Rabi matar yayanta da suke uwa d'ya uba d'aya tace ta turomata yaranta su rage mata zaman kad'aici,

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Cike da nishad'i suke tafiya suna hira suna tuna zamanin yarantansu jifa jifa suna dariya,

Wannan na d'aya daga cikin abunda yake k'arasa Sani k'aunan KB da respecting d"inshi sam bai d'aukeshi matsayin wanda yake aiki k'ark'ashinsaba, dagashi har Mami,

*Bari muje waye Sani*
Sani dai ada mak'ocin su Kabir ne tare suka taso suna primary Allah yayi ma mahaifin Sani Rasuwa,


. Mahaifiyarsa ta d'aukeshi suka koma Gombe da zama kasancewan dama yar can ne, anan yacigaba da Rayuwa har ya kammala duk karatunsa daganan yafad'a aikin soja Sai kuma wata jarabawa ta fad'omasa Gwamnati ta dakatar dasu sakamakon wani matsala da a kasamu Sojoji dashi, bak'aramin damuwa Sani da mahaifiyarsa sukayiba, ana haka Allah yakawo Kabir garin Gombe duba wani campani dayakeso yasaya, kwatsam Allah ya had'asu ba k'aramin murna sukayi da ganin junaba nan sukayi ta hiran bayan rabuwa anan Sani yake gayama Kabir halin da yake ciki ba k'aramin tausayasa masa Kabir yayiba, Baiyi k'asa agwiwaba, daya tashi tafiya ya tafi dashi dazummar nima masa aikinyi, tofa alokacinne kuma Alhaji ya'u yad'aura d'amaran ganin k'arshen Kabir tahanyoyi da dama da ya ajiye motarsa za azo asama sa bom, bak'aramin tashin hankali Mami ta shigaba, ahakane tanima masa masu tsaronsa ciki har da Sani wanda yakasance ogansu kuma shine drivern Kabir duk inda zaije duk da wani lokaci Kabird'in yakan k'i fita dashi,


🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴
"Hello Kila Kabir fa yataso ina fatan dai kuna cikin shirinku, pls kila wannan karon kar kabari asamu tangard'an da yaronnan zai kub'uta bai mutuba,
"Ka kwantar da hankalinka Boss gamunan adaji muna jiran shi yau kam Kabir saidai uwarshi ta haifi wani,
Cikin jindad'i Alhaji y'au yace "Gud Kila nasan zaka iya dahaka sukayi sallama,


Allah sarki Kabir sai hiransu sukeyi shi da Sani Habib ya fad'o masa arai ya k'irashi yana d'aga wayan yace "Hello Man ya kake? Ya hanya? "mhmm daban k'irakaba ai baza kasan ya nakeba,
"Haba karkace haka wlh nayi ta nimanka bana samun ka,
"Ok inaga matsalan network ne,
"kunyi nisane?
"ba muyi wani nisaba,
"Ok to Allah yakare,
"Ameen daga haka suka ajiye wayan,
Bai wani d'auki lokaciba wayan Mami ya shigo inbai mantaba wannan shine wayanta na hud'u tun fitowansu yayi murmushi yad'auka "Hello Mami na,
"na'am Kabir kuna inane?
"Gamunan Mami mund'anyi nisa, banijinki sosai Mami ki kashe inna isa zank'iraki,
Yana fad'an haka yakashe wayan, tafiya kad'an suka k'ara suna dai dai kan wani tafkeken Gada sukaji k'aran bindiga y akarad'e wajan da sauri Kabir ya zuge glass yana kallon motocin masu tsaronsa yanda suke musayan wuta da wasu gungun matasa ga wasu motocin kuma sunjuyo sai gudu sukeyi, cikin firgici Sani yajuya kan motan, ya k'ure mata gudu cikin zafin nama Kila yaraka musu baya harbi yakeyi ba k'ak'k'autawa tun Sani yanaji har ji da ganinsa ya d'auke tuni motan tafara wulagigi akan titi ahaka motan ta hantsila cikin gada😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

Wayyo Mamin Kabir
Babu wani tsaro da wani ya isa yabaka sai wanda ubangijinka yabaka😭


Kullu nafsin.......

*Ummu fatima ce* 😘
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏσŸ°Ύρ²°ΌσŸ°Ύρ²°ΌσŸ°Ύρ²°ΌσŸ°Š *DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹





*ALLAH yabar k'auna*🀝🏻

🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 1⃣0⃣



Cikin farin ciki da jin dad'i kila ya faka motarsa yafito yatsaya akan gadan yana kallon yanda jininsu KB yake gudu akan Ruwa, motarsu kuwa tuni idon Ruwa yajata ya afkar da ita wani tafkeken rami,

Busar da wani iska mai zafi yayi yaciro waya a Aljihunsa ya k'ira Alhaji ya'u,

Alokacin Alhaji ya'u yana tsaye da waya ahanunsa k'irjinsa sai bugawa yakeyi, tsoronsa d'aya kar asamu matsala wajen kashe KB don yasan wannan shine damarsa ta k'arshe,

aiyana ganin k'iran Kila hanunsa har b'ari yakeyi ya d'auka murya na b'ari, yace "kila yadai?
Wani mahaukacin dariya kila ya fashe da shi sai da yagaji dan kansa yafara magana

"Boss kayi yanda kakeso yau aduniyannan, kafin kaima naka wa'adin yacika,

cike da tsoro yace "banganeba Kila?,
"matsiyacinnan yabak'wanci lahira, nagama dashi,

"Dagaske kakeyi Kila?!!!

"ai bamu tab'a wasa irin hakaba,

Cike da nishad'i da jin dad'i Alhaji ya'u yafara masa Alk'awura da haka suka ajiye wayan, yau jinsa yake duk duniya bawanda yakaishi farin ciki, don yasan ya mallaki dukiya angama don yagama target dama da ya kashe Kabir zai je wajen boka yamasa aiki akan Mami ta amince ta aureshi, shiyasa ma baiyi shawaran kisan Kabir da matarsaba, donkar kishi ya d'ibeta bayan aurensa da mami ta tonamasa asiri, dariya yake tayi shi kad'ansa afalo cikin nishad'i,

can kuma yazabura yamik'e

Makullin motarsa ya sura da sauri da kanshi ya tuk'a kansa bai tsaya ko inana sai gidan Mami a falo ya sameta ita da uncle Musa da yakawo mata yaransa da tace akawosu su d'ebe mata kewa kasncewan dama yanason zuwa don ya kwan biyu baizo sun gaisa da k'anwar tashiba, cike da girmamawa da mutunta juna suga gaisa Mami ta k'walawa sauda k'ira da tun zuwansu suka shige kitchen wannan na d'aya daga cikin abunda yasa yaransuke son zuwa gidan Mami ta kanbarsu su shiga kitchen suyi ta jagwalgwalon girkinsu su dafa wannan su dafa wancan, tanakallonsu,

Da saurinta ta iso Mami ta umurceta data kawo ma Alhaji ya'u abun motsa baki,

"Dadyn su ziyarace haka da Ranannan? Saida yahad'iyi Ruwan da ya kurb'a sannan yace "zan wuce ne nace barinzo mugaisa kwana biyu ban lek'oba, "aikuwa ka kyauta d'azu kuwa mukayi waya da "yata tace wai yau sam baka k'irataba nace k'ila kana busy ne, "mhmmm Rabu da Nafisa darunta yana da yawa kullum inban k'irata sau hud'uba ta dinga mita kenan, dukansu sukasa dariya,

"Ina Kabir ne? Inason muyi magana dashi akan sabon sakataren sannan da yakawo sam ban yarda da yaronba, Mami takalli yayanta sannan ta kalli Alhaji ya'u Amma kuma ai Abdul yaron kirkine d'an k'anin mahaifiyar muce, uncle Musa yace "tabbas bana zaton za'a samu Abdul da aikata mummunan Abu, cikin diriri cewa Alhaji Musa ya kallesu yanacewa "to kun san sha'anin mutane nima tseguntamin akayi shiyasa ma nace sai nasamu shi Kabir d'in munyi shawara

"Eh yana da kyau kuyi shawaran ma, bayanan ai yatafi Abuja Dady yad'an had'e rai oh narasa meyasa sam Kabir bai d'aukeni matsayin da na d'aukeshiba, yanzu ace yaronnan Zaiyi tafiya amma yakasa sanar dani?, to ai shikenan Allah ya dawomin dashi lfy

Mami cikin rashin jin dad'in abunda Kabir d'in yayi tace " kayi hak'uri Dadynsu sam narasa meke damun Kabir da irin wannan Halinsa
"ba komi ya wuce da yaushe ya tafine?
"Tun da safe ya tafi ina tak'iran wayansa ma layinsa bayi aiki tafad'a tana k'ok'arin k'ira,

Rass taji k'irjinta ya buga kiran yana fara tafiya ya katse ba tare da ance komiba,

Atsorace Mami ta kalli uncle Musa "yanzu kanma kwat2 layin baya fita sab'anin d'azu da'ake cewa ba Network, tak'arasa maganan da matsanancin damuwa,
K'asa2 Alhaji ya'u yakemata wani kallo aransa yace lallai da sauran rina akaba ko yaya zakiyi lokacin da kika samu lbrn mutuwar d'annaki ohi?

Uncle Musa yace "inaga dai matsalan Network ne kinsan hanyan Akwai Qauyukan da basu da service,
"Amma fa yaci ace yanzu suna cikin Abuja yaya ,

Alhaji ya'u ya amsa da cewa kinsan halin Kabir da sha'awan k'auyuka yanzu haka sasu tsayuwa yayi awani wuri daba network
asanyaye Mami tace "Eh zai iya yiwuwa, saidai fa d'azun can munyi waya,
"ki kwantar da hankalinki Insha Allah bakomi, ni zan wuce yafad'a yana mikewa
"to Allah yasa nagode agaida mutan gidan
"zasuji,

Baijima da fitaba Uncle Musa ma yamata sallama yana cemata ta kwantar da hankalinta,
To kawai tace masa amma kar ga Allah tanajin ajikinta kaman d'annata ba k'alau yakeba,



Saidai fa tun fitansu Mami take zaune awajen kamar andasata duk jikinta ba k'wari k'afafunta sai rawa sukeyi sai niman wayan Kabir, da Sani takeyi amma maganar bata canza zaniba,

Har akayi sallahn isha Mami bata daddaraba kowani bayan seconds tana k'ira amma shiru sosai yanzu kan ta tsorata da jin shirun d'annata,
Wasa2 Har Mami tayi shirin kwanciya ba wani canji,

Da haka ta yanke shawaran k'iran yayanta tasanar dashi koda tagayamasa shima ya tsorata, amma kasancewanshi na miji sai kawai ya share ya dinga k'rfafa mata gwiwa,
Haka dai yalallab'ata dacewa lfy ne yake kawo shiru, Da k'yar bacci b'arawo ya d'auketa sai dai wasu irin mafarkai marasa dad'i ne suka addabeta ak'arshe dai hak'ura da kwanciyan tayi,

Tun lokacin data saba yin nafilanta baiyiba taje ta d'auro Alola tazo ta tada sallah,

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴
*Rayuwa kenan duk Abunda Allah ya k'addara ma bawa ba makawa sai ta sameshi saidai Addu'a yana rage k'arfin mummunan k'addara, shiyasa yana da kyau "yar'uwa da kin idar da sallahn asuba kar kitashi awajen har sai kinyi Addu'an safiya da maraici irin wanda Annabin mu ya koyar damu basai lallai kin Haddaceba kinimi Hisnul musulum d'inki kina kaeantawa kada kibari yaranki sufita baki karanta musu wannan Addu'an da da Annabi yake karanta wa Hassan da Hussainiba ki dafa kansu kikaranto musu kaman haka _u'izukuma bi kalimatullahi tammatan min kulli shaid'anin wahammatan wamin kulli ainin lammah_ inkika dafa kansu kikamusu wannan magana ta k'are basu ba kambun baka basu ba kidnaping wane maye wane matsafin da yake tsafi da yaran mutane *Ya Allah ka karemu da kariyanka*

Duk yanda kaso da k'in mutum baka isa kasheshiba sai wa'adinsa yayi,

Da k'arfin gaske ruwan yake gangarawa da bayin Allahn da basujiba basu ganiba har ya kawosu bakin Gab'a anan suka kwana basu ko san inda sukeba,har garin Allah ya waye alokacin d'ai d'ai kun mutane suka fara fitowa a k'auyen wasu sun fito d'iban Ruwa wasu kuma itace,

Hakan yake awurin Malam Bukar mai d'ori da k'aton jarka ya fito da igiya abayan kekensa, sauri yakeyi ya gama tunkafin Dijah tafito donyasan indai tafito waje bazata barshi ya d'iba,
Agefen Rafi ya ajiye jarkansa sannan yanufi cikin jeji yin itace agefe ya kafe kekensa yana shirin haye Ruwa,

Nanfa idonsa ya sauk'a akan samaruka guda biyu kwance cikin halin mutuwa ko rayuwa, sosai ya tsorata duk da halin jarumta irin na malam Bukar,
yazuba musu ido yana nazari Abunda ya d'aure masa kai shine ganin d'aya da kakin soja d'aya da bak'ak'en kaya cikin jarumata irin nashi ya k'arasa har inda suke bakinsa d'auke da Addu'a ba k'aramin tsoro da tausayibane yakamashi lokacin da yaga harbi ajinkinsu cikin gaggawa ya hau kekensa bai tsaya ko inaba sai police station,

Nannfa yasanar dasu abunda idonsa yagani ba b'ata lokaci suka garzaya da maotansu wajen cikin jagorancin Malam Bukar mai d'ori,



*tofah magana nagaba ina lbrn Mami? Ina Alhaji ya'u? gadai Kabir da Sani zasu mutu ko zasuyi rai sai Allah shi yabar ma kansa sani rayuwa kenan sai naka yakasheka bare kuma ya taimakeka mmm muje zuwa



Ummu fatima ce 😘
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*MY NATION*πŸ‡³πŸ‡¬

*ALLAH yabar k'auna*🀝🏻

🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 1⃣1⃣


A gefen Hanya suka faka motan suka shigo wurin da k'afa da hanu Malam Bukar ya nuna musu inda su KB suke,

Bak'aramin kad'uwa police d'in sukayiba musamman da suka lura Ba k'ananan mutane bane,

Ogansu da kansa yaja mota ya tafi asbiti suka taho da ambulance akatafi dasu,

Nan likitoti suka rufu akansu sukaciremusu harsashi ajikinsu, Sani kusan bulet hud'u aka ciremasa, ga raunukan da yaji yayin da akacirema KB d'aya, sai dai ansameshi da karaya aduka k'afafunsa,

Har la'asar ana abu d'aya akansu, sai daf magriba suka kammala agajiye Doctors d'in suka fito, har lokacin police d'in sunanan babban likitanne ya mik'a ma police d'in hanu, suka gaisa, "yadai likita ansamu nasara?


"Eh to mundaiyi musu aiki amma dai ba wanda ya farfad'o acikinsu,

Police d'in ya mik'a masa ID card wannan a aljihunsa muka samu, ya karb'a ya duba
*Kabir Mahmud tugga* yagani ajiki da sauri ya d'ago ya kalleshi "oficer ai wannan Babban likitane kuma d'an shahararren d'an kasuwan nanne Alhji Mahmud Tugga,


Kai police d'in ya jinjina yace "shiyasa nanumaka kagani kasan jiya anyi taron manyan likitoti a Abuja, maybe can yanufa masu hamayya dashi kokuma "yan fashi sukamishi wannan aika aikan, so yanzudai zamu d'aukeshi mukaishi National Hospital Abuja, Inyaso kuyita treting d'in seceuritynsa anan inya d'ansamu releif sai amai dashi cikin Adamawa.


🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Gidan Mami na lek'a bak'aramin kad'uwa nayiba lokacin da na hango Mami zaune abakin gado ta jingina kanta ajikin gini, tanajiyo hargowan mutanen da suka cika gidan wasu "yan'uwanta ne wasu kuma "yan zuwa jajene, yau kwana uku kenan ba Kabir ba labarinsa, ko ataron da akayi na Abuja ma lbr yasamesu Kabir bai halacci taronba, bincike iya bincike kullum yinsa akeyi amma ba lbr,

hanunta tasa tashare hawaye k'waya d'ayan da yagangaromata Zuciyanta sai zogi yakemata, ahankali take tuno Abumda mijinta yagaya mata ranan da zai Rasu, *Fatima kikula min da Kabir Don nasan duk mainiman yaga bayana yanzu hankalinsa zai koma kan Kabir shima za'ayi k'ok'orin ahalakashi kamar yanda akaso amin abaya shiyasa akecewa dukiya fitinace, don nasan abumda suke nima kenan awajena dukiyata gashi kuma yanzu zai koma hanun sa*

"Kabir ta fad'a tana share k'walla dai2 lokacin akayi nocking sauda ce tashigo tad'an rusuna "Mami wai kije inji su Dady, sai da tashiga bayan gida ta wanko fuskanta sannan ta zira Hijabinta tafito acan babban falo tasamesu, su biyune Uncle Musa da Abban Habib, tazauna daura dasu suka gaisa cikin k'arfin Hali, ta kalli yayan nata "yaya har yanzu ba wani lbr?
Ko boudy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login