Showing 78001 words to 81000 words out of 155892 words

Chapter 27 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

474

tashi zan dawo dama ai ba kai kake maidani gidaba,

Cikin zafin Rai Yafito daga motan 😠 yazo gabanta ya nuna mata seat "Shige, ba musu ta shiga da tsoro ya kirb'a murfin motan kaman zai b'alla, ya zaga ya shiga ya figi motan, tun shiganta ta kifa kanta akan cinyoyinta tana kuka, tafiyansa kawai yake ba tare da yabi ta kantaba,

Sund'anyi dogon tafiya taji ya tsaya, ya bud'e Motan yasako k'afafunsa ta waje ya juyamata baya, "Ke tashi ki fito ya fad'a gami da kunna Wak'an *Ya Habiby Anta Ayni* na larabci wanda mishary yayi

D'agowa tayi ta bud'e murfin motan ta fito trus tayi tana kallon katafaren Gidan daya kawota, *"Wayyo Allahna!!* nashigesu ta fad'a atsorace tana k'arema gidan kallo ba motsin kowa sai kukan tsuntsaye danginsu d'awisu da saurnsu, "Ba Magana nake mikiba, ya fad'a cikin dakewa, zagowa tayi tazo gabansa ta tsuguna abun tausayi, ya lura tana da mugun tsoro indai zasu kasance su biyu to zaiga tsantsan ladabi da nitsuwa agunta,

Murya na b'ari tace "Likita Dan Allah Kamaidani Gida kaji?

Hararanta yayi yace "da wannan Hijabin kika fito? Da sauri ta girgiza kanta,
"To a'ina kika sameshi?

"Ajakana nazo dashi
"ok dana hanaki fita dashi saboda turarenda kika saka.masa shiyasa kika fito dashi? Wato ban isa hanaki abuba ko?

"Dan Allah kayi hak'uri wlh hazan sakeba namaka Alk'awari duk abunda ka hanani bazanyiba,
"Dagaske kike fad'a?
"Eh wlh dagaske nakeyi,
"ok tashi ki cire Hijabin kizo nan kusa dani kiji, a tsorace ta 😳 tana hawaye "Dan Allah kayi Hak'uri! Ta fad'a tana hawaye

"ok bazaki abunda naceba ko? Mu zauna kinga nan gidanane ba bak'ona bane, zamu iya kwana ahaka ni dake,

Wani irin kuka ta rushe dashi, Dai2 lokacin taji Kukan Kuliya abayanta, asaba'in da tara ta daka tsalle ta haye kan cinyansa, tana hango kuliyan ya nufosu ta kutsa ta tsakaninsa ta shige cikin Motan, can gidan baya ta shige ta zauna, tana 😳

Murmushi Kb yayi dai lokacin kuliyan ta kwanta ajikin k'afansa ya sunkuyo yana shafa ta "Gud my pretty gwanda da Allah yakawoki naji dad'in ganiki by this time around, kinmin dai dai, ya juyo ya kalli Dijah data takure can baya tana tslli2 tsilli da ldo .

Ya kuma murmusawa ya maida dubansa kan kuliyan yana shafata, Dijah ta sake rushewa da kuka ganin duhun magriba ya fara anma ko ajikinsa tsab ta lura da shi zai iya aikata abunda yacen wato su kwana a wajen,

"Pls baby kimin shiru bafa satoki nayiba, kar ki taramin mutane koda yake ba wani d'an Adam anan sai dabbobi kala2 ko zamuje ki gansu? Ya fad'a yana kashe mata ido dan so yake yak'ara tsoratata,

"to lnba satoni kayiba me kayi? Haka kawai ka kawoni irinwannan gidan? Dan Allah kaji tsoron Allah ka maidani, tafad'a araunane.

K'afafunsa yasako cikin motan sannan ya rufe ya kalleta "Dawo gaba dan kinsan niba drivernki bane ko? Da sauri ta tsallako ta dawo, yaja motan suka fito sai yanzu taga masu gadi abakin gate suka bud'e masa ya fita a wani super maket yatsaya ya sayi abun da yake da buk'ata sannan yafito yatsaya a Masallaci ya gabatar da sallahn magrib suka nufo Gida,

A lokacin Mami tana zaune akan sallahya tunda ta idar da sallah ta da'uki Qur'ani tana karantawa intayi izu ta tsaya tayi Addu'a tayi tawassali Allah ya kare mata d'an nata daga sharrin masu binshi da sharri,

Ahaka taji shigowan motan Kabir, ahankali ta rufe Qur'anin ta gyara rufan Hijabinta, ta fito a falo ta tarar da Nafisa ta yaye labulen window cike da farin ciki tana kallon motan har wani rawa ta taka lokacin dataga ya bud'e Motan, Tanajin motsin Mami tayi saurin b'uya abayan labule, wuceta tayi kaman bata gantaba, ta fita dai dai lokacin Dijah tafito daga motan ta nufo cikin gida shikuma ya tsaya d'aukan shopin d'insa sannan ya nufi pert d'insa,
*"Kabir!* *Kabir!!*
K'iran Mami ya shiga kunnensa, yadawo da kallonsa gareta yanayin yanda yaganta yasashi saurin nufota ahanya suka had'u yana Murmushi gami da shafa kansa yace
"i'am sory my sweet Mami, na tsaya a super market ne, Hanunsa ta kamo suka dawo jikin Motan Dijah tace "Sannu Mami
"yauwa kawai tace atak'aice, asanyaye Dijah ta wuce aranta tana tunanin Mami tana fushi da ita bisa zarginta da takeyi akan tasa musu wani abu a Abinci, hawayene taji ya ciko idonta ahaka ta shige ciki.

"Kabir kanitsu kaji abunda zan gaya maka kayi Addu'a kafin kafita?

"Eh nayi Mami sannan nayi na dawowa,

"Gud akwai matsala Kabir a hanyanka ta shiga pert d'inka dan haka ga buta can d'auka kayi Alola sai kazo ka karanta 'kula'uzannan guda uku sau uku uku ka karanta ayatul kursiyyu da A'uzu bi kalimatillahi da Bismillahillazi la ya durru sai ka wuce insah Allah ba abunda zai sameka,

Cike da mamaki ya kalleta "Mami wai waye ne haka mai niman ganin bayana? Kuma me namasa?

"Kadaiyi abunda nace kawai,

"Mhmm Mami haka zasu ganni su barni Ni ba asirin da zai kamani,

Mami ta masa kallon Gaskiya har yanzu kai yarone, tace "Kabir sihiri gaskiyane kuma yana tasiri ga wanda aka masa makarinsa kenan Addu'a da wa innan k'ul'a'uzai da aka sauk'ar dasu lokacin da akayi sihiri ma Manzona Allah (s.a.w) inhar ka lazimcesu to sihiri bazaiyi tasiri ajikinba dan dama dalilin sauk'ar dasu kenan,

Wucewa yayi ya d'auro Alola ya dawo tare suka karanto Addu'o'in sannan yayi Bisimillah yana gaba tana biye dashi har cikin pert d'in yana shiga ya zube akan kujera gami da dafe kansa, yana jujjuyawa.

Da sauri Mami ta lek'a fuskansa "Kabir are u ok!?

Murmushi yayi yana kallonta "i'am ok Mami na, ba abunda zai sameni ta sauk'e ajiyan zuciya.

*"Alhamdulillah* Allah ya k'ara karemu da kariyansa, ka kula sosai Kabir sannan kakiyaye cin abun hanun kowa har sai kaji daga gareni Ibeen Khadijah da Nafisa,

"Mami Nafisa kuma? Mezaisa ta cutar dani? Itama Khadijahn dukda bangama yarda da itaba inaga kaman bazata samana wani abu muciba, inaga kaman gaskiyan Nafisane curry ne acikin Abincinnan.

Mami tad'an murmusa "Ko kad'an Kabir Dijah bazata samana wani abuba, kodakaga na tuhumeta, sarai nasan me nakeyi yarinyane ita amma tana da basira sai ka lura zaka gane, na ankarar da itane dan ta lura kar tayi sakaci itama abun zai iya ritsawa da ita,

"Saboda me Mami? Itakuma meye nata aciki?
"saboda kana tare da ita Kabir ayanzu a idon duniya suna mata kallon matarkace ni da kai ne kawai mukasan matsayinta agidannan,

Rasssss yaji k'irjinsa ya buga "Mami dama tana da wani matsayine dayawuce wannan?

Wani kallo ta masa "kamanta cewa yanzu zaman tagama karatu takeyi? Zaro ido yayi yana kallonta zuciyansa sai harbawa takeyi da sauri,

Shiru tayi tana nazartansa "yadai Kabir d'ina,?

Da k'yar yasauk'e ajiyan zuciya ya lumshe idonsa "Mami gani nake kaman kinyi fushi danine yasa kike fad'in Haka.

"Haba Kabir nayi fushi da kai? Sam banyi fushi dakaiba, my son, burina a kullum shine ganin farin cikinka, farin ciki nake nimamaka Kabir, kai ba iya rik'e mata biyu zakayiba gashi ana shirin aurenka da "yar'uwanka bazan takurakaba Kabirun Dady tana gama school zan maidata ga iyayenta kaman yanda kabukata tun farko.

Shiru kawai yayi yana binta da kallo kaman yau yafara ganinta, ta shafi fuskansa tana murmushi tafita.


Har ta kusa fita sannan ta dawo da baya "Barin turo Khadijah ta dafa maka koda indomie ne dan tunda na dawo agajiye nake nakasa aikata komi banyi girkiba, daga haka ta fice,

Zaune tasami Nafisa a falo tana Kallo, rana na farko dataji bata son ganin Nafisa a idonta hakanan taji ta fice mata arai,


Itako Nafisa tana ganin ta ta mik'e tana murmushin Nasara "Welcome Mami, da d'an murmushi tace thank u Nafisa,

"Mnnmm Mami zan d'anje gida Gobe zan dawo, da safe.

"Allah yasa muna raye, ta tura k'ofan Dijah ta shiga akan sallahya tasameta yanda ta idar da sallahn kenan ta kifa kanta ajikin gado Hawaye na tsiyaya afuskanta, yanzu in Mami ta cigaba da fushi da ita ya zatayi? Ina zata sa kanta? Ita kad'ai ke sonta wanda aka kawota da sunansan wai yace ya tsaneta! Kallon 'yarshan lami yake mata, kallon mara gata wacca iyyenta basa sonta, Guduwa kawai zatayi tabar musu gidan ta fad'a aranta,

"Khadijah! Mami ta fad'a tana zama abakin gado da sauri tashare hawaye ta dubeta,

"What Khadijahn Mami kuka kuma? ina raye? Meyayi zafi Khadijah na?, ta fad'a tana kwantar da kanta acinyanta.


Cikin sheshek'a tace "Mami wlh bani bace kuma bansan wayasa acikiba kiyi Hak'uri kidaina Fushi da ni,

Cikin matsanancin tausayi take shafa kanta "Yi Hak'uri Khadijah na Banyi fushi dakeba kuma bazan tab'a fushi dakeba insha Allah, wani sak'o na isar miki Khadijah kiyi hatarra na yarda dake πŸ’― kowani bazaki iya cutarwa ba bare mu, kidaina tunanin zarginki nayi kinji?

Kai ta d'aga Mami ta mik'ar da ita tashare mata Hawaye,

"jeki ki dafa ma Kabir indomie a pert d'insa maza kizo akwai maganan dazamuyi dake,


Da sallamanta ta shiga ganin baya falo yasa kai tsaye ta shige kitchen ta kunnna Gas ta d'ora, bayan yagama wanka ya fito gajeren Wando yasa da singlet farare tas, yafito falo, jin motsi a kitchen ne yasashi shiga tana tsaye tana firan Dankali, Riga da wandone ajikinta farare na bacci dan tunda tayi wanka kawai tayi shirin bacci, batasan Mami zata sata fitaba, bak'in Hijabi ne ajikinta ta tattareshi ta d'ora akan wuyanta, tun daga sama Har k'asa yake kallonta, Maganganun Mami na d'azu na masa yawo akai, wata zuciyan tace kai Man ya kaman ka damu? Mezakayi da wannan k'wailan? No badamuwa nayiba, Mamine banason taga banmata biyayyaba bata cancanci haka agareniba,


jin kaman ana kallonta ne yasa ta juyo da sauri ta juya tana gyara Hijabinta, ahaka ya tako yazo yatsaya abayanta yayi Huging nata, "yan mata meya kawoki nan? Da izinin wa kika shigamin kitchen Har kike girki?

Cikin in ina tace "Mami ce tace inzo in dafa maka,

"mhmn shine ba niman lzini? Ko kin manta yau matata tana gidannan,

"cikin b'acin rai da tuk'uk' tace matarka ko 'yar iskanka?

Murmushi yayi ya zago gabanta yad'aga Hab'anta, yana kallon Fuskanta, kallo d'aya tamasa tayi saurin kauda kai ta juya, da k'arfi ya kuma juyo da ita ta sake sinne kanta sai lokacin ya tuna gajeren wandone ajikinsa yasan duk yanda yakai da son tsokananta tayi ta tsiwa bazata sake tayiba dan haka yasaketa yafita,


Tree quater ya canza yazo yazauna a falo haka nan yajishi bayajin dad'i,

Yana zaune ta fito da k'aton plate Dankali tasoya da kwai sai ta dafa masa indomie da yasha d'anyen kifi da vegatables sai k'amshi yake.

Agabansa ta dire ta mik'e zata, "Ke zonan ina zaki?

Ta turo Baki "Naga ai nagama abunda aka turoni inyi,

"No dasaura zoki zauna anan, Zama tayi agefensa ya mik'a mata spoon "Bismillah
"Ni nak'oshi!
"Baki isaba yarinya kiyi abinci kice bazakiciba, Me kika barbad'amin Aciki? Ko kinsa wani gubanne?

Ta tab'e baki tana kallo sa da zan samaka wani Abu a Abinci da tun a Ruganmu a Gidanmu nasa maka kaci inma mutuwanne da yanzu wani ake zance ba kaiba Likita.

"Mhmm naji karb'a kici yafad'a yana maamki furucinta ashe ta iya magana haka,

Wani spoon ya d'auka yasaka yafara ci loma uku tayi ta ajiye,

"Saifa muncinye tare
"ni nak'oshi d'azufa kikayi Alk'awarin kindaina musu dani

Mai dakai tayi suka cigaba da ci.

Mami ta shigo da sallama tana kallonsu Khadijah yanajiki shiru baki gamabane? ta k'araso dasuri Dijah ta ajiye spoon d'in Kb yace tanacin Abincine

juyawa Mami tayi inkingama maxa kizo ki kwanta dare yayi inajiranki yanxu




UMMU FATIMA 😘
.
[7/19, 8:20 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š

4⃣4⃣


Mami tana fita Dijah ta tashi asanyaye zatabi bayanta,

kabir ya Harareta gami da d'anjan tsaki yacigaba da cin Abincinsa, "Malama kikawomin Ruwa, kinba wa Mutum Abinci ba Ruwa",

Wurin da freach yake tayi ta d'auko masa goran Ruwa ta ajiye agefensa,

"Oya zauna waye zai tattara miki wajan innagama? Komawa tayi ta zauna,

tana zaune har yagama ta tattara wajen ta kai Kitchen ta wanke duk abunda ta b'ata ta maidashi ma'ajinsa, ta Goge kitchen d'in.


Tana fitowa kai tsaye hanyan fita tayi,

"Ke Khadijah zo nan Kb ya fad'a a Gadarance, kaman Bazata dawoba sai kuma ta dawo a d'an gefenshi ta tsaya tana tura Baki "Gani
"D'an zo kimin tausa ya fad'a yana mik'e k'afafunsa, Hararansa ta shigayi sama da k'asa ta juya yayi saurin finciko Hanunta ta fad'o k'irjinsa, da iya k'arfinsa ya matseta, tana kiciniyan k'wacewa yafara kissing d'inta, lumshe idonta tayi ta kwanta luf ajikinsa tana numfashi ganin haka yasa ya birkitota yana shirin..ciremata Riga dama tuni ya rabata da Hijabinta... Kawai sukaji ana knoking. "Khadijah! Suka jiyo Muryan Mami daga waje tana k'ira, arazane Dijah ta zare Bakinta acikin nashi tana k'ok'arin tashi, ya manneta ajikinsa, Murya na b'ari tace "pls pls Likita Mami ce dan Allah kasakeni zata shigo, k'ara k'ank'ameta yayi yana kallonta da birkitattun idanuwansa, "So What in Mami ne? Akwai abun da zaki b'oye matane? Keda kika ce mata anmiki Fyad'e? Gwanda kibarta ta gani da idonta basai kinje kina b'ata bakinki wajen Bata lbr ba,

Yasake k'ok'arin Manna Bakinshi da nata yana tura hanunsa Cikin Breast d'inta, dai dai Lokacin Mami ta tura k'ofan ta shigo, a birkice Dijah ta tureshi ta zame k'asa tare da fashewa da Kuka, dan kunya Kam tagama jinsa, "Khadijah baki gama cin Abincin bane? Mami ta fad'a cikin dakewa, tana kallon Kabir da yake ta Sissine kai, tarik'e Hab'a "lfy kuwa Kabir wani muguntan kamata take kuka? Batajira abunda zai ceba tajuya tanacewa, "Inkingama cin Abincin dai Khadijah kizo ki kwanta haka kema ki huta ma Ranki dare yayi, tana fita Khadijah ta mik'e dasauri tana kuka tayi hanyan fita shima da sauri ya mik'e yabi bayanta tana shirin antayawa da gudu ya rungumota jikinsa, zubewa tayi ak'asa ta had'a hanunta Biyu tana kuka "dan Allah Likita kabari Mami cefa take k'irana dan Allah kayi Hak'uri baniso wlh,


Ya lumshe idonsa ya bud'e yana kallonta, sannan ya tsuguna ya sake rungumota, "fad'amin mene ne bakiso? Kafin tasake cewa wani abu, yafara k'ok'arin fitar da ita a Hayyacinta, tuntana Tirjewa har taji yana shirin cin nasara akanta, Saboda Kb Namijin Duniyane na Gaske ba na Wasaba, k'ok'arin ciremata Riga yafarayi nan ta ankara tadage iya k'arfinta ta tashi da k'yar ta fice anan tabarshi yana maida Numfashi, tsawon Lokaci sannan yaja tsaki yad'ago Hanunsa yana lissafin sauran kwanakin da suka rage aurenshi da Nafisa,


A k'ofan shiga Falo Dijah ta tsaya tana share Hawayenta ta kama Bakin Hijabinta, tayi ta Goge Bakinta tana zubar da yawu, sai Allah ya isa take jerawa ba k'k'k'autawa, ta gyara Riganta da aka kusan ciremata tayi, Sannan tashiga, atsaye tasamu Mami a Falo tazuba ma k'ofan shigowa ido, wani irin kallo ta dinga Binta dashi, sannan ta juya ta shige bed room d'inta ba tare da da tace mata komiba,

Akasalance Dijah ta shige d'akin lya alokacin iya tana shirin kwanciya, Dijah ta haye Gadon ta kwanta luf tana sauk'e ajiyan zuciya, wani irin yanayi takeji ajikinta, gaba d'aya takasa Fahimtan meke damunta, "wlh bazan tab'a yafe masaba, ta fad'a asnyaye batare da tasan yafito filiba,

"Keda waye kuma? Iya ta tambaya tana k'are mata kallo,


"To kekuma lya me Ruwanki? Nayi da kene? Ta fad'a da Muryan kuka.

Iya tayi Murmushi "a'ah a'a Maida wuk'an, Khadijah am bani nakar zomonba, Ratayanma ba abaniba, Amma dai kid'an matsamin agadona kwanciya zanyi,

Ta turo Baki "yanzu lya duk filin nan bai lshekiba sai namatsa?

"Oh yau Naga k'arfin Hali Nida gadona, akan kebaki dashine kodai akaina zaki sauk'e fitinanki, baga d'akin kiba can.


Mik'ewa tayi Fuuu ta fita lya tayi Dariya tana girgiza kai, "Oh Dijah Manya" Allah dai ya kyauta

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Lokacin da Nafisa ta shiga Gidansu tun daga falo take ta rafka ma Mamanta k'ira da sauri ta fito kafin tace wani abun Nafisa ta fad'a ajikinta, "Mama ya wuce wlh ya tsallaka naci wannan Game d'in ya fad'a tarko d'aya", ta fad'a cike da tsantsan farin cikin samun Nasara,

Maman ta kamo hanunta tana dariya suka zauna, "To yabatun Abincin? Sunci?

"Basu ciba, Nan ta kwashe yanda akayi ta gaya mata,

"Inbandake Nafisa yazaki barbad'a musu garin Magani akan Abinci? Ai dole su gani, acikin tukunyan Abincin zakisa tun yana wuta ya nuna dashi duk iya muna funcinta bazata ganiba,

"Ai yanzun haka zan musu, inta d'ora zanje inzuba dole suci, Haka suka dinga tattaunawa har sukaje suka kwanta,


Washi gari kusan Azahara, Nafisa tace bari ta fara gwada aikinta ta gani bayan ta shirya, tak'ira, Kb alokacin yana zaune a Office shi kad'ai yana Brawsing, yana d'auka ta kashe Murya "Helo Kb kazo gida ina niman ka yanzu2

Dum yaji maganan ya cire Wayan akunnwnsa ya sake duba sunan Nafisan dai ya sake gani, ya mayar Kunnensa, Yace "Helo sake maimaitawa tayi, sosai yayi mamaki anma kasancewan bata tab'a mishi irin hakaba sai yayi tunanin ko wata matsalance, mik'ewa yayi yana fad'in "Wani Gidan?

"Nan Gidanmu man"

"Ok gani zuwa yafad'a yana gyara necked tied

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login