Showing 48001 words to 51000 words out of 155892 words
yayi sakacin aura mata kai wlh yayi ban kwana da 'yarsa sai alahira su had'u dansai naga Bayanta,
Kawai sai yaciro Hankaceif ya mik'amata, cikin muryan 'yan iska yake mata magana nidai banjiba, daga nan na sauk'a agun Nabarsu,
"Oh! Ni Fatima Khadijah har Akwai wani Muryan 'yan lskane?
"Eh Akwai Mami dandai ban iya bane danamiki kinji, insun sakeyi zan koya sai inzo inmiki, Shinema yake yawanyin irin Muryan.
Kuma Rananma Naganasu a k'ofan pert d'insa sunason suyi irin lskancin Abunda su Salame sukeyi a garinmu ita da Mijinta, saura k'iris suyi sai yamatsa basuyiba,
"Mami datayi mutuwar zaune tace yayane lskancin gwadamin ingani,
Sunkuyar da kanta k'asa tayi tana jin kunyan fad'a sai kuma ta tuna dama tanason Tona musu asiri, ldonta arufe ta Rungumo hanunta ak'irjinta tace Haka,
Mami tajinjina kai Aranta tana tunanin yaranta irin na Dijah tayi tunanin yanzu tadaina ashe dai baizobane kawai,
"Wai Runguman juna kikaga sunyi?
"Eh amma dai ya matsa da Baya basuyiba amma wlh sauran kad'an suyi, Inagama Hala suntab'ayi.
Mami tasauk'e ajiyan zuciya "kibarsu zanyi maganinsu
Aure za'a musu kwanan nan,
"Ko anmusu auren ma, lskancinsu zasu cigaba dayi Mami,
Wlh sam Nafisannan bata da Kunya, Tafad'a tana d'aure Fuska.
"Hakane Amma dai kidinga Amfani da abunda ldonki yagani, Zargi ba kyau Khadijah,
Kidaina Zarginsa Sannan kidinga Gaisheshi, kina girmamashi, yanada matsayi Mai Girma awajenki,
Tayatsina Fuska tace "awajena kuma Mami?
Awajen Nafisa dai, Ni wlh banison gaisheshi, Nafasan Likita yanada jinkai da Kallon Banza.
Mami tad'anyi Murmushi "To ai Umurnina zakibi Khadijah, Ba Halinsaba.
Zata kuma magana Mamin takatseta
"Gama karyawanki Khadijah kije yau ke zaki mana Abincin Rana,
"Mami inason lnje Gidan Uncle kwana biyu Sauda batazoba,
"To jeki in kingama sai kije Amma ba kwana zakiyiba,
Ad'okance ta tashi tashiga kitchen.
Sai Misalin 1:00 tagama ta shirya komi a daining tashiga wanka tana fitowa tayi sallah Doguwar Rigan Shadda dark pink tasa wanda yasha aiki da bluen zare tayi Roling da bluen mayafi fuskanta bawani kwalliya mai yawa daga pawder sai kwalli da tazizara a idonta sai pink Jambaki da tasa, ta saka falat shoe blue da jakansa sai ta manne idonta da glass mai farin kwalba hanunsa pink agogonta ma fatansa pink, Best Colournta kenan.
Ita kanta sake baki tayi tana kallon kanta a madubi don sam batasan tana da kyau Hakaba, turare ta fesa mai Sanyin k'amshi ta d'auki wayanta tafito.
Yayi dai2 da Shigowan Kabir Caraf idonsa ya sauk'a akan Dijah da sauri yad'auke ldonsa ya nufi gun Mami da take kan daining tana jiran fitowan Dijah, komawa d'aki tayi kaman mai niman wani abun can kuma ta fito ta matso Mami ahankali tace "Natafi,
Mami tajawo Kujeran da yake kusa da Kabir ta turamata,
"Zauna kici Abinci tukun inba hakaba kifasa fitan,
Badon tasoba ta d'auki plate tad'iba ta tsiyayi Juice tafara tsakuran Abincin,
Cikin Mutuwan jiki Kabir yake cin Abincin yana satan kallon yatsunta da suka sha lalle sunyi jaa mai kyau, aransa yana son Sanin wai wannan d'in Wacece? Atunaninsa lya ce tazo da ita, can dai zuciyansa ta kwab'eshi, dan haka yanitsu yamaida Hankalisa ga Abincinsa, wayarsa tafara Ruri.
*My Lovely wife* sunanda yabayyana akan screen d'inkenan, Dijah data d'auki cup d'in Juice zata kai bakinta ta d'an lek'a Wayan, dai2 lokacinkuma takafa cup d'in abakinta, Wani irin tarine yasark'eta Juice d'in data kurb'a ya watsu aka fad'an sa Na Hanunta da yake B'ari kuma yazube masa ahanun Riga, ad'an zafafe ya d'ago ya sauk'e Idonsa akan fuskanta.
Cak ldonsa yatsaya akan Fuskan ta.
*Ummu Fatima* π
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*YAU (24/4/2018) AYAU NE FATIMA TA TACIKA SHEKARA GUDA DA RASUWA,*
ππππππππππ
*FATIMA TA YI DOGON JINYAN CIWON ZUCIYA NA TSAWON SHEKARA GUDA KAFIN ALLAH DAYAFINI SONTA YA KARB'I KAYANSA*π
*FATIMATA 'YA MACE K'WAYA D'AYA DA ALLAH YABAMU KUMA YA JARRABEMU DA SOYAYYARTA DA KUMA LALURANTA DA KUMA ZAFIN RABUWA DA ITA SHEKARA GUDA KENAN AMMA ADUK LOKACIN DANA TUNA SAI ABIMYAZAMO TAMKAR YANZU YA FARU*ππ
_ina masoyan Ummu Fatim ina baran Addu'anku Allah yabani lkon cin wannan jarabawa Allaj yayi ma Fatima Rahma yasadamu da lta agidan Aljannah_
_nayi anfani da wannan dama na saudauk'atr da wannan page ma duk wata mai suna *FATIMA* BABBA KO YARINYA_
_INA FATIMOMI NA NA GROUPS MASU K'IRANA DA MOMINSU NASADAUKAR DA WANNAN PAGE GABAD'AYANSA GAREKU KUYIMA TAKWARANKU ADDU'AH_
ππππππ
*UMMU FATIMA CE*π³π¬
π *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......π
*page* 2β£9β£
Ji yayi kaman Mafarki yakeyi, Tabbas saboda tsaban iya shegen da yarinyan tayi tamasa lokacin da yake Gidansu, shiyasa yake yawan Mafarkinta abacci, Amma ba a irin haka yake ganintaba, Sannan Bai tab'a Ganinta a ldo biyu ba saidai yayi tunaninta aransa,
Kau da kansa yayi gefe ya kalli Mami da ta kafeshi da ldo, sai kuma yaasunkuyar da kansa yanajin yanda tarinta yake k'aruwa,
Nan wayan tasake d'aukan Ruri, juya wayan a hanunsa yashigayi Mamaki Biyu a zuciyansa na farko, Khadijah yaushe tazo gidansu? Meyakawota?
Ad'ayan b'angaren kuma yana Al'ajabin Sunan daya fito akan wayansa asaninsa bawata mace datasamu wannan matsayin awurinsa, yaushe aka samasa Sunan?
Sory! Sory!! Sory Khadijah Kalman da Mami take fad'ane yadawo dashi gurin,
Sake Kallonta yayi alokacin tarin yad'an tsagaita tana ta gyaran Murya sabo da yanayin da takejin cikin Mak'ogwaronta, d'agowanda zatayine suka sake had'a ldo saurin janye ldonta tayi,
Nan wani tarin yakuma tasowa, ahankali take buga k'irjinta, sai kuma ta mik'e da sauri ta nufi d'akinta tashiga bayan Gida,
Mai da Kansa yayi yacigaba da juya spoon d'in Hanunsa acikin Abincin kunnuwansa suna jiyomasa irin tarin da takeyi,
Dogon tsaki yaja yakalli Mami da take masa wani Kallon da yakasa banbance nameye..
Mik'ewa yayi "Mami Wannan Stupid Girl d'innane ko?
Kallonsa kawai takeyi batare da tace komiba,
Yad'an yatsina Fuska "tana da Matsalan Heart shine take irin wannan tarin?
Kodayake najima da ajiyeta a ajin Mahaukata first Class,
Mik'ewa Mami tayi ta wuceshi batare data kalleshi ko tace wani abunba d'akin Dijahn ta shiga ta tura k'ofan toilet d'in tashiga, alaokacin tasamu tad'anyi Amai tarin yafad'amata, "Sannu Khadijah Mami tafad'a tana kunna Ruwa ta wankemata baki ta rik'ota suka fito ta zaunar da ita abakin gado,
Tsaban ta galabaita ko zamanma kasayi tayi sai Mamine tarik'eta, tarasa mezatayi no. Kabir ta lalumo awayanta,
Yana d'auka cikin fad'a tace "to ai sai Kazo kadubata, tunda dama kaine Likitanta, batajira cewansaba takashe Wayan bai b'ata lokaciba ya tura k'ofan yashigo,
Kansa ak'asa yace "Mami kina da Bak'i, suanajiranki afalo.
"Tom sai kazo karik'eta ina Zuwa,
Jiyayi abun yamasa banbarak'wai, amma bayanda ya iya ya iso Hanunsa nab'ari yarik'eta, Harara Mami tabishi dashi har tafita.
Afalo ta tarar da Bak'intan su Ukune Maman Habib ce sai d'ayan Dattijuwa da kaganta kaga Kamilan mace mai Dattako sai kuma wata 'yar matashiya, tazauna suka gaisa cikin kulawa,
Maman Habib ce tafara magana,
"Mominsu munzo miki dawani magana ne mai marik'ar muhimmanci.
kintuna da yarinyannan Aliya wacce Natura su Kabir wajenta?
"Eh na santa, Mami ta fad'a agajarce.
"Yauwa to wannan kakartace kin ganeta Randa mukaje Gidan da daddre ad'akinta Muka sauk'a,
Cikin damuwa Mami tace "na tuna,
"Yauwa narakota wajenkine,
Mami ta gyara zama tana Fuskantan Dattijuwan,
Saida tayi Gyaran Murya tace "Dama nazone akan Maganan da mukayi na Auran yarannan kinsan mu mutanen da dason cika Alk'awari bakamanku ba, tunda mukayi Magana anhanata sauraran kowa dama Akwai wani yaro da yake niman Aurenta tobayi da aikinyi, shikuma yamtsa, da mahaifinta yaga sunason junansu shine yace zaibashi aurenta ko bai kawo komiba anma yaje yanemo sadaki,
To yaron irin mutananne masu tsatstsauran ra'ayi, fir yak'i wai abarshi zaiyi komi da kansa bayason ta rainashi, intak'aicemiki yanzu dai har abun yana niman ya haifar da fitina tsakanin lyaye.
Shine Mahaifinta yaturoni wajenki yace kawai kuzo a satinnan dazamushiga ayi auren basai ankawo komiba, Burinmu kawai akau da zancen wancan d'in.
Wani lrin zufane yaketo ma Mami dan ita kan tunda dataga Kabir yak'i Nafisane yabata zab'i kan cewa ta zab'a mishi da kanta, shiyasa taje kan maganan Aliyan sabida tayi tunani intamatsamishi akanNafisan za'a iya samun matsala abun zai sahfi Zumunci.
"Yadai naga kaman kinshiga rud'u?
Dattijuwan ta Tambaya,
Mami ta nisa, nan takora mata bayani kancewa yanzu Tunda yadwo yace zai Auri Nafisan,
Dattijuwa tayi dariya "indai wannan ne Ranan Juma'a me zuwa kuzo ku karb'a ma Kabir Auren Aliya, inyaso duk lokacin dayashirya wajen zamanta sai yazo yad'auki Matansa, ai Kabir Mijin Mata Hud'u ne.
Sannan duk lokacin da ya shirya sai ya Auri ita 'yar'uwar tashi bayan tama ai yana da sararin k'ara wasu Biyun.
"Hakane Hajiya mungode da wannan Karamcin, Allah yak'ara Girma insha Allah kujirayemu awannan Rana.
Kakarshi tana d'aki muje sai ku Gaisa.
Tana tafe sunabinta Abaya Har d'akin lya sai da Mami ta warware ma iya komi sannan tabasu wuri dan su tattauna yanda abun zai kasance, kaman yanda lyan ta buk'ata.
Afalo tabar su maman Habib tashiga d'akin Dijah don duba Wainan da ake toyawa.
Ak'ofan d'akin ta tarar dashi sai share gumi yakeyi agoshinsa kaman wanda yayi dambe ko tsere, ldonsa sun kad'a sunyi jajazur.
"Lfy Kuwa? Mamin ta Tambayeshi.
D'an tab'e Fuska yayi "lfy Mami Jirana akeyi ina da Bak'o a part d'ina.
"Tom ka bata magani ne?
"Mhmmm zanturo muku dashi Mami,
Inagama kaman ba ciwontanbane Don naga tayi Amai, daga Haka ya wuce dandama Allah Allah yake ya wuce yanaga kaman Mamin ta d'ago Halin dayake ciki,
Azaune ta samu Dijahn ta jingina bayanta da Gado Daga ita sai towel, dan tana gama aman, tafad'a bayi tayi wanaka sam tamanta da wani Kabir da akabashi jiranta har sai da ta zauna taji yaja dogon tsaki ya tashi ya fita.
Sannu Mamin tamata ganin tadawo Hayyacinta, barin zo khadijah tafad'a, sannan ta koma gun bak'inta,
Afalon tasamesu dukansu sai zabga godiya kakan Aliya takeyi ma lya, da Alamun sunyi magana mai k'arfi sosai Har jikin mota mami ta musu Rakiya.
Afalo tadawo tasamu Khadijah sanye da Riga da sket na atamfa wannan karon Hijabine ajikinta,
Agefenta Mamin ta zauna ta d'an shafi kumatunta,
"Khadijah ki hak'ura da zuwan gidan Uncle d'in kinnan, barin k'ira miki Saudan tazo, kedama bason Hayaniya kikeyiba ba zaman Gidan zaki iyaba dan nasan yanzu bak'insu na nesa sunfara zuwa, gashi ba dad'i kikejiba.
Kwantawa Dijah tayi a ciyanta "Ayyah Mami na warkefa, dama Wlh Juice d'inne ya wuce ta layin Abinci,
Mami tasaki dariya "to yanzu yadawo layinsa kenan?
Ki Hak'ura da fitannan Khadijah, Munyi Waya da Wata mai gyaran Jiki zatazo tafara miki gyaran Jiki kafin lokacin Bukin su Sauda, lansin kifito sodai amatsayinki na wacce ta zab'eki ababbar k'awa, ko bakyaso?
Sam Dijah bata son musu ma Mami shiyasa kawai tace
"Inaso Mami.
"Yauwa yanzu zata iso kufara.
"To barinje wajen wancan tsohuwan, Kafin ta zo.
Wajen la'asar mai gyaran jikin tazo,
Tsawon sati guda anayima Dijah gyaran da ita kam sam batasan ma'ana ko amfaninsaba, Hasalima gani take anyimugun takura mata, fitowanta daga Wanka kenan tana shafa mai taji Sallama nan ta bada izinin ashigo Wurgi tayi da Kwalban man tazo ta Rungume Jamila tana Murna abakin gado tamata masauk'i, tana dariya Jami idon ki kenan? Ta zira Hijabi ajikinta, sannan ta fita samo mata abun motsa baki.
Jerin Akwatuna tayi tozali dashi A falo, kallo tayi tabinsu dashi, sannan ta kai dubanta ga Mutanen falon, Mutum na farko data fara tozali dashi Alhaji ya'une zaune gefensa Abban Habib ne da Uncle, sai Mami da wasu mata biyu da batasansuba, da Alamu sune zasu kai kayan Aure, Dammm taji da wani Furucin da yafito abakin Abban Habib "bayau akasaba yin auren Mata Biyu lokaci d'ayaba kedai matsalan shine Rashin sanar dashi da akayi, Baikamata ayi ma na Miji irin wannan aurenba, da kin sanar dashi, na tabbata ba za'a sami matsala da Kabir ba yarone mai Ladabi, yanzu shi azatonsa matar d'aya ce gaskiya wannan shine Rashin Adalcin da aka masa,
sai dai muyi fatan Allah yasanya Alkhairi.
Cikin b'acin Rai Alhaji ya'u yace "kaidai d'ane inka haifeshi baka isa dashiba, amma inba hakaba ai da duk hakan bata kasanceba, saidai inason inrok'eki Fatima kibarni da Nafisa ni nasan ta hanyan dazanbi in sanar da ita wannan magana don nasan son da takeyima Kabir in tasamu wannan labari zuciyanta zai iya bugawa itakenan min k'waya d'aya Aduniya in haka ta faru ni aka cuta, nabarku lfy daga haka ya tashi ya fice.
Jikinta sai b'ari yakeyi ta k'arasa ta duk'a ta gaishesu Sannan ta d'auki abun da ta fito d'auka tabar wajen,
"Jamila nakai sati lna niman wayanki bayashiga, Dijah ta fad'a cikin sanyi lokacin tana ajiye Drinks da takawo mata.
"kedai bari wlh wayan ce tasamu Matsala, ke tare da mutuminkifa mukazo amma ya koma yadai matsane sai da yaga gidanku wai kina ta masa wasa da hankali,
Murmushin k'arfin Hali Dijah tayi jikinta ba k'arfi sam batasan meyake damuntaba yanzu yanzunnan tajita haka.
"Kahdijah wai wannan duk Hutun da akayine haka kinganki kuwa? Jamila ta fad'a tana k'aremata kallo, "Jikinki yayi wani fresh kaman ka tab'a jini ya fito, sai wani shining kikeyi ga wani k'amshi dake fita ajikinki na daban.
"Kai Jami kema baki ga yanda kika canzaba wlh kinyi k'iba da yawa, kinyi Haske, tafad'a atak'aice, dan batason zancen yaja dayawa, saboda yanayin ya da take jinta.
Jamila ta k'yalk'ayley da Dariya "kai Khadijah baki da dama zauna inmiki kwalliya akan Hanya nake.
Bamusu Dijah ta zauna Jamila ta Resa mata kwalliya, tsayawa kallon Fuskanta tayi a mirrow sai kuma ta kwashe da dariya,
"Kinsan Allah Jami da Aljana nayi kama nikam bazan iya fitaba,
"ke kinganki kuwa yanda kikayi kyau wlh ko amarya sai dai haka nikam zan tafi zo ki rakani.
Riga da wando na pakistan tasaka Yellow bak'aramin karb'anta kayan sukayiba gyalansa tayafa tasaka takalminta flat shima Yellow suka fito,
Wannan karon kam a falo tasami Mami ita kad'anta kuma bataga Akwatinanba, Jamila tayi ma Mami sallama, Har sunjuya Mami tace "Khadijah yaki d'aki ta wuce tafito mata da Ledan kayan Cosmetics, suka fita.
Daga d'ancan Nesa daf da gate ta hango Kb da Nafisa shi yana zaune akan Farin Kujeran Roba, Sanye yake da Blue Jeans da t shirt Yellow, da Hula fesing cap shima Yellow, Nafisa kuma tana tsaye daf dashi kaman zata fad'i akansa, Shadda ne ajikinta Ruwan K'asa da yasha aiki daga sama har k'asa, tasha lalle da kaganta kasan tana cikin farin ciki ba kad'anba,
*Tofaha jama'a wai Kabir mata nawa zai Aurane?* π€
Ku biyoni yanzu aka fara
Ummu Fatimaπ
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*UMMU FATIMA CE*π³π¬
π *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......π
*Godiya da fatan Alkahiri gareku mai tarin yawa bansan yanda zan kwatantamuku irin farin ciki da dad'in danajiba na irin Addu'oinku Ga Fatima da Ummanta da masumin a groups da masumin ta prvt duk nagani saidai inbiku da d'ad'd'aya ne ina Amsawa naga barin muku adunk'ule Nagode matik'a 'yan mata Allah yabaku maza nagari wanda zakuyi zaman lfy da soyyaya ma dawwami yabaku 'ya'ya masu Albarka* π€²π»
*Matan Aure Allah yasa Albarka acikin zamantakewanku da mazajenku yadawwamar dazaman lfy acikinku ya Albarkaci yaranmu ya k'aromana da masu Albarka*
Group din Maman Hauwa bansan yanda zangwada muku nima lnayinkuba Gaskiya irin yanda kuke gwadamin. saidai zangayyaceku Ranan Dinnern Kb da Nafisa da Aliya πππ
*page* 3β£0β£
Ta zuba masa ldo kaman ta cinyenshi, hanunsa Rik'e da waya yana danne2 jifa2 kuma yana d'agowa ya kalleta, ya mai da Kansa.
Kallo d'aya Dijah ta musu ta sunkuyar da kanta suna cigaba da Hiransu da Jamila, saida suka matso kusa kafin Nafisa ta d'ago sukayi ldo Biyu Nan danan Fuskan Nafisa yakoma kaman anwatsa mata Gaushi,
Tarasa meyasa tayi mugun tsanan Dijah ko Kallonta batasonyin Musamman yau dataganta cikin Kwalliya jitayi kaman taje ta shak'eta, wani lrin Mugun Kallo take binta dashi ba abundama yafi bata Haushi kaman irin yanda taga tasake agidan kaman gidan Ubanta, har Mutane take taramusu agida dan tsaban samun waje,
Shirun da Kb yaji tayine yasashi d'agowa ya kalleta ahankali yamaida kallonsa inda take Kallon,
Dijah kuwa da taga duk wa ita suka zuba ldo sai dai kowa da lrin yanda yake mata nasa kallon,
Nanda nan kuma taji Dijahn nata sun motsa, ta zunguri Jamila ta nuna mata su sai kuma suka kwashe da dariya, Sanin Halin Dijah da Kb yayine yasa shi janye Idonsa daga Kallonta, yaci gaba